Showing 3001 words to 6000 words out of 132173 words
Chapter 2 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf
yake matukar birgeta hade da kyawawan halayensa
kwankwasa kofa taji da sauri ta tashi daga kishingidar da tayi hade da bada umarnin a shigo ya
shigo hannunsa daya a aljihu daya akansa yana shafawa fuskarshi dauke Da murmushi ya
janyo stool ya xauna jenniper ta bishi da kallon mmk ya kalleta kina mmk ko ? Kai ta girgixa
masa kada kiyi karya dan karya bata dace da kyakykyawar surarki ba mamakin ta ya karo duk
da bayau aka saba ce mata me Kyau ba ya kalli gefen dakinta banyi karya ba tabbas mmk kike
na gani na awajanki xakiyi tunanin me naxoyi me yakawoni ? Ya kalleta kina son jin amsar
mmkin da kikeyi ko ? Kada ki damu danni mutun ne me damuwa da damuwar wasu musamman
wayanda suke kusa dani wannan ta wadatar ki cire duk wani tunani da xai kawo miki xiyara
naga kamar kina cikin damuwa ? Ta girgixa kai tana satar kallon gefan fuskarshi kinyi lunch ?
Nayi ta bashi amsa kai tsaye anya kuwa ya fada yana kallon lips dinta fuskarshi dauke da
murmushi wannan lips din beyi kama da Wanda yaci abinci ba tayi dariya tana mmkin xakewa
irin tashi to shikenan nasan kyawawa basa karya sunana mahboob kamar yanda Momy ta fada
kikaji kuma nima danta ne haisam shi yake bina ina so idan ba damuwa mu zama frnds ta xaro
ido tana mishi wani kallo a tsorace ko ban miki bane ? Ya fada yana kallanta ranshi a dan bace
ta girgixa kai tana ajiyar xuciya a a ta fada muryarta na sarkewa kin amince ?,ya kuma
tambayrta kai ta daga masa yayi murmushi hade da mikewa daga kan stool din ngd kawata
jenniper anjima zanxo muyi hira yanxu xanje na kwanta sbd na gaji ngd yaya mahboob mention
not ya fada daidai lokacin daya bude kofar dakin ya fita tare da jifan ta da wani shu'umin kallo ta
sauke numfashi tana mmkin hirarsu da shi yana magana atsare kamar wani marubucin novel
yanayin maganarshi tmkr ta cikakkun mayaudara anya kuwa ? Koma mayaudarine tabbas yana
da kirki ya kuma son darajar mutane duk da kasancewar ta Krista ya amince da alaka da ita me
karfi mamanta tasha fada mata ana abota da mutane nagari mace ko namiji hade dasa
kyakykyawan niyya sukam dabi'arsa kawance babban abune Wanda yake da matukar
muhimmanci kafi karfina mahboob ta fada cikin kwarin gwiwa hade da Sa kanta akan filow dinta
4:00pm ta shiga kitchen dan ta Dora abincin dare telephone din kitchen tai kara ta karasa kusa
da ita ta amsa muryar yaya khaleel taji ki kawomin tee da sauri ta amsa da toh ya ajjiye wayar
ta Dora masa tee din cikin mintuna kalilan ta gama ta nufi hanyar dakin nasa waya ta taddashi
yanayi xuciyarta taji takusa bugawa dan ta fahimci da mace yake wayar oh sorry ki dinga
fahimtar abu kafin ki yanke hukunci meyasa kikeson dagawa kanki hnkl ? Na fada miki babu
wani abu uxiri xaki dinga min ayyuka sun min yawa plx plx plx share hawayanki zanxo kd kada
kidamu kinsan bana son kuka ko ?? Ki daina waiwayo yayi yana kallonta da hnklinta Sam baya
jikinta mmk ta bashi yanda yaga jikinta a matukar sanyaye murmushi yayi hade da cije lips
dinshi na kasa jenniper ya dai shiru sai da ya bugi center table ta waiwayo da sauri lfy ya fada
yana mata wani irin kallo da sauri tace lfy ta juyo xatabar dakin jenniper ya kira sunanta da
muryarsa me dadin ji har cikin ranta taji dadin futar sunan ta daga bakinsa kina da wata
damuwa ne yaxuba mata kyawawan manyan idanunsa fuskarsa adake bayabo ba fallasa ta
kalleshi kwarjinin shi yasa ta saurin sunkuyar da kai tuni jikinta ya fara rawa babu komai yaya
khaleel OK ya fada ya juya mata baya yana danne dannen wayarsa ta kwabe fuska tana kallon
kyakykyawan bayansa ta juya ta fita tarasa me yasa takejin tsoron yaya khaleel meyasa yake
mata kwarjini meyasa take matukar jin kunyarsa ?? Dawa yake waya ?? Mecece dinshi ?
Kirjinta yai mata xafi ranta ya baci idonta ya cicciko da hawaye meyasa take jin haushi haka ??
Meya ke shirin faruwa da ita baxai yiyu ba ta fada afili mahboob ta gani agabanta kamar an
jefoshi ya akayi ne my frnd ta kalleshi hade da saurin yin yake no no babu komai nafada miki
kyawawa basa karya yaken takuma yi tana son barin wajan dan tana bukatar hutawa tayi
tunanin magance matsalar da takeson xama damuwarta oh yanxuma tunanin kike yi ? Da sauri
ta kalleshi batason lokacin da ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka a a abokina ina son xuwa
na karasa girkin Dana Dora ya kalleta yana kanne ido daya muje in taya kawata girki da sauri ta
girgixa kai a a abokina wannan kyakykyawan jikin naka da yasaba da Hutu bana son ya kusanci
wahala ta girki ya rike haba ina bazan bari kawata tayi girki ita kadai ba kada muyi jayayya oya
kibiyo ni yayi gaba tabi bayanshi xuciyarta a cunkushe Sam bataso ya takura mata lokacin da
takeson tunanin mafitar bakon al'amarin da yaxo mata binshi tayi xungui xungui har cikin
kitchen din
BY UMMEEY
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍ JENNIFER✍✍✍
7&8
Binshi tayi abaya ranta bai soba ya shige kitchen din ya waiwayo ya kalleta dame zan fara ya
tmby ta ta kada kai da abinda ka iya tamayar masa da amsa asanyaye dan bata San mexata
sashi ba ya wuce ciki yana bude buden food flas oh jennifer ya fada yana yarfe hannu kin gama
kenan kai ta girgixama Sa da saura dan yanxu zan dorawa Momy kunun gyada ya khaleel kuma
zan mishi spinach nd egg stew ya kalleta yana murmushi ban iya ba dama wayace ka iya ta
fada tana Dora tukunya akan gass hk ya koma gefe suna hira tana aikinta amsa masa hirar
kawai take xuciyarta babu dadi a hk har tagama gaf da sallar mgrub ya kalli agogon hannunsa
me Kyau da tsada lokacin sallah yayi dam!! .. taji kirjinta ya buga xan tafi amma ki tabbata yau
dake xamuyi dinner ta kalleshi ya Matso kusa da ita kada kiyi tare xamuyi da family kai ta daga
masa tana jinjina xakewa irin tasa ya wuce tai ajiyar xuciya ta shiga tunanin da takeson yi tun
daxu yahanata me yake shirin faruwa da itane ?? Ya akayi takejin haushin wayar daya khaleel
yayi ?? Tasa hannunta a kai hade da fadin oh! Meyasa zanjefa kaina cikin halin kaka nikayi ??
Wacce take kokarin Sa kanta yanxu ma takasa sbd tsoro da kuma firgicin halin daxata tsinci
kanta jikinta a sanyaye ta debo abincin ta Jere a dining ta wuce daki tai wanka ta canza kaya ta
kurawa wayarta kallo tana kallon number yaya khaleel kwankwasa kofa akayi ya shigo kamshin
turarensa me sanyi tashaka ta kalli fuskarsa Wanda shima idonshi akanta Jennifer me ya
sameki ? Da sauri ta saki fuska bakomai yaya mahboob OK ki taso muje ina?? ta fada wajan
cin abinci ya fada hade da juya wa yana kokarin bude kofa itakam bata tabajin in da akai
hakaba tayaya xata je taci abinci da iyayen gidanta ?? Bin bayashi tayi da kallo babu inda xata
ta kwasowa kanta takaici da bacin rai tai kwanciyarta karar wayarta taji tana dubawa sunan
Momy ta gani jikinta na rawa ta daga Jennifer jiranki mukeyi da mmk ta amsa da ina xuwa
momy mikewa tayi da sauri ta nufi dining area ganinsu tayi xaune a falon dukansu babu yaya
haisam ko yana ina ?? Oho mishi bakaramin dadi tajiba narashin ganinsa a kunyace ta karaso
Momy gani ta dago kai momyn tana kallonta mahboob yace adinka cin abinci dake kuma ya
fada miki amma mukaji ki shiru da mmk ta kalli mahboob takasa cewa komai dadi da farin ciki
sosai ya kamata Momy ki kyaleta nayi fushi da ita mahboob yafada yana kallon agogon
hannunsa 20 mints muna jiranta Momy tayi murmushi mahboob aboki yana fushi da kawarshi
ne ? Momy fushin kadan ne ba dayawa ba yafada yana hararar Jennifer da mmk ya hana ta
cewa uffan Rubayya ta kallesu da mmk itama ya mahboob wace kawarka ? To yarsa ido
yacewa rubayyan Jennifer ce new frnd dina rubayyan tayi dariya ina tayaka murna kayi dacen
kawa ina tayaki murna bakiyi dacen abokiba sukayi dariya mahboob ya harari ruby cikin daure
fuska da kina kusa dani sai na mauje miki baki ta shagwabe fuska Momy ba gaskiya na fada ba
? Hajjo da tana gefe batayi mgn ba tasa baki gsky kika fada Rubayya inba Jennifer dinba
waxaiyi kawance da mahboob Rubayya tasa hannu ta rufe baki tana dariya kasa kasa ba
ruwana hajjo dama bakinku daya mahboob ya fada yana kallon hajjo da tafara xuba abinci kai
kasani hajjo ta bashi amsa da sauri Jennifer ta amsa cokalin hajjo ta xuba mata abincin sannan
ta xubawa kowa nashi tunda taxo wajan zahra bata kalle inda take ba shikuwa ya khaleel
hnklinshi nakan waya yana danne danne babu wanda yasaran tofa nashi zancen sbd sanin hali
ta xauna tana cin abincin suna taba hira jefi jefi idon mahboob akanta kunya duk ta kamata
takasa sakewa xuciyarta tai mata dadi babu abinda bata sakawa axuciyarta ba itakadai tasan
dalilin jin dadinta wayar zahara tai kara ta daga murmushi tab a fuskarta wlkslm Anty Jidda tayi
wata irin dariya irin ta shakiyanci muna tare dashi ta kalli ya khaleel dayake juya cokali muna
dinner nefa OK zan fada mishi ta ajjiye wayar ya khaleel Anty jiddanka tace ta kiraka bk daga
waya ba ya kalleta sai kuma yayi murmushi nagani ina sone sai nagama cin abinci zan kirata
kin San hirarmu bata karewa gaban Jennifer ya fadi dama yana mgn irin hk ? Kowa yayi mmkin
mgnr shi mahboob yace wow ! Khaleel yakamata fa kayi mgn me Kyau akan aurenka da Jidda
yayi murmushi yana kallon mahboob tunanin dana keyi kenan Dana gma shiryawa zan yi kokari
ya mike yana kallon wayarsa da sauri Jennifer ta bishi da kallo xuciyarta na mata zafi karaf ya
kalleta hade da jifanta da wani kallo Wanda takasa fassarasa kamar na tuhuma ko kuma na
ramuwa ya wuce suka bishi da kallon mmk hajjo ta tabe baki miskili kafi mahaukaci ban haushi
Wanda yaron kamar aljani hk yake babu me shiga maganar sai in kai kakuma yinta zahra tace
hajjo kin sawa ya khaleel ido fa baki na Sa masa ba idoba ja,ira kawai Rubayya tace kwantar da
hnklinki hajjo menene na tada jijiyar wuya ko kishi kike ? Zan saba muku fa sukayi dariya
dukansu banda Momy da hnklinta ya rabu sbd jin abinda khaleel ya fada mikewa Jennifer tayi
cikin wani yanayi zan je na kwanta sai da safe OK Jennifer suka amsa mata dukansu banda
zahra da tabita da harara yake Jennifer tayi cikin kwarin gwiwa baxaiyiyu kasami soyayyar kowa
ba dolene kasamu masoya da kuma makiya koda bakai musu komai ba ta bude tadakinta ta
xauna gefen gado hade da cire dankwalinta tana kallon agogo 8:25 ta gani kirr wayarta tayi kara
ya khaleel taga sunan Sa kan screen din wayar gaban ta na faduwa ta daga asanyaye taji
muryarsa coffee ! Ya kashe ajiya xuciyarta ta mike da sauri ta nufi kitchen ta hada masa ta nufi
dakinsa tayi sallama waya yakeyi yana kyalkyalar dariya...... babyna kinsan abinda nakeso ya
kuma dariya hade da fadin kada kiyi mmk komai yana canxawa zanzo kd kodan na saki farinciki
nasan kinyi missing dina sosai nima nayi dan jiya bacci dake nayi araina.......ya dago kai yna
kallon Jennifer da take a tsaye da cup din coffee tayi wuri wuri tana ajiyar numfashi murmushi
yayi hade da cije lip dinshi na kasa ya dai Jennifer ?? Ya fada yana daure fuska da sauri ta
sunkuyar da kai babu komai ta ajjiye cup din ta juya kinga " yafada ta tsaya hade da waiwayowa
idonshi akan waya yana danne danne kina da damuwane yafada cikin ko in kula girgixa kai tayi
a a ta wuce ta mmjin tambayar nan tashi
BY UMMEEY
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍
9&10
Daki ta shiga hnklinta atashe akasalance ta xauna akan gado tana mai da numfashi xuciyar ta
arikice wannan irin yanayine wannan ?? Ranta tajishi abace hade da damuwa sosai muryar ya
mahboob taji yana sallama ta amsa ya shigo idonshi akanta ta kalleshi tana kallon agogo 9:40
ya kalli agogon yana hararta nasani dare yayi sallama xamuyi ya janyo stool ya xauna yana
fuskantarta kawata ta amsa da ya mahboob kin taba soyayya ? Da sauri ta kalleshi a a ta bashi
amsa tana mmkin tmbyr meyasa ? Ya kuma tmbyr ta ta sunkuyar da kanta tana jujjuya xoben
hannunta sbd ban shirya ba dariya yayi me sauti kadan Jennifer soyayya ba,a shirya mata tabe
baki tayi dan tafara gjy da tmbyr kurillarsa da Kyau ya fada yana kallon lip din da ta tabe xan
bige wannan karamin lip din daake tabemin shi dariya ya ba ta kalleshi bafa ....... Ya daga mata
hannu bacci kikeji ko ? To karma ki fara hira xamuyi ta xaro ido tana kwabe fuska nagaji ya
mahboob ya katseta da fadin ki fadamin gsky kin taba soyayya ?? Zanyi ta nan gaba amma
banta ba yinta ba tabashi amsa ya mike yana dariya naji amma......toh kyakykyawa kamarki da
wuya ya bude kofa sai da safe nima baccin nakeji ya fice ta bi bayanshi da kallo hade da
murguda baki ko ina ruwanshi da soyayyar ta ? Wata keso ? Sam bata Sani ba ! Batasan
Wanda takeso ba tayaya xatayi soyayya yanxu bayan akwai muhimman abubuwan da sai ta
gama cimmusu baxata Sa kanta a soyayyar kowa ba har sai babban burinta ya cika hnklinta ya
kwanta mafarkinta ya xama gsk soyayya ta yan gata ce ba irinta wacce Nan gaba kadan
batasan ya xata kasance mata ba
7:30 ta shiga kitchen ta shirya break fast ta Jere su a dining agajiye ta shiga dakinta tayi wanka
kafin mutanen gidan su shirya ta kwanta bacci ya kwasheta sbd jiya batayi baccin kirki ba
mahboob ya shigo dakin dan kiranta break fast ya ganta tana bacci ya kalli beautiful face dinta
cikin tausaya wa yasa hannu ya shafa fuskar ya dade yana kallonta yana tunanin wani abu
aransa ya fice daga dakin
12:23 ta farka agigice tana kallon agogo da sauri idonta ya sauka kan food flast din da cup da
flast din shayi komai da komai na break fast dinta a ajjiye a sauke numfashi tana tunanin waye
da wannan aikin ? Yaune rana ta afarko da ta taba wannan shirmen dolenta tacire duk abinda
ke kokarin sata ka kasala da rashin bacci toilet tashiga ta shirya ta fito tayi break fast din
agaggauce dan taje ta Dora lunch kafin time ya kure da sauri ta gama ta kwashe kayan ta nufi
kitchen ta Dora abincin rana
Yau takama Saturday weekend da yamma ta na kitchen wajan shirya abincin dare ta hango su
Rubayya da zahra wajan Malam Mahmud da yake xuwa duk weekend yana koya musu karatun
kur,ani hnklinta na kansu sauri takeyi tagama taje wajan da tasaba buya taji karatun nasu dan
yana Sa ta nutsuwa da shiga wani yanayi Wanda itaka dai tasan yanayin bayan ta gama ta
sanda ta nufi bayan wajan tanajin karatukansu radau tana kuma lekensu jikinta asanyaye
damka taji bata wasa ba andamki gashin kanta cikin mugunta muryar Yaya haisam taji
munafuka ubanki kike sauraro ?? Wato munafurcine ya kawoki gidan nan ko ?? Koda yake
kinajin axabar da Allah ya tanadarwa mushrikai irinku ?? Ke wacce iriyar jahila ce dakikiya
arniya kaxamai yan wuta ta fashe da kuka me ciwo bayanxu xakiyi kuka ba har sai lokacin da
Allah ya kamaki akan budulce masa da kikayi ya halicceki kiki bauta masa ki bautawa wani
bayanshi ya hankadata ta bige da bango ta fadi wanwar akasa kalleni nan ya kwatsa mata
tsawa da kyar ta kalli idonsa da ya kankantar dashi sbd masifa natsaneku dakuda addininku ya
wullo mata key din dakinshi ki gyaramin daki kifito da kayan ciki masu datti ki wanke kaxama
datti kaxanta yayi tsaki ya wuce da kyar ta mike hannunta tafe da wajan da ta bige sbd xogin
daya ke mata hango ya khaleel tayi xaune akan kujera hannunshi rike da waya yana danne
danne akan idonshi komai ya faru hawaye ne masu xafi da daci suke subo mata hk ta mike
hannunta rike da kanta ta wuce ta gabanshi bata samu kallon arxiki bare na tausayawa ta shiga
dakin ya haisam da yai kaca kaca ta hau gyara taci wuya sbd kayan sawarsa barabaje atsakar
dakin ta gyara tass ta wanke toilet ta fidda masu datti ta fito daga dakin tai wajan injin wanki
hnklinta atashe ta gabanshi ta wuce yana waya hawaye ya sauko mata duk jarabar ka baxaka
dau rayuwa ta ba tana wankin tanajin takaici sosai na cin mutuncin ya haisam
By UMMEEY
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍
11&12
Ta gama wankin da sauri ta shanya ta koma daki xuciyarta tunkushe tana kuma mmkin bakin
hali irin na haisam tana nan xaune aka kira sallar magrub da sauri ta tashi daga kwanciyar da
tayi tana sauraron kiran sallar xuciyarta na kwadai ta mata abubuwa da dama karar wayarta taji
jikinta asanyaye ta duba Maman David xuciyarta tayi sanyi kadan ta daga oyoyo mamana
oyoyo Jennifer mama ta amsa kina lfy dai ko ? Lfy nake mama ya papana da su David suna