Showing 27001 words to 30000 words out of 99609 words

Chapter 10 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

maqalewa tana matsar kwallar gulma da kyar ta iya furta mom dama
baban jidda ne ya ce na kawo mai ruwa ina shiga dakin na ganshi ya fadi a kewaye kuma ya
kasa tashi tana ida zancan ta fashe da kukan munafurci mom tashi tsaye tayi cikin rudani muje
bedroom din nashi naga ko lafiyar baby, mom na gaba fatuha na baya tana aika gwalo suka
shige part din direct bedroom din sadiq ta shige yanan zaune inda fatuha ta barshi yayi yayi ya
tashi amma ya kasa mom ce ta qaraso tare da kiran sunan shi cikin damuwa ya juyo yana
kallan fatuha na bayan mom tana matsar kwalla da sun hada ido da sadiq ta aika mai gwallo
shikuma ya aika mata harara, sannu baby kaji bari mu taimaka ma ka tashi, no mom ba ku
iyawa a miqomin phone din tana saman stool na kira *ola* da *Sunday* cikin sauri mom ta miqa
mai wayar fatuha na gefe rabe zuciyar ta fes.


Bugu daya biyu *ola* ya daga kiran sadiq, sadiq ya sheda mashi yana neman shi, shi da
*Sunday* cikin Sauri suka qaraso bedroom din, ganin su mom tsaitsaye yasa jikin su *ola* yin
sanyi hango sadiq su kayi zaune a toilet yayi zaman yan'bori a hankali *ola* ya qaraso tare da
gaida mom cikin hausar su wadda bata fita amsa mai tayi sadiq a hankali ya ce *ola* taimaka
min na tashi kai da *sunday* OK boss Sunday d ola suka taimaka ma sadiq ya miqe suka
daurashi saman bed mom sai sannu take mai itama fatuha sannu tamai wani irin mugun kallo
ya mata, ya kauda kai mom ce tace baka ji fatuha na ma sannu bane lumshe ido yayi tare da
ware su yace ban ji ba ya qara maida idanuwan shi ya rufe, wayar shi mom ta Curo ta kira
doctor yakub ba ayi minti 39ba sai ga doctor yakub riqe da briefcase din shi ya shigo, fatuha ta
mai isowa har bedroom din sadiq gaida mom yayi sannan ya shiga duba sadiq tare da tataba
inda ya bige sannan yayi yan rubuce rubuce, gyaran murya yayi ya ce Alhamdulillah buguwa
ce amma be goce ba kuma be kare ba abin ya zo da sauki mom murmushi tayi tare da
hamdala, sannan doctor ya bashi magani da ze shafa da kuma na ciwan jiki sannan yayi ma su
mom sallama ya tafi, mom da fatuha kuma suka fita cikin cool voice nashi sadiq yace da ola ya
taimaka ya kai shi bathroom ya watsa ruwa amma ya fara goge man da ke zube a toilet sai da
ola ya wanke toilet din tas sannan ya taimakawa sadiq ya shiga toilet, ola na bakin kofa yana
jiran sadiq yana gama wanka ya kira ola ya taimakamai ya fito ko da ya fito ola ya fito mai da
jalabiya milk bayan ya gama shafe jikin shi da mai sannan ola ya taimakamai ya shafa mai
magani sannan yasa jalabiya ya koma saman bed ya lumshe ido ,ola ne ya bare maganin da
ruwa ya bashi ya sha yana gama sha ya lumshe ido bacci mai nauyi ya dauke shi, ola ya koma
saman sofa ya zauna Sunday kuma ya kwashe kayan da suka baci da mai ya fita.

Wash Qur'an yau nayi aiki inama a ce fatsima na kusa ta qara bushewa da dariya, ta kalli bed
jidda na kwance tana sharar bacci dariya tayi tace "Allah sarki angal wato(angel) yau na naqasa
baban ki se hakuri angal na san in zafi yayi zafi har sunnan ki sai ya fada ta kara fashewa da
dariya tare da rausayar da kai ,Amma fa gaskiya ban duba mai ba ta ida zancan tana cire
kayanta ta shige toilet tayi wanka daure da towel ta fito lokacin jidda tatashi, murmushi tayi ma
jidda tare da daukarta dan lokaci 4:00pm saura malamin jidda ya kusa zuwa wanka ta mata a
tare suka fito suka shirya sallah su kayi saboda anata kiraye kirayan sallah bayan sun gama
sallah fatuha ta rako jidda har waje lokaci har malam ya zo ji tayi itama tana sha'awar karatun,
cikin gida ta juya tare da Shiga bedroom din mom, mom na zaune saman daduma karasowa
tayi tare da murmushi ta tanbayi mom itama tana so ta fara zuwa malam na qara mata karatu
mom ta ce babu komai washe da baki ta fita ,taje wajan malam itama ba laifi fatuha ta Dan san
sururi da yawa sai karatun nata ba tajiweed shine ka dai ya dan bata karatun ba laifi sunyi
karatu sosai inda fatuha ta natsu tana ta karatu, dan wannan malamin ba karamar malami
bane.


Bayan sun gama karatu misalin karfe 6:00pm suka shigo gida cikin farinciki, mom na zaune
saman three star tana kallo abba na gafenta gaishe su tayi cikin na tsuwa sannan ta shige daki
jidda kuma ta fada jikin abba tana zuba mai surutu kiran sallar magrib ne ya sa abba tashi ya
wuce masallaci ,jidda kuma ta shige bedroom lokacin fatuha ta fito daga toilet daure da tawel
tayi arwalarta à toilettes din, murmushi fatuha tayi tace, "Jidda yi maza kiyi alwala kiyi sallah kiyi
ma baban ki addu'a, be lafiya kinji" waro ido jidda tayi tace Anuty me ya samu daddy tareda
ruga wajen kofa zata fita, janyo ta fatuha tayi tace, yi hakuri mu fara yin sallah sai na kai ki kinji
jidda toh tace mata tana matsar kwalla fatuha kuma na lalashin ta.


Bayan sun gama sallah fatuha ta shirya jidda cikin night dress din ta blue n white wando da
Riga ba qaramin kyau su kayi mata ba ,ta ja hannu ta suka wuce part din sadiq.

Suna Shiga suka samu ola zaune saman sofa, sadiq ma zaune saman bed ,yana shan coffee
da gudu jidda ta fadi jikin shi tana kuka, daddy lalashin ta ya shigayi angel menene yake damun
ki ,bata fuska tayi tace "Daddy ashe baka da lafiya shine baka fada min ba? ta ida zancan tana
matsar kwalla" sorry angel lafiyar daddy qlau, waya fada maki daddy be lafiya? fatuha ta nuna
da ke manne jiki kofa kamar ka ce tak ta arce wani irin kallan tsana ya gefa mata tare da qaqaro
murmushi yayi wa jidda yana kallan fatuha , angel na rasa yadda akayi grandma ta samomaki
new Anuty mahaukaciya ya ida zancan yana kallan fatuha ido cikin ido, kauda kai tayi tare da
turo baki gaba, daddy new Anuty ba mahaukaciya bace ba injiwa ya ce maki ba mahaukaciya
ba ce fatuha ko wani irin tsoki ta ja tare da jan kofar bedroom da karfi ta fita lumshe ido sadiq
yayi yana tunanin irin hukuncin da zaiyi ma fatuha in ya tashi.


*Taku har kullun mai qaunar ku Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*

‍♂

*writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★

http//,mobile. Facebook.
Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167refid-52&red
opare-speed_dial_yn_=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com


*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com


37_38


Fatuha bedroom ta shigo tare da yin sallah isha'i saboda tana da arwalata, bayan ta gama
sallah ta rage kayan jikin ta yar rigar bacci tasa wadda yanzu ta zamar mata jiki, in batasa ba ko
bacci bata iyawa kanta ta qarewa kallo ta cikin mirror ita kanta mamaki kanta take saboda ta
wani qara haske da kyau sannan komai na jikin ta ya ciciko rufe idanuwan tayi tare da ware su,
ta sauke su kan qirjinta Wanda yanzu ya fara cikowa sosai, murmushi tayi tare da jin kunya ta
bar gaban dress mirror din ta fada gado tare da yin addu'a lumshe idanuwan tayi sadiq ne ya
fadu mata a rai tayi sauri ware idanuwan ta tare da sakin dariya saboda duk lokaci da ta tuna da
zaman yan borin da sadiq yayi sai ta dara a haka har bacci ya kwashe ta.



Duk juyi dayayi sai ya zabga tsaki saboda bacin rai ola ne ya juyo ya ce boss are u ok ,
lumshe ido yayi yace "Yess" ok good night, boss if u need something talk to me please, ok tare
da juyawa ya gyara kwaciyar shi a hankali ya shafa gashin jidda sannan ya lumshe ido, daya
lumshe ido fatuha yake gani tana mai dariyar qeta wata irin iska ya furzar mai zafi daga bakin
shi ba abinda zai hana shi yima fatuha horo mai tsanani Wanda ko wani aka ce tayima irin cin
kasin da ta mai ba zatayi marmarin maimaitawa ba, tsaki ya kuma ja saboda takaici a haka har
baccin barawo ya dauke shi.

*Asuba ta gari..*

Tunda asuba fatuha ta tashi saboda tasan in yau bata tashi da wuri ba Allah ka dai ya san
jarabar da sadiq ze mata ,dan tsaki ta ja can kuma tayi murmushi tace, ko ba komai ina ganin
mai kyau Qur'an naji dadi, sannan ta shige toilet tayi wanka tare da yin brush da dauro alwala
tayi sallah sannan tasa uniform komawa tayi ta zauna saman bed tana kallan agogo karfe shida
take so ta shiga part din sadiq.


Ba laifi daya tashi sallah asuba kafar ta saki tunda har ya taka bada taimakwan ola ba, toilet ya
shiga yana shiga abinda ya faru jiya ya fara dawo mai kamar yanzu, murmushi yayi yace fatuha
baki ji sannan ya qara jan tsoki ya dauro alwala tare da yin wanka ya fito ko da ya fito jalabiya
white yasa ya tada sallah yana gamawa ya koma ya kwanta saboda har yanzu jikin nashi yana
jin shi wani irin.

Bude handle din kofa tayi ta fito direct part din sadiq ta wuce kai tsaye, bedroom ta shige kallo
daya tayi ma daki hango ola tayi kwance yana ta share bacci har da munshari saboda dadi,
dariya ta so ta kubuce mata ta guntse dariyar kallan bed tayi sadiq kwace rungume da jidda
murmushi tayi a hankali ta qarasa tare da leka fuskar sadiq ta ga dai bacci yake cikin dubara ta
shiga janye jidda daga jikin shi, hannu ta ya kama a tunanin shi jidda ce zaro ido waje fatuha
tayi tare da fara matsar kwalla a tunanin ta tashi yayi jin beyi magana bane ya sata lumshe ido a
hankali ta zare hannu ta ta dau jidda suka fita, direct bathroom ta dire jidda ta fara yi mata
wanka , washe da baki jidda tace Anuty good morning , tap ke kika san wannan dariya jidda tayi
ta ce inakwana fa nake nufi Anuty aiyo aini ban sani ba, a ina ake koya maki wannan abun wai
washe baki jidda tayi tace "A school "aiyo wai makarantar da zaki yanzu daga mata kai jidda
tayi Alamar eh, murmushi fatuha tayi tare da daukar jidda suka fito bedroom ta dire ta saman
bed tare da janyo lotion tana shafa mata, kai Amma gaskiya yarannan nada dadi jidda zaki
rinqa koya min ko murmushi Jidda tayi tace Anuty kije daddy ya fara koya maki nima ai shi ya
fara koya min ta ida zancan tana washe hakura, fatuha zaro ido tayi tace tap lalai yarin ya har
yanzu baki san bakin halin ubaki ba Qur'an wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta, washe
baki fatuha tayi tace ah ni nafi san ki kowa yamin kinji kinga daddy aiki yake zuwa ko, daga kai
jidda tayi tare da cewa toh Anuty zan koya maki murmushi fatuha tayi tare da zurawa jidda
uniform suka fito dining area lokacin su baba jinmai sun gama jera komai bude kololin ta fara
marfesun kaji ne da soyanyan chips da egg da tea, murmushi fatuha tayi dan tunda ta zo birni
ba abinda keyi mata dadi kamar chips shiyasa duk sanda akayi sakin tunbi take taci sosai
zuba ma jidda tayi a plate tare da jamata kujera ta zauna ,zata fara feeding nata kenan sai ga
su mom sun iso , gaishe su tayi cikin ladabi suka amsa plate ta janyo ta fara saving nasu mom
sai murmushi take ita dai fatuha ta mata ko Dan abin dariyar ta ta cikin saving nasu sai ga sadiq
ya qaraso dining yana tafiya a hankali yana dingishi ,a hankali fatuha ta kalli qafar wata irin
dariya ce ta zo mata saboda yadda yake harba kafar kamar tsangal gumtse dariyar tayi ta
cigaba da abinda take shiko sai aika mata mugun kallo yake , cikin na tsuwa ya qaraso wajan

mom tare da yi mata pack a goshi ita da abba, abba murmushi yayi tare da shafa sumar shi,
baby ya jiki shagwabe fuska yayi yace abba da sauki ,good amma dai gaskiya yau baza kaje
aiki ba ko dan bata fuska yayi ya ce zani abba, gaskiya baby bazaka office yau ba ka bari zuwa
gobe ka warware sosai, abba,shhh kawai ka hakura kaji ya ida zancan yana shafa gefan fuskar
sadiq fatuha ko Sakin baki tayi da hanci, tace "Ohni sangami duk wani shaqiyanci ya iya, yo in
banda iskanci qatoto da shi sai zuba shagwaba yake sai ka ce Jidda kai kwarankwatsi mai kyau
dan bariki ne "duk wannan maganar tana yinta ne a zuciya kallan da sadiq ya wurga mata ne
yasa ta dawo hankalin ta Jidda ya janyo jikin shi yau daddy ne zeyi feeding angel so bana
buqatar ganin ki a nan tare da warce spoon din hannu fatuha, mom ce ta bala mai harara bata
fuska yayi kamar qaramin yaro ya cigaba da feeding din jidda tana mai surutu, fatuha ko qoqari
tashi tayi mom tace,"Ah fatuha aike sauki kika samu zauna ki ci abincin ki kan lokaci" murmushi
tayi tare da kada kai ta zauna ta zuba dai dai cin ta tasa hannu ta fara cin hankalin ta kwance
tana ci tana lumshe ido saboda tana san chips sadiq bala mata harara ya ke tayi wata loma da
tayi sai da abin ya kusa bashi dariya da haushi duk suka hade mai ita ko ko a jikin ta su mom
ma har karsu suke.

Bayan angama breakfast har bakin mota sadiq ya raka jidda, fatuha na riqe da lunch box din
jidda sai da ta tafi sannan suka juyo zasu koma gida, da gudu fatuha ta wuce sadiq sai da taje
bakin kofa sannan ta juyo ta mai gwalo tare da kwakwayar yadda yake tafiya ta fashe da dariya
ta shige da gudu cije lips din shi yayi tare da tura hannu shi cikin sumar sa, oh Allah ka bani
inkwan cima yarin yar nan sannan shima ya qarasa parlour ko da ya shigo ba kowa sai baba
jinmai da ke kwashe kayan breakfast, gaishe ta yayi ta amsa washe da baki, part din shi ya
wuce ya murda handle din kofar ya ji rufe mamaki ne ya rufe shi fatuha da ke jingine jikin kofar
tace, me kyau kwarankwatsi ban budema kofar nan sai na gama aiki na Dan nasan halin ka kai
mugune wallahi, ka na shigowa zaka bigeni sadiq da ke wajan kofa yayi sororo yana mamakin
raini da fatuha ta mai cige lips yayi tare da barin gurin saboda ya san idan ya cigaba da
tsayawa har kashe ta sai yayi dan bacin rai ,fatuha jin ya tafi yasa ta cigaba da aikin ta tanayi
tana yan'wake wakyan ta har ta gama tuni daki yayi kyau sosai sannan tabi part din da turaran
wuta tuni part din ya dau kamshi da kyau sannan ta qara gudun AC dakin ita kanta sai da taji
kamar tayi bacci dan Kyan da part din ya mata.


A hankali taje bakin kofa ta murda handle ta leqa taga ba kowa, sannan ta fito da sauri ta
wuce sadiq da ke kwance saman three star idanuwan shi lumshe kamar me bacci yana kallan
fatuha ta ruga daki da gudu ta kule, tsoki ya ja tare da tashi duk kiyi ki gaba zan kamaki ne tare
da wucewa part nashi dan bacci yake ji ko da ya shiga part din shi da kanshi sai da yayaba
kyan da part din yayi, ga kamshi se tashi yake da sanyi irin yadda yake so lumshe ido yayi ya ja
jiki ya hau bed ya kwanta.

Tana shiga bedroom kayan jikin ta ta rage ta shiga toilet, tayi wanka sosai dan yanzu ba
qaramin jin dadi take ba in tana wanka amma da a kauye sai anyi da gaske ,yanzu ko fatuha
ansan muhinmancin wanka, daure da towel ta fito ta goge jikin ta tare da shafe jikin da lotion
mai kamshi da feshe jikin ta da turare yar huda da murza duk ba wata kwalliya tayi ba masha

Allah fatuha tayi kyau, uniform din ta ta zura sannan tataro gashin ta Wanda ya cure gudaya
tana qoqari kamashi amma ta kasa saboda yawan shi da tsaho bata fuska tayi tace, "Allah sarki
inna da kina kusa da kin gyara min magana da su kayi da mom ce ta fado mata daure kan tayi
da sauri ta haura upstairs dakin mom ta shiga ba ta nan neman ta ta shiga yi, kitchen ta shiga
tare da tanbayar su rabi'a ina mom, tace mata tana part din abba ,toh tace tare da komawa
parlour ta samu wuri ta zauna tana kallan film din India tana washe hakur.


Mom ce zaune da abba a bedroom din shi tana zaune saman kujera a hankali ya qaraso ya
rungume ta ta baya, murmushi tayi, madam kullun qara kyau kike baki tsufa gashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login