Showing 3001 words to 6000 words out of 99609 words

Chapter 2 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

magidanta da suka fita siyaya
safe har su qarasa rafi yan'mata ne da sa'anin su birjik suna diban ruwa haka suma kusa
qarasa duk yarin ya data gansu indai sa'ar su ce sai ta matsa saboda tasan hali in bata matsa
ba ta ci na jaki fatsima ce ta hango Rabi'u shi da larai suna tadi fatuha ta zuguru ta nuna mata
da baki kin tuna abin da ya mana jiya qur'an ina sane wallahi ai ban yafe mai ba kawo kunnan ki
kiji abinda zan mai magana su kayi a kunne wadda ko ni salma banji sannan suka kwashe da
dariya kai fatuha billahilazi hiyasa nake sanki wallahi kin san maganin dan iska ta ida zan can
tana daukar tulun ta fatuha tayi gaba haka suka jero suna tsokana sannan kowa ce tayi gidan
su


Tana shiga gida inna har ta sheka koko nata na cikin kwannan samira ta Kafa kai ta shanye
baffa ya fitu daga uwar daka washe da baki yauwa yar albarka har kin gama dibar ruwan eh
baffa na gama kai nake jira mu tafi to bari na dauko fatanya na a buka sai mu wuce to ta ruga
da gudu ta dauko hijabin ta suka ma inna sallama suka fita
Sadiq ne ya futo daga toilet sanye da bathrobe a jikin shi ahankali ya leka fuskar Jidda da
ke bacci yana shafa kanta ahankali ya kai mata kiss a goshi ta bude ido tayi ta sakar mai
murmushi daddy good morning morning sweetheart oya tashi muje ayi wanka tam papa daukar
ta yayi suka shiga toilet ya wanke ta tas suka fito yana mata tsakulkuli tana gantsarewa tana
dariya daddy please stop naqi dear ba daddy zaki ma wayau ba no daddy ba wayau zan ma ba
fa to menene to um wani abu ta ida tana hada hancin ta dana sadiq tayi yayi kamar an mintsilai
ya ce oya tashi na shirya ki tam papa mai ya shafa mata ya sa Mata jeans blue n pink T-shirt
mai kyau da manyan flowers ya raba mata gashin ta gida biyu ba karamin kyau tayi ba Masha
Allah pack ya mata oya wuce wajan grandma ganin zuwa dana gama shiryawa to daddy ta fita
da gudu ya bita da kallo shiryawa yayi cikin kakinshi na sojoji tare da gyara sumar sa ba
Karamin kyau yayi ba wow duk inda namiji ya ke to sadiq ya kai briefcase nashi ya dauko
wanda ke gefen gado tare da ficewa dinning area ya nufa mom good morning morning son how
was your night cool mom and your's tare da Kai mata pack same good atsaitsaye yayi break
saboda ya kusa makara ya fita yaran shi suka fara qamewa tare da miqa gaisuwa motar shi
wadda Tasha wanki benz fara mai daukar ido ya shige yaran shi ya rufe suka fice daga gidan



Baffa da fatuha ne a gona sai aiki suke cikin jin dadi fatuha na ma baffa hira sosai ya ke
jin fatuha a ranshi fatuha ce ta katse shurun da cewa baffa zanyi fitsari to fatuha ki qarasa can
gefe kiyi kin ji ki kulla da kafar ki to baffa ta kutsa kai cikin gona sai da tabatar baffa baya
hangen ta sannan ta lalaba ta qara shigewa jejin tayi wani sasake naga tana diba ta dana
kulewa a leda tana dariya ta matse azanin ta baffa da yaji shure ne ya fara kwala mata kira da
gudu ta qara so baffa gani tana hanki yauwa yar albarka yo Ina kika shige yin fitsarin baki ta
washe ta qara gyara zanin ta hannuta ya ja suka zauna suna cin dumaman tuwon da inna ta
aiko masu da shi suna gama ci bacci ya kwashe fatuha baffa ya ce ikwan Allah har kinyi bacci

kenan ya tashi ya cigaba da aikin shi


Cikin natsuwa yake aikin shi a office din Masha Allah sanyi AC sai ratsawa yake sosai
abokin shi majid ne ya shigo ah big man ashe ka shigo yap tun 8:00 hannu ya mika mai suka
gaisa ya samu guri ya zauna big man ya mom and sweetheart lafiya lau yauma rigima tamin
zata biyo ni taga uncle majid Allah sarki me yasa baka zo min da ita ba haba wallahi tana zuwa
nan zata cikani da to much of surutu um kai dai ka sani mutun sai muskilan ci naji din inwannan
surutun ya kawo ka to ka fita to ban fita tunda ba kaika kawo ni ba sadiq shuru yayi ya cigaba
da aikin shi kiran sallah la'asar ne yasa suka fito su Kayi sallah suka koma bashi ya dawo gida
ba sai 5:30 part nashi ya shige ya yayi wanka ya wuce bedroom din mom zaune take sama
sofa tana karanta azikar yayi sallama ya Mata pack Jidda ce ta rugu ta bashi hug dady I miss u
miss u more dear

After ya gama lunch ya shirya Jidda da kanshi ya ja hannu ta suka je parking space yaran
shi har sun taso ya daga masu hannu alama su ka dai zasu kaitsaye gidan Anuty bilki ya nufa



Dai dai wani ma daidaicin gida su kayi parking mai gadi ya wangale masu gate Masha
Allah gidan ya hadu sosai plat ne mai kyau su hannan na filin gida suna wasa ganin uncle sadiq
ya sasu rugawa aguje suna mai oyoyo ya chabe su yana masu wasa tare suka karasa palour
Maman hannan na ganin shi ta washe baki ta qwalawa talatu kira ta kawo mai abin motsa baki
dangin su fruit da sauran su har kasa talatu ta duka ta gaishe shi ah baby yau kai na a gidan
nawa hala mom ce tace ka zo ah yayi smile oh kina nufi ban zuminci ko kamar hakan dai a'a
aunty ke ma kin san bana zaman a naija sosai but now na dawo Nigeria zanrinqa zuwa har saiki
gaji dani toh shikenan Allah yas da gaske kake haba anuty billy ya ida yana shagwabe fuska
ohni baby wai yaushe zaka daina shagwaba duba fa har da diyar ka budurwa dariya ya fashe
da ita ni dai sister kin samin ido wallahi sannan ya kora lemo toh naji na daina um wai ina mai
gidan ah bayanan yana dubai ok sai end of is week zai dawo Allah ya maido shi lafiya ameen
hira sukai sosai da yar 'uwarsa Kira kirayan sallah magrib ne yasa suka tashi sadiq ya wuce
masalaci


Misali karfe 5:30 baffa ya gama komai da yake a gona fatuha kwance kamar meyin bacci
dare saboda yasan halin ta in ta kwanta bacci bata San a tashe ta yasasa daukar ta har suka
iso gida inna na ganin su ta washe baki tare dayi malam sannu da zuwa tare karbar fatuha da
ke sharar bacci baffa daura alwala yayi ya tafi masalaci bashi ya dawo ba sai bayan isha'i lokaci
fatuha ta tashi tana cin abinci hira suka dan taba sama sama sannan suka wuce ma kwantan su
Inda fatuha ta matsu gobe tayi dan ta aikata abinda ke ran ta


Bayan isha'i sadiq ya dawo yayi salama da sister nashi sannan ya raba ma su hannan

tsarabar su karku so kuga murna wajan su bayan sun fito haka ya biya da Jidda wajan shan ice
cream ya mata siyaya sosai sannan suka dawo tun akan hanya ma bacci ya dauke jidda dan
haka tana kwance a kafadar shi cikin sallama ya shigo mom na palour tana kallo ita da baba
jinmai baba jinmai ta tashi washe da baki tare da amsar jidda shi kuma ya wuce dakin shi yasa
ice creams din a firijin


Baba jinmai tana zuwa daki tayi ma jidda wanka ta samata night dress nata blue rigar dai
dai gwiwa shima yana zuwa daki wanka yayi saboda ya gaji sosai ko da ya fito mom har ta
shinfide jidda saman bed kayan bacci shi yasa tare da jawo laptop din shi yana shan coffee ya
dade yana aiki sannan bacci ya dauke shi
Kira kiran sallah asuba ne ya tada fatuha baki ta washe kai narantsa da Allah jiya da kyar
bacci ya suran yadda na matsu yau tayi wallahi talihi yau Rabi'u sai ya gane kuran shi qur'an
ciki sauri tatashi tayi sallah


Yau dai ba laifi fatuha ta taya inna aiki sosai ba dan komai ba sai Dan tabarta ta fita saida
suka gama komai ta gyara zaman zanin ta wadda kullun jiya na leda na habar zanin san ta ce
inna zani gidan su fatsima to fatuha karki dade to inna ta fita da gudu gidan su fatsima ta shige
inna fatsima na tsakar gida tana wanke wanke gaisheta tayi ta amsa fatuha ya inna inna lahiya
lau ki ce ina gaishe inkin koma gida to za ta ji inna ina fatsima tana uwar daka to fatsima da ke
shara bacci saman tabarma fatuha ta daka mata bugu ke tashi firgigit ta tashi kai fatuha ke
banza tashi muje oh na tuna fa Qur'an ban san sanda bacci ya sure ni ba dankwalinta ta daura
suka fita suna tafe suna tsoka dai dai wata gona suka ci birki Rabi'u ne gindin bishiyar
mangwaro da alamar rake ya gama sha bacci ya sureshi saboda duk ga abin rake zube fatuha
lafe jikin bishiyar bedi ita da fatsima suna lekan shi fatsima bilahillazi yayi bacci ta kwashe da
dariya ai sai ya ci uba nai quli leda ta ciro daga habar zanin ta tufi Rabi'u cikin sanda ta bude
ledar ta busa mai garin ta ruga da guda bayan bedi Rabi'u da ke bacci cikin bacci ya fara jin
radadi da susa Ba arziki ya tashi yana sushe sushe yayi zuru zuru su fatuha da ke bayan bishi
sai dariya suke sannan suka fito daga nesa ta tsaya Rabi'u ta kwalamai Kira ya waigo ai dama
na fada ma kwarankwatsin ba'a buguna na hakura fatsima ta bushe dariya ka je gida mai tafasa
tama magani kaji rabe ya dago idanun shi sunyi jaaa bala'iiiii Zan ci uban Ku dama kune kuka
fesa min asosa narantse na sha magani sai na zo har gida na ci uban ku yo Zan can banza ko
ka zo mukarama wani injin fatuha taja hannu fatsima suka bargun suna dariya shikuma Rabi'u
na soshe soshe


*Taku har kullu Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*

*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*blood sister deeja*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
(We the best)

7_8
Soshe soshe Rabi'u ke yasha wuya sosai idanunan sunyi jawur sai ihu yake ado ne zai wuce ya
hango shi yana birgima ya qaraso subhalillah lahiya Rabi'u me ya faru wallahi fatuha yana ihu
haka malam ado ya taimaka mai ya kai shi gida jikin nan nashi yayi jawur abunka da ba
fulantanin mutun inna maitafasa tana gyaran tafasa taji sallamar Malam ado ta tsame hannu ta
dake cikin tafasa ta yafa mayafi lahiya Malam ado me ya sami Rabi'u ni dai wallahi ban Sani ba
amma da alama sosa ce toh fa kai ko Rabi'u mai ya hada ka da sosa garin ya haka ta faru ta
ida zan can tare da riqe haba zani tana matse kwalla cikin murya wanda yasha wahala ya ce
inna wallahi fatu ce da wannan iskancin kambuuu alqawalin Allah ban yadda yau sai naga uban
ta jauro billahilazi ta idaa zancan tana yarfa hannu sama Malam ado ya ce a daiyi hakuri yarin
ya ce yarin ya uban wa tana dafe qirji yarin da aure yau haihuwa badi shegiya yarin ya mai
Kama da mayu wallahi Malam ado ban hakura shigo da shi namai magani na je na samu uban
nata haka aka shigo da Rabi'u yayi zuru zuru aka shinfide shi bisa tabarma


Qur'an fatuha baki da mutunci yo ni ta wasa ce ai dama na fada maki saura malam dalha ai
qule nake da shi kwarankwatsi hehe kai qawata ina san ki qur'an fatuha ta washe hakura nima
haka billahilazi haka suka dawo gida ko da suka dawo gida fatsima gida ta wuce gidan su
fatuha ta shigo gida da sallama yau zuciyar ta fes take da farin ciki inna da ke shara ta amsa
sallama ta kauda kai yanzu Dan Allah fatuha kin kyauta kenan tunda safe da kika fita sai yanzu
zaki dawo bata idaa rufe bakin ta ba mai tafasa tayi sallama cikin tsiwa inna ta amsa keeeee!!
ta cakumo wuyan fatuha inna ta ce lahiya mai tafasa lahiya lahiya kenan bari uban ta jauro ya
zo billahilazi yau ban yadda kuma duk abinda ya samu daa na ke ce ni zaki kashe ma daa har
kin isa inna sai bata hakuri take amma taqi sakin fatuha wanda tayi wiki wiki da ido dan tasan
tayi baki ta turo gaba ke ki cika ni tare da finci ke kanta daga ruqwan da maitafa ta Mata yo ba
dan naki bane jiya ya bige ni ba kuma na Rama yau ta ida zancan ta murguda baki dan uban ki
in zaki rama saiki samai a sosa inna ta ce fatuha ince jiya ban maki magana ba yo inna jinayi
ban iya hakuri ta fada cikin tsiwa haka maitafasa ta gama zage zagen ta da kumfar baki ta tafi
acewarta in Malam jauro ya dawo zata zo ta same shi


Daddy please muje shan ice cream sweetheart akwai a fridge muje na baki ok papa thank
you ya lakace mata hanci that is my angel ta washe hakura part nashi ya kaita ya bata ice
cream shi kuma ya shige gym room nashi ya dade yana gym sannan ya fito riqe da towel a
hannu shi yana goge zufar fuskar shi gefen da Jidda take ya kalla har tayi bacci ahankali ya

karasa saitin fuskarta yayi kala tausayi my angel I now you miss your mom why kausa me yasa
kika tafi kika barni nida Jidda why kausar yana maganar kamar zautace yana share hawayan
fuskarshi I miss u more my wife naso ace yanzu kina ganin angel my wife dake take Kama
sosai naso ace tare zamu bata good caring ya kai lips din shi dai2 goshin Jidda ya mata pack


*Asalin labari*

Malam idi zaunan dan kauyan Kano ne wato rano su fulanine sosai Allah yayi ma malam idi
rufin asiri dai2 gwargwado yana kiwon shanu sosai har ma da kaji gashi mutu min kirki shiyasa
kowa ya sanshi a kauyan rano yana da mata tani sosai yake san tani Allah ya basu ya'ya 3
maza 2 mace 1 kabiru shine babba mai bimai Ibrahim sai rukayya

Zaune suke zaman lafiya cikin kauyan inda lokacin kabiru ke aji shida na secondary shi
kuma Ibrahim aji 5 rukayya na aji 3 sosai suke karatun su saboda Malam idi mai san karatune


Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau garin rano zaman lafiya yayi qaran ci saboda barayi
na zuwa su kwashe ma mutun dabobi sannan su kashe ka kai da iyalan ka Malam idi ne ya
shigo gida cikin sallamar shi tani da ke wanke wanke ta amsa ince dai malam lafiya wallahi tani
kauyan nan ba lafiya kabiru da ke uwar daka ya leko sukayi tsaitsaye can idi ya yanke shawarar
saida dabobin shi su koma birni cikin garin Kano ba yadda idi ya iya haka ya saida shanun shi
cikin ikwan Allah ya samu kudi mai yawa ya sama masu ma dai2 cikin gida a rijiyar zaki sannan
yaba abokin shi Malam tanko kudi Wanda ke birni ya samai shago a kasuwa kwari a zuba
komai ciki ya tataro iyalan shi suka dawo cikin garin kano lokacin Ibrahim ya gama secondary
da yake Ibrahim yaro ne mai San karatu result nasu na fitowa ya sami admission a biyuke idan
yake karanta business admin shikuma kabiru ya cigaba da kasuwan ci tare da mahaifin su sosai
suke samun rufin asirin su

Kwanci tashi asarar mai rai yau Ibrahim ya gama karatun shi inda ya samu aikin kwangila
sosai yake samun cigaba inda ya hadu da Hauwa'u auran soyayya ankai amarya rijiya zaki
kusa da gidan kabiru inda yake zaune da matarshi Aisha tsakanin amarya da Ango soyayya
sosai suke zubawa bayan wata biyu hauwa'u ta fara laulayi sosai take samun kullawa wajan
mijin ta da surukar ta har ma da Aisha matar kabiru lokacin rukayya na FCE cikinta ya shiga
watan haihuwa bata wani sha wahala ba sosai ta haihu dan ta mai kyau sosai ibrahim yayi
murna sosai


Kwana bakwai da haihuwa akayi suna inda yaro yaci suna idiris wato suna Malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login