Showing 84001 words to 87000 words out of 99609 words

Chapter 29 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

Advertisement

89_90


Shirye shirye suke sosai kasancewar yau ake kamu. da misalin karfe 4:00pm kowace ka gani
shiryawa tak'e ciki'n ashobe. Fatuha da ke zaune cikin toilet tana sana'ar kuka knocking din
kofar da akayi ne ya sata miqewa tana share hawayan ta, hanan dak'e baki'n kofar tace "Fatuha
ki fito me make up ta zo har an gama ma basma ke ka dai ake jira?" to tace tare da yin sauri ta
watsa ruwa ta fito,


Ko da ta fito shaharariyar me make up fandi ta zo fatuha kawai take zaman jira. tana daure
da towel ta fito ta sauna tana shafe jikin ta da mai. Anuty bilki ce ta shigo da kayan da zasu sa

washe da baki ta aje kayan, a'a fatuha dama ba'a gama make up din ba d'aga kai fatuha tayi ,
ya kamata kuyi sauri ku shirya kar ku bata lokaci saboda da kun dawo zaku dinner to tace
sannan Anuty bilki tasa kai fa fice. a hankali fandi ta fara tsantsara mata make up kafi'n ka ce
me fatuha ta fito wasu maroon materials tasa gown mai Stone's masha Allah tasha kyau har ta
gaji, ga head tasha ita kanta me make up ta yaba da irin kyan da fatuha tayi . su fatsima ne
suka shigo sanye da ashoben su ash atamfa mai ratsin maroon suma sun sha head kun san a
tare suka fito da basma kusan kaya colours daya suka sa har yan mata amaryar anko daya su
kayi. motoci ne masu numfashi da tsada suka faka amaran suka shige ba a zame ko ina ba sai
meenah event hadadan hall na party iyakar haduwa hall din ya hadu. kuma ya qayatar
kasancewar kamun na mata zala ne shiyasa ba ango ko daya sai yan'mata da iyaye yan
asharale ne suka fara buga ganga tuni hall ya dau sauti amaran zama su kayi ma zaunin su
aka fara gudanar da shagulgula. can na hango su fatsina da nana da Zara anshige fili anata
kwaso shoki haka suma qawayan basma biki yayi biki sai dai muce alhamdulillah .


Fatuha ko duk wannan bidirin da ak'e zuciyar ta naga muradi'n ranta, ji take kamar ta rushe
da kuka kallan kowa take da ke farin ciki da walwala angel ta hango itama ba laifi ta saki jikin ta
tana warwasawa,

Anci ansha inda aka raba turaru kan wuta da atamfofi masu tsada sosai aka raba kaya kamar
ba'a so, sai kunsan yama liqis taro ya watse suka dawo gida,


Ko da suka dawo wanka amaran suka qara tare da dauro alwala suka gabarta da sallah
magrib da isha, sannan amaran aka fara shirya su cikin wani wanka ni kai na har mamaki nake
irin shirin da akayi ma bikin. lace suka sa blue mai ratsin dark blue mai shegen tsada ga make
up da aka qara zuba masu sai kamshi suke yan matan amaraya ko pink lace suka sa mai ratsin
white kowa ce tasha make up fatuha ko saboda tsabar kyau kasa gane ta kake ,dan ba
qaramin kyau tayi ba kuma ga anuri da y'a sauko mata na amare. basma ma ba'a barta a baya
ba tayi kyau bâ l'ai fi,


Shiryawa angwayan suke cikin getzner shad'a blue tasha aiki da dark blue zare ,duk
wannan shirin da sadiq keyi jin shi yake susuku dan kwata kwata baya tare da walwalar shi ,
links yasa ma hannun rigar shi sannan ya daura agogan shi hublot tare da zura takalmin shi
black mesarath tuni ya fito yana sheqi da wani irin kyau sajan shi yayi lufluf ya kwantan can
gashin shi ya leqo ta cikin wula .feshe jiki'n shi yayi da turare masu kamshi da sanyi dadi kusan
shigar su iri daya da majeed shima ba'a barshi baya ba Dan yasha kyau har ya gaji, sai
murmushi yake saki fararan haqoranshi na bayana , abokanan angwayan ma ba'a bar su abaya
ba Dan suma sunsha kyau Khaleed sai rawar kai yake zuba wa haka shima Dr yakub ba'a bar
shi a baya gayu su kayi na sosai ,

Cikin natsuwa suka fito suka shige moto cin su mais alfarma da tsada, dan a da'ko amaran
ko da suka iso amaran sun shirya tsaf motoci aka fara shiga kowace amarya ta shige motar
angwanta,


Murmushi majeed ya saki yana bin fatuha da wani irin kallo mai cike da so da kauna, a
hankali ya kai hannu ya taba hannu ta tare da kallan lalan dake hannu ta yace, "My love lalan
nan yayi kyau?" smile tayi wanda iya karshi laban ta tare da qara manewa karshan kofar tana
tuna abin santa.

Kallo sadiq yabi basma da shi ba laifi ta mai kyau. yau ce rana ta farko daya fara ganin
kyan ta ayanawa yayi a ranshi, tunda ya ga basma haka to ya fatuha zata kasan ce? wani irin
kishi ne ya lulube shi tare da qunar zuciya juyowar da yayi ne su kayi ido hudu da basma smile
ya sakar mata tare da kauda kai,

A dai-dai affcent center motocin suka faka lokacin har wasu sun halara tun daga bakin hall
din kana jiyo irin sautin dake tashi ,wajen y'a hadi bâ karya, ga wasu kujeru sa ak zagaye haldi'n
farere Tass, jerawa yan'matan amarya su kayi shigar farrar matériel sulayi sa baki'gwagwaro sa
a la d'aura mais a k'ai, Angwayen KO bakin Sweet suka sa y'a sa farar taklmi m'asha Allah
shigar ta su yayi kya, amaran suka shiga tsakiya sadiq sai bin fatuha yake da kallo bugun
zuciyar shi na daduwa, ita kanta fatuha ta qasan ido take kallan sadiq tare da jin kishin shi,


A natse suka shigo hall din, nan tale wajen y'a gwarare da shewa da ihu, tuni aka canza
salan kida da sauti majeed hannu sa na maqale dana fatuha yadda ya shige mata kamar zai
maida ta ciki .sadiq ya cika tap dan har ya fara ganin jiri riqe hannu basma yayi dan ba yadda
zaiyi dan baya so ya bata ma qanshi rai .ko bai so basma so na aure ba yana sonta a
matsayin ta na kanwar shi , ko da suka shigi gurin zama suka yi aka fara gudanar da shakali,
can na hango su Anuty Raheenat anata kai kawo anzu shagali ashe abin ba ita ka dai bace
har da yan Real Hausa fulani writers. can na hango Fulani da Anuty Rahama nalele suna rab a
ma mutane kayan motsa a baki, nima dai ba'a barni a baya ba Dan na Shiga a dama dani shoki
kawai ake kwasowa.


A hankali majeed ya matso daf da kunan fatuha yace, "My love yanzu fa gobe kin zama
tawa ko? yana magana yana wasa da yan yatsunta" sadiq dak'e gefe yana kallan su baki'n ciki
na cin shi, dafe kirjin shi yayi domin yafara yi ma sa nauyi , a hankali ya miqe ya bar guri tunda
ya fito d'aga hall din jiri ke di barshi, KO gaban sa baya gani. Sa kyar y'a isa inda yayi parking
fin motarsa ya ya daura hannu shi kenan ya ji an riqe hannun. waigowa yayi su kayi 4 eye's
da Dr yakub girgiza kai Dr yakub yayi yace sa...!! be ida rufe baki'n shinba sadiq ya fadi jikin shi
sumame rudewa Dr yakub yayi yasa sadiq a mota ya bar harabar gurin da gudu.

MC yaba amarya da ango damar su yanka cake ,saukowa sukayi a hankali daga sama.
majeed ya yanka yaba fatuha a baki hall din ya dau ihu sadiq aka kira da basma amma ba ango
ba alama haka MC ya rinqa kira ango ganin abin kunyar dak'e shirin faruwa yasa Khaleed hawa
a matsayin ango yaba basma cake a matsayin sadiq tuni hall ya dau tafi, basma iyakar cika ta
cika bata taba jin bacin rai ba irin na yau, yaune ta tabatar da sadiq be Santa kuma ba zai taba
Santa ba tunda har ya iya wulaqantata gaban bainar jama'a. idanuwan ta ne tap da qwalla, tana
tausayawa kantada Irina rayuwar sa zatayi a gidan SadiQ. haka akayi turo kusan duk abinda
ango zaima amarya Khaleed ne yayi ma basma.

Ko da fatuha ta juya bata ga sadiq ba tuni idanuwan ta suka kawo ruwa. dama shi take gani
tana jin sanyi a ranta .

Ko da Dr yakub yaja mota basu zame ko ina ba sai asibitin shi ,suna shiga aka turo gadan
daukar marasa lafiya sadiq da yanzu idanuwan shi sun fara budewa haka yake ganin asibitin
na juyamai oxygen ne manne a hanci shi numfashin shi sai sama sama yake Dr yakub ko har
ya fara matsar kwalla. emergency aka wuce da shi doctor sun Dade a kanshi Dr yakub ma kasa
shiga yayi sai zarya da yake a baki'n kofar kusan 1 hour suka dauka sannan aka fito da sadiq
sanye da oxygen a hancin shi daki aka bashi tare da samai life sport machine sai qarin jini da
ake mai a hankali Dr yakub ya qaraso gaban shi tare da yin kneel down gaban gadan sadiq,
hawaye ne kemai zarya a hankali ya kai hannu ya shafa sumar kan sadiq yace "Friend why me
yasa kake bama kanka punishment haka? why sadiq ya ida zancan hawaye masu zafi na
gangaro mai wayar shi ce dake ringing ciki aljihu ya tsuro tare da kallan suna dake maqale a
screen din majeed kashe wayar yayi gabaki daya tare da janyo wayar sadiq ya kashe sannan
ya dau kayan sadiq da aka cire mai yaba daya daga cikin ma'aikatan asubitin su wanke.

Bayan ankamala dinner kowa ya dau hanyar zuwa masaukin shi majeed sai kiran Layin
sadiq yake baya Shiga dana Dr yakub. hakura yayi da Kiran tare da maida wayar aljihu.


Bangaran basma ko kuka take sosai tare da taqaicin amincewa da auran sadiq ,Khaleed sai
bata hakuri yake tare da ganin rashin kyautawar sadiq ya rasa dalilin da zai mata irin wannan
cin fuskar bayan tana qanwar shi kuma matar da zai aura, shi a ganin duk wanda yasa mu
basma a matsayin mata ya mure ya rasa me yasa sadiq ke nuna rashin ko in kulla a kanta da
wannan tunanin suka qaraso gida ko Godiya bata mai ba ta shige gida da sauri tare da tsananta
kukanta.


Motar su fatuha na fakawa majeed ya fara jero mata kalaman soyayya tare da jan ta a jiki,
ganin zai wuce Gona da iri yasa fatuha saki'n kuka lalashin ta majeed ya Shiga yi tare da
yimata pack ko saurara shi ba tayi ba ta bale murfin motar ta fita da sauri.

Bangaran sadiq ko bashi ya tashi ba sai wajan 2:00am na dare a hankali yake ware sexy
eye's ball's din shi da wani irin ishin ruwa ya tashi. Dr yakub da ko rintsawa baiyi ba ya miqe da
sauri ya qaraso wajan shi cikin cool voice sadiq yace "Ruwa" da sauri Dr yakub ya bude fridge
ya dauko rubar ruwa ya bashi ko da ya sha ruwan miqewa yayi yana qoqarin cire jini da ake
qaramai riqe, hannu Dr yakub yayi yace, "Captain me kake shirin aika tawa? ya fada bakin shi
na rawa" kallan shi sadiq yayi yace so nake na tafi gida bana so majeed ya gane bani da lafiya
ya ida zancan yana cire Karin jinin wasu hawaye ne masu zafi suka zubu ma Dr yakub yace,
"Sadiq wai me yasa kake so ka raya rayuwar wani ka bata taka? why sadiq Dr yakub ya fada
yana jijiga sadiq" kuka sadiq ya Saki tare da cewa "Bazan taba bari majeed ya mutu saboda
bakin ciki na ba nafi san farin cikin majeed a kan na kowa a duniya bani da dan uwa sama da
majeed saboda haka ban taba bari saboda ni ya rasa rayuwar shi sadiq ya ida zancan yana
kuka mai tsuma zuciyar mai saurare" a hankali ya ida cire kayan asibiti tare da zura kayan shi
wayar shi ya dauka tare da kunna ta Dr yakub mutuwar tsaye yayi yana bin sadiq da kallo tabas
yanzu yasan me sadiq yake nufi so yake ya rasa rayuwar shi ya zamamar dole ya kawo
karshan abunan ko saurarashi sadiq beyi ba saima car key daya dauka tare da fita yana
ingisawa.....



*_Muje zuwa fan's_*

*Kuyi hakuyi Sa wannan bâ yawa*


*_taku har kullun salma mas'ud nadabo_*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★We are the best★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


91_92
A hankali yayi parking motar shi tare da yi mata key. harabar gidan tsif ba motsin kowa sai
motoci birjik kamar wanjan saida mota. a hankali ya cigaba da takawa duk da yana jin jikin shi
kuka kuka ya fara ji sama sama hakan ne ya sasa tsayawa tare da kallan agogo hannu shi
mamaki ne ya lulube sadiq a hankali ya fara bin inda kukan ke fita fatuha ce zaune sama resting
chair tana rai ra kuka. qarasowa yayi gaban ta firgigit ta daga a dan tsorace ganin sadiq ne yasa
ta fada jikin shi tare da sakin wani kukan, daurewa yayi tare da zamewa ya janyo ta suka zauna
a hankali yake shafa mata bayanta ba wanda yace ma dan uwan shi komai ,sun dau kusan 5
minutes a haka fatuha ce ta dako tana kallan sadiq ciki'n sanyin murya tace 'Uncle" ya naji jikin
ka zafi? dan smile sadiq yayi yace "Nima haka naji jikin nawa" kallan shi take cike da tanbayoyi
amma sai ta kasa tare da komawa tayi lamo a fafadan qirjin shi kunsan a haka suka zauna har
bacci ya dauke fatuha idanuwan sadiq biyu yana kallan fatuha har sai da ya fara jin kiran sallah
asuba sannan ya tashe ta. sannan yace "Dear tashi asuba tayi?" qarayin lamo tayi a jikin shi
shafa gashin kanta yayi yace "Fatuha" a hankali ta ware eye's ball's din ta, tace "Na'am" tashi
mu shiga gida jiki ba qwari ta tashi har tayi gaba ta tsaya tare da cewa "Yau ne zan rasa farin
ciki na! yaune mafarki na zai rushe" wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata tace, "Yanzu
duk wani rayuwa da mukayi zata zama tarihi mai kyau? ina ma fatan alheri Allah ya baku zaman
lafiya da basma tana ida zancan ta fashe da kuka mai ban tausayi" a hankali sadiq ya janyo ta
jikin shi ya rungume shima hawaye na mai anbaliya cikin sanyi murya sadiq yace "Fatuha ki
kasance mai biyaya a daki'n mijin ki? majeed na sonki please karki bari majeed yayi kuka dake
dai-dai da rana daya? duk wanda yayi hakuri a rayuwa zai ga ribar haka ya ida zancan yana
share hawayan shi tare da sakar ma fatuha lalausan murmushi" itama shi ta mai tare da
shigewa cikin gida.


Duk inda ka wuce had'a had'a ake na shagali abinci ke ta yawo da kayan motsa baki, kaji
ko har ture su ake da naman rago yan'matan amarya na zaune a dak'i sai shirya fatuha ake
saboda wudil za'a wuce da ita sai an daura aure aje dako ta. tunda ake mata make up take
kallan agogo tana irga mintinan da suka rage ta zama malaqi majeed. hawaye ne tap da
idanuwan ta bayan angama make up din ta zura kayan ta atamfa mai ratsin green pink brown
masha Allah kayan sun mata kyau tasha danqareriyar sarqa ta gold da yan hannu sai sheqi
take. Anuty bilki ce ta leqo tace, "Fatuha ku fito ga moto cin da zasu kai mu wudil?" gaban tane
ya yanke ya Fadi dan har wani jiri take gani a haka su fatsima suka sata tsakiya aka lulube ta
anata zuba guda, mota suka shige driver ya jasu suka har ba kan titi.


Wanka angwayan kawai suke suna shiryawa Khaleed ne ya kalli sadiq tare da aika mai
harara tare da cewa "Wai ina kaje jiya?" bala mai harara sadiq yayi yace "Ina ruwan ka da inda

naje? kai dai wallahi ka fiye sa ido? irin kune ana ruwa kuna irgawa" dariya majeed yayi yace
"Kai dai tashi kayi wanka kaji baby ga kayan ka can tun dazu na aje ma ina so yau ka kasance
cikin farin ciki kamar yadda kowane ango keyi majeed ya ida zancan yana zura kayan shi" a
hankali sadiq ya miqe ya shiga toilet majeed .ya bishi da kallo tare da ida shiryawa tunda sadiq
ya shiga toilet yake kuka kamar qaramin yaro sai da yayi san ransa sannan yayi wanka ya fito.
ko da ya fito Dr yakub ne ka dai daki'n kallan shi sadiq yayi tare da kauda kai ya cigaba goge
jikin shi da qaramin towel, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login