Showing 24001 words to 27000 words out of 99609 words
Chapter 9 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
artabun da suka sha da sangami jiya kawai shahada tayi tare da qundun bala ta bude kofar ta
shiga taré da yin sallama, ba kowa parlour hakan yasa ta murda handle din kofar bedroom
sadiq ta hangoshi tsaye gaban dress mirror a hankali ya dago sexy eye's ball's din shi wani irin
kallo ya wurga mata tare da jan tsoki, cikin tsawa ya ce "Yanzu ne time din da ya kamata ki
shigo eeh? baki san tana zuwa school bane, koko rashin sanin muhinmanci ilimi yasa kika
zauna baki zo ba eeh? nuna ta yayi da yatsa yace as from to day karki qara kai wannan time
din baki zo ba stupid girl kawai" duk da bata san Kalmar da ya fadi aqarshe ba amma jikin ta ya
bata zagin ta yayi sai da ta fakaici idan shi sannan ta bala mai harara tare da daukar jidda daga
saman bed zata fita da ita har ta kai bakin qofa, ya kara daka mata tsawa yace "Kin makarar da
ita? yanzu Kuma ina zaki kaita? oya wuce ki mata wanka a bathroom dina, wiqi wiqi da ido
fatuha tayi dan ita bata san me ye bathroom ba, wata uwar tsawa ya kuma daka mata oh waike
wata irin yarin ya ce ehh ki kai ta ban daki na kiyi mata wankan yar qauye kawai mtss, saura
kuma inkin je kinmin kauyan ci jiki ba kwari fatuha ta shiga toilet din ba laifi dan kauyanci da tayi
kadan ne sannan tayi ma jidda wankan, tana mata tana zuba mata surutu dauke da ita ta fito
sannan ta zauna da ita saman bed sadiq na zaune saman sofa yana kallansu shafe jikin jidda
tayi da mai sannan ta dau uniform din jidda zata sa mata nan fa kar ku ga zare ido dan ta rasa
ta inda zata samata rigar saboda gown ce irin mai kamar biri da wando dinan tayi tsuru tsuru,
sadiq jan tsaki yayi tare da fisge rigar ya Shiga sama jidda fatuha duk tana kallan yadda ya ke
samata sai da ya gama shirya jidda sannan ya mata pack, daddy good morning , morning too
angel how was ur night, cool daddy. good, fatuha ko ta saki baki tana kallan su.
Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan sadiq ya dau briefcase din shi ,fatuha kuma ta dauki
jidda suka sauko downstairs mom da abba na zaune a dining area har sun fara breakfast cikin
ladabi sadiq ya gaishe su haka ma fatuha da jidda mom ce ta kalli fatuha washe da baki ta ce
"Ya kwanan baqunta?" murmushi fatuha tayi tare da jama jidda kujera ta zauna cikin natsuwa ta
shiga saving din jidda abinci, da ta gama sai ta zauna shima cikin dari dari sannan ta sa hannu
cikin plate din.. wata irin tsawa sadiq ya daka mata wadda tasa fatuha fara matsar kwalla, cikin
kakausar murya yafara cewa "Wai bana ce maki ki daina feeding din angel da hannu ki bane
eeh" Mom ce ta kalle shi tare da wurgamai harara , baby wai me yasa ka ke haka ne eeh fada
ta mai sosai sannan shima Abba ya dara da ce mai "Kai haka ake a rayuwa? kai kullun cikin
zafin rai sadiq wai me yasa baza gyara halin ka bane eh baby?", shiru sadiq yayi tare da aikawa
fatuha harara ita ko tayi kamar bata gani ba sai ma gwalo da ta aika mai cikin na tsuwa suka
gama breakfast.
Briefcase din shi sadiq ya dau ka fatuha na dauke da jidda suka fito harabar gidan, haka
fatuha ta rinqa zare ido tana qarewa yaran sadiq kallo *ola* ne ya qaraso cikin sauri tare da
amsar briefcase din sadiq ya kai mai mota fatuha na biye ta shi suna zuwa gaban mota fatuha
ta aje jidda cikin mota ,zata juya sadiq ya fisgota ta fado jikinsa,da sauri ya ture ta tare da taka
mata qafa da booth din kafar shi ya murzashi sosai, jin za tayi ihu yasa ya matse mata baki da
hannun shi da karfi yana kallan ta ido cikin ido ,idanun fatuha sun cika da kwalla tap saboda ita
ka dai tasan azabar da take ji ,ture ta yayi tare da nunata da yatsa ya shige motarsa har zai
tada yajiyo muryarta tana magana da yake ahankali take magna shiyasa baiji abinda take
fadi,kwafa yayi ya tada motar suka bar harabar gidan. fatuha ko Allah ya isa ta Shiga jeramai
tare da shigewa gidan a guje.
*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★
http//,mobile. Facebook.
Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera_speed_dia
l_yn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*Godiya ta musanman ga masoya na ❤ina jin dadi addu'ar ku ta fatan alheri nima ina san
ku ana mugun tare*
*Wannan safin nakune masoya na asha karatu lafiya*❤
33_34
Parlour ta qaraso tare da share yar qwallar da ya taru à idonta, Mom na zaune saman three star
tana kallo juyowa tayi cikin murmushi tare da kallan fatuha, ita ma fatuha murmushi tayi tare da
fara kwashe kayan abinci da ke dining area, ah fatuha da kin bari rabi'a ta zo ta kwashe, washe
baki tayi tare da cewa barshi kawai hajiya, mom murmusawa tayi tare da cewa "Ni ko fatuha da
kin daina ce min hajiya nan da yafi! Ki rinqa kira na da sunnan da sadiq ke kira na" murmushi
fatuha tayi tare da cewa, toh, sannan ta kwashe kayan ta kai kitchen mom kuma ta cigaba da
kallan ta tana ayana wasu abubuwa à ranta,tana fituwa direct part din sadiq ta wuce ta gyara
part din sosai, tana gamawa ta shiga toilet shima toilet din sai daya sha wanki dan fatuha gyara
tayi bana wasa ba, tana gamawa ta washe baki tare da zama saman sofa tana qarewa dakin
kallo hotan sadiq ta hango manne jikin bango tangameme shi da kausar sunyi murmushi.
A hankali ta qaraso wajan hotan tare da washe baki tana kallan hotan, ohni ashe sangami na
murmushi ah ji yadda ya washe hakura dan Allah ai da haka yake kullun daya fi kyan gani,
murmushi tayi tare da daura hannu saman pic din ,um gaskaya kana da kyau Qur'an chan kuma
sai ta bata fuska tare da cije lips dinta dariya tayi sannan tace, "Kwarankwatsi zaka zo ka same
ni wallahi ba kasan *wacece fatuha ba yar gidan baffa jauro*" sannan ta bala wa pic din harara
ta fita daga part din.
Tana sakowa downstairs ta shige bedroom dita wanka ta kumayi, tana fitowa ta shafe jikin ta
da lotion tana shafa lotion din tana washe baki , Qur'an wanga mai sanyi garai ga kamshi tap
wallahi birni tayi sai da ta gama shafe jikin da mai tas sannan ta sa wasu uniform din.
Cikin school yayi parking tare da fituwa ya budewa jidda murfin mota smile ya mata me sanyi,
sannan ya ciro mata lunch box dita ya miqa mata, bata fuska jidda tayi tare da cewa "Daddy
am going to miss u daddy" saman kanta ya shafa tare da cewa "Sorry angel soon za'a tashi
aiko se inna dawo gida sai muje shan ice cream ko my angel" washe baki tayi tare da yi mashi
pack sannan ta shige class yana kallanta har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shige
mota yatafi.
Bayan ta gama shirin ta tafito parlour ba kowa sai kamshi da ke tashi na girki, kitchen din ta
nufa tare da sallama baba jinmai ke girki sai rabi'a na gyara salat murmushi tayi tare da gaishe
su washe da baki baba jinmai ta amsa taré da cewa "Yar albarka kin zo taya ni aiki ne?" daga
kai tayi alamar Eh, can kuma fatuha ta bata fuska tare da cewa baba wai ina kike kwana jiya
kika barni ni ka dai, washe baki baba jinmai tayi tare da cewa, ah aini fatuha banan nake kwana
ba a gida na nake kwana se da safe na zo ,turo baki fatuha tayi tace gaskiya baba yau binki
zanyi,ah ba za'ayi haka ba ki zauna nan nima ai gidan bacci ke kai ni baba jinmai ta shiga
lalaba fatuha.
Taya su aiki tashiga yi sosai can baba jinmai ta miqawa fatuha kwano ta debo man da za'a
soya kaji a stor, wani irin murmushi tayi tare da Shiga stor din nan ta zuba a kwano tare da qule
wani a leda tasa a aljihun skrit din ta tafitu sannan tayi ma baba jinmai sallama ta koma parlour
ta cigaba da kallo tayi tana washe baki, mom ce ke saukowa daga stairs sanye da mayafi da
car key a hannu ta kallan gefan da fatuha take tayi tare da cewa "Oh na manta, nayi da ke jiya
zan kai ki gyaran kai wallahi na manta gashi yanzu fita zanyi" murmushi fatuha tayi ta ce ba
komai gobe maje , toh shikenan inna manta ki tuna min please toh ta ce mata tare da rakota har
bakin kofa sannan ta koma parlour ta cigaba da kallo.
Tana kallo har bacci ya kwashe ta a parlour, cikin bacci taji ana sallama tashi tayi tare da ware
idanuwan ta ta sauke su kan Anuty bilki, ware ido ta kuma yi tana qarewa Anuty bilki kallo dan
tabas tayi mata kama da sadiq sai dai sadiq ya fita kyau sosai qaqaro murmushi tayi bakin ta na
rawa ta gaida Anuty bilki zama tayi tare da amsawa tayi ma fatuha murmushi, um hajiyar ba ta
nan ta fita, murmushi Anuty bilki tayi tace ai na sani munyi waya yanzu zata dawo ba dadewa
zatayi ba, fatuha kitchen ta shige ta fada ma baba jinmai anyi baquwa lemo ta zuba mata a tray
da kyan motsa baki tare da ce mata gata nan zuwa taga baquwar , Anuty bilki ko kayan jikin ta
ta rage tare da haurawa upstairs dan ta watsa ruwan , fatuha na zuwa parlour taga ba baquwa
sai afra da ke bacci saman kujera baba jinmai ta qwalawa kira ta fitu a rude ita ma Anuty bilki da
shigar ta bedroom kenan ta sauko turus baba jinmai tayi a parlour lafiya fatuha me ya faru baba
wallahi baquwar ce ban gani ba gashi ta bar yar ta a nan Anuty bilki ce ta qaraso, washe baki
baba jinmai tayi tace, ah wai Bilkisu kike nufi ai yar gidan ce amma tayi aure ganin gida tazo yi
murmushi fatuha tayi tace, "Aiyo aini ban sani ba shiyasa" itama Anuty bilki dariya tayi sannan
ta haura sama tare da ba fatuha afra ta kula da ita kafin ta fito.
Misalin karfe 12:00pm jidda ta dawo school ita da Jamal, kasan cewar school daya suke da
yan'yan Anuty bilki cikin murna fatuha ta tare su , kasancewar fatuha me san yara ce shiyasa ta
ja jidda da Jamal bathroom ta masu wanka suka fita tas sannan ta sa masu kaya ta zo da su
dining area suka ci abinci sannan ta dawo parlour da su suna dan taba hira sama sama, can sai
ga hannan ita ma ta dawo daga school washe da baki ta qaraso ta fada jikin Anuty bilki wash
mom I am tied sorry sweet je kiyi wanka ki canza kaya fatuha ko washe baki tayi tana qarewa
su hanan kallo, tsakanin hanan da fatuha kunsan sa'anin ne shiyasa tunda ta shigo fatuha ke
kallan ta hakan sai yasa ta tuna da fatsima kwalla taji ta zo mata gaskiya ta San tayi kewar su
inna da fatsima daki ta shige tayi kwanciyar Hanan ce ta shigo ta shige toilet tayi wanka
sannan ta fito daure da towel suna hada ido da fatuha tayi murmushi.. sannu ki ,yauwa fatuha
tace mata, nan hanan ta fara janta da hira sama sama, hanan dama kawa take so gashi ta
samu aiko nan hira ta barke tsakanin su in fatuha ta fadi wani abu hanan tayi dariya sosai har
cikin ta ya kule.
Sai yama likis su hanan suka tafi, har bakin mota fatuha ta rako su ita da jidda kamar kar su
tafi saboda fatuha taji dadi hirarsu da hanan.
Bayan sun tafi suka koma bedroom din jidda, taci gaba da zubama fatuha surutu can kamar
kamar aj mintsi neta ta tashi ta koma parlour kadan kadan ta leqa waje.
Motar sadiq ce ta kunno kai cikin gidan, wani irin murmushi fatuha tayi tare da yin Sauri da
haura sawa, upstairs part din sadiq ta shige direct toilet din shi ta shiga ta fido da man da ta
kule a leda ta juye shi qasan toilet din sannan ta fito tana dariya tana waigen part din ji tayi ta
fada jikin mutun, idanunta ta zaro cikin tsoro da fargaba ,tayi lamo tana jiran aradu, wata irin
tsawa sadiq ya daka mata tare da ture ta ta tafi tagalgal zata fadi ya fisgota tare da qanqance
idanu yana kallonta , fatuha kuwa har ta fara matsar kwalla, cikin kakausar murya yace "Ke
wace irin mahaukaciya ce ? ya karasa zancan da murya mai sauti" Wanda yasa fatuha sakin
kuka saboda a iya rayuwar ta ba Wanda ya taba mata irin wannan ihu, kuka take sosai tana
girgiza mai kai janta ya cigaba dayi har sai da ya kai last stairs sannan ya ban kada ta ta fadi
qasa tayi zaman yan bori nunata yayi da yatsa tare da cije lips din shi ya dau briefcase din shi
ya shige part nashi fatuha ko kuka tayi san ranta da kyar ta tashi saboda qugun ta ya riqe
bedroom ta Shiga shiga à toilettes dan watsa ruwa, bata jima sosai ta fito daure da tawel
yashirya cikin Riga da skt na yan kanti sosai tayu kyau masha Allah ta fito parlour can kuma sai
tayi murmushi ta haura sama.
Sadiq na Shiga daki saman bed ya fada tare da lumshe ido, yana maida numfashi a hankali
wata irin tsanar fatuha na ratsashi ware sexy eye's dinshi yayi tare da tashi tsaye, ya je gaban
fridge ya bude ya curo fresh milk ya sha sannan ya fara jin zuciyar shi ta daina kuna, ya tashi
ya cire uniform dinshi yashiga toilettes .
*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★
http//,mobile. Facebook.
Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red
opare-speed_dial_yn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com
*hehe qawalliya roman jaba wannan page naki ne amal*
35_36
A hankali ya murda handle din kofar toilet ya zura kafar shi ji kake suuuu gwajaf yayi faduwar
yan bori, fatuha da ke maqale bakin kofa ta kasa kunne jin faduwar sadiq ya sata bushewa da
dariya har da rawar tanbola dan shauqi bude kofar tayi ta shigo bedroom din tana shigowa ta
qara fashewa da dariya, saboda zaman da sadiq yayi a qasan toilet qarasowa tayi bakin toilet
din, a hankali sadiq ya dago sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha wani irin kallo ya
wurga mata dariya ta kumayi tare da bala mai harara, ah me kyau ansha qasa dariya ta kumayi
tare da gyara tsayuwa toh me kyau bari na kirama hajiya ta kirama mai dauri saboda nasan ka
goce koka kare ta qara bushewa da dariya ,sadiq ko cije lips yayi yana jin wani irin radadi da
tsanar fatuha na ratsa shi kallan banza ya wurga mata yana qoqarin tashi amma ya kasa wani
irin radadi qugunshi ke mai, cije lips yayi ya zauna dan baya iya tashi dariya fatuha tayi tace,
"Kwarankwatsi baka iya tashi Qur'an ka bugu ba kadan ba qila ma ka kare ko ka goce", dariya
ta kumayi ta nuna idanuwan ta da yatsu biyu sannan ta nuna idan sadiq Wanda ke binta da
kallan tsana, daure fuska tayi tace ka tuna turani da kayi dazu a matatakala na fadi? toh Allah
ya isa ba kasan wacece fatuha ba ko? kaje kauyan wudil ka tanbayi *wacece fatuha diyar baffa
jauro qawar fatsima*, sannan ta qara fashewa da dariya ta ce "Kuma daga yau zan fara nuna
ma irin kallan haukar fatuha ,kuma wallahi kasani fatuha ba'a mata abu ta hakura ko ta
dangana, a lokaci ba hakuri nayi ba shi yasa na rama, ta bala mai harara tana qoqarin fita,
sadiq ko wani miyan bakin ciki ya hadiye yana jin wani irin bakin ciki ,ji yake kamar ya tashi ya
shaqe fatuha har sai numfashin ta ya kusa daukewa ya sake ta lumshe idanuwan shi yayi.
Washe da baki fatuha ta fito daga part din sadiq sai da ta dai daita kanta sannan ta fara matsar
kwallar gulma, bedroom din mom ta nufa tana yarfe hannu a hankali ta bude kofar mom ta
hango kwance saman bed tana karanta azkar, cikin na tsuwa ta shigo tana matser kwalla mom
ce ta dago su kayi 4eye's da fatuha murmushi ta saki tana qoqarin tashi ta ce, fatuha qaraso
mana jikin kofa ta qara