Showing 51001 words to 54000 words out of 99609 words
Chapter 18 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
k'owa, inda sabo ya saba d'ama shi
mutun ne ba mai san hayani ya b'ane part nashi ya wuce tare da shigewa bathroom ya sheqa
wanka,y ana fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jalabiya white ba qaramin kyau ta mai ba ,
fitowa yayi d'aga part din na shi ya wuce men parlour direct dinning area ya wuce abinci ya
zuba dan ka dan shinkafa da miya ce tasha k'ayan had'i loma biyu zuwa uku yayi ya ture plate
din dan kwata kwata b'aya jin d'adin jikin shi gaba ki daya ,yayi missing din jidda b'ama ya
ganewa yayi missing nata sai ya je bacci zai ji bed din wayam sai dai yayata juyi har ya samu
bacci ya dauke shi, gashi b'aya so ya je gidan Anuty bilki yasan yana zuwa zata ce Jidda ta
kawo shi shiyasa yake h'akura bangaran su mom ko duk san da ya tanbayi ranar dawowar su
sai mom ta ce sai sun gama abinda suke.
Jiki ba kwari ya k'oma part din shi, wata irin fever yake ji sama sama ga qirjin shi na mai zafi,
magani ya cura d'aga bedside drowe ya sha sannnan kwata ta tare da rufe jikin shi da blanket.
Asuba ta gari fatuha na tashi ta tsala wanka tare da gabatar da sallah, Sannan ta koma bacci
cike da kewar su inna dan g'abaki d'aya yanzu kauye take so ta koma, zama gidan yanzu ya
fara hawar mata kai abu d'aya ke mata dadi yanzu shine in malam ya zo k'oya mata karatu
shima da sun g'ama ya tafi zata shigo gida kamar maya gaskiya ta gaji da irin wannan rayuwar
gashi kwanan ta lura mai kyau ko abinci baya ci, anya yana gidan ma kuwa ba ita ka dai suka
bari ba Sannan ta ja dan guntun tsaki tare da gyara kwaciyar ta.
Ba ita ta tashi ba sai kusan karfe 10:30 brush kawai tayi tare da gyara gashin kanta ya
kwanta har gadan baya, Sannan ta fito parlour sanye da gwon black mai kyau masha Allah
fatuha tayi kyau ga wani haske da ta qara, gashi kullun yan matan ci bayana yake a jikin
ta. Jin bata ji kamshi bane yasa gaban ta ya fadi leqawa kitchen tayi taga wayam ba rabi'a ba
alama d'an bata rai tayi ta d'awo parlour tare da wucewa dining area bule kulolin jiya ta fara yi
jiya ma k'usan ita ka dai ta ci abincin dan guntun tsaki ta kuma ja tare da kwashe kayan ta wuce
kitchen, gyara kitchen d'in ta shiga yi sai da kitchen din ya fita tas Sannan ta d'aura ruwan zafi
k'an wuta ta fita sai da ta gama gyara k'o ina Sannan ta dawo kitchen ,ta juye ruwan zafin cikin
Plack's sannan ta soya kwai ta juye a plate ta rufe yan ciki ta fido a fridge suma ta wanke ta
gyara ta d'aura a tukunya t'are da gyara k'ayan miya ta zuba da k'ayan kamshi tuni kitchen din
ya gwaraye da k'amshi d'adi, parlour ta fito tare da haurawa up stair's a hankali ta murda handle
din kofar part din sadiq wani irin sanyi da kamshi dadi suka doki hanci ta, lumshe id'o tayi tare
da ware su tare da qarewa parlour k,allo tsit parlour ba k'owa, h'akan ya tabatar mata da mai
kyau ya tafi wajan aiki kofar bedroom ta nufa tare da bude ta a hankali ta shiga d'akin k'amar
yand'a ta saba, sanyi AC ne kawai ke tashi sai kamshi k'ayan d'akin ta fara tatarewa duk da
d'akin ba wani dati yayi ba blanket ta janyo zata linke sai taji anja, ware ido tayi waje tare da
fara jin tsoro ko lafiya qara jan blanket din tayi taji anja dawowa tayi gaban bed din tayi ta tsaya
a hankali ta kai hannu duk da zuciyar na dukan uku uku saboda tasan yau Tuesday sadiq na
zuwa office kuma b'aya kai wannan lokacin bai fita ba, a h'ankali ta sa hannu ta fara yaye
blanket din dai dai fuskar sadiq taja ta tsaya Chak, saboda ba abinda sadiq yake sai rawar dari
.cikin rudewa fatuha ta ce "Mai kyau me ya same ka?" ta fadi bakin ta na rawa inbada rawar dari
ba abinda ya ke sai hawayan fever d'ake bimai fuska dan ko magana be iyawa sai ma rintsa ido
da yayi yana qoqari janyo blanket ya rufe jikin shi, riqe blanket din fatuha tayi har da yar kwalata
mai kyau dan Allah me ke damu ka hannu ta kai ta taba goshin shin wani irin zafi taji rau take
nan ta hau reramai kuka duk fever da ke jikin sadiq sai da fatuha ta dan bashi dariya, saboda
yadda ta rude sai ka ce yau ta fara ganin ana fever amma sai ya guntse dariyar tare da qara
lumshe ido dan bai San ganin wannan kukan ko mutuwa yayi ai sai h'aka fita tayi d'aga d'aki
ganin zaman be fishe ta, tana zuwa bakin k'ofar fita suka ci qaro da ola shima zai shigo ya ji ko
lafiya Oga bai fito ba ganin fatuha na kuka yasa shi tsayawa tanbayar ta lafiya kora mai bayani
kawai tayi sannan. Shima ya haura sama part din sadiq wayar shi dake aljihu ya Ciro ya kira
doctor yakub Sannan ya zauna saman sofa fatuha kuma na zaune kusa da sadiq tasa ruwan a
ruba da towel tana dadana mai akai saboda jikin nashi ba qaramin zafi yayi ba cikin 15 minutes
doctor ya qaraso gaishe shi fatuha tayi tare da matsa mai ya zauna, shi kuma ola ya fice , duba
sadiq ya Shiga yi yan rubuce rubuce yayi tare da gwada BF din shi ya hau sosai kallan sa
doctor yakub yayi tare da gwada kai ya curo allura ya mai fatuha dake gefe sai ka ce ance ita za
ayima wa hada su rutse ido dan ba abinda ta tsana k'amar allura, bayan ya kamala duk abinda
yake Dr yakub ya juyo cikin fara'a yace insha Allah anjima zai tashi kuma insha Allah fever zata
sauka k'arki d'amu anjima zanzo, mai da magunguna dan Allah inya tashi ya samu yaci abinci
dan babu alamar ya ci abinci idan zan d'awo zan dawo da ledar ruwa to fatuha ta ce mai tare da
mai Godiya ta rakoshi har b'akin kofa ta koma ciki. Ko da ta koma ciki ,kitchen ta shige ta
qarawa farfe Sun da take ruwa Sannan ta koma part din Sadiq leqa fuskar shi tayi ganin yana
bacci yasata sakin ajiyar azuciya tare da taba goshin shi Alhamdulillah zazzabin ya sauka
Sannan ta rage gudun AC d'aki ta fara gyara part din.
*_kuyi h'akuri da wannan page din nayi typing na shi sabod'a masoya masu san ji d'aga gare
ni insha Allah gobe zan maku sweetest page_*
*_taku har kullun salma mas'ud nadabo_*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*_Writing by_*
*_salma mas'ud nadabo_*
*_Edit by_*
*_Raheenat_*
*_REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM_*
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com-Real-Hausa-fulani-writers-forumRHFWF-173984973194167/?refid=5
2&red=opare_speed_dial_&yn=H-R
*_Email_*
realhausafulaniwritersforum@gmail. com
*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
61_62
Sai da ta g'ama gyara part din tsaf sannan ta koma kitchen, lokacin har farfesun yayi ta juye a
kula tare da plate ta zuba a tray tare da bread a hankali take taka upstairs saboda ta cika tray
din da kayan abinci, baki kofa ta aje tray din Sannan ta bude k'ofar ta shi har cikin bedroom ta
aje a stool qar'a leka fuskar sadiq tayi a qaro na biyu murmushi ta saki tare da zama gefan shi
tana kallan yadda sajan shi ya kwanta luf har mamakin kyau irin na sadiq take ,sai dai yayi yar
rama sannna fuskar tayi fayau dariya tayi tace "Ohni sangami ciwo yayi k'amu k'ayi bulun buqwi
tunda likita ya tsulama allura kaji zafi sai bacci k'ake qila ma suma kayi saboda zafi, yadda kayi
bacci kamar ba masifafe ba amma da ka warke zaka fara cika mana gida da tsuwa na huta da
masifar ka ko ta kwana biyu ce wallahi um bari na lalaba naje nayi wanka a toilet din ka tunda
kai ka zama gawar shanu dan tashin ka ba yanzu.
Tashi fatuha tayi ta bude wardrobe ta Ciro qaramin towel ta tare da rage k'ayan cikin tasa towel,
duk wannan abinda fatuha keyi duk a kunnan sadiq dan ya d'ade da tashi kawai dai yayi lamo
ne toilet din ta shige ta sheqa wanka ta fito ko da fito cikin sanda take tafiyar har ta qaraso gefe
bed leqa fuskar sadiq tayi tana riqe da qaramin towel tana goge gashin kanta, Allah sarki ba
wan Allah sai bacci kake b'aka san wainar d'ana ke toyawa ba wai da zaka tashi d'ana sha
masifa, yarfe gashin k'anta tayi wanda hakan yasa ruwan gashin ya watso ma sadiq a fuska dan
motsa ido yayi hakan yasa fatuha zaro ido tare da yin lamo tana zare ido tana yar fe hannu
ganin ya juya ya gyara kwaciyar shi ya sata sakin a jiyar zuciya baki dressing mirror din shi ta
tsaya tana k'allan mayu kan d'ake baje akan dressing mirror tsuru tsuru tayi tana tunanin man
da zata shafa can ta kai hannu kan wani mai na gashi k'asan cewa fatuha ba boko yasa ta
d'auka ta fara shafawa sadiq dake k'allan ta ta qasan ido sai dariya yake guntsewa in taqaice
maku duk wani mai d'ake saman dressing mirror sai da ta shafa dan taji ya mai kyau ya ke ji
Sannan ta fita d'aga d'akin, tana zuwa bedroom din kaya tasa sadiq d'ake d'akin d'ariya yayi
sosai har da riqe ciki dan guntun saki ya ja tare da cewa "Yar kauye kawai Sannan ya tashi a
hankali duk da har yanzu b'aya jin karfin jikin shi" waka yayi Sannan ya fito yasa jalabiya ash
mai kyau Sannan ya gabatar da sallolin shi, yana idawa ya qara koma wa ya kwanta dan karfin
hali kawai yake.
Sket da riga tasa na atamfa mai ratsin dark green da coffee sai gyara gashin kanta da tayi
tare da yin ture ka ga tsiya, Sannan ta qara fesa turare rufe bedroom din tayi ta fito Sannan ta
haura upstairs direct bedroom din sadiq ta shige kwance ta gan shi amma sai dai wannan
lokacin idanuwan shi biyu murmushi ta saki tare da qaraso wajan shi cikin sanyin murya tace
"Mai kyau ya jiki?" lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha jim yayi yana qare mata kallo ba
qaramin kyau tamai ba musanman dan qaramin lips din ta pick kauda kai yayi tare da cewa da
sauki ya lumshe ido smile ta kuma yi tare da janyo tray dake saman stool ta cigaba da saving
nashi cikin natsuwa kasan cewa tasan be cin abinci , shiyasa ta zuba mai farfesun yan cikin
k'adan ciki dan ball,
Cikin sanyi murya ta kuma cewa "Mai kyau" ware sexy eye's ball's din yayi ya qara sauke su
kan lips din ta cikin shagwaba da sanyi murya tace "Mai kyau dan Allah ka ci farfesun nan ka
ga likita yace ka ci abinci" hade rai sadiq yayi tare da lumshe ido tare da yin magana cikin cool
voice nashi yace "Bana jin yunwa fatuha" dan bata rai tayi tare da rausaya kai tace "Dan Allah
k'aga ko akauye inna in bani lafiya in banci abinci ba har dure take min dan na samu lafiya ka
ga yanzu mom bata nan bale ama dure dan Allah ka ci ta ida zancan tana rausaya kai tana
k'allan sadiq dake kallan ta kamar qaramin yaro" qara hade rai yayi yace "b'afa naci leave me
alone pls" zaro ido fatuha tayi tace "Kai kasan wannan" murmushi yayi wadda be yi niya ba
yace "Fatuha wai yaushe zaki waye?" dariya tayi tace "Sai ranar d'ana fara zuwa boko ka ga da
jidda nan ita ke koyamin yanzu kuma tana gidan Anuty bilki ta ida zancan tare da yin raurau da
ido" ai ta kusa dawowa kin ji um to kina san karantun ne, bai ida rufe bakin shi ba Dr yakub ya
shigo, cikin salama tare wurgawa sadiq harara d'ake kwance gaisheshi fatuha tayi har qasa
sannan ta dau ball din farfesun ta aje a tray tana qoqarin fita, ah wai fita zakiyi da kin tsaya ai
murmushi fatuha tayi tace "Ina da abinyi ne a kitchen shiyasa ok wannan abincin fa nawaye
kallan sadiq tayi dake ta faman aika mata harara tayi tsaye tare da sada kanta qasa ,juyowar Dr
yakub yayi su kayi ido hudu da sadiq mtww h'aba captain me yasa kake haka ne please wai
bana sha fada ma ba ka rage damuwa um saboda tsabar damuwa ka daurawa k'anka hawan
jini, me yasa kake abune kamar Mara tawakali ai kowa ya Sani duk me rai mamaci ne tunda
kausar ta bar duniya ka daina walwala ka maida zuwa asibiti kamar zuwa kasuwa haba captain
ko Dan lafiyar ka da matsayin ka ka hakura da wannan tunanin please, lumshe ido sadiq yayi
k'amar yakub na magana da dutse tsaki Dr yakub yaja yace "To wannan abincin da k'aqi ci me
hakan ke nufi?" ware ido yayi yana aika ma fatuha da harara dan shi kwata kwata be buqatar
wani abinci a cikin shi amma saboda tsabar naci irin na fatuha yanzu ta sasa ya ci abinci dan
guntun tsaki yaja yana kalla yakub dake ta masifa yanzu ka daure ka ci abinci ko nama alura ai
dai ba saina fadama ila da alura kema mutun ba inbai ci abinci ba, duk yadda ya so ya kwace
ma qincin abinci sai da yakub ya takura mai ya sha farfesun k'adan ba tare da bread ba ba laifi
farfesun ya mai dadi duk da b'akin shi ba test aje ball din yayi fatuha ta dau tray din ta fita alura
Dr yakub ya mai tare da daura mai ledar ruwa saboda ya lura sadiq be san cin abinci yana
lafiyar ma yaci kadan bale yanzu.
Dawowar fatuha ce tasa Dr miqewa yace "To ni zan wuce dan Allah ki kulla da cin abincin shi
inbai ci ba ki kira Anuty bilki ki fada mata ai yasan halin ta" d'aga kai fatuha tayi sannan ta
taimakamai da daukar mai briefcase din har sai da suka zo b'akin kofa ta mai sallah ta rufe
gidan bedroom din sadiq ta kuma dawowa harara ya bita da shi sannan ya ja saki murguda mai
baki itama tayi tare da zama saman sofa, keee wakike murgudawa baki rau rau da ido fatuha
tayi tace "Bada kai nake ba" D'awa kike to? ya fada cikin sigar masifa um ba da kai nake ba
wallahi mtww wallahi karki bari na tashi dan na tashi saina karkaryaki, bama na hana ki yawo ba
hijabi ba eh amma ai a waje ka ce ba'a gida ba,yaja tsaki mtww sannan ya juya ya lumshe ido.
*_Taku har kullun salma mas'ud nadabo_*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*_Writing by_*
*_salma mas'ud nadabo_*
*_Edit by_*
*_Raheenat_*
*_REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM_*
★We are the best★
http/Mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=,H-R
*_Email_* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*_Facebook_*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
63_64
Juya b'ayan da sadiq yayi yasa fatuha jan dan guntun tsaki tare da kallan agogan dake maqale
a bango kusan karfe 8:30 na dare, tashi tayi ta bar part din ta koma part din su tana shiga
bedroom din ta rage kayan jiki ta tare da shiga toilet ta sheqa waka ta fito daure da towel ko
shafa mai ba tayi ba ta bude wardrobe ta Ciro kayan baccin ta riga da wando pink masu Mayan
flowers da zanan ya'yan cartoon d'aure gashi k'anta tayi da wata yar kibiya ta d'aure kai sannan
ta fesa turara har zata kwanta sadiq ya fado mata a rai ta barshi a d'aki shi ka dai ,gashi baya
da lafiya tashi tayi zubur zata fita sai Kuma taci birki tace "Ko naje tijara zai mun dan ba mutunci
gare shi ba" karma ya tsinka ni wata zuciyar tace haba fatuha duk rashin mutuncin mutu be
lafiya ai dole ya shafa wa mutane lafiya riqe handle din kofar tayi kamar me na zari can kuma ta
bude ta wuce part din sadiq ta shiga dakin har yanzu bacci yake parlour ta d'awo ta kuna kallo
dan ba wani bacci take ji ba cikin jin dadi take kallan arewa24 suna shirin tarkwan kauna gaba
ki d'aya film din ya mata d'adi sosai sai da aka kamala film din misalin karfe 10:00 na dare
sannan ta leqa dakin sadiq b'akin bed din ta tsaya tana qaremai kallo a hankali ta kai hannu
zata taba goshin shi amma ta k'asa sai dunqwule hannu tayi tana nazarin jikin naji ganin ya
motsa ya sata gyara tsayuwa tana kallan yana yin shi lumshe ido tayi a hankali ta kai hannu ta
goshin sadiq ji tayi zafi rau kamar