Showing 30001 words to 33000 words out of 99609 words
Chapter 11 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
har da jikoki,
dariya tayi tace "Ya za'ayi na tsufa bayan mijin kullun yaro yake komawa" hancinta ya ja cikin
tsokana , um next week zan koma uk kan maganan gaskiya this time around ban tafiya ni ka
dai, tare nake so mu tafi murmushi mom tayi tace "Kamar kasan abinda ke raina kenan smile
yayi um kuma sai gashi na rigaki fada ba, ya ida zancan tare da yi mata kiss a kumatu, ni ko
abban sadiq kunyi waya da jawad kuwa? dan murmusawa yayi yace "Eh jiya munyi waya ya ce
min yanzu shukura tsohhon ciki gare ta, so yake in ta haihu sai su zo ganin gida murmushi mom
tayi ,Allah ya sauke ta lafiya kamar kasan nayi missing nashi wallahi ya kamata jawad ya dawo
Nigeria da aiki amma nasan ba lalai ne yazo ba saboda na lura yafi san London sosai , um ke
dai ki ce danki kike san gani yauwa gobe ki shirya ina so muje wajan ammi muyi masu sallama
kafun mu tafi ,to tace mai tare da tashi zata fita janyo ta yayi jikin shi please in kinje karfa ki
dade ki bar tsohon mijin ki da jira kinji murmushi tayi tare da kashe mai ido.. lol ah tsofafi na
konewa hehe.
( shawara ga mata please mata ya kamata musani tsufa baya hana soyayya karki ce dan kina
da manyan ya'ya ki ce ke kin girma ita soyayya bata girma, kuma gyara da tatalin miji shi ke
qara dankwan soyayya, so da yawa wasu matan suke jawa maza jansu bin mata saboda kina
ganin kin girma komai sai ki daina ,in mijin ki mai so ne daga nan zai fara bin ya'ya cikin shi a
waje suna mai yana jin dadi please mata mu kiyaye) .
Fatuha da ke zaune saman kujera tana kallo, mom ce ta sauko daga upstairs, cikin ladabi
fatuha ta gaishe ta tare da tuna mata maganar gyaraan kai , toh shikenan je ki shirya mu tafi ,
mom bada wannan kayan zani ba eh kisa kayan gida toh tace mata ta shige bedroom , mom ko
part din abba ta koma ta tanbaye shi zata fita ya bata izini, sannan ta dawo dakin ta ta shirya
cikin atamfa black mai ratsin red n yellow bubuce mai kyau tuni mom ta fito sosai bedroom din
fatuha ta wuce tsaye, ta same ta ta rasa kayan da zata sa washe da baki mom ta qaraso, fatuha
har yanzu baki shirya ba shagwabe fuska tayi taca "Wallahi mom na rasa kayan da zansa ne,
zabamin dan Allah "to tace mata wata hadadiyar gown mom ta janyo brown colour mai ratsin
milk da Stone's a jikin rigar mai dogwan hannu ce sai veil milk , masha Allah fatuha ba qaramin
kyau kayan suka mata ba cib suka mata qirjin ko kamar tasa bara saboda yadda kayan suka
mata rolling veil din tayi da gashin ta data daure sai abin ya bada kala ta fito fes, takalmi tasa
black mai kyau suka fito , direct parking space suka wuce mom ta jasu suka fita sai fatima
salon da ke gandu.
Basu wani dade ba a Solon din ba sosai an gyara gashin fatuha Dan ko ba'a sa mai ba
saboda laushishin gashin ta dan in aka sa mai, ze iya konewa gyara shi kawai akayi masha
Allah ita kanta fatuha sai da ta tsorata da gashin ta saboda har qugunta ya kai, da yaji gyara
amma sai ya rage yawa su Kansu yan wajan yaba gashin su kayi ana gamawa suka dawo
gida, a parking space mom tayi parking suka fito har zasu shiga gida sai ga driven jidda ya
kunno kai yayi parking da gudu jidda ta qaraso tare da rungume fatuha tace "Anuty kinyi kyau
,waya maki kawalliya?" dariya fatuha tayi dan ita ba Wanda ya mata kwalliya daukar jidda tayi
suka qaraso parlour sadiq na zaune saman two star yana shan coffee gefensa kuma baba
jinmai ce tana dan taba hira da shi da alama tafiya zatayi.
Cikin sallama suka qaraso, sadiq ya amsa sallamar, fatuha ke dauke da jidda , jidda ta zame
daga jikin ta ta Ruga wajan sadiq ta rungume shi wasa ya shiga yi mata tana dariya qarasowa
Mmy tayi ta zauna saman three star ta ce "Oya a wuce aje a cire uniform, kin bar Anuty na jiran
ki " sadiq ne ya dago ya kalli fatuha ya wani tabe baki tare wurga mata harara ya miqa mata
jidda, baba jinmai ko sai yaba kyan da fatuha tayi take tare da yima su mom sai da safe fatuha
kuma ta ja jidda zuwa bedroom.
*Taku har kullun mai qaunar Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
* *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refi
d=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com
*fan's ana mugun tare dinnan sosai*
39_40
Bayan ta gama ma jidda wanka ta shafe ta da mai tare da saka mata kaya jeans n t-shirt tasa
mata.. riga pink wando bleu sannan ta gyara mata gashin ta. Aiko tuni jidda tafito tayi kyau
masha Allah. toilet ta koma ta dauro alwala kasan cewa 4:00pm tayi ita da jidda suka gabatar
da sallah suna idarwa fatuha ta cire veil din kanta tana kallan gashin ta a mirror tana washe
baki, jidda ce ta ce "Anuty gashin kine haka.. jiyowa fatuha tayi washe da baki tace "kema kin
gani ko. Ai Allah daga yau na gama yawo da dankwalli wallahi wannan gashi kamar ba nawa
ba. "gaskiya Anuty kina da gashi dama ki qaramin.. Jidda ta ida zancan tare da washe hakura..
Murmushi Faruwa tayi tare da maida dakwallin ta janyo hijabinta dana jidda suka wuce wajan
malam
Sosai suke karatun. Damma karutun ya zo ma fatuha da sauki dan duk wani qari da malam ya
mata jiya ta juye mai shi.. Shikansa yana yabawa da qoqarinta.. qara musu yayi. Dan haka
basu suka shiga gida ba sai 6:00pm
Sadiq dake tsaye gaban dress mirror yana gyara sumar shi a hankali ya ji anbude kofar
dakinsa... Aiko cikin zafi rai ya juyo a tunanin fatuha ce ta zo mai da wani saban rai ni sai
idanuwan shi ya gane mai majid...
bata fuska yayi tare da juya mai baya.. smile majid yayi ya qaraso with full confidence nashi ,
"big man fushi kake dani ko.
kauda kai sadiq yayi ya nufi wajan drowe yana ciro kayan shi.
murmushi majid yayi tare da zama saman sofa tsaf.
sadiq ya gama shiryawa fuskar shi daure ya dau phone inshi da ke bedside drowe. ze fita majid
ya riqe mashi hannu tare da shagwabe fuska sorry bros, juyawa sadiq yayi ya wurga mai harara
"leave me alone tare da fisge hannu shi ze murda handle kofar kenan majid yace, "haba sadiq.
am sorry nine fa majid. juyawa sadiq yayi ya kalle shi , ya qara bala mai harara "kasan da haka
shine ka manta dani ko. "sorry kasan bana zama sosai shiyasa amma ai na kusa dawowa nan
da aiki. Kaga dawo ka zauna muyi magana.
Jin hakan yasa sadeeq sakin handle din ya dawo ya zauna , "baby meya samu qafar ka naga
kamar kana dingishi
jan tsaki sadiq yayi ya ce "tsautsayi ne kawai.. "eyya sorry , " Tashi muje parlour na gaji da
zama a bedroom, "OK.. Majid yace
parlour suka koma suka dasa sabuwar hira basu suka daina hira ba sai magrib.. dauro alwala
sukayi tare da wuce wa masallaci
"Anuty.
"na'am... "dan Allah ki koyamin qarin dazu ban iya ba sosai, "to shikenan nima zaki koya min
na boko ko. "eh zan koya maki mana Anuty. "To bari mu fara yin sallah
Tashi sukayi tare da dauro alwala suka gabatar da sallah bayan sun idar fatuha ta qara
biyawa jidda karatun sannan jidda ta fara koyawa fatuha ABCD karku so ku ga... kwamatsala da
kyar da kyar ta dan iya shima ba sosai ba amma tasa ma ranta sai ta iya ko dan ta rinqa jin
abinda sangami ke cewa wani locaki
Bayan sun dawo masallaci majid ya fada two star "wash am tied...
Guntun tsaki sadiq yace "kai dai Ka bani daga zuwa masallaci har ka gaji sai ka ce ba namiji ba
mtss.. fruit ya curo a fridge ya fara ci majid ya zuro hannu suna ci suna hira, "ni fa kaga wallahi
na gaji da wannan gwaranci aura zan zo nayi wallahi..
smile sadiq yayi ya ce "aiya kamata kam,
"aikaima ya kamata kayi wani auran sadiq.. Duba da yau kusan shekara kausar 5 da rasuwa.
sadiq ya kamata kayi aure haka ko saboda angel.. bata fuska sadiq yayi yace, "majid bana
tunanin zanyi wani abu wai shi aure yanxu. tunda na rasa kausar na rasa wani bari na
rayuwata. majid kafin a samu mata kamar kausar sai antona.. kausar tatara komai dana ke so
agun mace. bana tunanin akwai wata ya'mace da zata iya maida gurbinta... ya ida zancan
hawaye masu zafi na zubomai,
kallan tausayi majid ya mai da cewa. "sorry baby. na famama inda kema ciwo ko. girgiza kai
yayi tare da goge hawayan shi da bayan hannu yayi smile yace .. "majid baka famamin komai
ba. indai tunanin kausar ne ba yau na fara ba. yau kusan 5 year da ita nake kwana da ita nake
tashi majid , murmusawa majid yayi tare da qoqarin canza topic dan a duniya ba abinda ya
tsana irin damuwar sadiq haka shima sadiq ba abinda ya tsana irin damuwar majid , kallan ball
suka shiga yi tare da yin musu dama sun sama ba yau suka fara ba damma yanzu sun girma
ne. dada ne har kuka sai Sadiq ya sa majid cikin nishadi suke kallo
"Kinga zo muje mu ci abinci muyi sallah na maki wanka kafin baban ki ya biyo mu. washe baki
jidda tayi parlour suka koma dining area suka wuce fatuha ta fara saving nasu tuwo shinkafa ce
miyar taushe taji Alayahu da kaji cikin nutsuwa suke ci a plate daya...
bayan sun kammala fatuha ta kwashe kwanikan ta kai kitchen jidda kuma ta haura upstairs dan
tayi missing daddy tun da ta dawo daga school bata qara ganin shi ba. bata iya jira har sai an
mata wani wanka. a hankali ta murda handle din kofar a zaune ta gansu a parlour rugawa tayi
jikin majid tana cewa. " small daddy I miss u.. smile majid yayi. "miss u angel how are u, "fine
uncle , sadiq ne ya murmusa yace "ni fa yanzu fushi nake da angel tunda tayi new Anuty take
mantawa da daddy. bata fuska tayi kamar zatayi kuka "uncle bafa haka bane new Anuty na da
kirki kuma tana min wasa kuma kasan wani abu daddy sai ta zamo daga jikin majid taje ga
Sadeeq tahau yimai rad'a akunne. jin abinda take gayamai yasashi yin wani killing smile...
{Wanda koni Salma ban san me jidda take cemai ba,}
"Na zo maki da ice cream amman tunda dadynki kawai kika fadamawa bana baki ice cream
din.
Jin abinda majid yace shiyasata tsalle tana kuka sai ya bata ganin da gaske kukan ta ke sanyi
na gaske shiyasa shimata ta bari se ze tafi ya dauko mata.. washe hakori tayi tace "thank u
small daddy tare da yimai pack tanamaici gaba da cewa.. Aunty bata San na guduba dan
wanka zata min fa.. murmushi majid yayi ya ce "to diyar Anuty kice ina gaida Anuty.
kallan shi sadiq yayi a zuciyar shi yace da kasan wacece fatuha da ko hanya daya baza ka so
ta hada ku ba balle kuma wata gaisuwa tabe baki yayi tare da jan tsaki ciki ciki
Tana fitowa daga kitchen ta fara neman jidda ba ita ba alamar ta upstairs ta haura saboda tasan
bata wuce part din sadiq tana last stairs kenan sai ga jidda ta fito daga part din washe da baki
murmushi fatuha tayi tace.. "shine baki jira na maki wanka ba sokike daddy yamin fada ne...
girgiza kai jidda tayi fatuha ta dauke ta direct bathroom ta dire ta ta fara yi mata wanka sai da ta
wanke ta tas sannan suka fito ta aje ta saman bed ta janyo lotion da night dress din jidda sai da
ta shafe ta dashi. sannan ta zura mata kaya
"Big man bari na zo na wuce dare nayi.
"tun yanzu dare be wani yi ba na dauka fa kwana ka zo min wallahi kaga mun dade bamu hadu
ba. murmushi majid yayi.. yace "next time zankwana.. "To shikenan.
har bakin mota ya raka shi ya Ciro ice cream din jidda ya bashi "gashi aba angel nasan Anuty
ta maqale ta shiyasa bata fito ba ka shafa min kanta , "ok ka gaishe min da Umma da ammi "to
zasu ji Alhaji da baba fa me suka tsarema da baza ka ce a gaishe su ba... dariya sadiq yayi tare
da kai mai duka "wallahi majid ka rainani tunda na ce a gaida mutan gida ai suma sun shiga,
harara majid ya bala mai ba "waninan ammi da Umma kawai ka ce kuma da yaushe ma ka
girmeni har kake fadi na raina ka , harara sadiq ya qara wurga mai aidai na baka 4 hours ko
qarya nayi. Ya qarashe tare da hade ran wasa. dariya majid ya fashe da ita tare da ba mota
wuta.
Sai da safe ace ma mom na zo tana part din abba. "Toh sadiq yace mai da daga mai hannu har
sai da motar shi ta fita sannan sadiq ya koma cikin gidan ,
dauke da jidda fatuha ta fito. Aiko nan take sukaci karo da sadiq a parlour...
B'allama fatuha harara yayi da kauda kai...
Itako tayi kamar bata gani ba. yana gaba suna bayan shi jidda na zuba surutu suna shiga part
din a parlour fatuha ta aje jidda tana qoqari fita
"keee.. Yace da Ita.
Nan taja birki ta tsaye zuciyar ta na duka uku uku dan bata manta rashin kunyar da ta mai ba da
safe ,"ba dake nake magana. ya fadi cikin daka tsawa. juyowa tayi tana zare ido , "kije kitchen
ki hada min coffee ki kawo min.. zaro ido fatuha tayi waje um kwarankwatsi ban san me hakan
ba. tsoki yaja mtss "yar kauyan banza toh burni nake nufi tea mara madara zaki hadu ki kawo
min karki sa sugar a ciki.. ya ida zancan tare da balla mata harara abin ma dariya ya so ya ba
fatuha wani lokaci sadiq in yana harara kamar qaramin yaro a zuciyar ta tace bema san idan
yana fada wani qara kyau yakeba
ta dan ja tsaki ta fita.. saida ta gama hada mai ta kai mai yana zaune parlour yadda ta barshi
jidda na saman cinyar shi da alama bacci ya dauke ta hannu ya miqa ze amshi coffee tana
bashi ya saki cup din ya fadi gaba daya ruwan tea din ya zube mata a kafa wani irin ihu fatuha
ta bude baki zatayi janyo ta yayi tare da to she mata baki yana kallan ta ido cikin ido
idanuwanan tana sun ciko da kwalla hawaye daya nabin daya..
murmushi yayi komin banza ya sata kuka gashi matsar da yayi ma bakin bana wasa bane dan
bakin sai radadi yake mata sai da tayi kuka san raita sannan ya sake ta tare da hankada ta ta
fadi kasa sannan ya tashi ya kashe kayan kallo ya matso gaf da ita har tana jin saukar
numfashinshi yace cikin cool voice na shi "wannan ka dan na maki akwai saura nan tafe.. ya ja
saki tare da daukar jidda sai da ya kai bakin kofar bedroom ya juyo tare da yin killing smile din
shi yacigaba da cewa. "kuma ki tabata kin gyara gurin kafin ki bar wajen.. Yana fad'in hakan ya
shige bedroom ya barta tana matsar kwalla tare da jera mai Allah ya isa, kuma indai gyara
gurine wallahi banyi mugu kawai sannan taja kafar ta wadda ta kone wajan har yayi ja bakin
tama haka saboda ya ji matsar manya
Direct bedroom dinta ta wuce tare da rage kayan jikinta
bathroom ta shige tayi wanka ta fito daure da towel tana shafa mai tana jera wda cigaba da jera
mishi Allah ya isan
A haka har ta gama shirin tafada saman bed se bacci
*Fan's kuyi hakuri da wannan page din yau bana jinyin typing din saboda ina wani dan aiki*
*taku har kullun mai qaunar ku Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★
http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANI WRITERSFORUM.com
41_42
Kiran sallah asuba ne ya tada fatuha, arwala ta dauro tare da yin wanka bayan ta idar da sallah
ta shafe jikin