Showing 45001 words to 48000 words out of 99609 words

Chapter 16 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

mata ta guntse tare da daukar jidda.


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼â€â™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Salma mas'ud nadabo*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=,52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSFULANIWRITERSFORUM.com




53_54

*Ina farin cikin tayamu marnar zagayowar wata mai Albarka,wata mai falala,wata mai dubin
nasarori da ni'imomi , yan uwa Dan Àllah kada mubari wanga babbar garabasar ta wuce bamu
samu nasarori da yake ciki,mudinga istigfari da hailala neman gafara à wajen Allah,mu yawaita
Adu'a da karatun Alkur'ani mai girma, mu dinga nafiloli da rokon Allah ya biya mana bukatun
mu na Alheri,Allah Ubangigi ya bamu ikwan yin ibada a cikin wanga watan mai Albarka watan
Ramadan Allah yasa muna da raban ganinshi Ameen Dan Alfarman anabinmu Muhammad
Sallah'llahu allaihi wa'sallam*



Sadiq na gaba tana biye dashi à baya, bakin bedroom din ta taci birki tana qoqarin bude kofar
sadiq ya juyo fuskarsa ba yabo ba falasa yace"Iina kuma zaki da ita bayan tayi bacci? um
dama wanka zan mata shafa sumar jidda yayi tare da cewa "Ki samata night dress kawai
saboda tayi nisan bacci" Allah ya taimake ta jidda ta taba fadin Kalmar shiyasa ta gane mai
yake nufi,haurawa sama yayi ita kuma ta shige daki tare da kunna haskyan dakin shin fide jidda
tayi sannan ta soma rage kaya jikinta ,sai da ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito daure da
qaramin towel cikin natsuwa ta shafe jikin ta da mai tare da zura night dress din ta riga ce pink
mai zanan cartons jikin rigar, rigar dai dai gwiwa ta tsaya sai dan siririn hannun kamar na vest
gashin ta ta sharce ya baje a gadan bayan ta bayan ta gama shirya kanta ta shirya jidda cikin
kayan bacci, sanna ta dauke ta a hankali take taka upstairs din saboda yau jidda ta qara nauyi
cikin natsuwa ta murda handle din kofar part din sadiq parlour ba kowa sai sanyi AC dake tashi
da kamshi direct kofar bedroom ta bude tsaye ta hango sadiq gaban dressing mirror yana goge
sumar shi da qaramin towel sanye yake da bathrobe white hakan yasa ana ganin lalausan
gashinshi na qafa kauda kai fatuha tayi, tare da yin sallama juyowa yayi ya qare mata kallo ,
mamaki gashin fatuha ke ba shi gashin har yaso ya mata yauwa juyowa yayi ya cigaba da abin

da yake shin fide jidda tayi tana qoqarin fita,lumshe ido sadiq yayi tare da ware su yace
"Fatuha" juyowa tayi tana kallan shi can sai tayi qasa da eye's ball's din ta, ki hada min coffee
toh tace tare da fita downstairs ta dawo tare da shiga kitchen ta hada mai coffee ta dawo, ko da
ta dawo yana zaune a parlour yana kallan news aje mai tayi saman stool tare da ficewa cikin
natsuwa ya shiga shan coffee yana kallan news amma sai dai ku san kallan news din kawai
yake ba wai dan yana fahimta ba kashe kayan kallan yayi ya koma bedroom saman bed ya
kwanta tare da janyo jidda jikin shi lumshe ido yayi ba wai dan yana jin baccin ba ,saboda gaba
ki daya kwanakin nan da tunanin kausar yake kwana.



Tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da yin addu'a bacci ko minut 10 ba tayi ba bacci
ya kwashe ta.


Kiran sallah asuba ne ya tashe ta wanka tayi tare da dauro arwala tana fitowa uniform tasa tare
da gabatar da sallah, sannan ta shafa mai da fesa turare parlour ta fito ko ina share kwal hakan
ya tabatar mata da rabi'a ta zo kitchen ta shiga washe da baki ta gaishe ta cikin fara'a ta amsa
kasan cewar yau Saturday shiyasa fatuha bata je part din sadiq da wuri ba , rabi'a ta shiga
tayawa aiki doya suka fere suka dafa sannan suka yanka fatuha ta gyara albasa rabi'a ta fasa
kwai ta kade tare dasa albasa da percil da tonka santé da tafarnuwa da sauransu.. fatuha na
kallo soya doyar da take , rabi'a da taga fatuha ta iya suyar sai ta sakar mata ta shiga gyara
fruit saboda za'ayi ma sadiq juices da su bayan ta gyara ta markada ta juyo a jug ta saka
qanqara ta kai dining area kafin ta dawo fatuha ta kamala soya doyar ta juye a kula rabi'a
shigowa tayi da murmushi tace ,"Ah sannu da qoqari" murmushi fatuha tayi ki kai kula dining ni
bara na soya kwai to fatuha tace tare da wanke hannu ta a zing ta dau kula ta wuce dining area,
bayan ta aje kulla ta dawo parlour ta kunna kallo arewa24 tana kallan gari ya waye washe da
baki take kallan dan tana jin dadin shirin ganin goma ta gota yasa ta haura upstairs tana bude
parlour zaune taga sadiq saman three star, idanuwan shi lumshe abin ya so ya dan bata
mamaki saboda be saba bacci a parlour ba sallama tayi sadiq da ke jingine kamar me bacci ya
ware sexy eye's ball's din shi kan fatuha tare da amsawa kalla shi tayi ta tabe baki tare da
gaishe shi amsawa yayi kamar be san magana fatuha ko shiga daki tayi amma sai dai yau tana
ganin suku suku da sadiq yayi, yayi yawa sai taga yayi kamar wadda be samu bacci ba tabe
baki ta yi tace ke "Fatuha ina ruwan ki?" duk wannan zancan a zuci takeyin shi tada jidda tayi
washe da baki jidda ta tashe tana cewa,Anuty good morning? murmushi fatuha tayi tare da
daukar ta ta kaita toilet ta mata kwanka suka fito suna dariya tsane mata jiki tayi sannan ta
shafa mata lotion kasan Cewar akwai wasu kayan ta a dakin shiyasa anan fatuha ta shirya ta,
jeans n t-shirt tasa mata rigar white sai jeans blue masha Allah tayi kyau sosai fita tayi daga
dakin tabar fatuha na gyara daki.


Washe da baki ta fada jikin sadiq daddy morning, morning too angel, how was ur night angel,
cool daddy n Ur's daddy same ya ida zancan yana mata pack, daddy yes sweet, um me ya sami

eye's din ka sunyi ja, lumshe ido yayi yace angel daddy ciwo ido yake, sorry daddy ,a kira uncle
yakub ya duba ka please daddy, na warke ai har ma nasa magani ,sure daddy? yes angle pack
ta mai tare da cewa daddy am Hungary, ok ina Anuty ? Anuty na busy now, OK muje nayi
feeding naki ko sweet, OK daddy daukar jidda yayi yana mata wasa tana dariya sai da suka
qaraso dining area ya ja kujera ya zauna sannan ya d'aura jidda saman cinyar shi ya shiga
saving din su sai da ya kamala ya fara feeding din jidda yana bata tana bashi cikin jin dadi.


Bayan ta gama share bedroom din tas ta dawo parlour ta kwalwale shi tas, ta kunna Burne a
socket tare dasa turaran wuta tuni part din ya dau kamshi mai sanyi gudun AC ta qara lumshe
ido tayi tare da zama saman three star tana qarema dakin kallo, ita kanta part din ya mata kyau
yadda ta gyara shi ji tayi kamar tayi bacci tashi tayi ta fita daga part din.

A hankali take sakowa daga upstairs jidda dake saman cinyar daddy ta kwalawa fatuha kira,
cikin jin dadi Anuty juyowa fatuha tayi har sai da gashin ta iska ta kada shi fari tayi da ido tace
"À" dariya jidda tayi tace "Daddy ka ga yadda gashin Anuty yayi lumshe ido yayi ya ware su kan
fatuha yana qare mata kallo gani yake kamar idannuwan shi ke mai gizo kwanan kullun qara
canza mai take kawar da zancan yayi ya cigaba da abinda yake, saukowa jidda tayi daga
cinyar shi riqe da doya a hannun ta fada jikin fatuha Anuty na'am bude bakin ki na baki yam toh
fatuha tace tare da bude dan qaramin bakinta ji tayi jidda ta bata ragowar doyar hannunta sadiq
da ke zaune saman kujera dining yana kallan su ta qasan ido har mamakin yadda jidda ta saba
da fatuha haka yake, tabe baki yayi ya shanye ragowar tea din da yake sha ya miqe ya wuce
su ya haura upstairs fatuha ko dining tazo ta cika tunbin ta sannan taja jidda suka koma parlour
suna cikin kallo rabi'a ta fito tare da yi masu sallama, har bakin gate suka rakata bala mai gadi
sai tsiya yake ma jidda ita kuma sai turo baki take fatuha ko dariya abin ya bata janyo jidda tayi
suka dawo cikin gida suka cigaba da kallo.


Wani irin sanyi da kamshi ya doki hancin shi part din kwal kamar ba'a kwana ciki wani irin
sanyayan ajiyar zuciya ya saki tare da sakin handle din kofar, bedroom ya shiga nan ma wani
irin lalausan smile ya saki komai ya mai yadda yake so take ya ji wani irin bacci na fizgarsa
saman bed ya fada tare da sauke ajiyar zuciya bacci da baiyi jiya ba shi ya kwasheshi.

Sun sha kallo har sun gaji ba su suka bar parlour ba sai 1:30pm shima kiran sallah ne ya
tashe su, arwala suka dauro sannan suka gabatar da sallah suna idarwa suka dawo parlour, ola
ne yayi knocking din kofa fatuha ta tashi ta bude mai washe da baki ya kalle ta, cikin hausarsa
mara fita yace madam sannu ,yawa fatuha tace , dama wannan malam min ne da ke koya maku
karatu ne ya zo yanzu, murmushi fatuha tayi ta ce malam ai ba da rana yake zuwa ba ta fadi
tana leqa waje bari ina zuwa daki ta shiga ta janyo hijabin ta tare da daura zani saboda mini
skrt ne jikin ta sannan ta fito lokacin har ola ya koma bakin aikin shi malam na zaune saman
tabirin mai gadi suna dan taba hira cikin natsuwa fatuha ta qaraso tare da gaishe shi, murmushi

yayi ya amsa, ah malama fatuha murmushi kawai tayi kinga yau na zo tun 2:00pm wallahi ina
da wata safga anjima shine nace da naki zuwa qara na zo yanzu tunda kwana biyo ba muyi
karatun ba murmushi fatuha ta yi ta ce aiko dai malam mun gode bari na kira jidda toh yace
mata tare da tashi daga tebirin bala mai gadi ya koma inda suke gabatar da darasin, fatuha na
shiga gida tasa mata hijabin ta suka fita.

Cikin jin dadi suka gabarta da darasin su inda malam yayi masu qari tare da yi masu yan
tanbayoyi suka bashi amsa sai da ya tabatar sun gane misalin karfe hudu ya sallame su, ya
wuce akan cewa gobe karfe hudu zai zo insha Allah littafan su suka kwashe suka shiga gida
dama daure da arwala fatuha take sallah ta gabatar sannan ta cire zanin ta shiga wanka tana
fitowa daure da towel ta tsane jikin ta tare da shafa jikin ta da lotion har ta dauko uniform din ta
zata maida ta tabe baki, tunda na gama aiki ai sai na sa na gida dan ni na fara gajiya da su ta
fadi tana turo baki wardrobe ta bude ta curo wata pink gwon mai dogwan hannu rigar simple ce
mai kyau tayi shap sosai tayi mata kyau rigar ita kanta sai da ta yaba rigar parlour ta dawo ta
zauna, jidda na zaune tana kallan carton itama ta zauna tana kallon.


Ring din wayar shi dake bedside drowe ne ya tasheshi dan guntun tsaki yaja tare da kai
hannu ya dau wayar ,ba tare da ya duba suna ba,hello yace cikin alamar gajia ta daya
bangaran a kayi dariya , sadiq tashi yayi zaune tare da saki guntun murmushi, wallahi sadiq
baka da kirki Allah yasa ma ka gane mai magana yar dariya yayi tare da shafa sanjan shi ba
Khaleed bane dariya Khaleed yayi yace ashe dai kana gane mutane dan guntun tsaki sadiq ya
ja ya za'ai na kasa gane muryar childhood friend dina, ah ka kyauta ina majid ai ya fika zuminci,
haka dai kace toh yau na leko Kano insha Allah zan shigo toh shikenan sai ka zo indan ka zo ka
kira ni toh yace tare da yanke wayar agogwan dake manne a bangwan daki ya kalla ware sexy
eye's ball's din shi yayi ohno na kwanta ina ta bacci har 4 ya gota tashi yayi tare da yaye blanket
din jikin shi toilettes ya shige ya sheqa wanka yafito daure da karami'n tawel à kugunsa, sanye
hannun shi riqe da qaramin towel yana tsane sumar kan shi yana cikin shafa lotion wayar shi ta
fara ruri hannu ya sa ya dauka tare da karawa a kunne, hello big man ganin a filin gidan ku,
smile sadiq yayi yace are u serious, yea angayama kowa irin kane Mara zuminci dariya sadiq
yayi kai friend nine fa koma yane , toh shikenan ganin zuwa katse wayar yayi tare da zura
jalabiya white ya fito daga part din shi ya wuce su fatuha a parlour suna ta karatun dan fatuha ta
dake sai jidda ta koya mata karatun boko yanzu haka har ta iya ABCD.


Yana fita farfajiyar gida ya hango Khaleed jingine jikin motar shi mai tsada kallo daya zaka mai
kasan shima dan hutu ne, kuma gaye ne sanye yake da shada tasha diki mai kyau Khaleed
chocolate colour ne yana da saje da yakara bayanar da kyawunsa, yana da manyan ido
murmushi ya saki ganin sadiq ya qara so fararan haqoran shi suka bayana cikin jin dadi sadiq
ya qaraso tare da miqa mai hannu suka gaisa, Ashe dama zan kara ganinka a duniyar nan?
murmushi Sadiq yayi bagashi ba ai kai ma baka zama shiyasa haka kuma dan last week ma
na dawo daga London har muka hade da yaya jawad wajan shopping shi da matar shi har ya ke
ce min sun kusa zuwa gida jira kawai yake Anuty shukara da haihu su zo, murmushi Sadiq yayi

ya ce haka ya fada min suna tattaunawa har suka qaraso kofar parlour cikin parlour suka shigo
har yanzu su fatuha na nan inda ya bar su ,Sadiq yace "Fatuha" dagowa tayi ita da jidda tare
da gaishe da Khaleed murmushi Khaleed yayi tare da amsawa yana bin fatuha da kallo Sadiq
ya katse mai tunanin da cewa "Fatuha ki kawo mana glass cup?" tace mai toh tare da shigewa
kitchen ,jidda ga uncle Khaleed smile jidda tayi Khaleed murmushi yayi ya ce karka ce min
angel ce ta girma haka ,ita ce mana zaro ido waje Khaleed yayi yace kai amma gaskiya mun
yadda zuminci, come here angel kusa da shi jidda ta matso kallan ta yayi tare da daukar ta suka
haura upstairs sai tanbayar ta ya ke tana zuba mai surutu suna shi ga part din Sadiq saman two
star Khaleed ya zauna tare da daura jidda a cinyar shi ,sadiq fridge din bedroom ya bude ya
curo lemu ka masu sanyi ya kawo ma Khaleed lokacin yayi dai dai da shigowar fatuha dauke da
tray da cup's amsa tray din Sadiq yayi tare da yi mata nuni da ta dau jidda, Khaleed sai bin
fatuha da kallo ya ke kiran jidda tayi suka fita a tare tana fita Khaleed ya sauke ajiyar zuciya,
yana kallan Sadiq, Sadiq din ma kallan shi yake ,big man ina kuka samo beautifully girl, wake
nan ya fadi a taqaice wadda ta dau angel yanzu murmushi Sadiq yayi yace "Fatuha she is my
sister baka ga muna kama ba ya fadi zancan yana cigaba da zuba ma Khaleed juice" amma ai
nasan kai ne dan auta baka da wata sister bashi glass cup yayi na lemo yana qara saki wani
murmushin Wanda iya karshi lips din shi, she is my consin sister yanzu ka gane ko murmushi
Khaleed yayi yace amma fa tana da kyau karka ce min basma ce ta zama mai kyau haka
tanbayar Khaleed ta kusa fara kai Sadiq wuya amma sai ya maze yace ba ita ba ce wannan
diyar sister mom ce eyya shi kan Sadiq yana mamaki karyar da ya zauna yana shunfuda ma
Khaleed toh me inya ce me aiki ce dan guntun saki ya ja a zuciyar shi ,Sadiq mom fa , mom ba
ta nan sun tafi uk da abba OK hira suke sha sosai suna kallo.




*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼â€â™‚


*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com


57_58

*Godiya ta musanman gare ku mosayan ⤠wannan novel ina jin dadi 💃🏼yadda kuke
comments🤓 a kan wannan littafi hakan ya nuna min ana mugun tare í ¾í´í ¼í¿½ wannan shafin naku
ne ,Dan Allah duk wadda nayima laifi ta yafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login