Showing 18001 words to 21000 words out of 99609 words
Chapter 7 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
da dad ta Ina zancan tana matsar kwalla...sorry angel tare da
goge Mata kwalla sannan ta jata jikin ta..baba jinmai ta je kauye lokacin da zata tafi kina bacci
shiyasa angel... Grandma shi kuma daddy fa ya tafi ya bar little princess din shi at home...sorry
angel ai zai dawo kin ji....um grandma please call him... Ok angel amma sai kinyi breakfast
sannan... ok " oya muje nayi feeding naki
Alhaji ne yayi gyaran murya ya ce..um kina shan fama babanta ya maki rigima ita ma ta
maki...murmushi tayi tare da shafa sumar Jidda Wanda tasha gyara.... a hanakali tayi feeding
Jidda sai da suka gama tsaf sannan shima Alhaji ya wuce office
After sun gama cin abincin mom ta Kira sadiq...yana zaune saman kujerar shi ta office idanun
shi a lumshe kamar meyin bacci wayar shi ta fara ruri a hankali ya bude sexy eye's ball din shi
ya sauke su kan screem din wayar....sweet mom ne rubuce hannu ya Kai ya dauka ....
daga dayan bangaran ...hello baby ya kake ya aiki ...lafiya lau mom.... Dama wannan ja'ira ce
ta matsamin ka tafi aiki baka tashe ta ba sai rigima take...murmushi yayi daga bangaran shi
hakan sai ya qara fituwa da zala kyan shi numfasawa yayi yace mom bata wayar...ok ...Jidda
dake zaune saman cinyar mom ta washe baki tare da amsar wayar...daddy.. yes angel bata
fuska tayi kamar yana ganin ta"tace shine daddy ka tafi work baka tada little princess din
kaba..."sorry angel lokacin kina bacci bana so na tada little princess na bacci that is why my
angel ...ok daddy inka dawo zamuyi wasa ko...yes mana ...washe hakura tayi....sannan ta ce
um daddy ta qara bata fuska daddy baba jinmai tatafi kauye ban dani bayan tamin promise tare
zamu...sorry angel next time tare zamu kinji...."Yeeee love u dady..."Love u more angel bye
sannan ya katse wayar tare da binta da kallo.
Yanzu tunda kinyi wayar da daddy naki sai ki huce ko dariya tayi ta cigaba da zuba ma mom
surutu
Aiki baffa yake sosai fatuha na gefe tana taya shi tare da bashi labari in ta fadin abin dariya ya
dara haka har suka gama
Cikin sallama suka shigo inna na zaune saman kujerar tayani gulma tana dama hura saboda
baba jinmai nasan hura musanman damun inna..washe da baki suka qaraso fatuha ko jikin
baba jinmai ta fada tana Mata oyoyo..Ah'Ah wanake gani kamar mutanan birni sannu da zuwa
sannan baffa ya samu guri ya zauna ...inna ce tace...ohni fatuha yaushe zaki girma kin fada
mata jiki salan ki karya ta baki ta turo gaba Kai inna har wani nauyi ke gareni tare da matse yar
kwalla ..baba jinmai ko dariya abin ya ba
*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★ we are the best★
https://mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refi
d=52&ref=opera_speed_dial&_tn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
25_26
Basu suka dawo gida ba sai bayan isha lokacin har jidda tayi bacci, dauke yake da ita har suka
qaraso parlour, lokacin rabi'a tana qoqari fitowa daga kitchen' wani irin kallo ya wurga mata Jiki
ba qwari ta gaishe shi har tayi gaba yace" Keeee!!" Tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba , Harara
ya qara wurga mata cikin ktsawa yace mata "Sai ki zo ki amshe ta ko?" Jiki a sabule ta amshi
jidda ,Kiyi mata wanka sannan ki Samata night dress ki kawo min ita daki na dan ban yadda ta
rinqa kwana da ke ba ki koya mata halin bera tsaki yaja Mtsss, sannan ya wuce part din Abba.
Abba ne zaune saman two star fuskar shi manne da glass, sanye yake da fara jalabiya blue
remote ne a hannu yana kallan news, Mom na gefen sa tana yanka fruit.
Cikin sallama ya shigo tare da gaishe da abba, Cikin fara'a Abba ya amsa yace "Ah har kun
dawo daga zuminci?" Eh abba, to masha Allah ina jidda ? jidda tayi bacci, OK" sun dade suna
hira sama sama daga nan Sadiq ya wuce part nashi ,ko da ya shiga dakinshi ya iske ankwantar
da jidda shima bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito sai da ya gama shirin shi na bacci
sannan ya hada coffee yana sha yana dana laptop din shi ,ya dade a haka sannan ya ture
laptop din tare da janyo jidda jikin shi bacci ya dauke shi.
Bayan an gama gada kowace ta wuce gidan su, Cikin sallama fatuha ta shigo gida lokaci baffa
ya dawo gida yana zaune bisa tabarma inna na kusa da shi baba jinmai na gefe su, gefan baba
jinmai ta je ta dauna washe da baki itama baba jinmai murmusawa tayi sun danyi hira sama
sama da fatuha daga nan bacci ya sureta.
Baba jinmai ce tayi gyaran murya tace "Dama jauro ina so muyi wata magana da kai."inna da
ke kusa da baffa tayi qoqari tashi baba jinmai tace "Kema zauna"haka ko akayi inna ta samu
guri ta zauna.
Dama so nake nama magana kan fatuha ina so in zan koma birni sai mu koma tare, Zaro ido
baffa yayi waje yana kallan yar uwar tashi à zuciyarsa yace "Anya ko baba jinmai tasan me take
fada kuwa?"qara murmusawa tayi ta ce jauro ina fatan ba za ka watsamin qasa ido ba a ganina
fatuha nima diya tace jauro, Baffa tsale yayi ya dare ya ce be san zancan ba babu inda fatuha
zata tanan kauyen nan tare da shi baze lamunci hakan ba, baba jinmai ce ta fara matsr kwalla
tana cewa "Ba komai jauro dan ka ga Allah be bani haihuwa ba shine zaka wulaqanta ni kan
diyar ka, jauro da Allah ya bani haihuwa da yau ba zanji zafin abinda kayi min ba, tana maganar
tana ta kuka inna sai lalashin take, Ganin kukan da take yasa jikin baffa yayi sanyi dan shi a
ganin babu abinda baba jinmai zata nema a rayuwar shi ya hana ta.
Bayan da ya iya haka ya hakura ya amince tatafi da fatuha, aiko washe da baki tamai godiya
tare da yimai alqawarin zata riqe amanar fatuha sosai daga nan kowa ya wuce dakin shin.
Ko da ya tashi ya gama shirin shi ciki uniform masha Allah yayi kyau sosai, Ze dau briefcase
din shi shikenan jidda ta tashi washe da baki tace "Daddy morning" morning too angel , hum
yau ma daddy guduwa zakayi ka bar little princess din ka a gida? langwabe kai yayi ya ce
"Sorry angel daddy work ze je kinji kuma yara basa zuwa kema very soon zaki fara zuwa school
ai kinaso ko angel" washe baki tayi tace "Yes daddy zan fara zuwa school kamar yadda su yaya
hannan ke zuwa da Anuty basma ko?" Eh mana angel' tsale tayi ta kai mai hug thanks my
daddy ,smile yayi tare da yimata pack please angel ki tsaya rabi'a ta maki wanka kin ji? naji
grandma na cewa kullun se kin rigima, Bata fuska tayi tace
"Daddy..." shhhh tare da yi mata pack à kumatu ya fice.
A dining area ya hadu da abba shima yana breakfast, mom na gefen shi ahankali ya qarasa
yayi masu pack sannan ya samu waje ya zauna ya fara breakfast lafiyayan chips ne da plantain
and egg sai tea mai kauri Wanda ya sha ovaltine, cikin natsuwa suka gama break din su abba
da Sadiq tare suka fito inda yaran Sadiq ke ta kwasar gaisuwa wajan abba tare da qamema
Sadiq din cikin natsuwa moto cinsu suka fita daga harabar gidan.
Ko da fatuha ta tashi wanke wanke tayi, sannan ta dau tulun ta gidan su fatsima ta biya tare
suka fito suna tafe suna hirar su, kandala suka hango dauke da tray gyadar ta qarasowa su kayi
wajan ta, Kallan su take jiki ba kwari Harara suka wurga mata taré da cewa "Bamu gyada ta
murtala jikinta baqwari ta fara zuba masu gyadar tasan ko zata mutu baza su bata kudin gyadar
ba, kuma ta matsa masu su tona mata asiri " sai da ta gama zuba masu sannan fatuha ta amsa
tace "Cikin Murtala da dan mai gari ya mana alqawari ne muka amshi gyadar, Sannan kice mai
ko ya bamu murtalar mu ko kuma murtala ta rinqa haihuwa sannan suka wuce suka barta tsaye
tana matsar kwalla.
Suna isa rafi suka aje tulu na su gefen rafi suka wuce gonar mai gari suka fara tsinkar
mangwaro da gwaba sai da suka diba san ransu sannan suka zo zasu fita mai gadi ya kama su,
kai kai uban wa ya baku ikwan shigowa gonar mai gari? har ku tsinke mai mangwaro, Fatuha
ce ta turo baki gaba tace bala ne ya bani izinin shigowa ,shegiya mai kama da mayu, shi bala
din sa'an kine inama kika san bala din?harara fatsima ta wurga mai in baka yadda ba sai ka kai
mu wajan shi ka ji da kunnan ka ta ida zancan tana gyara Daurin zaninta.
Aiko haka akayi mai gadi jan su fatuha yayi har gaban bala, sai yan' harare harare suke su daya
,kaisu yayi suma bala ba yani sai ya ce shi ya ce su dinba dan yasan in bai ce ba tuna mai asari
zasuyi, sannan yasa mai gadi ya sake su wani irin dadi suka ji suna ta shewa suka isa rafi suka
debo ruwa.
Bai zame ko ina ba sai *Yandutse college* dan samoma jidda admission be sha wani wahalla
ba ya samama ta inda duk angama abinda za'ayi, ranar Monday sai ta fara zuwa school sannan
ya wuce office, a cewar shi inya dawo gida da yama zai samamata malamin adini.
Kwanci tashi asarar mai rai yau sati baba jinmai daya a wudil inda take ta hada kayanta dana
fatuha, Fatuha sai kuka take har da majina dan ita a ganin baba jinmai bata mata adalci ba ita
tace mata tana san birni da zata kwashe ta su tafi toh Wallahi sai nayi rashin mutunci idan
munje sunje kenan, baba jinmai ce ta juyo haba fatuha sai ka ce za'a cinye ki sai kuka kike
haba fatuha kinsan muna tare kuma zan kula da ke kamar yadda inna zata kula da ke, fatuha
dan Allah kiyi shuru kinji, Inna da ke gefe duk da tana jin wani irin amma tasan baba jinmai ba
zata tayi abinda zai cutar da fatuha ba amma ko yaya tana jin zafin rabuwa da fatuha saboda
fatuha yarinya ce mai shiga rai, a hankali inna ke lalashi fatuha har tayi shuru haka shima baffa
da ke gefe haka baba jinmai ta gama hada kayan fatuha cikin yar leda gari yayi zafi ta miqa
mata ta rungume.
Baffa kuma yaje taro masu mashin, Sallama fatsima tayi ta shigo falon kallo daya zaka mata
kasan itama ta ci kuka har ta gaji, wani saban kuka suka dasa ita da fatsima da kyar aka lalashe
su sannan baffa ya shigo ya sheda masu gamai mashi din.
Suna kallan su har suka bile baffa ya goge yar kwallar shi dan shi ka dai yasan yadda yake ji,
suna isa tasha suka samu motar Kano basu wani dade ba motar ta tashi.
Idanuwan shi lumshe kamar wanda ke bacci, zaune yake saman resting chair yayi crossing
leg's nashi Taba shin da akayi ne ya sasa ware sexy eye's ball's din shi ba kowa bane sai majid
murmushi yayi yace "Yaushe ka zo ban sani ba?" yanzu na shigo mom ta ce min kana nan
sannan ya zauna daya daga cikin chairs din ,OK ya aiki? Alhamdulliha soma nake na dawo nan
da aiki, kai Allah ya taimake ka har yau basu ma transfer din ba? Aiko dai ai bana fatan hakan
wallahi murmushi sukayi su duka suka cigaba da magana à matsayin su na abokai kuma
yan'uwa.
*Tah ku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refi
d=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
27_28
Misalin karfe 5:00pm motar su fatuha ta tsaya a tasha lokacin har bacci ya dauke ta tana
kafadar baba jinmai rungume da jakarta gari yayi zafi.ahankali baba jinmai ta shiga tashin ta..
Aiko nan tatashi tanayin wani wiqi wiqi da ido da qarewa tashar kallo. mutanene birjik..haka
suka zuro kafafun suka fito daga motar. Baba jinmai ce ta zaro wayar ta cikin zani. y'ar baby
nokia ce. bugu daya biyu' mom ta dauka. washe da baki baba jinmai da cewa.. "hajiya gani na
iso ina tasha...daga bangaran mom murmushi tayi ta ce.. "masha Allah yanzu zan aiko driver ya
dauke ko'... "Toh hajiya. Sannan ta katse wayar tana Murmushi ta kalli fatuha.. Yanzu za'a zo
daukar mu kin ji yan'nan. kada kai fatuha tayi dan ita a wannan lokacin haushin kowa take ji ...
Ba'a fi 30 minutes ba driver ya qaraso tare da kwashi kayan su ya zuba cikin mota inda yayi
yayi da fatuha ta bashi Jakarta ta qi ba yanda ya iya haka ko suka tafi
Kai tsaye sultan road suka wuce nan fa fatuha ta fara zare ido tana qarewa unguwar kallo
kamar wanda ta zo aljana haka take gani... Washe baki tayi ta juyo tace... "Baba jinmai dama
ashe aljanna kike zuwa... Baba jinmai dariya tayi ita da driven tace.. "aa fatuha nan ba aljanna
bane birni kenan... "kai amma kwarankwatsi kinyi da kika zo dani dafa tare da fatsima kikaso
zuwa ko... "ke da kikaita kuka baki san zuwa' "Qur'an yanzu ina san birnin.. ta'ida zancan
lokacin yayi dai dai da isowarsu katafarin gate din gidan Alhaji Ibrahim. Zanso kuga yanda
fatuha ke zarar ido
Dai dai parking space su kayi parking baba jinmai ta kwaso masu kayan su fatuha dai na
maqale da ledar ta, ta gari yayi zafi
Katafaran parlourn gidan suka shiga. Qauyanci wajan fatuha ba'a magana dan ko zama taqiyi
saboda tayals sai da baba jinmai tayi da gaske sannan ta zauna saman carpet tana ta zara ido
Mom ce ke saukowa daga upstairs cikin murmushi tace... "ah sannu da zuwa baba jinmai tare
da qarasowa parlour da zama saman two star tana facing din su baba jinmai d'in, "ya hanya.
Tace da ita tana murmushi.
Alhamdulillah, baba jimmai tace.. "oh tare da yarinyar kuka zo kenan gaskiya naji dadi.
"fatuha dake rabe jikin baba jinmai ta gaida mom cikin girmamawa " baba jinmai ce ta washe
baki tace... "Ai diyar qanina ce jauro,
"a'a ki ce min yar tashi ta yi girman haka ' "aiko dai hajiya.. Sunyi hira sama sama inda fatuha ke
rabe jikin baba jinmai tana qarewa gidan kallo tare da santinsa
Lafiyayan abinci mom ta basu shinkafa da miyar kaji wadda taji kosulo.. kauyanci ko wajan
fatuha ba'a cewa komai saboda bata tab'a cin irin abinci ba dan haka ta saki tinbi ta ci har da
side kwano da qari... Baba jinmai dadi taji dan taga fatuha ta saki jikinta
Bayan sun gama cin abinci mom ta kai fatuha dakin jidda ta gwada mata toilet da duk yadda
zatayi anfani da komai na toilet din tare da Ciro mata uniform din yan'aiki farar Riga da skirt dai
dai gwiwa
ba laifi fatuha duk abinda mom ta gwada mata haka tayi..
wanka sosai tayi da dirje jikinta tare da wanke kanta da shafo .masha Allah gashin fatuha har
gadan baya sai dai rashin kulla da shine yasa duk ya cure gu daya amma hakan bazai hanaka
ganin kyan gashin ba. daure da towel ta fito.. Mom na zaune saman sofa tana jiran fitowar ta.
Koda ta d'ago kanta mom d'in. tayaba kyau irin na fatuha. Hakan yasata yin murmushi.. ita ko saitahau sunne kai.
"Ah har kin fito..
D'aga mata kai tayi alamar Eh , uniform din mom ta dauka ta bata' ga wannan kayan kullun su
zaki rinqa sawa akwai su da yawa cikin wardrobe ranar Friday ne kadai zaki sa kayan gida
suma akwai su cikin wardrobe. na ki kuma anfidda su waje sannan in kayan sunyi dati ki aje su
akwai mai wanki zai wanke maki su ya goge.. Washe da baki fatuha ta ce, "toh
Mom har takai bakin kofa ta dawo tare da cewa, "gobe ki shirya za'a kaiki wankin kai.. "to tace
tare da yima mata godiya.. mom na fita ta shafe jikin ta da mai tare janyo kayan da mom d'in ta
aje mata a saman gado farar rigar ta fara janyowa ta saka amma sai da tasha wuya sannan ta
iya balle mab'allin rigar.. Saidai dai dai gwiwa rigar ta tsaya mata. "Kwarankwatsi gidan