Showing 69001 words to 72000 words out of 99609 words
Chapter 24 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
ya fara jawabin cikin natsuwa kamar yadda kuka Sani
Inayi maku murna da zuwa wannan taro na qara dankwan zuminci. tare da yi maku albishir da
abubuwa da yawa na farin cikin a wannan shekara mun samu kimani naira billion dari cikin riba
kasuwancin mu sannan mun talafawa gidan marayu tare da asibitoci sannan anbiyawa mutun
30 kujera maka , kabara wajan ya dauka tare da hamdala, sannan Kuma ga muhimiyar sanawa
ita ce majeed ya samu matar da zai aura, sadiq dake zaune saman kujera gaban shi ya qara
yankewa ya fadi, muryar Alhaji babba ce ta dawo mai dodan kunne, ba kowa bace sai yar gidan
ibrahim wanda yake ruqu fatuha Kuma har gidan iyayan ta muje munyi bin cike ashe ma akwai
sanaya a tsakanin mu Kuma sun aminci sun bada. wani irin gumi ne ya karyo ma sadiq mai
matsanan cin zafi take nan ya fara ji wutar shi na dauke wa ba sadiq ba hata mom sai da ta
girgiza da wannan furin cin, wata kalmar ya qara jefowa a karo na biyu sadiq Kuma mun yanke
shawarar bashi kanwar sa basma tare da sharadi idan har ya kawo wadda yake so nan da sati
daya kamin asa biki to za'a basa dama ya auri wadda yake so basma ma kuma ta hakura zabin
shi wannan shine hukuncin dana yanke. sannan ya kalli baban basma Alhaji khabiru cika mana
taro da addu'a.
Gabaki d'aya parlour juyawa sadiq yake da kyar ya samu ya miqe, majeed in ban da washe
baki da yake ba abunda yake dan ko ta kan sadiq bai bi ba haka basma baki har kunne sadiq
ne ka dai da mom basu farin ciki sai hanan. yana fitowa d'aga parlour parking space ya nufa
cikin sauri ya bale murfin motar ya shiga da gudu ya fisgi motar ya harba kan titi gudu yake
tsulawa kamar zai tashi sama yana isowa gida ya danna horn bala mai gadi na bude mai geta
yace "Subhanalal " saboda yadda sadiq ya shigo da motar yana shigowa ko dai-daita parking ya
kasa ya bale murfin motar ya fito cikin sauri ya wuce part din shi yana shiga ya zame bakin kofa
tare da dafe kanshi♀ maganar Alhaji babba na dawo mai. mikewa yayi ya shige bedroom
saboda har yanzu bai dai na ganin jiri ba, wani irin kuka sadiq ya saki mai tsuma zuciyar mai
saurare kneel down yayi a wurin can Kuma ya mike yashiga fatali da kayan d'akin kamar saban
kamu. sai da yayima d'akin fata fata ya shiga toilet da kayan jikin shi sakar ma kanshi shower
yayi, maganganun Alhaji babba namai yawo a brain wata zuciyar tace "Wato jiya fatuha tabama
majeed izinin turawa gidan su?" hadeye kukan da yake yayi tare da fitowa sharkaf ya zauna
kasan carpet be damu da kayan dake jikin shi ba.
Bangaran fatuhu ko tunda su mom suka fita gabanta ke faduwa, ta rasa dalilin haka ta rasa
suku nin ta jin an bude kofar d'akin ya sata waigowa mom ce tsaye bakin kofa murmushi fatuha
ta saki wanda iya karshi laban ta, mom har kun dawo da wuri haka? eh tace tana qoqarin danne
damuwar ta tare da qarasa shigowa zama tayi kusa da fatuha cikin sanyi murya tace "Fatuha
gobe da safe ki shirya zaki je wudil baffa nasan ganin ki?" sannan ta tashi ta fita kallo fatuha
tabi mom da shi take nan jikin ta ya haubari da tsoro tsoro ko dai uncle ya kai qarata kauda
zancan tayi tasan ma ba zanyi hak'a ba ,amma zuciyar ta na cike da tanbayoyi, ganin bata da
amsa ta hakura.
Ola sadiq ya kira a waya bugu d'aya zuwa biyu ya dauka ina san ganin ka sadiq ya fada a
taqaice ,ko da ola ya zo ganin Watsin da akayima dakin tsoro ya bashi kallan sadiq yayi da
magana a bakin shi ganin fuskar sadiq ba annuri yaja baki ya tsuke. nuni ya mai d'aya gyara
d'akin shi Kuma ya shigida saman sofa hawaye daya na bin daya kamar ba soja ba,
Gabaki d'aya gidan Alhaji Ibrahim ba wanda ya rintsa, d'aga angel sai abba ne kawai suka
samu bacci bangaran sadiq inban da kukan zuci ba abinda yake, fatuha tunanin me yasa baffa
ke neman ta? take ko dai inna ce ta rasu? ba'a San fada mata girgiza kai kawai tayi.
Tunda safe fatuha ta tashi ta shirya cikin riga da sket din ta na atamfa yellow mai ratsin
white a jiki masha Allah kayan sun hauta sai fuskar fayau, bayan ta kamala ta fito parlour cikin
natsuwa ta gaida mom da abba d'ake ta break angel na gefe itama ganin bata ga sadiq ba yasa
gaban ta ya qara faduwa a karo na biyar jiki ba qwari ta zo ta hada tea kurba biyu zuwa uku ta
aje , mom ce tace "Fatuha har kin koshi?" eh mom dama in zan yi tafiya bana wani cin abinci to
mom tace , sannan ta qara da cewa ga driver nan zan h'ada ku da shi in ya kai ki yau zai maido
ki ki gaida mutun gida sannan inkin Isa ki kira ni ki fada min. lagwabe kai fatuha tayi tace
"Wallahi mom jiya wayar ta lalace" garin yaya? fadowa tayi d'aga dressing mirror ta dauke, eyya
to bari na baki baby Nokia in kin dawo a sake wata to fatuha tace tare da shi ga daki ta dauko
sim din ta miqa mata wayar .mom tayi ta zura sim din ciki har ta kai bakin kofa ta dawo tare da
haurawa sama part din sadiq ta nufa a hankali ta murda handle din kofar taji Kule gam tsoro ne
ya kamata amma ba yadda ta iya haka ta dawo tare da yima mom sallama angel ko sai rigama
take sai tabi fatuha mom ta hana.
Shigewa mota tayi driver ya harba da su kan titi cikin dan qanqanin lokaci suka Isa wudil.
cikin kwatan can fatuha har driver ya kawo ta gidan fitowa tayi a hankali tana qare ma gidan su
kallo gabaki daya gidan ya canza a yadda ta San sa mamaki ne ya bayana a fuskar ta qarasa
Shiga tayi cikin sallamah inna d'ake parlour ce ta fito tare da yima fatuha maraba da zuwa duk
da fatuha ba'a cikin jin dadi take ba bata yadda inna ta gane ba, parlour ta janta suka Shiga har
yanzu mamaki ne shifide a fuskar ta tace cikin sanyin murya "inna waya gyara gidan nan?"
murmushi inna ta saki ina yaran nan sadiq wallahi shi ya mana abin arzikin nan murmushi
fatuha ta saki mai cike da jin dadi baffa ne ya yaye labilan ya shigo har qasa fatuha ta tsugunna
ta gaisheshi amsa mata yayi a taqaice sannan ya samu wuri ya zauna. itama fatuha qasa
tayima kanta mazauni tana jiran jawabin baffa gyaran murya baffa yayi tare da cewa "Fatuha
nasan cewa na maki laifi amma kiyi hakuri ina fatan bazaki watsamin qasa a ido ba? ina fata
bazaki bani kunya ba ?duk wannan jawabin da baffa keyi kan fatuha na qasa ,d'ago kai tayi tace
"insha Allah baffa bazan baka kunya ba" yauwa diyar albarka, dama dan uwan sadiq ne ya zo
neman auran ki tare da iyayan shi jiya da dare, mukanmu munyi mamaki da wannan zuwa
fatuha ganin halacin da zura'a suka mana gashi nasan baban yaran hakan yasa na amince dan
na lura yaran mai natsuwa ne Kuma dama neman auran budurwan anso iyayanta su zaba
mata miji Na gari da wannan nayi la'akari na zaba maki majeed a matsayin miji. dagowa fatuha
tayi a razane dan sai yanzu ta fahimci inda aka dosa idanuwan ta tap da kwalla suka ciko nan
take hawaye suka fara anbaliya a fuskar ta me yasa mai kyau zai mata irin wannan horan me
yasa fita tayi d'aga parlour da gudu ta fada dakin inna ta saki kuka mai tsanani mai ban tausayi,
inna ce ta dafa bayan ta tana lalashin ta, haba fatuha bai kamata ki watsawa muta nan qasa a
ido ba Kuma kowani mutun da qadarar dake zuwa mashi .fatuha idan dai majeed alkairi ne a
gare ki Allah ya tabatar haka inna ta riqa bitana tausar fatuha har ta samu tayi shuru tana sakin
ajiyar zuciya ko ruwa kasa sha fatuha tayi sai bayan sallah la'asar suka dau hanyar kano wayar
tace dake cikin jaka taji qara message sai a lokacin ta tuna da mom tace ta kira ta curo wayar
tayi ta karanta message din kamar haka,
_Sister ina matukar farin cikin Sanar d'ake yau buri na ya cika, tun jiya nake qoqarin kiran ki
wayar takin Shiga ba wani albishir bane ila yaya sadiq ya kusa zama miji a gare ni ,sannan ina
taya ki murnar zama inlow a gidan mu cikin family din mu d'aga basma._
Wani irin kuka fatuha ta saki mai cinrai ko ida karanta sakwan ba tayi ba wayar ta fadi jikinta in
banda bari ba abin da yake. ashuru driver ya juyo haba fatuha komai yayi zafi maganin shi Allah
bai kamata kina kuka irin h'aka ba ,duk wannan magana da ashuru yake fatuha ba jin shi take
ba kalmar sadiq yazama miji Na kawai qwawalwarta ke fada mata har suka iso garin kano
fatuha na sheka kuka kamar ranta zaifi ta, ko da ashuru yayi horn aka bude geta kafin ya tsada
motar ta bale murfin motar ta fita da gudu sadiq da yanzu ya ji Qarar shigowar mota d'aga labila
yayi tare da koma ya cigaba da zarya a bedroom din.
Da gudu fatuha ta haura sama ko kallan muta nan parlour batayi ba part din sadiq ta wuce
Allah ya bata sa'a tana bude kofar ya bude, ganin bata gashin a parlour ba yasa ta shigewa
bedroom da gudu . fadawa tayi jikin sadiq tare da sakin kuka mai cinrai ,rintse ido sadiq yayi
yana jin yadda fatuha ke sheqa kuka cikin sarkewar murya tace "Uncle dan Allah karkamin
wannan horan wallah bazan iya dauka ba, dama ace mafarki nake abin da nake ji ba gaske
bane ta ida zancan tare da sakin saban kuka ta zame kasa.......
*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★We are the best★
http/mobile.Facebook.co m/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_ speed_dial_&yn=H-R
*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM
75_76
Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan taja jiki ta hau saman bed ,tarasa dalilin da yasa mai
kyau yake yin irin haka. kuka ta kuma rushewa da shi data tuna a irin yana yin data ganshi,
h'aka ta riqa raira kuka kiran sallah magrib yasata tashi jiki ba qwari ta dauro alwala tare da
gabatar da sallah. zaune tayi bisa daduma abin tausayi ganin tunanin be fishe ta yasa ta janyo
AlQur'ani tana karantawa har aka kira sallah ishi bayan ta idar da sallah ta ja jiki ta koma bed ta
cigaba da raira kukanta abin tausayi turo kofar da akayi ne yasata miqewa tana kallan kofar,
angel ce tsaye bakin kofar qarasowa tayi d'akin tare da hawa saman bed din tace "Anuty waya
saki kuka?" murmushi fatuha ta qaqaro wanda iya karshi laban ta tace "Ido nane ke ciwo" sorry
Anuty , ki fito parlour kuyi dinner naji shuru ne baki fito ba ke da daddy shiyasa na biyo ki.
dadday dai yace ya koshi, ko kema kin koshine? ta fadi zancan tana kallan fatuha Dan smile
tayi tace ban qoshi ba ina nan zuwa naci komin dare fita jidda tayi d'aga daki'n fatuha ta cigaba
da raira kukan ta har sai da kanta ya fara ciwo, ganin bame lalashin ta yasa tayi shuru tana
sauke ajiyar zuciya bacci barawo ya sace ta.
Bangaran sadiq in ban da juyi saman bed ba abinda yak'e da kyar ya samu ya rintsa.
*Asuba ta gar'i*
Ko da fatuha ta tashi jiki ba qwari tayi sallah sannan ta qara komawa ta kwanta saboda kanta
dake mata ciwo. Kuma taci sa'a yau weekend ba ita ta tashi ba sai karfe 11:30pm ware ido tayi
tare da kallan agogan d'ake makale a daki'n, cikin sauri ta mike tare da shiga toilet ta watsa
ruwa. ko da ta fito mai kawai ta murza sai after dress d'ata zura parlour ta fito ba kowa dining
area ta wuce tare da bude kulolin dak'e jere wanjan chpis ne da farfesun yan'ciki zuba wa tayi a
plate tare da had'a ruwan tea sannan ta zauna. loma biyu zuwa uku tayi ta ture plate din dan
kwata kwata bata jin d'adi abincin.
Babban abinda ke daure mata kai ta rasa laifin da tayi ,yanke shawarar zuwa bama sadiq
hakuri tayi duk da bata san laifin data mai ba dan bata iya jurewa wannan horan. tashi tayi tare
da kwashe kwanikan ta kai kitchen sai da suka dan taba hira da su baba jinmai sannan ta fito.
Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta murda handle din kofar tare da shigowa cikin
sallama zaune sadiq yake saman two star da laptop gaban shi kallo d'aya zaka mai kasan babu
annuri a fuskar shi. dogo kai yayi ya kalli fatuha tare da lumshe ido ya kauda kai yace "Just
leave me alone" sadiq ya fada a tsiwace tare da tatara takadun d'ake gaban shi da laptop din ya
shige bedroom tare da buga kofar da karfi. kuka fatuha ta saki tare da fita d'aga part din da
gudu jin ta fita yasa sadiq jinji Na da kofar bedroom ya lumshe ido.
Da gudu ta wuce mom a parlour ta shige daki saman bed ta fada tare da sakin kuka mai cinrai.
kuka taci ta gaji, mom d'ake parlour bin fatuha tayi da kallo tana mamakin mai ya h'ada su,
koma dai minene ai sun saba zasu shirya ne amma abin mamaki basa kai haka kauda zancan
mom tayi tare da cigaba da kallan ta, duk yinin yau babu wanda yaci abinci cikin su fatuha inban
da kuka ba abinda take shi ko sadiq sai baki'n rai dayake fama da shi,
Iskace mai sanyi da ke ta kadawa da alama ruwa za'ayi saboda damuna data fara shigowa.
qara cida ce kawai ke tashi b'akin widow sadiq ya tsaya a hankali ruwa ke saukowa kallan
ruwan yake yanda yake saukowa da karfi a wannan karan lumshe ido yayi tare da ware su, ya
koma saman bed ya kwanta bangaran fatuha tunda aka fara ruwa tak'e lilibe cikin blanket
Gaba ki d'aya yini yau ba wanda yayi ma wani magana cikin fatuha da sadiq, horan dak'i
sukayi wa kansu ba tare da sun nemi abin sama bakin sallatin su ba , har bacci ya kwashe su.
Shiryawa yake cikin manyan kayan shi kasan cewar yau zasu je family meeting, fatuha ce ta
fado mai a rai kawar da tunanin yayi dan har yanzu be huce ba ko yana hucewa sai ya d'awo
dag'a meeting cikin Isa yake saukowa d'aga upstairs ,lokacin har su mom sun shirya suna
parlour zaune suna jiran fitowar sadiq da fatuha ganin sadiq ya sako yasa mom cewa angel,
kira Anuty mu wuce , ko da angel ta shiga d'akin kwance ta samu fatuha qudindine cikin blanket
, fitowa tayi da sauri d'aga bedroom din tace "Grandma Anuty bacci take" toh fa! amma ai fatuha
bata kai haka tana bacci .shiga d'akin mom tayi tare da qarasawa wajan bed din fatuha tace a
hankali, a hankali fatuha ware idanuwan ta da suka yi nauyi saboda tsabar kuka, kallanta mom
tayi tace "Mike damun kin fatuha?" dafe kai tayi tare da cewa mom "Kai nane ke ciwo" eyya
sorry dama meeting zamu tunda b'aki jin dad'i ki zauna kawai a gida to kawai tace tare da
shigewa blanket, sannan mom ta fita ko da ta fita sadiq ta aika ma harara tare da ayana ma
ranta in sun dawo zatayima abin tufkar hanci.
Katafarin parlour su da aka ware danyi meeting suke zaune, tunda sadiq ya shigo gaban
shi ke yankewa yana faduwa yarasa dalilin h'akan addu'a da ke bakin shi ya furta dan samun
na tsuwa. majeed ya shigo tare da zama gefen sadiq tare da miqa mai hannu suka gaisa da
kyar sadiq ke danne zuciyar shi kan majeed tare da bata hakuri, Alhaji babba ne ya shugo
sanye da babba riga tasha aiki sai sheqe kayan suke, cikin sallama ya shigo tare da zama a
kujerar sa ta musanman wato kakan su sadiq, ammi na gefan shi ta dama sauran jikoki da iyaye
na gefe da yan uwa .
Taro ya fara budewa da addu'a sannan ya fara jawabin cikin natsuwa kamar yadda kuka Sani
Inayi maku murna da zuwa wannan taro na qara dankwan zuminci. tare da yi maku albishir da
abubuwa da yawa na farin cikin a wannan shekara mun samu kimani naira billion dari cikin riba
kasuwancin mu sannan mun talafawa gidan marayu tare da asibitoci