Showing 87001 words to 90000 words out of 99609 words

Chapter 30 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

da ya gama shafe jikin shi da lotion mai kamshi da sanyi dadi
sannan Dr yakub ya balo magani ya miqawa sadiq dan bata fuska sadiq yayi yace "Wannan
fa?" daure fuska Dr yakub yayi yace "Magani mana" bai ida rufe baki'n shi ba akq turo kofa aka
shigo .murmushi sadiq ya saki tare da qarasawa ya rungume jawad zame jiki yayi tare da bata
fuska yace, "Sai yauma zaka zo?" smile jawad yayi yace "Sorry baby tun jiya na zo kuma na zo
nemanka aka ce ba kanan" dan lagwabe kai yayi tare da cewa "Toh shikenan, ina Anuty
shukura?" tana wajan mom ok hadadiyar fara shada ya janyo white getzner tasha aiki ta gaji
malin malin su jawad ne suka taimaka mai ya shirya tuni ya fito yayi kyau bayan sun gama
shiryawa suka fita,

Zaunawa sadiq yayi tare da kallan agogo dak'e manne a bago'n daki'n. kusan karfe 1:30pm
saura minti talatin a daura auran su. hak'a ya rinqa dane zuciyar shi yana bata hakuri.


Suna Isa wudil gida ya dau gud'a baba jinmai ta fito da sauri tana cewa "Ladingo amaryar
fa ta iso ?" inna washe da bak'i ta bude masauki da su fatuha zasu sauka kusan tare suka
shigo. Anuty bilki na riqe da ita masaukin suka sauka nan aka fara jera masu kayan motsa baki,
yan'matan amaryar ko alwala suka fara daurawa suna sallah kasancewa azahar tayi haka itama
fatuha ta gabatar da sallah sannan suka zauna aka fara gudanar da biki. gwago ce ta aiko a
kira fatsima tashi tayi ta fita har Nana zata bita sai kuma ta dawo ta zauna ko da fatsima ta Isa
gidan su shima cike yake da baqi ,babban abinda ya daura mata kai har da dangin baban ta, to
ko suma biki'n fatuha suka zo? watsar da zancan tayi tare da shigewa daki inda gwago take
washe da baki gwago ta tarbi fatsima ta fara mata magana duk yadda naso naji me ake cewa
na kasa ji. hakan yasa ni da Anuty Raheenat muka bar gun jiki a sabule lol.


Duk inda ka waiga a cikin masallaci Sheikh Isyaka Rabi'u mosque ya cika da manyan
mutune. saboda daurin auren, sadiq na hango ciki'n din bin jama'a, a Nata mai Allah ya sanya
alheri duk wannan abu Dr yakub na lura da yanayin shi majeed ma sai murmushi yake saki
daka ganshi kasan yana cikin farin ciki. haka shima Khaleed dan yasha kyau har ya gaji kamar
ango gyara lasfika da kayine yasa gaban sadiq ya yanke ya Fadi .take wani irin zufa ta fara
karyo mai da bugun zuciya, tabas yasan ana daurawa ya zama gawa wani irin jiri ya fara gani
da kyar ya fara barin cikin taro ga wani irin tari da yake don tado masa. A hankali yake takawa
dan yanzu ya fara yin nisa da masallacin,


Cikin masallaci ko *_MALAM JAURO YA BADA DIYAR SHI KAN SADAKI NAIRA DUBU

DARI GA DAN ALHAJI IBRAHIM WATO SADIQ IBRAHIM, MALAM ALIYU YA MIQA DIYAR
shi KAN NAIRA DUBU DARI WATO FATIMA ALIYU GA DAN ALHAJI KHABIR WATO
ABDULMAJEED KHABIR, TARE DIYAR shi BASMA YA MIQA TA GA DAN ALHAJI SANI
WATO KHALEED KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI -* kowa na masallaci mamaki ne ya lulube
shi. sadiq wanda fitowar shikenan majeed ya biyo shi tare da cewa "Baby?" waigowa yayi tare
da buda baki zai ce majeed jiri ya debe shi ya fadi qasa sumame" da sauri majeed ya qaraso
tare da sakin kuka yana cewa "Duk laifi nane hawaye namai zarya" Dr yakub da kusan tare
suka iso wurin yace "Ba kuka za kayi ba? muyi sauri mu kai shi asibiti" jikin majeed na rawa ya
bud'e murfin mota yana kuka ganin ba zai iya tuqinba yasa doctor yakub ya amsa. car key din
suka bar harabar masallaci da gudu kuka majeed yake yana cewa "Ban taba tunanin abin ya kai
haka ba? am so sorry sadiq ka yafemin sai sanbatu yake a haka suka iso asibitin" sai da aka
wuce dashi emergency sannan majeed ya zame jikin bango tare da sakin kuka. wayar shi ya
curo cikin aljihu ya danna number umma bugu daya zuwa biyu ta dauka kuka majeed ya saki
yana cewa "Umma saboda ni ina ji ina gani baby zai rasa ransa? Ya fadi hakan tare da sakin
kuka" ita kanta umma ta tausayawa sadiq.

Kafin ka ce me, asibitin ya cika da yan'uwa. majeed na ganin abba ya fada jikin shi yana kuka
kamar qaramin yaro yace "Shikenan abba baki'n ciki na zai kashe baby,?" a hankali abba ke
shafa bayan shi tare da zaunar da shi d'aya d'aga ciki'n kujerin dak'e gurin. ajiyar zuciya kawai
majeed ke saki ciki'n sanyi murya abba yace "Ba laifin ka bane majeed kaji? har da laifin sadiq
da yayi nauyin baki ya kasa fad'a? ko yanzu da ku kayi saurin aka sauya daurin auran? indai
fatuha tace bata san sa dole ya sake ta" kuka majeed ya saki tare da cewa a?"Abba wallahi da
kunne na naji irin son da suke ma juna su? abba dan Allah a taimaki rayuwar baby ? ya ida
zancan yana qara saki'n kuka" haka abba ya rinqa lalashin shi har yayi shuru, ammi sai da ta
matse kwalla saboda tausayi , sai yanzu suka san abinda ke damun sadiq.


Abba biza yasa aka mai dan a fitar da shi waje saboda a wannan qaran ciwon yayi tsanani.
dan yafi buqatar amai aiki gagawa tare da samun qwararin likito ci.


Su baffa na Isa wudil ya sanar da su an daura auran, fatuha wani irin kuka fatuha ta saki
dan yanzu ta tabatar da ta zama malaqin majeed kuka take kamar ranta zai fita. lalashin ta su
Anuty bilki suka shigayi da kyar aka samu fatuha ta shirya. ko da ta shirya daki'n baffa aka kaita
ya mata nasiha sosai duk wannan nasihar da baffa ke ma fatuha kuka take har da shesheqa
abun gwanin ban tausayi. a haka aka tataro ta aka sata mota taci kuka sosai sai anjiyar zuciya
da take ta saki ,dan ko fatsima bata nema ba.

Bangaran fatsima ko su gwago sun gyara ta sosai duk da bata jin Son majeed amma a yadda
ya mata bayani da yadda su gwago suka mata hakan yasa ta fara jin son sa dan tayima kanta
alqawarin bashi farin ciki, haka suka shige motoci amaran aka harba da su kan titi ,

Tunda fatuha ta ga an iso kano ta qara saki'n kuka mai cin rai, sosai take kuka kamar ranta
zai fita. suna isowa family house aka bude mata murfin kofar luuuu ta fadi jikin Anuty bilki
sumamiya...




*Taku har Kullu salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★We are the best ★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFUROM.COM


93_94


Daukar fatuha akayi aka maida ta mota tare ja suka bar harabar gidan hannan sai matsar
kwalla take basu zame ko ina ba sai asibitin da aka kai sadiq suna shiga lokaci majeed na
qoqarin fita kamewa yayi yana bin su da kallo kamar gunki ganin fatuha yasasa bin bayan su
wasu hawaye masu zafi namai zarya duk wannan abun da ya faru saboda shine shiga da
fatuha emergency akayi


Bayan yan mintuci aka fito da ita dakin da aka aje sadiq aka aje ta kafin anjima jirgin su ya
tashi har yanzu kwance yake bai san halin da ake ciki ba,

A hankali fatuha ta fara ware eye's ball's din ta tana bin dakin da kallo yunqurin tashi tayi ta

kasa da yar ta iya miqewa ta juyo ganin sadiq kwance kefan ta ya sata cire drip din dake hannu
ta matsa kusa da shi kuka tasa ganin halin da yake ciki a hankali ta fara cewa mai kyau meya
same ka duk tabi ta rude sai fama kuka take har sautin kukan ta ya fara fita waje mom da
shigowar su asibitin kenan suka shige dakin a tare kuka fatuha take tana cewa mai kyau ka
tashi wallahi na rasa ka mutuwa zanyi Allah bana iya zaman aure da majeed please ka tashi ta
ida zancan tana kuka mai cin rai mom ce ta janyo ta, ta rungume tana shafa bayan ta shhhh ya
Isa haka fatuha ki kwantar da hankalin kinji indai mai kyau ne ya zama naki dagowa tayi tana
kallan mom da mamaki murmushi ta sakar mata tace yanzu ba kuka ya kamata kiyi ba kulla da
mijin ki ya kamata kiyi idan kun dawo kunji bayani gabaki daya wani lalausan murmushi fatuha
ta saki majeed dake gefe smile ya mata sai ji tayi duk kunya ta kamata da sauri take qoqarin ta
fita daga dakin basma ce ta tare da ina zaki ki kibar mijin ki, ko kin mata kema baki da lafiya
kina buqatar kullawa harara wasa ta aikawa basma gaba ki daya dakin ka fashe da dariya
Khaleed dake gefe ne yaja basma suka wuce gida dan ta samu hutu kafin anjima akaita dakin
shi kusan a tare suka fito da majeed yana qoqarin bude mota, motar jawad ta tsaye shida
shukara suka fito tare da fatima sai matsar kwalla take qarasawa majeed yayi tare da cewa a'a
sai ku fito min da mata ba tanbayar izini harara jawad ya kai tare da cewa kai dai wallahi ka
raina mutane ya kaimai duka ya goce yana dariya janyo fatima yayi jikin shi cikin cool voice
yace my wife me ya saki kuka haka kina so ki bata min kwalliyar ki dan murmushi fatima tayi
tare da rufe face nata lol su fatsima anqaro wulaqanci


Bayan an gama shirya komai flight din su sadiq ya tashi sai London suna isa london babba
asibiti suka sauka kusan amaran tare suka tafi saboda suma honeymoon za suyi a chan
Khaleed sai zuba ma basma soyayya yake haka shima majeed haka fatima ko sai kunya yake
bata ko da ka wuce da sadiq asibiti emergency suka wuce da shi saboda yana buqar aikin nan
kusa fatuha ta kasa zaune ta kasa tsaye sai addu'a take fatima ce ta dafata tace fatuha ya
kamata ko wani abu ne ki dama cikin ki insha Allah lafiya lau sadiq zai fito haka basma da
fatima suka rinqa bata baki sannan ta ci abinci, bayan ta kamala cin abincin duk da ba wani ci
tayi ba su fatima suka mata sallama akan zasu wuce masaukin su, su huta anjima su dawo
haka ko akayi fatuha ta dawo ta zauna haka shima majeed yana asibitin dan ba da shi suka
koma masauki ba, sai kun san yama likis aka fito da saki tashi fatuha tayi tabi ganda har aka
bashi dakin sannan doctor ya nemi ganin majeed magunguna ya bashi tare da mai congrat an
gama aiki lafiya kowani lokaci yana iya tashi bakin majeed har kunne tare da hamdala da gode
wa Allah ko da ya dawo albishirin da yayi ma fatuha kenan tare da curo wayar shi ya bama su
mom albishir sannan suka shaidamai suma gobe zasu iso fita yayi ya bar dakin tare da shaida
ma fatuha tare zasu dawo da su basma to ta ce mai tare da shigewa toilet dan ta dauro alwala.

Bayan ta gabatar da sallah tana qoqarin linke daduma sadiq ya fara motsawa kusa da shi ta
matsa ta tsaya a hankali ya fara bude sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha kallan ta
yake kamar wanda bai taba ganin ta ba tare da fara bin asibitin da kallo, cikin sanyin murya
yace ruwan, ruwa ta tsiyayo mai a glass cup ya kafa kai ya shanye tare da lumshe ido ya ware
su yace fatuha na'am tace tana qoqarin taba sumar shi riqe hannu ta yayi tare da cewa ina mijin
ki miya kawo kinan bai ida rufe bakin shi ba majeed yace akwai wani mijin ne bayan kai ya ida

zancan yana qarasowa gaban gadan, kallo sadiq ya bi da shi mai cike da mamaki daga mai gira
majeed yayi yace karfa kayi mamaki da kai aka daura aure badani ba Ni ga matata fatima ce ta
shigo tana smile basma ta biyo bayan ta tana jingine da qafadar Khaleed mamakine ya lulube
sadiq Khaleed yace karfa kayi mamaki dama over taking kamin yanzu kuma na dau abita ya
ida zancan yana dariyar shaqiyanci ai sai ka miqe yanzu tunda an daura da fatuha rife fuska
fatuha tayi tana qoqarin barin gun riqe hannuta sadiq yayi tare da sakin smile yace kun fiye sa
ido ya fada cikin cool voice saboda har yanzu be jin shi yadda yake ba amma jin wannan labari
ba qaramin dadi ya mai ba sai kallan juna suke shi da fatuha, haka suka dinga raha suna bama
Sadiq kulawa har ya fara jin ya warke, kiran sallah magrib ne yasa su ka fita tare da matan su
dan su dauro alwala a masaukin su kasancewa masaukin ba nisa da asibiti suna fita fatuha ta
tashi tana qoqarin itama shiga toilet din riqe ta sadiq yayi tare da janyo ta fado saman fadadan
qirjin shi a hankali ya hada bakin su guri guda ya fara kissing nata sun dau minti suna a haka
sannan ya sake ta tare da hada face nasu guri daya yana wasa da yan yatsun hannuta a
hankali ya bude Baki yace my wife smile fatuha tayi tare da lumshe ido cikin cool voice sadiq
yace fatuha bani da abinda zance sai dai Na gude ma Allah daya baki ni ban taba tunanin zan
shiga wuni hali saboda rashin ki ba hannu fatuha sadiq ya janyo tare da daurashi saitin zuciyar
shi yace fatuha ke ce rayuwa ta idan babuke babu ni bana jin zan iya rayuwa babu ke I love u
form the bottel of my heart ya ida zancan yana langwabe kai yace please ki ce kina so na
please ya ida zancan kamar qaramin yaro rungeme shi fatuha tayi tana hawayan farin cikin
zame jikin ta ta yi tana qoqarin ta shi riqe ta sadiq yayi yace baki ce komai ba rufe fuska tayi
tare da saurin shigewa toilet jingina nayi jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya tana smile cike da
farin ciki ta gabatar da alwala ta fito har ta fito sadiq Na binta da kallo ta gabatar da sallah tana
idar wa majeed ya shigo da take away ya aje tare da shafa kan sadiq pack ya mai tare da sakin
lalausan murmushi yace please for give me bros lumshe ido sadiq yayi yace mention not tare
da laqace mai hanci dariya sukayi lokaci daya sannan majeed yace ai saika miqe ka warke
tunda ga muradin ranka kusa da kai ya ida zancan yana kashe ma sadiq ido duka sadiq ya kai
mai na wasa ya goce tare da qarasowa saitin kunnan shi ya mashi wata magana dariya suka
saki a tare majeed ya fita da sauri yana cewa mu dai asuba ta gari dariya sadiq yake har da yar
kwalla pack fatuha tamai tace mai kyau me yace ma haka har ya saka wannan dariyar smile
yayi yace zaki Sani amma not now amma very soon zaki ji ya fada yana kashe mata ido
murmushi tayi tare da janyo lafiyayan abinci ta fara feeding nashi yana amsa.


Ko da majeed ya koma masaukin su fatima Na wanka cikin toilet daure da qaramin towel ta
fito ganin shi zaune saman bed yasata yan noqe noqe ta fara shirin duk kunya ta isheta shima
rage kayan jikin shi yayi ya wuce toilet ya watsa ruwa tare da dauro alwala ya fito,

Shiryawa tayi cikin pink night dress masu kyau masha Allah ta yi kyau sosai Kuma kayan
sun hauta saman bed ta hau tare da shigewa cikin blanket tayi lamo ko qala majeed be ce mata
ba shima ya shirya sai da ya gama shirin shi yace fatima a hankali ta dago yace mata tashi ki ci
abinci dan smile tayi tace Na koshi ai naci abinci a asibiti ai wannan daban ne dana asibiti ki
tashi mana ya ida zancan yana langwabe kai ba musu fatima ta tashi zaune tare da zama
saman carpet kaza ce lafiyayan majeed ya bude tasha rumo ta gaji a hankali majeed. ya rinqa

feeding din fatima tana amsa sai da suka ci suka koshi sannan ya dauke komai tare da bata
umarni ta dauro alwala, brush tayi tare da dauro alwala haka shima majeed tare da ja masu
sallah raka'a biyu suka godewa Allah, bayan sun idar majeed ya kama kanta ya mata addu'a
sannan ya dauke ta kamar baby sai kunya take ji ya daura ta zaman bed kissing nata ya fara
cikin salo yana shin shin kamshi turaran ta ganin zasu wuce gona da iri ya Sani fita jiki a sabule
har ina tuntube saboda harara da majeed ya wurgo min


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login