Showing 60001 words to 63000 words out of 99609 words

Chapter 21 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

Advertisement

fatuha fita daga gidan sadiq ya fita da ido bata zame ko ina ba
sai gidan su fatsima tana Shiga ta shiga kwalla mata kira ba fatsima ba har gwago a rude suka
fito saboda jin muryar da suka dade suna kewa, da gudu fatsima ta fada cikin fatuha tare da
sakin kukan farin cikin murna ba'a magana d'akin ta ja fatuha sai dai yanzu fatsima duk tayi
sanyi nan take taba fatuha labari ranar daurin auranta mijin ya rasu fatuha sai da ta tausaya
mata sannan suka koma gida a tare lokacin inna har ta bama Sadiq masauki tare da kayan
motsa baki jidda kuma na maqale da ita.

Kun san a tare suka wani da fatsima inda sadiq ke ta fushi fatuha ta barshi shi d'aya, basu
suka rabu da fatsima ba sai gab da magrib lokacin baffa ya dawo shima cike da farin cikin inda
ya dinga jan sadiq a jiki suna taba hira Sama sama. inda inna ta cika mai fura da nono da
tuwan dawa miyar kuka tasha manshanu sosai sadiq ya saki jiki yaci abincin.

Misalin karfe 8:30pm b'ayan sun d'awo d'aga masallaci sadiq ya wuce masaukin shi, b'ayan
fatuha ta gama sa k'ayan bacci ta shirya jidda itama cikin nata sannan ta h'ada ma sadiq coffee
kamar yadda ta saba a gida ta ja hannu angel suka wuce masaukin cikin sallama ta d'aga
labilan d'akin suka shigo, amsawa yayi a taqaice ta aje mai coffee ya amsa tare da aika mata
harara wasa hannuwanta biyu tasa a kunne alamar bada hakuri hira sukayi sama sama inda
angel ke ta zuba qiriniya har bacci ya kwashe ta daukar ta fatuha tayi tana qoqarin fita sadiq ya
masu pack a tare suka wuce d'akin fatuha.


*Washe gari*

Tunda safe fatuha ta tashi ta share tsakar gida tasses, ta hura icce ta dora koko tare da
dumama tuwan jiya, ta juye a kwanan samira tana qoqarin fitowa d'aga kitchen din inna ta fito
d'aga uwar daka washe da baki tana bin tsakar gida da kallo , alalai fatuha anyi hankali har
qasa ta gaida inna ta amsa cikin fara'a sannan ta shige qurya ta fido jidda ta wanke ta tas ta
shirya ta cikin jean n t-shirts masu kyau sannan itama ta shige kewaye tayi wanka, b'ayan ta fito
ta shirya cikin riga da sket na lace red mai kyau sai yar huda d'ata murza da lipstick ba qaramin
kyau tayi ba sannan ta dau kwanonin da tasama sadiq abinci ta nufi d'akin inna da ke surfa gero
tace "Aiko dazu da sasafe tare suka fita da baffa ki gona" murmushi fatuha ta saki tace shine
baffa beje dani ba ko? ta zuburo b'aki tare da shigewa ciki ta aje mai abincin tana fitowa ta ci
qaro da fatsima washe da baki ta tarbeta kusan a tare su kayi kallaci sannan suka fita yawo
ganin gari duk inda fatuha ta wuce sai antanka da irin kyanda tayi da natsuwar da ta qara haka
aka rinqa Layin ganin ta inda ta rinqa baje tsaraba tana rabawa fatsima ko tasha tsaraba kamar
ba gobe.

Kwana su biyu a kauye inda yan kauye ke cewa fatuha ta zo da larabawa sun sha yawo da
sadiq har rafi sai da ta kai shi, da gona mai gari inda suke satar mangwaro a da, sosai ya ji d'adi
kauyan ba dan k'adan ba,


Fatuha ce riqe da trolley tana rusa kuka ita bata komawa, sai da inna tayi da gaske sannan
ta shige mota sadiq yasa trolley a boot tare da yima baffa shatara na arziqi baffa duk yadda
baffa yaqi amsa haka sadiq ya matsa mai amsa tare da samai albarka fatsima har da yar
kwallata sannan suka dau hanyar kano. ********** ********** ******

Akwana atashi ba wuya wajan sallah fatuha dai ta fara zuwa makaranta inda aka sata jss1
sosai take maida hankali kuma tana gane karatun gashi Allah ya zuba mata qoqari na ban
mamaki, dan har tafi masu qoqarin ajin a yanzu a tare suke zuwa da jidda a yanzu jidda na
primary 2 kusan duk makarantar su d'aya da su hanan da basma hakan ya qarasa suka shaqu
duk inda kaga hanan to zakaga fatuha ko basma sosai suke maida hankali akan karatunsu.

K'amar yadda aka saba tashin su misalin karfe 3:30pm driven yayi parking suka bale murfi
motar suka fito a tare, sanye fatuha take da uniform din ta riga mai dagwan hannu milk sai sket
dark green dai -dai gwiwa sai dan qaramin hijab milk jidda kuma biri da wando milk a ciki rigar
saman green kallo d'aya zaka masu kasan sun gaji likis tun a parlour jidda ta fara wurgi da jakar
ta, ohno why this angel bari dai grandma ta fito ta Zane ki, sama nayi da ido ina tunanin wake
wurgo wannan turancin kamar a mafarki ashe fatuha ce ohni salma😧, daukar bag din jidda tayi
tana zunburo baki ta kai bedroom din ta,

Har fatuha ta shiga bedroom din ta ta fara cire mabalin rigar ta, ta tuna da ice cream din ta
d'ake bedroom din sadiq cikin fridge da sauri ta fito ta haura upstairs a h'ankali ta bude part din
ta shige parlour ba kowa sai kamshi d'ake tashi, bedroom ta shige tare da nufar fridge din ganin
Sadiq tsaye yana qoqarin cire rigar uniform din shi tace uncle waigowa yayi cikin smile yes dear
um, ya naga ka d'awo yau da wuri haka uncle? na gama aiki ne gobe da safe flight dina na
zuwa london ze tashi zani wani course ne ba zata ya zo min h'ada kayana na d'awo yi , dan
bata fuska tayi tare nufar fridge ta dau ice cream tana ta kunbure kunbure ta fice Sadiq ya bita
da kallo.



*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼â€â™‚

*Writing by*

*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*


📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com



*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM


*69_70*

*_í ½í±í ¼í¿½Godiya gare ku mosayan â¤wannan novell din, ina jin d'adin y'adda kuk'e commentsí ½í¸ ana
mugun tare irin sosai din nan._*🤸🏽â€â™€í ¾í´¸í ¼í¿½â€â™€


*_wannan shafin naki ne Maimuna Lawal Allah ya bar zuminci har ya'ya da jikoki Ameení ¾í´._*


*F* atuha na shig'a bedroom din ta, ta aje ice cream din saman bedside drowe d'an gabaki
d'aya ice cream din yafita ran ta, a duniya ba abinda ta tsana kamar mai kyau yayi nisa da ita,
ita kanta har mamakin h'akan take jiki ba qwari ta ida cire school uniform din ta tare da shigewa
bathroom ta sheqa wanka ta fito, b'ayan ta tsane jikin ta tabi da lotion mai kamshi tare da sanya
black after dress din ta mai Stone's d'aure gashin kanta tayi kamar ganmo tare da Murza yar
hod'a da lipstick masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, fitowa tayi d'aga bedroom din ta
wuce na mom cikin sallama ta shiga mom Na tsaye gaban dress Mirror tana shirin da alama fita
za tayi cikin fara'a ta amsa,tace "Mom fita zakiyi ne?", eh wallahi zani gidan ammi ne, d'ama
yanzu nake cewa ko zaki raka ni ?dan murmushi fatuha tayi itama tana san zuwa wajan ammi
din nan amma tunda ta zo sau biyu ta taba zuwa g'ashi tana san ganin basma, amma
Assignment ba zai bari ba gashi malam anjima zaizo , mom kin manta yau Wednesday, oh haka
fa na manta fa shafa next time munje kuma wallahi mom ina san zuwa basma har ce min take
bani da kirki bana zuwa, ai ta fada duk zaryar da suke maki b'aki zuwa masu kema kin fara
k'oyan h'alin uncle din naki, dan smile fatuha ta saki mai cike da jin d'adi ita dai duk abinda za'a

ce d'aga mai kyau yake so take ,mom ai baya san yawo uncle shiyasa. ke kuma sai biye mai
kike ko? zuminci fa abin wasa bane mom ta ida zancan tana daukar handbag din ta kusan a
tare suka fito, angel na zaune a parlour tana k'allan cartoon ganin grandma zata fita yasa ta
tashi grandma zan biki please nop yau malam zaizo zuburo b'aki tayi gab'a tana sanyin kuka
please grandma ki je dani,angel kiyi h'akuri grandma ta je kin ji? muma ranar Friday mun tafi
kinji? d'aga kai jidda tayi b'adan taso, ba har b'akin mota suka raka ta suka juyo.

A dai-dai b'akin kofa suka ci qaro da sadiq sanye da 3 quarter black da white t-shirts da
alama gym zashi, k'auda kai fatuha ta yi ala dole fushi take da sadiq, smile yayi tare da d'aga
angel sama yana mata wasa tana d'ariya ko k'allan inda fatuha take beyi ba saboda ya lura yau
rigima take ji, rabawa tayi ta gefan shi zata wuce ta cika tap qiris take jira ta fashe, ruqo hannu
ta yayi h'akan yasa ta tsaya chak a wajan, ta kasa kwace hannu ta sai binshi da take da kallo,
aje jidda yayi qasa yana aje ta kamar jira take tayi cikin gida da gudu, fisko fatuha yayi ta fado
fafadan qirjin shi har tana jin bugun zuciyar shi lamo tayi a qirjin nashi, a hankali ya d'ago da
habar ta yana kallan ta lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha cikin cool voice din shi yace
"Fushin na menene?" um dan b'ata rai tayi tana qoqarin zamewa d'aga jikin shi tunda be san
fushin me take ba, dan matse ta yayi da karfi ta saki yar qara, ta fara matsar kwalla, d'aga nace
zanyi tafiya sai fushi fatuha 3 days fa kawai zanyi kin ji dear, turo b'aki tayi gaba ni ba fushi nake
ba. to me kike? ba komai, ok tunda ba fushi kike ba please ki h'ada min k'ayana na rasa k'ayan
da zansaka ki riga kin shagwaba uncle da yawa, dan zunburo b'aki ta kuma yi maicike da
shagwaba, please karki ce bakiyi, zanyi mana promise ,promise good girl sannan ya mata pack
a goshi ya fita.

B'ayan ta kamala h'ada mai k'ayan sannan ta kalli agogon d'ake mane a d'aki kusan karfe
4:30 sauri fitowa tayi d'aga part din ta wuce bedroom, d'auro alwala tayi tare da gabatar da
sallah tana gamawa ta d'auko alQur'anin ta saboda yau laraba, alqur'ani kawai suke yi tare da
janyo hijab din jidda tun a parlour ta zura mata suka fita a tare, lokacin har malam ya zo karatu
suka yi sosai INSA malam y'a masu qarin bayin akan hadisi, sai gab da magrib suka shigo
cikin gida, alwala k'awai suka gabatar tare da yin sallah b'ayan ta idar ta tsaya yin lazimi sannan
tayima jidda assignment tayi nata kiran sallah isha ne ya tashe su bayan sun gabatar suka fito
parlour sukayi dinner sannan kowa ya wuce bedroom din shi saboda sun gaji likis.


*Asuba ta gari*

Sallah asuba fatuha tayi tare da yin wanka, mai kawai ta shafa tare da sa yar gown iya karta
gwiwa sannan ta fito bedroom din jidda ta shiga tayi mata wanka tare da shirya ta cikin unform
sannan ta bar d'akin, kitchen ta shiga cikin sallama baba jinmai nata jefa bafanke gaishe ta
fatuha tayi cikin fara'a ta amsa sannan suka gaisa da rabi'a, bude fridge tayi tare da fido yan
cikin rago ta gyara ta d'aura kan wuta tare da zama tana taya su baba jinmai aiki ,sai hanata
suke amma taqi sai da farfesun yayi ta juye a kola tare da h'ada coffee tasa a tray direct part din
sadiq ta wuce ,a hankali ta murda k'ofar parlour ba kowa aje tray din tayi saman stool ta nufi
bedroom din tsaye ta h'ango sadiq yana qoqarin sa necktie sallama tayi tare da gaisheshi cikin

fara'a ya amsa sannan ta qaraso ta amshi necktie din tana samai bayan ta samai ta kalle shi
uncle u looking so handsome tare da mai pack shima pack ya mata tare da daukar suit din shi
black ya riqe a hannu ta ,janyo trolley din tayi suka fito parlour lokacin angel ta turo kofar tare da
cewa "Daddy ta fada jikin sadiq" hug nata yayi d'an shagwabe fuska angel tayi daddy am going
to miss u daddy, me to angel, amma daddy zaka min tsaraba teddys yes angel washe b'aki tayi
tace "Anuty fatuha k'ema ki fadama daddy tsarabar da zaimaki" smile tayi tare da cewa "Duk
abinda daddy yake so shi nake so yamin tsaraba" kallan ta sadiq yake me cike da so sannan ya
zauna saman one star tray ta janyo ta zuba mai farfesun a ball saboda sadiq mutun ne mai san
farfesu shiyasa fatuha kullun sai ta mai dan ta faran ta mai, feeding din shi farfesun ta fara yana
sha angel itama tana bashi haka suka rinqa feeding din juna su cikin jin d'adi happy family
sannan suka fito tray din fatuha ta kai kitchen ta wuce bedroom tasa uniform tare da d'auko
school bag din ta.

Fitowar ta parlour yayi dai dai da fitowar su mom da abba cikin natsuwa ta gaishe su pack
sadiq ya masu shida angel itama fatuha pack tayi ma mom suka fice a tare mota d'aya suka
shiga da sadiq driver na ja sai da aka zo school din su yayi parking, gaba ki daya idanunta
sukayi rau rau alamun zatayi kuka, suka bama sadiq hug suka fice yana kallan su har suka
shige classes sannan driver ya ja mota sai airport.


Tunda sadiq ya tafi su angel suke missing nashi mom har mamaki suke, bata ko yar
rahanan sun daina inkaga suna raha to sadiq ne ya kira waya haka shima can cike yake da
kewar su inda yake jin kamar wata yayi ba kwana uku ba.

Akwana a tashi ba wuya wajan Allah yau kwana sadiq biyar kuma yaune ranar dawowar shi,
zo ku ga murna wajan su fatuha sai zuba rawar kai ake mom sai janta take dan yanzu fatuha ta
tashi d'aga yar aiki dan tuni sadiq ya yan'tata duk wani abinci da sadiq ke so fatuha ita da kanta
ta mai sannan ta jera a dining area.
Bedroom ta shige tare da yin wanka, k'aya ta fido ta rasa wanda zata sa duk wanda ta fido
sai ta maida can ta h'ango wata red gown me Stone's, aje ta tayi a gefe ta tsantsara kawalliya
ba qaramin kyau tayi ba sannan ta zura riga masha Allah indai maganar kyau ake fatuha ta kai,
angel ce ta shigo da gudu itama sanye da gown pink tace "Anuty daddy ya dawo?" waigowa tayi
tare da yin fari da ido suka fito a tare shigowar sadiq parlour kenan su fatuha suka fito, k'allo
sadiq ya bisu da shi mai cike da so rugawa su kayi a tare suka rungume sadiq d'ariya ya saki
zaku ka dani ya fadi mom dake saukowa d'aga upstairs dariya ta saki tace "Sadiq kai da yaran
ka kuna dirama wallahi" smile yayi tare da hug din mom in taqaice maku duk wani girki da
fatuha tayi sai da sadiq ya ci inda yake ta binta da k'allo.

B'ayan ya hutu ya fido tsaraba yabama fatuha I phone 6 waya dadi da murna wajan fatuha
ba'a magana jidda kuma Tap Apple mai shegyan kyau tare da new Teddy's h'aka suka dinqa
zuba murna baki har kunne.

*2years letter*

Wata kyakyawar matashiyar budurwace da baza ta wuce 16 years ba ta rugu da gudu d'aga
upstairs gudu take amma komai na jikin ta amsawa yake sanye take da 3 quarter pink sai riga
white mai gajeran hannu ban gaje mutun da tayi ne ya sata tsayawa chak, cikin cool voice din ta
tace "Sorry tare da rabawa ta gefan shi ta wuce" mutuwa tsaye majeed yayi yana binta da k'allo
kafadar shi ya d'aga tare da sakin killing smile yabi stair's din da k'allo ,wai gowa ya kuma yi ko
zai ga yarinyar amma ba alamar mutun. sama ya hau direct part din sadiq ya wuce a hankali ya
murda handle din kofar ya shigo sadiq na zaune saman three star yana kallan news cikin
sallama ya qaraso amsa mai sallamar yayi tare da aika mai harara wasa, sai yau zaka nemeni
dan raini senses? dariya majeed ya saki tare da cewa "Sorry " ya zauna ni dai yanzu ba wannan
zancan ba wacece na gani yanzu kamar d'aga part din nan ta fito? gaban sadiq ne ya yanke ya
fadi qaqaro murmushi k'arfin h'ali yayi yace "Fatuha ce" *(Ohni salma🤦â€â™€ yaushe fatuha ta waye
haka🙄lol)* ok majeed yace tare da cije lips dinsa yana ayana wasu abubuwa a
ransa......hmmmm

*Muje zuwa fan's😘*


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼â€â™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★We are the best ★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

71_72

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login