Showing 66001 words to 69000 words out of 99609 words
Chapter 23 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
miqa d'auke, laptop din ta dake saman bed take qoqarin sadiq
ta hango kwance yana bacci , murmushi tayi tana qare ma kyakyawar face din shi kallo hannu
ta kai kan screen din laptop din can kuma ta janye hannu ta daukar laptop din tayi ta aje saman
sofa yadda zata riqa hango shi duk abinda take, toilet ta shige ta watsa ruwa tare da dauro
alwala daure da towel ta fito ko da ta fito lokacin sadiq shima ya tashi dan ba alamar shi ta cikin
laptop din bed ba kowa sama ,cikin Sauri ta shirya tare da gabatar da sallah sket din
makarantar ta ta janyo tasa tana gama sawa ta zura rigata tana bale ma balin riga ta, ta hango
sadiq tsaye shima yana bale nashi dariya suka saki a tare morning uncle, morning too dear kin
rigani tashi na riga ki shiryawa baki da sauri dan turo baki fatuha tayi dama can ka tashi idan ba
hhhhh, kwarankwatsi ban tashi ba fashe wa fatuha tayi da dariya saboda tasan tsokanar ta yake
kashe laptop din yayi domin ta qarasa shirya wa.
Kusan a tare suka fito lokacin angel har ta shirya cikin uniform din ta tana dining area ita da
mom da abba cikn natsuwa suka qaraso, gaishe da su mom su kayi suka amsa a tare sannan
suka ja kujera suka zauna saving din su fatuha tayi sannan suka fara break cikin jin dadi bayan
sun kamala pack sukayi ma mom, abba ne yace lalai gidan nan ana gwada min banbanci jiya
ina kallo mom dinku kukayi ma pack ni kuma ko oho ba komai zan rama dariya sukayi su duka
tare da ba abba hakuri kusan a tare suka fito mom ta rako su har bakin kofa yaran sadiq sai
qamewa suke, shigewa motoci sukayi abba ya shige nashi suka bar harabar gidan.
Sosai yau sun sha karatu har da test sai da sukayi na history sosai fatuha ke maida hankalin
ita da kawayan ta, Nana da Zara sune kawayan ta na makaranta kuma yan'yan masu kudi ne
masu ji da Wayewa da yan matanci, fatuha ko tun tana jss2 ta zana JSSCE saboda qoqarin da
hazaqa yanzu haka SS2 take hanan na SS3 Basma kuma ta gama, Nana ce ta kalle ta bayan
uncle ya fita daga class tace "Niko fatuha ina wannan uncle din nan naki mai kyau?" kallan ta
fatuha tayi tare da aika mata harara ina ruwan ki da uncle dina, laaa fatuha yaushe kika zama
haka? inji Nana, Zara d'ake gafe tace "Karki ga laifin ta wallahi ai dani ce fatuha da tuni na
canza zani wallahi, hmmm ku wai me kuke nufi ban fa gane wannan hausar taku fatuha ta fada,
hehe Zara da Nana sukayi lokaci daya, wallahi rainin hankalin nan namin dadi serious, to bari
kiji ki zauna nan kwado ya maki kafa wallahi dani na sami damar ki da tuni na dama wallahi inji
nana, ku dai Baku da aikin yi ni ina da . uncle kuma nifa a matsayin wana na d'auke shi ba
komai ba Allahu Akbar bugu fatuha ta kaima Nana da Zara da littafin dake hannu ta.
Basma ce zaune ita da umma tana taya ta kwalema a d'akin ta, pic din sadiq ne ya fado hannu
ta kai ta dauka ta kurawa pic din ido umma ce ta taba ta firgigit ta dawo d'aga duniyar tunani
tare da qoqarin aje pic. din murmushi umma ta saki yar auta me ke damun kine kwana biyu
naga duk kin rame kin zabge kamar mara lafiya hawayan d'ake maqale a idanuwan tane suka
zubu tare da riqe hannu umma, tace " Umma na rasa me ke damuna tun zuwan da yaya sadiq
yayi kwanaki na rasa meke damuna wallahi ummaí ½í¸ ina son yaya sadiq ta ida zancan tare da
rushewa da kuka" lalashin ta umma ta shigayi haba auta me abin kuka? share mata hawaye
umma tayi duk wata mace mai lafiya dole taso sadiq saboda ya tare duk abinda mata ke so
basma insha Allah zan taya ki da addu'a, idan sadiq alheri ne a gare ki Allah ya baki shi inko
haka ta faru sai nafi kowa farin ciki da kinga sai a h'ada da naki dana majeed tunda shima jiya
yake fada min ya samu wadda yake dai-dai tawa da ita , murmushi basma ta saki tare da fita
d'aga dakin da gudu umma ta bita da kallo tayi murmushi irin nasu Na Manya.
Misalin karfe 12:30pm suka tashi dag'a makaranta kasan cewa yau friday angel na gefan ta
suna jiran drive, hadadiyar motace baka ta faka gaban su fatuha kauda kai fatuha tayi kamar
motar ba gaban su ta tsaya ba ,saboda glass din motar tinted ne ko na ciki ba'a gani zuge glass
din akayi hakan yasa angel washe baki tare da cewa "Second daddy?" majeed sanye cikin
uniform din shi na aiki murmushi ya saki bale murfin motar angel tayi kamar tana jira ta shige
gaishe shi fatuha tayi a taqaice tare da cewa angel fito kin san driver ne zai zo daukar mu ta
fada, murmushi majeed yayi yace "To ni zan d'auki kyankyawa yau na kai ta har gida dan tun
dazu na kori driven" dan zaro ido waje fatuha tayi tace "Sokake uncle ya Mani fada KO?" ah
uncle ba zai maki fada ba ai yasan ni zan dauke ku dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi laban
ta ta bude murfin motar ta shiga cikin natsuwa ya ja motar inda yana driven yana kallan fatuha
ta cikin mirror .sai da ya zo dai dai b'akin geta yayi horn bala mai gadi ya bude mai geta parking
yayi su fatuha suka fito tare da mai Godiya sai da suka shige cikin gida yayi ribas ya fita.
Shiga office din majeed sadiq yayi amma wayam ba majeed dan tabe baki yayi tare da
fitowa d'aga office din ,da khaleed ya ci karo wanda shigowar shi yanzu kenan cikin fara'a sadiq
ya tarbe shi, "Ah wai har yanzu majeed be dawo ba?" oh kama san da fita kenan eh munyi
waya nace mai zanzo shine yace min yaje daukar baby shin d'aga school, baby sadiq ya
maimai ta wallahi bansan sanda majeed zaiyi hankali ba wallahi mtww yaja Khaleed suka wuce
office din shin.
Bayan sunyi lunch fatuha ta shirya tsaf cikin lace din ta maroon anmata dinkin bubu da lace
din sosai kayan sun fido ta ,dan kwalin ta ta daura shi hawan hawan daurin ya zauna kamar
gwagwaro janbaki ta shafa maroon da yar hod'a kwalliya sosai ta zauna ta tsantsara veil din ta
ta dauk'o white ta yafa masha Allah fatuha ba qaramin kyau ta zuba ba,
Tana fitowa parlour ta sami mom da majeed sunata zuba hira yana sanye da blue shad'a
tasha aiki, cikin zazakar muryata fatuha tace "Mom zan je gidan mami, to, shikenan ki gaishe
min da su zasu ji, majeed ne yayi karaf yace " Tunda tafiya nima zanyi bari na aje ki a can?" to!
fatuha tace tare da yin gaba majeed yabi bayan ta shida kanshi ya bude mata murfin mota ta
zauna sannan ya bude ma kanshi ya shiga,
Ko 20 minutes basu dauka ba suka Isa gidan Anuty bilki, inda majeed keta janta da surutu
har ta dan saki jiki da shi yana yin horn mai gadi ya bude ya shigo da motar tare da yin parking
qoqarin fita d'aga motar take majeed yace "Baki ji ba, waigowa tayi sannan yace karfe nawa
zaki koma gida?" da yama ta fada a taqaice. toh! shikenan zanzo daukar ki Godiya ta mai tare
da shigewa cikin gidan.
Da gudu hanan ta rugo ta rungume ta kai amma naji dad'i wallahi, gaishe da mami tayi dake
zaune parlour tana kallo sannan hanan ta ja ta bedroom suka baje suna ta zuba hira cikin jin
dadi kai ka ce yan'uwane yadda suke nuna ma juna so sai kusan yama likis majeed ya zo gidan
Anuty bilki inda ta rinqa zuba mai shaqiyanci shida sadiq sun raina ta basu san zuwa gidan ta
sai da dalili shi dai Sosa keya kawai yake sannan suka bar gidan suka nufo gidan,
Tunda sadiq ya kunno kai da motar sa driven na ja shi kuma yana b'aya, gyaran murya yayi
yace "Wancan motar kamar ta majeed? yallabai ita ce ai dazu dana zo daukar fatuha, Hajiya
tace min ai majeed ya kaita to qila sun dawo ne, wani qulolin bakin ciki ya tsayawa sadiq har
yana jin ya qasa hadiye miyau kusan a tare suka shigo gidan sai da fatuha ta fito majeed shima
ya fito murmushi fatuha ta saki tana ma majeed godiya, qoqarin bude kofar motar driver keyi yi
sadiq yayi magana a tsawace karka bude ya fadi, shi kan shi driver terere yayi da mamakin
canji sadiq lokaci d'aya .zaunawa sukayi a motar sadiq na hango fatuha da majeed, har tayi
gaba ta dawo ,oh na manta wayana a motar smile majeed yayi tare da bude motar ya curo
wayar ya bata, tare da cewa gaskiya yadda na dako wayar nan ya kamata ki bani number ki
dan murmushi tayi tace uncle number ta eh mana ya fada ko baza'a bani ba zan baka mana
curo wayar shi yayi d'ake gaban aljihu ya bama fatuha ta rubuta mai number ta sannan ya shige
mota ya bar harabar gidan.
Yana fita sadiq ya bude murfin motar cikin zafi, shigar fatuha bedroom ke da wuya taji an
banka do kofar cikin zafin rai waigowa tayi a dan tsorace fisgota sadiq yayi tare da fizge wayar
da dake hannu ta yayi wurgi da ita ta bigi Bango ta dawo a tarwatse ware ido fatuha tayi tare
da sakin kuka, manna ta sadiq yayi da b'ango ya koma mata kamar zaki idanuwashi sunyi jawur
kamar garwashi cikin kakausar murya yace "Waya baki izini fita gidan nan bada driver ba?"
kuka fatuha ta kuma saki ko bakin magana ta rasa ganin bata da niyar bashi amsa yasa sadiq
sakinta tare nufar kofar fita ya banka ta da karfi ya fita hata mom dake part din ta sai da taji
bugun kofar da sadiq yayi. zame wa fatuha tayi awurin tare da sakin kuka, koda sadiq ya Shiga
part nashi cili yayi da bribriefcase din shi saman three star ya zauna tare da lumshe ido yana
maida numfashe sama sama. ware idanuwan shi yayi saboda d'aya rintse fatuha da majeed ya
yake gani shafa ganshin kanshi yayi da hannu yace noooooooo! Cikin d'aga murya........
*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
í ½í±®í ¼í¿¼â€â™‚
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
í ½í³˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*í ½í°„
★We are the best★
http/mobile.Facebook.co m/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_ speed_dial_&yn=H-R
*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM
75_76
Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan taja jiki ta hau saman bed ,tarasa dalilin da yasa mai
kyau yake yin irin haka. kuka ta kuma rushewa da shi data tuna a irin yana yin data ganshi,
h'aka ta riqa raira kuka kiran sallah magrib yasata tashi jiki ba qwari ta dauro alwala tare da
gabatar da sallah. zaune tayi bisa daduma abin tausayi ganin tunanin be fishe ta yasa ta janyo
AlQur'ani tana karantawa har aka kira sallah ishi bayan ta idar da sallah ta ja jiki ta koma bed ta
cigaba da raira kukanta abin tausayi turo kofar da akayi ne yasata miqewa tana kallan kofar,
angel ce tsaye bakin kofar qarasowa tayi d'akin tare da hawa saman bed din tace "Anuty waya
saki kuka?" murmushi fatuha ta qaqaro wanda iya karshi laban ta tace "Ido nane ke ciwo" sorry
Anuty , ki fito parlour kuyi dinner naji shuru ne baki fito ba ke da daddy shiyasa na biyo ki.
dadday dai yace ya koshi, ko kema kin koshine? ta fadi zancan tana kallan fatuha Dan smile
tayi tace ban qoshi ba ina nan zuwa naci komin dare fita jidda tayi d'aga daki'n fatuha ta cigaba
da raira kukan ta har sai da kanta ya fara ciwo, ganin bame lalashin ta yasa tayi shuru tana
sauke ajiyar zuciya bacci barawo ya sace ta.
Bangaran sadiq in ban da juyi saman bed ba abinda yak'e da kyar ya samu ya rintsa.
*Asuba ta gar'i*
Ko da fatuha ta tashi jiki ba qwari tayi sallah sannan ta qara komawa ta kwanta saboda kanta
dake mata ciwo. Kuma taci sa'a yau weekend ba ita ta tashi ba sai karfe 11:30pm ware ido tayi
tare da kallan agogan d'ake makale a daki'n, cikin sauri ta mike tare da shiga toilet ta watsa
ruwa. ko da ta fito mai kawai ta murza sai after dress d'ata zura parlour ta fito ba kowa dining
area ta wuce tare da bude kulolin dak'e jere wanjan chpis ne da farfesun yan'ciki zuba wa tayi a
plate tare da had'a ruwan tea sannan ta zauna. loma biyu zuwa uku tayi ta ture plate din dan
kwata kwata bata jin d'adi abincin.
Babban abinda ke daure mata kai ta rasa laifin da tayi ,yanke shawarar zuwa bama sadiq
hakuri tayi duk da bata san laifin data mai ba dan bata iya jurewa wannan horan. tashi tayi tare
da kwashe kwanikan ta kai kitchen sai da suka dan taba hira da su baba jinmai sannan ta fito.
Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta murda handle din kofar tare da shigowa cikin
sallama zaune sadiq yake saman two star da laptop gaban shi kallo d'aya zaka mai kasan babu
annuri a fuskar shi. dogo kai yayi ya kalli fatuha tare da lumshe ido ya kauda kai yace "Just
leave me alone" sadiq ya fada a tsiwace tare da tatara takadun d'ake gaban shi da laptop din ya
shige bedroom tare da buga kofar da karfi. kuka fatuha ta saki tare da fita d'aga part din da
gudu jin ta fita yasa sadiq jinji Na da kofar bedroom ya lumshe ido.
Da gudu ta wuce mom a parlour ta shige daki saman bed ta fada tare da sakin kuka mai cinrai.
kuka taci ta gaji, mom d'ake parlour bin fatuha tayi da kallo tana mamakin mai ya h'ada su,
koma dai minene ai sun saba zasu shirya ne amma abin mamaki basa kai haka kauda zancan
mom tayi tare da cigaba da kallan ta, duk yinin yau babu wanda yaci abinci cikin su fatuha inban
da kuka ba abinda take shi ko sadiq sai baki'n rai dayake fama da shi,
Iskace mai sanyi da ke ta kadawa da alama ruwa za'ayi saboda damuna data fara shigowa.
qara cida ce kawai ke tashi b'akin widow sadiq ya tsaya a hankali ruwa ke saukowa kallan
ruwan yake yanda yake saukowa da karfi a wannan karan lumshe ido yayi tare da ware su, ya
koma saman bed ya kwanta bangaran fatuha tunda aka fara ruwa tak'e lilibe cikin blanket
Gaba ki d'aya yini yau ba wanda yayi ma wani magana cikin fatuha da sadiq, horan dak'i
sukayi wa kansu ba tare da sun nemi abin sama bakin sallatin su ba , har bacci ya kwashe su.
Shiryawa yake cikin manyan kayan shi kasan cewar yau zasu je family meeting, fatuha ce ta
fado mai a rai kawar da tunanin yayi dan har yanzu be huce ba ko yana hucewa sai ya d'awo
dag'a meeting cikin Isa yake saukowa d'aga upstairs ,lokacin har su mom sun shirya suna
parlour zaune suna jiran fitowar sadiq da fatuha ganin sadiq ya sako yasa mom cewa angel,
kira Anuty mu wuce , ko da angel ta shiga d'akin kwance ta samu fatuha qudindine cikin blanket
, fitowa tayi da sauri d'aga bedroom din tace "Grandma Anuty bacci take" toh fa! amma ai fatuha
bata kai haka tana bacci .shiga d'akin mom tayi tare da qarasawa wajan bed din fatuha tace a
hankali, a hankali fatuha ware idanuwan ta da suka yi nauyi saboda tsabar kuka, kallanta mom
tayi tace "Mike damun kin fatuha?" dafe kai tayi tare da cewa mom "Kai nane ke ciwo" eyya
sorry dama meeting zamu tunda b'aki jin dad'i ki zauna kawai a gida to kawai tace tare da
shigewa blanket, sannan mom ta fita ko da ta fita sadiq ta aika ma harara tare da ayana ma
ranta in sun dawo zatayima abin tufkar hanci.
Katafarin parlour su da aka ware danyi meeting suke zaune, tunda sadiq ya shigo gaban
shi ke yankewa yana faduwa yarasa dalilin h'akan addu'a da ke bakin shi ya furta dan samun
na tsuwa. majeed ya shigo tare da zama gefen sadiq tare da miqa mai hannu suka gaisa da
kyar sadiq ke danne zuciyar shi kan majeed tare da bata hakuri, Alhaji babba ne ya shugo
sanye da babba riga tasha aiki sai sheqe kayan suke, cikin sallama ya shigo tare da zama a
kujerar sa ta musanman wato kakan su sadiq, ammi na gefan shi ta dama sauran jikoki da iyaye
na gefe da yan uwa .
Taro ya fara budewa da addu'a sannan