Showing 63001 words to 66000 words out of 99609 words

Chapter 22 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf


*_Ina matukar Godiya ga masoyan wannan novel, ina jin d'adin yadd'a kuke bani goyan b'aya
wannan shafin naku ne duk masoyin CAPTAIN SADIQ._*



Ko da fatuha ta shig'a bedroom wayar tace ta hau ruri d'ake bedside drowe, cikin fara'a ta
d'auka saboda sunan dak'e maqale a screen din wato hanan, daukar wayar tayi tare da kallan
screen din kasancewar video call ne saman bed ta haye, "Hey yan'mata ya kike?" lafiya lau, wai
yaushe zaki zo gida ne? ina so muje gidan ammi birthday din basma ya kusa, a ina za'ayi
birthday din? inji fatuha kema kin san ba'a gida za'ayi ba, tap aikin san h'alin uncle wallahi ba ze
barni naje ba, nifa matsala ta d'ake kenan wallahi, ke komai uncle komai . Eh naji din, yanzu dai
ki mai dubara sai muje , gaskiya ina tsoran fushin shin kin manta randa muka je birthday din
haoula kenan, wallahi ban manta ba ina sane ras, toh yayi kyau , amma fa zan shigo insha
Allah .to shikenan ki gaishe min da angel tam ta katse wayar tare da kwaciyar ta.


Kamar yadd'a suka saba in suka h'adu haka suka rinqa zuba hira tare da yin musu, d'ama
sun saba baza su taba rabuwa ba tare da sunyi musu ba, amma duk wannan hirar da su
majeed suke tunanin fatuha na maqale a ransa, kiran sallah magrib ne ya tashe suka d'auro
alwala suka wuce masallaci. basu suka dawo ba sai bayan sallah isha, ko da suka dawo
majeed bai shiga gidan ba d'aga waje ya tsaya tare da jan motar shi yana tunanin ta inda zai
bulo ma fatuha dan a gaskiya a shirye yake da ya aure ta kota halin kaka.......hmmm tofa🤭


Ko da sadiq ya shigo gidan mom na zaune a parlour ita da angel suna kallo, kallan parlour
sadiq yayi tare da cewa "Angel ina Anuty?" tana bedroom Ddy. ok yace sannan ya haura sama
ko minutes 5 bai yi ba ya dawo parlour tare da wuce wa bedroom din fatuha, zaune take saman
bed tana assignment da laptop din ta sanye take da rigar bacci dai-dai gwiwa sai gashin k'anta
data nanade shi k'amar ganmo,

Bud'e kofar da akayi ne yasa ta d'aga eye's ball's din ta ture laptop din tayi tana qoqarin
tashi, harara sadiq ya aika mata, tare da cewa "Ina car Key's dina?" zuburo baki tayi gaba, wato
kin rai nani ko? shine zan fita kika d'auke min car Key's kika boye . sorry uncle wallahi bana so
ka fita ne ka sha rana, Kuma da ka fita ai da bakwan ka be same ka ba am sorry tasa
hannuwata biyu a kunne Allah yaba ka hakuri. matsowa sadiq yayi kusa da ita har tana jin
saukar numfashin shi ja mata baki yayi har sai da ta saki yar qara, tabe baki tayi tana shirin yin
kuka kul kika min kuka wallahi yau sai kin kwana kina kneel down kuma kin san zan iya, bani
Key's din, bedside drowe ta bude tare da zaro Key's din ta miqa mai tana qoqarin komawa

saman bed janyo hannu ta yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau ta mai ba, lumshe ido
yayi tare da ware su a k'anta murmushi fatuha ta saki mai cike da sakwanni iri-iri, rufe idanuwan
ki kiga wani abu cikin sauri da zakuwa ta lumshe idanuwan ta wani dan kit ya fido tare da bude
kit din oya bud'e wata hadadiyar sarkar gold ce wani irin ihu fatuha tasaki tare da rungume
sadiq ,shima rungume ta yayi tare da kai hannu saman gashin ta yawarware daurin data mai.
cikin cool voice din shi yace "Gashin ki yafi kyau a h'aka" smile tayi tare da dagowa d'aga
fafadan qirjin shi ta juya baya tana facing din dressing mirror tare da matsar da gashin ta gefe
samata sarkar sadiq yayi ba qaramin kyau sarkar ta mata ba juyowa tayi tare da cewa "Uncle
na gode" murmushi sadiq yayi nike da Godiya fatuha yau kusan shekarana uku bana tunanin,
bana zuwa asibiti .murmushi ta saki tare da fita d'aga d'akin tana Isa parlour ta fad'a jikin mom,
mom kin ga sarkar da uncle ya siya min? murmushi mom tayi irin nasu na manya amma dai
gaskiya mun gode wannan kyau ta haka, lokacin yayi dai-dai da fito warshi d'aga bedroom din
fatuha, angel ce ta turo baki tace "Daddy ni fa☹?" ja mata kumatu yayi tare da fido mata zube na
gold ya sa mata murmushi ta saki love u daddy tare da yimai pack, lalai abin ma yar h'aka ce
kenan? yaran ka kawai ka Sani ni Kuma ko oho mom ta fada, bayan mom yaje tare da zuro
kanshi ta wuyan ta sorry mom next time ke zan siyawa kin ji Dan smile tayi sannan shima ya
zagayu ya zauna sun dade suna hira sannan kowa ya wuce bedroom din shi.


Bangaran majeed ko cikin farin ciki ya koma gida, ko da umma ta tanbaye shi sai ce mata
yayi ya kusa cika mata burin ta, murna ko har ba'a magana ko da ya koma d'akin shi da ya
rintsa ido fatuha yake gani h'aka ya rinqa juyi saman bed har bacci barawo ya sace shi.


*Asuba ta gari*

Kasan Cewar yau weekend fatuha ta shiga kitchen tare da su baba jinmai suna aikin suna zuba
hira kunsan a tare suka gama komai ,da misalin karfe 10:30 take tsaye gaban dining tana jera
kayan abincin cikin natsuwa sallamar da kayi ne yasata dagowa tare da kallan kofar ta amsa a
taqaice majeed ne ,sanye da shada ash tasha aiki sai kamshi yake zubawa dining area yanufo
tare da yin smile fararan hakoran sa suka bayana. gyara murya yayi tare da cewa "Dama ashe
kyawawa na aiki, gaskiya kamata yayi ace warhaka kina barcci ?" dagowa fatuha ta danyi a
tunanin ta tuntuni ya shige ciki dan tasan kowaye a gidan saboda tasha ganin pics nashi dan
murmushi ta saki cikin yauki tace "Suwaye kyawawa anan? naga dai ni kadai ce ta ida zancan
tana wai gawa" murmushi ya Kuma saki a qaro na biyu fatuha kenan duk inda wata kyakyawa
take kin kai ai, idanma b'aki sani bâ to y au zan fada miki."wallahi kin h'ada d'uk wani abun da
ake nema wajen wata y'a mace, yar dariya ta saki wallahi yau uncle da tsoka ka zo gidan nan
ko?yau dai ranar tsokana ce? b'ata ida rufe b'akin ta ba sadiq ya shigo sanye da kayan gym din
shi da alama d'aga gym ya d'awo, tunda yaga fatuha da majeed tsaye gabaki daya anurin
fuskar shi ya sauya kamar an aiko mai da mutuwa daurewa yayi ya qaqaro murmushi my man
yaushe ka shigo? wallahi yanzu na shiga bama kowa parlour sai wannan kyakyawar d'ake ta
zuba aiki, Ni fa ko kallan ta ma kake ya Isa ya kosar da mutun d'aga yunwa .wani irin kallo sadiq
ya wurga ma fatuha tare da bin kayan jikin ta da kallo gown ce mai kyau sai dai ya matseta duk

wata sura na jikin ta ana gani, ganin kallan da sadiq ya mata yasa ta barin parlour ba shiri
,majeed Kuma ya bita da kallo har yana cewa har zaki gudu? ko tanka mai ba tayi ba ta shige
bedroom ,wai gowa yayi yana kallan sadiq ko lura da irin canjin da fuskar shi yayi bai lura ba ya
haura upstairs, sadiq ya biyo bayan shi bayan sadiq yayi wanka ya shirya cikin kanana k'aya
d'aya saba sawa suka fito tare da majeed dining area suka nufa, lokacin kowa ya halara gaishe
da su mom sukayi a tare, tare da jan kojera suka zauna, a'a yau wanake gani a gidan ?dan
murmushi majeed yayi yana sosa keya lalai ka kyauta, amma dai wuni ka zo yi? eh mana ki sha
kurimin ki mom nama kusa kwaso kayana na dawo nan da zama ya ida zancan sa yana
sunkuyar da kan sa kasa, dariya mom da abba sukayi sadiq ko ya cika fam kamar zai fashe.
janyo plate fatuha tayi zatayi saving din sadiq kamar yadda ta saba, sai da ta gama samin nashi
zatayi saving din majeed ya fakaici idanuwan su ya riqe hannu fatuha alamar kar ta zuba bata
dau abin komai ba a tunanin hutar da ita yake son yi, ta zauna ta fara cin abincin ta sadiq ne
yayi saving din majeed da kanshi sannan suka fara break duk wata loma da majeed zai kai sai
ya kai kallan shi ga fatuha idan sukayi ido hudu ya aika mata killing smile din shi duk wannan
abun a qwayar idanuwa sadiq, cikin bacin rai ya ture plate din shi cike da masifa da zafin rai ya
bar dining, kallo su M'y suka bishi da shi, fatuha ce tayi qoqarin tashi mom tace "Kyale shi ki
cigaba da cin abincin ki ,tunda kika ga h'aka ba qaramin bata mai rai a qayi ba d'aga kafada
majeed yayi tare da cewa " Indai sadiq ne ai ba yau ya saba haka ba" tunda sadiq ya bar dining
fatuha ta rasa natsuwar ta ,tunda safe ta lura yake d'acin rai ta rasa dalili...hmm!


Ko da ya shiga part din shi a parlour ya zauna tare da lumshe ido wani irin bacin rai na
damun shi ,Kuma gashi ya rasa dalilin h'aka dafa shin da akayi ne yasashi ware eye's ball's din
shi fatuha ce tsaye da plate a hannu ta cikin cool voice din tace "Uncle pls kayi break koma
waye ya bata ma rai kayi hakuri ta ida zancan tare da zama tana miqa mika ma plate din" amsa
yayi ya aje gefe yana kallan fatuha kamar me neman wani abu a fuskar ta can Kuma ya kauda
kai tare da cewa zanci kin ji tashi ki je bana san magana ne ya fadi yana lumshe ido fita ta zo yi
lokacin yayi dai-dai da shigowar majeed bigewa su kayi da junnan su, "ohshh majeed yace"
haka ma fatuha tayi b'aya waigowa sadiq yayi yana kallan su wani miyau mai daci ya hadiya.
dariya fatuha ta saki tare da cewa "Sorry , majeed" yace tunda nazo gidan nan kike bige ni, har
saida kika bige zuciya ta. zaro ido waje fatuha tayi tana dan kule bakin ta tace "Kai uncle ba
ruwana ta fadi zancan tana ida fita" ritse ido sadiq yayi tare da dunqule hannuwa shi yana mai
da numfashi sama sama majeed ne ya dafa shi lumshe ido yayi a hankali yana janyo natsuwar
shi zagayuwa yayi ya zauna , big man ina tunanin ka daina zafin ranan ashe har yanzu kana yi ,
wai ma waya bata ma rai haka big man?kawai am not in the mood shiyasa eyya sorry ko alura
ce ta motso ya fadi yana dariyar shaqiyanci pillow kujera sadiq ya wurga wa majeed wallahi ka
rainani kai naka bai tashi ba sai nawa, hhhh, kasan me ammi tace a'a tace wallahi next meeting
in bamu fido mata ba wallahi auran dole zata mana. Ni dai nayi mata wallahi very soon zaku
Santa ,amma kai ban sani ba kana nan kana ruwan idon nan naka, dan tab'e baki sadiq yayi
tare da cewa "Ba wani ruwan ido har yanzu b'anga wadda ta d'ace d'ani bane shiyasa?ko za
kayi bayani sanda ammi zata kwasoma yar kauye. Dariyar yake sadiq yayi tare da daukar
remote control...

*_Fan's ku d'anyi h'akuri da page din nan am to busy wallahi hakanan nayi page din dan farin
cikin ku A na tareí ¾í´_*



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼â€â™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM


73_74


*_this page is for you ummin mama_*


Sai baya'n sallah isha majeed ya bar gidan su sadiq, bayan sadiq ya d'awo party din shi ya
wuce yana shiga yaci qaro da angel na kallo cartoon, murmushi ya saki tare da cewa, "Angel?
ya qaraso kusa da ita ya zauna pack ya mata a goshi" daddy yes dear please gobe muje shan
ice cream please, sweetheart gobe ba time kin ga akwai work amma inna dawo da wuri zamu je
kijin angel ok daddy, daddy yau a nan zan kwana? ta ida zancan ta cikin shagwaba ." dan ja
mata h'anci sadiq yayi tare da cewa "Yanzu kin zama big girlfa? ko baki gani yanzu fa u are 9
year old ko baki Sani baby?" smile tayi ta ce "Haka kuma nima daddy zan zama kamar Anuty
fatuha ko idan na girma?" yes mana smile ta saki tare da yimai pack a goshi, good night daddy,

night angel.



Fatuha ce tsaye g'aban dressing mirror tana feshe jikin ta da turare da alama shirin bacci take,
dan kayan bacci ne a jikin ta pink da ratsin green riga ce dai-dai gwiwa mai dan siririn hannu
bayan ta kamala shirin ta, ta baza gashin ta har gadan bayanta. tsurawa dressing mirror din ido
tayi tana tuna lokaci da sadiq yasa mata sarka lumshi ido tayi tare da daurasu a wuyan ta saurin
ware ido tayi tare da cewa "U are very stupid fatuha tare da fita d'aga daki'n" bedroom din angel
ta shiga lokacin har ta shirya cikin night dress din ta, tana kwace cikin blanket a hankali fatuha
qaraso kusa da ita ware ido angel tayi kasan cewa bacci be dauke ta ba shafa gashin kanta
fatuha tayi tace "Angel bakiyi bacci ba?" um yanzu na d'awo d'aga party din daddy, ok pack
fatuha tayi mata tare da gyara mata blanket din ta kashe haskyan daki'n tare da rage gudun AC
dakin ta fita.


Ko da fatuha ta fita kitchen ta shige ta had'a coffee sannan ta daura cup din a dan qaramin
plate na glass ta haura saman, a hankali tayi knocking din part din come in aka ce hakan yasa
fatuha bude kofar a hankali ta shigo. sanyi AC ke tashi da kamshi na musanman cikin fara'a ta
qarasa shigowa sadiq na zaune saman three star sanye da night dress din shi maroon wando
da riga, cikin natsuwa ta samu guri ta zauna saman one star, miqa mai glass cup din tayi amsa
yayi yana smile kurba biyu zuwa uku yayi tare da kallan fatuha yace kamar akwai magana a
bakin ki dan murmushi tayi tana wasa da yatsun hannu ta, ina jin ki! uncle dama dama um gobe
ina so naje family house ne ni da hanan wani irin miyau sadiq ya h'ade take nan coffee din ya
fara fita ranshi ,waza taje gani family house ?ya fada cikin zuciyar sa qara h'ada rai yayi kamar
an aiko mai da saqwan mutuwa majeed ne ya fado mai a rai qara tsuke fuska yayi yace "Ban
shirya ma zuwan ki family house ba" ya fadi a taqaice, uncle... d'aga mata hannu yayi yace
"Yawon yayi yawa ina laifin kije gidan Anuty bilki, next time kin je can din ?ya fadi a taqaice dan
murmushi tayi wanda iya karshi laban ta, saboda bata san gardama da sadiq ko dan karya bata
rain shi, qoqarin fita ta take jiki ba qwari janyo ta sadiq yayi ta fado saman fafadan qirjin shi
dariya fatuha ta saki tare da dan dukan qirjin shi cikin wasa, murmushi ya saki tare da d'ago da
habarta yace " Na dauka kinyi fushi da uncle ne" dan bata fuska tayi tare da taba gefan fuskar
shi tace ba " Ba Komai uncle, Kuma dama can gidan Mami nayi niyar zuwa hanan ce tace na
tanbaye ka muje can" qarewa lips din ta kallo sadiq yake har ta kai aya, sannan yace "Ok!"
zame jikin ta d'aga na Sadiq tayi tace "Uncle bari na tafi" ok har kin fara jin bacci ne na dauka
hira kika zo taya ni dan smile tayi wanda ya bayana fararan hakoran ta tace "Ba bacci nake ji ba
kawai zan tafi ne saboda bana san dare yamin a nan ina jin tsora fita ni ka dai" d'aga gira sadiq
yayi ok good night, har ta kai bakin kofa ta jiyu tace "Oncle zaka taya ni hira kafin bacci ya
dauke ni?" yap ok zan kira ka video call ina je bedroom dawowa tayi ta mai pack a goshi
sannan ta fice d'aga part din.

Ko da ta koma bedroom laptop din ta ta kuna, a bangaran sadiq ma haka kiran fatuha ya
shigo laptop din sadiq dauk'a yayi yana kallan ta kamar tana gaban shi surutu ta cigaba da zuba

mai yana dariya har cikin shi na kulewa haka itama sosai sukayi hira inda sadiq yake jin bacin
rain d'ake damun shi ya sauka har tayi bacci suna video call smile sadiq yayi ganin fatuha tayi
bacci sannan shima ya kwanta, amma duk da haka ya kasa kashe laptop din kuma ya kasa
kauda idanuwashi d'aga kanta yarasa dalilin da yasa inda yana tare da fatuha yake bata guri na
musanman a zuciyar shi ita ka dai ce macan d'ake ganin murmushin shi fara'a shi da halin da
wannan tunanin bacci ya dauke sadiq ba tare da ya kashe laptop din ba.


*Asuba ta gari*

Addu'a cike a bakin ta tashi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login