Showing 21001 words to 24000 words out of 99609 words

Chapter 8 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

ga gidan
yan'iska ne yo jifa yadda rigar ta min, skirt din ta janyo ta sa tana sawa taga ya tsaya a gwiwa
shima..kut amma Qur'an mutanan sun rainani yo in ban da iskanci haka zanbi gari qafafu bude
tap bilahilazi ban fita haka guri ta samu tayi zamanta tana ta kunfar baki tare da jero Allah ya isa

Mom dake zaune parlour jin fatuha shuru bata fitu ba yasa ta leqo dakin zaune ta same ta har
bacci ya fara neman dauketa saboda gajiyar tafiya. tab'ata tayi tare da cewa "Fatuha... Nanta
ware manyan idanunta.. mom tasakar mata murmushi, "hala kin kasa sa kayan tashi kiga yadda
ake sawa.. nan mom ta shiga gwada mata masha Allah kayan sun mata kyau duk da fatuha
tsine wa kayan take a zuciyar tare da jin haushi kayan


Bayan mom ta gama gwada mata ta bata dankwali ta refe kanta ruf kamar wadda tayi acuci
yadda kan ya gwada sannan ta taja ta suka je parlour suka zaune saboda Sadiq sun fita da
jidda shan ice cream



Bayan sun gama shan ice cream suka biya shop rite ya siya wa jidda new Teddy's masu kyau
da kayan wasa jidda ko sai murna take a gajiye suka dawo gida . Sadiq na dauke da jidda a
hannu shi yana mata cakulkuli tana dariya *ola* na bayan su riqe da kaya cikin sallama suka
shigo.. mom na zaune tana kallo fatuha na gefan ta a takure,a ahankali Sadiq ya qaraso jidda
na maqale a jikin shi ya kai room pack, mom ce ta murmusa tace, "baby har kun dawo... "yes
sweet voice din Sadiq ne ya doki dudan kunnan fatuha ta waigo baki bude tana qare mashi
kallo shi da jidda sakin baki tayi a zuciyarta tace dama ashe ina da raban ganin yan'. makka kai
baba jinmai kwarankwatsi kin dubamin , duk wannan zancan da take idanun ta na kan su jidda ,
dagowar da Sadiq zeyi su kayi 4 eye's harara ya wurga mata tare da kauda kanshi, "mom
wannan wacece.. murmushi mom tayi tace "wadda zata rinqa kulla da jidda diyar qanin baba
jinmai ce. kallan fatuhan yayi wadda ke kallan su bata dauke ido ba harara ya qara banka mata
sannan fatuha ta Ankara ashe harara yake aika mata aiko itama ta fakaici idan mom ta banka
mai harara har da murguda mai baki, nanko ya saki baki yana mamakin wannan wacce Mara
kunyar mai aiki ce mom ta samu wadda bata da kunya a fusace ya tashi ya ce, "keeeee!! Ni
sa'an kine.. mom da ke zaune ta ce "Sadiq lafiya yarinya na zaman zamanta ka fara yi mata
bala'i ka bari mana ta kwana biyu sannan ka nuna mata bakin halin naka wai me yasa kake
haka ne baby. mom fada ta mai sosai cikin zafi rai ya bar parlour sannan ta shiga ba fatuha
hakuri fatuha washe da baki ta ce "ba komai, mom ta gwada mata jidda ba qaramin dadi fatuha
taji ba zata kulla da balarabiya bayan mom ta gama yi mata bayani sannan taqara mata da
batun zata riqa gyara part din baban jidda sosai.. fatuha taji dadin hakan.
a cikin zuciyar ta kuwa cewa ta ke Qur'an daba balarabiya ba ce da wallahi bani kula da Ita..
Shi kuma wancan balaraban ni zaiwa iskaci wai dan yana da kyau. Qur'an gyara mai zama
zanyi bilahilazi duk wannan maganar tana yin tane a cikin zuciyar ta




*Tah ku har kullun Salma mas'ud nadabo*

*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★


https//,mobile.facebook.
com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed
_dial_&_yn_=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



29_30

Mom ce ta haura upstairs ta bar jidda da fatuha zaune a parlour ,a hankali fatuha ta matso kusa
da jidda washe da baki tace "Ya sunnan ki?" smile jidda tayi tare da fada mata sunan ta, sun
dade a parlour zaune sannan jidda ta ja fatuha suka koma bedroom din jidda, jidda ta fara
kwaso wa fatuha kayan wasa, washe da baki fatuha ta amshi teddy, kai Al Qur'an birni dadi
garai yanzu sabida Allah ji wanga halita duk wasa ake da ita kai jama'a, jidda ce ta katse mata
zance da cewa" Anuty garin Ku ba wannan teddy ne? nima daddy ke siyo min" dariya fatuha ta
fashe da ita ke kekika san wani Daddy mtsss, kuma me Anuty da tedil (teddy) , jidda dariya tayi
tace Aunty ba sunan shi tedil ba sunan shi teddy ,Anuty kuma in mutun ya girme kane sai ka
rinqa ce mai Anuty, aiyo ai mu a kauyen mu yaya ake cewa ko gwago, Ah wanga suna Qur'an
dadi garai haka birni ya ke, jidda dai washe baki take tayi ta samu yar'uwa kamar ta me shegen
surutu.


Haka suka rinqa zuba hira tare da wasa ita dai fatuha, zuciyar ta fes dan a ganin ta ta samu
gurin zama kiran sallah magrib ne yasa suka tashi fatuha tayi alwala tare da jidda sannan suka
fito Dan gabatar da sallah.

Bayan sun gama sallah suka dawo parlour, parlour ba kowa sai baba jinmai da ke ta jera abinci
ita da rabi'a washe da baki fatuha ta gaida baba jinmai da rabi'a, baba jinmai ce tace, "Ah fatuha
anware kenan?" dariya kawai tayi , um ga abinci nan in kuna jin yunwa Ku zo Ku ci ki tabatar kin
ba jidda ta ci ta koshi inji baba jinmai, toh kawai fatuha ta ce mata sannan baba jinmai da rabi'a
suka shiga kitchen.

Kamar jira take su shige tayi tsale ta haye kujera dining area da kyar ta iya bude kulolin
farfesun yan'ciki ne sai dafaifan doya da miyar kifi, tunkan ta fara ci miyan tbakinta ya tsinke,
zubawa ta fara yi sai da kwanan ya kai har baki sannan ta tsayar da zubawa, jidda ko sai zaro
ido take tana mamaki irin ci na sabuwar Anty ta, lol.


Washe baki tayi tace, "Yauwa jidda sauko muci dan Qur'an ban iya ci a saman wannan abin ,
haka ko akayi suka sauko qasa suka fara ci, fatuha na ci tana zaro ido saboda dadi kuma ba
wai qaramar loma take ba haka zata dauko doya biyo ta turawa kanta ta kuma turawa jidda.




Zaune yake saman sofa da alama daga wanka ya fito, shafe jikin shi yayi da lotion mai kamshi,
yana gamawa ya feshe jikin shi da turare mai sanyi dadi wardrobe ya bude ya ciru 3quarte
black sai fara t-shirt hannu rigar dai dai tamatsa ba qaramin kyau yayi ba gashin nan nashi ya
kwanta abin sha'awa, ahankali ya kama handle din kofar part nashi ya fito.


Cikin natsuwa yake sakowa daga upstairs, sanye yake da bakin Sweet yayi matsifar yi masa
kyau, fatuha da jidda na zaune a kasa ga plate à gabansu sai loma fatuha ke tura wa jidda, dan
ita har ta koshi kuma da hannu take bata abincin, a fusace sadiq ya qaraso tare da dakawa
fatuha tsawa "Keeee! Are you mad, your very stupid" futaha ko ware ido tayi washe da baki ta
kalle shi tace, "Tap kai ka san wannan gwalangwatsin Qur'an" sannan ta cigaba ta dirkawa jidda
doya jidda ko sai amsa take hankali kwance, lumshe ido sadiq yayi ji yake kamar ya shaqe
fatuha dan haushi daka mata wata tsawar yayi ya ce, "Dan ubanki baki jin nane? uban waye
yace kiyi feeding din angel ba spoon eeeh?" Turo baki gaba fatuha tayi tace, yo ni ban san inda
fida (feeding) take ba ashe ba'a yaye taba Qur'an ban sani ba, sannan fatuha tace da jidda
shine kika saki tinbi ina ta dirka maki abinci ,to ta yaye kanta sai ka zubar da fida(feeding)lol.


Wani irin baqin cikine ya turniqe sadiq ya qara wurga mata harara , aiko itama ta rama, yo
ankan me mutun tunda na zo gidan su sai aika min hararata yake, ba Dan nayima Hajiya
Alkawari zan zamna da ita iya wuya ,da sai nace banyin aikin ko ana dole ne ,kama gode wa

Allah saboda Kuna kama da larabawane shiyasa na tsaya da bilahilazi da tuni nayi tafiya ta
aha, tare da gyara tsayuwar ta, sadiq ko baki ya saki yana mamaki irin wannan iskancin ta,
tsawa ya kuma daka ma fatuha wadda tasa yan'hancita katsawa dan ubanki ni sa'an kine
eeeeeh ido fatuha ta qara zarowa, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi duk sanda na
qara magana wannan dan banzan bakin naki ya maida min sai na fasa shi, ya qara wurga mata
harara sannan ya sa hannu ze dauki jidda, ihu fatuha ta saka hakan yasa sadiq juyowa yana
mata kallan wulaqance, Qur'an ba inda zaka da balarabiyannan kwarankwatsi, ko na fada ma
hajiya tunda ita ta bani ita, dariya abin ya kusa ba ma sadiq amma sai ya daure ya wurga mata
harara.


Mom dake bedroom taji ihu fatuha hakan yasa ta fito da sauri, ganin sadiq dauke da jidda
fatuna na gefe tana ihu yasa mom qarasowa, harara ta aikawa sadiq tare da cewa, "Lafiya
fatuha? me kuma ya miki?" turo baki tayi ta ce, "Yanzu saboda Allah hajiya ba ke kika bani
wannan balarabiyar ba, na kulla da ita , to shine wai daga yaga ina bata abinci ya hau zagina
har da ce min wai feda take sha" hajiya ko dariya abin ya bata saboda ta gano abinda fatuha
take nufi, sannan fatuha tace, "To shine hajiya yasa hannu ze dauke min ita Qur'an ban yadda
ya maido min abuta" hajiya ta washe baki tace "Yi hakuri fatuha ai baban tane shiyasa" aiyo toh
shine hajiya be iya fada min dan girman Allah, ki ce ya ban yarinyar dan Qur'an Santa nake
tare da matse kwalla, mom ko dariya abin ke bata sadiq ko mamaki abin ke ba shi yau shida
diyar shi za'a mai qarfin hali.


Toh shikenan sadiq bani jidda in ta mata wanka sai ta kawo ma ita ai shikenan anraba rigama
ko fatuha, sadiq bata fuska yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi.


Haka sadiq ya miqa wa mom jidda tare da haurawa sama, sannan ya dau alwashin sai ya
gyarawa wannan yarinyar zama dan yaga alamar da rashin kunya tazo.



Fatuha ko washe da baki ta amshi jidda, jidda ko sai raba ido take gashi cikin ta ya cika dam
kamar yayi magana.....




*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*

*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★

https//,mobile. Facebook.
Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed
_dial&_yn_=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITRESFORUM.com



*rip rip this page is for you my lovely one so enjoy the page this na for u no be so*

31_32

Washe da baki fatuha ta amshi jidda ta wuce da ita bedroom ta cire mata kaya direct toilet ta
shige da ita sai da ta wanke jidda tas sannan suka fito.


Ah bilahilazi birni tayi yanzu dubi sau biyu ina sab'e ki , jidda ce ta washe baki ta ce "Anuty
daddy ban san dati shiyasa" always yake min wanka yayi ma kanshi um tabe baki tayi tace yo
ke ki kasan wannan, washe baki jidda ta kuma yi tace baba na fa nake nufi Anuty aiyo wai
wannan baban naki ai dole yake wanka daga ganin shi ya cika tsirfa daddy nawa, um ke ni wani
mai ake shafa maki in anmaki wanka smile jidda tayi ta dauko mata lotion din ta mai kamshi
fatuha ta amsa, ah'ah wanga farin mai haka fa yo ai wannan kamar turare ne jidda ce ta fashe
da dariya tace Anuty ba turare bane maine ga turare na chan saman dirss mirror Wanda daddy
ya siyo min a uk, tir qashi me kuma uk, washe da baki jidda tace wata qasa ce haka a'a shi
baban naki har shawagi yake qasa qasa tap kinga matso na shafe ki da mannan kar yaji shiru
ya zo ya min tijara dan na lura dan ta kife ne baban naki ,haka ko ta shafe jikin jidda da lotion
tare da anyana man a ranta ita ma ta gama shafa basilin dan ita yanzu ta zama yar birni.


Sai da ta gama shafe jidda da mai tsaf sannan jidda ta gwada mata inda night dress din ta
suke kar ku ga abu komai fatuha ta gani sai ta mai sharhi bayan ta gama shirya ta tsaf, sannan

ta dauke ta dan kai ta dakin baban nata Wanda tayi ma laqabi da sangami.


Direct part din Sadiq suka wuce a hankali ta murda handle din kofar ta shiga , jidda tana ta
zuba mata surutu, tana shiga parlour ta saki baki da hanci bata san sanda ta dire jidda ba a
qasa wani irin sanyi dadi ne da kamshi ya doki hanci ta kasan cewa sadiq mutun ne mai san
sanyi da kamshi shiyasa part din shi yafi na kowa sanyi a gidan, washe baki tayi tana qarewa
parlour kallo saboda iya kar haduwa parlour ya hadu.


Jidda ko bedroom ta shige da gudu lokaci sadiq ya fito daga wanka, sanye yake da bathrobe
hannu shi riqe da towel yana goge gashin kan shi jidda ta ruga ta rungume shi daddy wani irin
murmushi ya saki tare da shagwabe fuska, um ni fushi nake da angel tare da daukar ta ya
zaunar da ita saman bed shine saboda kinyi new Anuty kika manta daddy ko angel, shagwabe
fuska ita ma tayi tare da daura hannu ta saman cheek din sadiq sorry daddy ta marairai ce
kamar za tayi kuka ,dariya yayi tare da fara yi mata cakulkuli, dariyar su jidda ta ankarar da
fatuha washe da baki ta nufi kofar bedroom ta bude a hankali ta shige, zaro ido tayi waje tana
kallan dakin baki bude kai Amma wanga gida ya hadu kwarankwatsi yanzu gobe ni zan gyara
wanga gurin , baki ta qara washe wa duk wannan maganar tana yin tane cikin zuciyarta, sadiq
dake ma jidda cakulkuli tana dariya jin kamar an bude daki an shigo yasasa da gowa a hankali
, ya sauke sexy eye's ball's din shi kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata ita dinma shi take
kallo tana aiyana irin kyau na sadiq tap amma dai sangami ba qaramin kyakyawa bane Qur'an,
washe baki ta kuma yi tace "Amma fa sai bakin rai kamar fir'auna tir da wannan hali wallahi ga
kyau ga bakar zuciya, ko da yake na kusa maganin shi ai, daka mata tsawar da sadiq yayi ne
yasa ta dawo daga dogon tunanin da take tayi wiqi wiqi da ido, ur are very stupid ina maki
magana kin yi shiru ehhh ?are u deaf or what tsawar da sadiq ya daka wa fatuha har wani fitsari
taji ya taho mata gadan gadan ganin yana nufo ta yasa ta bude kofar tafita dakin da gudu sai da
taje dai dai kofar parlour ta bude baki yadda zai jita tace Allah ya isa mugu kawai sannan ta
bude kofar ta ida fita a guje sadiq dake bakin kofar bedroom yana jin ta lumshe ido yayi yana jin
wani irin tsanar fatuha na ratsashi da mamakin rashin kunyar ta ,a hankali ya ja jikinsa ya koma
saman bed lokacin jidda har tayi bacci shima kwantawa yayi tare da kara masu gudun AC ya ja
masu blanket.


Tana isa daki ta kulle da makuli gudun kar sangami ya shigo wato sadiq toilet ta shige da
gudu tayi fitsarin data matseta saboda tsabar tsawar da sadiq ya daka mata shi ya haifar mata
da fitsari dole, tsoki ta ja tare da cire kayan jikin ta tayi wanka sai da ta wanke jikin ta tas
sannan ta dauki karami'n towel ta daure ta fito, rigar baccin da mom ta gwada mata ta Ciro ta
sa duguwar riga ce pink mai manyan follows milk rigar ta wuce gwiwa ba qaramin kyau tayi ma
fatuha ba, ita kanta sai da ta yaba kyan rigar sannan ta kwanta saman bed tare da janyo
blanket ta lulube ko 2 minutes ba tayi ba bacci ya sureta.

Asuba ta gari, tsaye yake gaban dress mirror yana shiri cikin uniform nashi kasan cewa yau
Monday ba qaramin kyau yayi ba kofar bedroom ya kalla tare da jan tsaki sannan ya kalli bed
jidda na bacci.


Fatuha ko yau bacci har da munshari ba ita ta tashi ba sai 6:00am, cikin sauri ta tashi tayi
alwala tayi sallah sannan tayi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba tayi sauri ta zura uniform
din ta kasan cewa mom ta fada mata jidda na zuwa school yasa take shirin cikin sauri cikin
sauri ta nufi part din sadiq dai dai bakin kofa ta tsaye gaban ta na dukan uku uku saboda ta tuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login