Showing 33001 words to 36000 words out of 99609 words

Chapter 12 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

Advertisement

ta da mai kamar kullun tare da fesa turare uniform ta zure sannan ta daure gashin
kanta Wanda da kyar ta kama shi, ganin be kamuwa yasa ta sake shi haka kawai ta fita direct
part din sadiq ta shiga tana karema parlour din kallo ,har yanzu glass din jiya nan zube a
parlour baki ta tabe ta shige bedroom sadiq na kwance jidda na maqale a jkin shi da alama
daga masallaci ya dawo bacci ya kwashe shi dan jalabiya ce a jikin shi ba night dress ba sajan
nan nashi yayi lufluf kwance, qare mai kallo fatuha tayi sannan ta bala mai harara kamar
idanuwan shi biyu a hankali ta sa hannu ta fara janye jidda daga jikin shi janyo jidda ya qara yi
ya maqale ta, abin ma dariya ya ba fatuha qara jan jidda tayi shima ya qara jan jidda haka suka
riqa ja inja qara leqa fuskar shi tayi taga dai bacci yake a hankali ta qara miqa hannu zata janye
jidda cikin dubara ta janye jidda direct bathroom ta dire ta, kamar kullun ta shirya jidda
murmushi tayi washe da baki tace Anuty I like u murmushi fatuha tayi tare da langwabe kai ta
shafa kan jidda tare da cewa jidda kisan ban iya wannan yaran ba, murmushi jidda tayi ina nufi
kina birge ni Anuty murmushi fatuha tayi wadda ya baya kyawawan hakuran ta tace nima haka
Jidda pack jidda tayi mata itama fatuha pack tama jidda.

Janyo hannun jidda tayi cikin ni shadi suka qaraso dining area tea ta shiga hada ma jidda mai
kauri, Wanda yaji ovaltine da madara tare bread n egg a hankali ta Shiga feeding din jidda tana
amsa itama in taji dadi se ta gutsuro bread din taba fatuha, mom da abba ne suka qaraso cikin
fara'a dining area cikin ladabi fatuha ta gaishe su ,cikin farinciki suka hada masu breakfast,
washe da baki mom ta amsa jidda ce ta washe baki tare da cewa morning grandma n grandpa
morning too angel suka amsa a tare bayan jidda ta gama hada masu ta aje masu cikin ni shadi
suke breakfast.

Tsaye yake gaban dress mirror sanye da bathrobe hannu shi riqe da qaramin towel yana goge
sumar kanshi da alama daga wanka ya fitu cikin tsuwa ya yake shirin lotion ya shafa tare da
saka uniform din shi sannan ya feshe jikin da turaruka masu kamshi booth din shi ya curo ya
saka black se sheqi yake tsaf ya fito sojan shi hula shi ya dauko ya sa sai agogwan shi silver na
zurfa wani irin kyau yayi ba dan kadan ba sai dai fuskar nan daure briefcase din shi ya dauko
tare da daukar wayar shi da ke bedside drowe a hankali ya bude kofar bedroom kallo daya yayi
ma parlour tare da jan dogwan tsaki fatuha kin rainani wallahi sannan yasa qafa ya fitu daga
part din a hankali yake saukowa daga upstairs tuni kamshi turaran shi ya mamaye parlour
fatuha da ke feeding din jidda ta dago idanuwan tana qaremai kallo cikin isa ya qaraso wayar
shi ya cure ya kara a kunne cikin natsuwa yake wayar , holle ole daga bangaran ola yace hello
boss, ka zo ka amshi briefcase din , to ya ce mai tare da kashe wayar ya qaraso dinning area
smile yayi tare da gaishe da su mom jidda washe da baki ta gaishe haka fatuha banza yayi da

ita kamar be ji tare da qare mata kallo yau kuma wani saban iskanci yima mutane yawo a gida
ba dankwalli duk yana yin maganar a cikin zuciyar shi a hankali ta janyo cup da niyar hada mai
breakfast hannu ta ya rike ya wurga mata wani irin kallo ya aje hannu tare janye cup din mom
ce ta aika mai harara sai yayi kamar be gani ya cigaba da aikin da ya ke ole ne ya shigo cikin
sallama suka amsa sannan ya amshe briefcase din sadiq ya fice da ita abba ne ya katse
shurun da cewa, ah ka ce min qafa ta warke murmushi sadiq yayi tare da cewa eh abba toh
masha Allah , abba ya maganar kwangilar kunko samu a'a munan dai muna fama amma insha
Allah this time around zamu samu abinda muke so murmushi sadiq yayi tare da cewa Allah
yasa mom ta amsa da ameen tashi yayi tsaye tare da cewa oya angel mu fati , ah baby karka
ce min ruwa tea din har ya isheka ba bread ba komai eh mom na koshi toh shikenan, hannu
jidda ya kama har sun kai baki ko abba yace yawa baby ina san fadama ranar Sunday tare da
mom din ku zamu tafi uk , OK sadiq ya ce tare da sa kai ya fita fatuha na biye da su da lunch
box din jidda har gaban mota sannan ta miqa wa jidda lunch box din tare yi mata pack sadiq
kallan su yayi tare da tabe baki sannan ya shige mota.


A hankali ta juyo ta shige gida, kwashe kayan breakfast din tayi mom na zaune a parlour tana
kallo fatuha ta zo ta wuce kitchen washe da baki ta gaida baba jinmai itama baba jinmai washe
da baki ta amsa ,rabi'a na gefe tana gyara kayan miya tayata fatuha ta Shiga yi suka gyara tare
sosai ta taya su baba jinmai aiki a kitchen saboda aiki na burge ta kusan tare da ita aka dafa
lunch baba jinmai ko dadi take ji har qosawa take suje kauye jauro yaga yadda fatuha ta koma
kamar balarabiya, bayan sun gama aikin fatuha ta wanke duk wani kwano da akayi anfani da
shi rabi'a ko sai hanata take amma taqi bari sai da suka gama komai sannan fatuha ta dawo
parlour, ko da ta dawo mom ta bar parlour bedroom ta shige tare da rage kayan jikin ta
bathroom ta shige ta watsa ruwa daure da tawel tafito bayan ta gama komai sannan ta tuna
ashe bata gyara part din sangamin ba, ko mai bata shafa ba ta zura kayan ta direct part din
sadiq taje ta fara gyara sai da ta gyara shi tas sannan ta zauna a parlour saman three star tana
maida numfashi lumshe idanunta tayi tare da ware su, fita tayi daga part din ta koma bedroom
ta kuma watsa ruwa sannan ta shefe jikita da mai tare da fesa turare da maida uniform din ta.



Misalin karfe 2:00pm su jidda suka dawo ,kasan cewa yau sadiq be da wani aiki tare suka
dawo part din shi ya nufa masha Allah gyaran part din ya mai yana jin dadi ganin part din shi a
gyare, duk rashin jin fatuha tasan aikin ta shiyasa wata rana yake daga mata kafa bathroom ya
shige ya watsa ruwa ya fito cikin wando da riga ya shirya, kayan sun mai kyau sosai. bangaran
su fatuha kuwa jidda na dawowa yadda ta saba yi mata haka ta mata sannan tace taje parlour
ko da ta fito parlour daddyn ta gani jikin shi ta fada tana zuba mai surutu shikuma yana
saurareta yana jin dadi, mom da abba ne ke saukowa daga upstairs abba sanye da shada
malinmalin brown mom na sanye da atanfa pink mai ratsin greed n bleu sanye da mayafinta ba
qaramin kyau sukayi ba, parlour suka qaraso washe da baki jidda ta sauka daga jikin sadiq ta
riqe hannun grandpa murmushi abba yayi yace "Sadiq yau da wuri ka d'awo daga wajen aiki
kenan?" smile yayi tare da cewa eh to mu zamu wuce gidan ammi mu masu sallama to Allah ya

tsare ameen jidda ce tace grandpa zan biku toh shikenan yima fatuha magana inji mom sai
muje tare ko, rugawa tayi bedroom fatuha kuwa tunda jidda ta fita wani irin bacci ne ya sure ta
ko da jidda ta shigo taga fatuha na bacci veil din ta ta dauka tare da fita ,grandma Anuty bacci
ta take toh shikenan tunda bacci take mu tafi kawai ta samu hutu ne washe da baki jidda ta bi
su abba, sadiq ya rako su har parking space sannan ya koma gida ko da ya koma wani irin
killing smile yayi upstairs ya haura sannan ya fito kitchen ya shiga ya dauko ruwa a fridge me
sanyi Wanda har qanqara ya fara saboda tsabar sanyi a hankali ya murda handle din dakin
fatuha ya shiga hangota yayi saman bed tana sharar bacci gashin ta ya baje saman gadon, cije
lips yayi sannan ya qaraso sai da yazo dai dai face din ta ya bude murfin rubar ruwan ya juye
mata shi, fatuha da ke bacci wani irin razana tayi ta tashi cikin gigice wa ta yunkura zata fita
saboda tsoro, sadiq ya janyo gashin ta tare da dauke ta da lafiyeyan mari ,wani irin kuka fatuha
ta saki tare da zama saman bed jajayan eye's din ta ta dago tana kalla sadiq wani irin murmushi
yayi yace "Fatuha yau zan koya maki hankali, bani kika so ki nakasa ba ? toni yau kona maki
gashi zanyi ya ida zancan tare ya matse mata fuskarta, idanuwan fatuha sunyi jawur sai kuka
take tana bama sadiq hakuri ashana ya Ciro a aljihun shi ya kunna tare da fusgo gashin ta wani
irin kuka fatuha tasa dan Allah me kyau kayi hakuri wallahi bazan sake ba ta ida zancan tana
qara rushewa da saban kuka, shhhh yimin shiru fitsarariyar banza nufo gashin ta yayi da wutar
take fatuha ta fashe da wani sabon kukan tare da tafiya luuuu ta sume, murmushi sadiq yayi
ganin suma tayi marar kunyar qarya kitchen ya koma ya dauko wani saban ruwan sanyi ya
dawo bedroom ya qara juye mata shi wata irin ajiyar zuciya ta saki tare da fashe wa da kuka
tana bama sadiq hakuri, cije lips yayi na qare mata kallo yarin ya ce sosai amma sai rashin
kunya duk à zuci yake wanga zancan , bindiga ya ciro ya daura mata akai tuni fatuha ta saki
fitsari ta sauke numfashi agwagwame cikin sarkewar murya tace dan Allah me kyau kayi hakuri
bazan sake ba, tsaki yaja tare da cewa fitsari ma kikayi ko? a'a wallahi ruwa ne haka wallahi,
murmushi yayi dan yasan qarya take sannan yace daga yau se yau kika qara min rashin kunya
sai na b'ula maki kai da wannan abar , girgiza kai tayi alamar baza ta sake ba, sannan ya
hankada ta kanta ya bigi gado ta qara sakin wani saban kukan sannan sadiq ya sa kai ya fita.





*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*

★we are the best★


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_dial_&_yn=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



43_45

Sai da fatuha ta ci kuka sosai tare da jerawa sadiq Allah ya isa, sannan ta tashi jiki ba qwari ta
nade zanin bed din Allah ya taimake ta katifar akwai leda dan haka ruwan da fitsarin be shige
cikin katifar ba iya karshi saman bedsheet tatare shi tayi ta aje ta shiga toilet ta watsa ruwa,
tana gamawa ta fito ta dauki bedsheet din ta wanke shi tas sannan ta fito da bokitin ta aje agefe
sai da ta shirya tsaf sannan ta dau bokitin ta fita ko da tafi dasu ola taci karo da Sunday yaran
sadiq suna ta shawagi a tsakar farfajiyar gidan, kai tsaye wajan shanya ta nufa ta shayan
bedsheet din sannan ta dawo ta zauna saman wata resting chair da ke a farfajiyar gidan lumshe
ido tayi tana jin wani tsoro sadiq na ratsa ta, wasu hawaye masu zafi na zubo mata, dan yau ba
qaramar wahala tasha a hannun shi ba take nan wani zazabi mai zafi ya lulube ta sakamakon
ruwan sanyin da sadiq ya sheqa mata, ganin masasarar taci qarfin ta yasa ta ja jiki ta koma
parlour saman three star ta zauna ta qudindine waje daya tana kyarma abin gwanin ban
tausayi.


Bangaran sadiq ko zuciyar shi fes bathroom ma ya shige ya sheqa wanka bai jima sosai ya fito
daure da tawel da Dan karami yana sane gashin kansa, gaban dress mirror ya tsaya yana
gyara kanshi da ya tuno da yanda fatuha tayi se ya saki murmushi jin dadi bayan ya gama
shiryawa cikin 3quarte da armless t-shirt din shi cikin shirin shi na zuwa gym , sannan ya feshe
jikin da turare masu sanyi kamshi a hankali ya bude handle din kofar tare da barin part din cikin
isa yake sakowa daga upstairs fatuha ya hango saman three star qudindine kauda kansa yayi
yana qoqarin fita har yayi gaba sai kuma ya dawo saboda barin da yaga jikinta nayi yasa yaji
tausayinta kadan azuciyarsa, a hankali ya qaraso gaban three star din ya leqa fuskar ta Wanda
tayi jawur ga shatin hannu shi kwace a fuskar ta lumshe ido yayi tare da waresu a kanta a
hankali ya kai hannu ya taba goshin ta ji yayi goshi zafi rau kamar wuta, a hankali fatuha ta
ware idanuwan ta ta fara rera mai kuka a tunanin ta wani muguntar ya zo yi mata, daurewa yayi
tare da cewa yima muta ne shuru kafi na kife ki da wani sabon Marin tsuru tsuru tayi tana kallan
shi ga wani irin zazabi da take ji ,lumshe ido tayi ta juya mai baya wayar shi ya ciro dake

aljihunshi bugu daya biyu Dr yakub ya dauka sannan ya sheda mai yana buqatar ganin shi , OK
ya ce mai tare qatse wayar sannan ya kalli inda fatuha take kwance hata gashin kanta jiqe yake
a hankali ya kai hannu ya dauki fatuha ita ko sai matsar kwalla take tana bashi hakuri banza
yayi da ita be dire ta ko ina sai bedroom din ta, saman bed ya direta sannan ya dau ko hand
dryer daya ke anfani da ita ya busar mata da kan ta fatuha ko sai bin shi take da ido AC din ya
rage ma gudu tare da rufe ta da blanket ya koma gefe ya zauna fatuha ko lumshe indo tayi
kamar me bacci.


Ba'a fi 50 minutes ba sai ga Dr yakub sadiq ne ya mai iso har bedroom dinta, dudubata yayi
sannan ya fito da alura da magunguna ya aje a gefe sai da ya gama zuko alura sannan yayi ma
fatuha magana, hajiya ki juya zan maki alura ko dan fever ta sauka ,waro ido fatuha tayi ta fara
kuka dan Allah kayi hakuri wallahi bana san alura kuka take sosai sadiq ta shiga ba hakuri,
banza yayi da ita kamar bai jinta, ohni fatuha yau na shiga 3 ban taba tunanin muguntar me
kyau ta kai haka ba duk wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta ,Dr ne ya katse shurun da
cewa please ki tsaya na maki alura kin ji ba zafi ba kuma ko dan ki samu sauki masasarar da
kike yi kinji ,Dr ya ida zancan yana smile wallahi bana san alura dan Allah kayi hakuri ka kyale
ni Dr yakub ne ya juyo ya kalli sadiq dake ta latsa wayar shi kamar ba mutun a wajan ka ji mara
lafiyar ka bata san alura kuma irin wannan fever se da alura yake sauka ,dago sexy eye's ball's
din shi yayi yana qarewa bed din kallo da fatuha take kwance saman bed din cikin isa ya qaraso
yace fatuha shuri tayi kamar bata ji shi sarai yasan tana jinshi ,wani saban rainin ne haka ji yayi
dama be kira Dr din ba ya barta ciwo ya kashe ta inya tashi daf da ita ya zo ya zauna tare janyo
ta kuka tasa tana cewa ni ka kyale ni bana so banza yayi da ita ya riqe ta gam Dr ya zunkuda
mata alura wani irin kuka ta saki tare da rungume sadiq gam tana kuka se da tayi kuka san ran
ta sannan ta fara sauke a jiyar zuciya dan guntun tsaki sadiq ya ja tare da zame ta daga jikin shi
fatuha ko yana zame ta ta koma ta kwanta saman bed tana sauke ajiyar zuciya, sannu Dr yakub
ya mata sannan ya dau briefcase din shi tare da yima sadiq bayanin yadda zata sha maganin
Godiya ya mashi sannan ya rako shi har bakin kofa yashiga motarsa ya tafi. shi kuma ya koma
bedroom din fatuha ja mata blanket din yayi sannan ya fita ita kuma bacci ya sure ta.


Bangaran su mom ko sun isa family house lafiya,d irect part din ammi suka fara shiga cikin
fara'a ta tarbe su da jin dadi asiya mai aiki ta kira ta kawo masu fura mai sanyi da kayan motsa
baki, aiko sakin jiki sukayi suka sha dan ammi ba irin iyayan mijin nan ba ce me takurawa
surukanta daukar su take kamar ya'ya ta Jidda ta janyo tana mata wasa ,yan'mata baba ina
baban naki kwana biyu shuru murmushi jidda tayi tace "Daddy nanan lafiya lau "to madala
kwana ki nake ji majid na cewa sadiq be ji dadi ba mom ce ta ce wallahi ko faduwa yayi a toilet
Allah sarki ai abun ya zo da sauki, masha Allah ai yanzu ya warware sosai da tare zamu zo ma
Eyya sun sha hira sosai da ammi daga nan suka wuce part din Umma lokaci baba be dade da
dawowa daga kasuwa ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login