Showing 96001 words to 99000 words out of 99609 words
Chapter 33 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
ya fara ko ta
ko ina ganin ze zarce yasata samai kuka. smile yayi tare da cewa sorry Sannan ya samata
kayan shima shiryawa yayi cikin manya kaya Sannan ya jata suka fito ko da suka fito lokaci su
fatima sun shirya ita ka dai suke jira ta fito, tana fitowa fatima tace "Sai muje ko? ta ida zancan
tana aika mata harar wasa" murguda mata bak'i tayi Sannan suka fice sadiq kuma ya wuce
wajan angwayan saboda kamun ba maza.
Suna shigewa mota fatima tace "Ke h'aka ake? d'aga shiga sa kaya saiki maqale da miji"
kam mikika daukan to nayi din ta fada tana aika fatima hararar wasa. dariya suka kwashe da ita
a tare suka ce kin tuna san da muke zuwa gonar mai gari? dariya suka kuma saki tare da kallan
juna suka yi tare da cewa Allah mun gode maka bamu taba tunanin ganin a haka ba rungeme
juna sukayi tare da hade bakin su suka ce Allah ya bar mana zumincin mu har ya'ya da jikoki
ameen. Fatsima harara ta aika mata ke mijina ya hana fadi wannan suna, dariya sukayi tare da
cewa sannu mai miji a h'aka suka Isa wajan kamun kasancewar sune Maya Mayan qawayan
amarya hada hada kawai suke biki yayi biki su Zara da Nana ma sai da suka zo ansha biki
sosai sai kusan yama likis suka dawo, gidan mami suka wuce direct.
Cikin sallama suka shigo angel d'ake zaune da friends nata ta qaraso tare da rungume
fatuha tace "Mom a I miss u?" miss u more dear, kin manta da mamanki tunda biki ya kama ko?
to ai gashi nan ni na biyo ki bana iya hakuri kimin nisa fatuha ta fada tana shafa kanta smile tayi
sannan ta koma cikin friends din ta.
Shirye-shirye ake na zuwa dinner ,ciki'n wata material lace green n black yan'matan amarya,
amarya kuma na sanye da black lace mai ratsin white sosai sun fito sunyi kyau musanman da
suka sha make up, cikin hadadi motaci akazo kwasarsu. fatuha ko motar sadiq ta shige wani irin
lalausan murmushi ya sakarma tare da taba hannu ta yana murzawa a hankali cikin salo, yace
"My wife kin sha kyau?" smile fatuha tayi tace na gode, shima yasha kyau har ya gaji yana
sanye da shada milk tasha aikin hannu, ga kamshi turaran shi dake wani fisgarta, murmushi ta
sakar mai me cike da sakwanni Sannan ya ja motar hannu sa daya na maqale dana fatuha.
Hall ya cika maqil anata gudanar da biki, inda abun ya zama abin sha'awa tare da birgewa
musanman fatuha da Sadiq dan sadiq baya iya boye irin San da yake ma fatuha koma a inane
nuna mata so yake. h'aka aka gudanar da biki inda Dr yakub yasha kyau shida amaryar shi
suka gaji sai dai mu ce Allah ya bad'a zaman lafiya.
Da misalin karfe 10:00pm taro ya watse sadiq ya wuce da fatuha gida, maqale qafa tayi ita
baza ta koma gida ba ya maida ta gidan mami? cikin yan'mata amarya fir sadiq yaki saurarata
haka ta cika tap kamar ta fashe, yana kunna hancin motar shi mai gadi ya bude masu geta
Sannan sadiq ya shiga tare da yin parking a parking space. kashe motar yayi tare da bude
murfin motar fatuha ko zaune tayi tana qoqarin fara rai ra mai kuka daukar ta yayi kamar baby
ya shiga da ita gida sai rigima tak'e zuba mai.
*Washe gari*
H'aka aka daura auran Dr yakub da hannu akan sadaki naira dubu dari, sai washe bak'i yake da
ka ganshi kasan yana farin cikin, ana kamala daura auran Dr yakub yaji alat account din shi
kallaan sadiq yayi tare da sakar mai murmushi sannan ya mai godiya, bayan an kamala biki
ango ya dau amaryar sa sai airport inda hanan ke ta zuba kuka.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dad'i inda sadiq ke bama fatuha kulawa sosai ga exam
suna tayi, alhamdulillah exam din ta zo mata da sauki sai dai har cikin ta ya dan fito.
Murna suke sosai na ganin cewa yau sun gama paper. sosai fatuha ke jin dad'i a gaskiya
bata da abinda zata ce ma mai kyau ya gama mata komai a rayuwa, ko da ta fito sadiq ne ya zo
daukar ta, kasancewar Saturday ne ya zo weekend gida cike da farin ciki ta qarasa gaban
motar tare da bale murfin motar ta shiga. su Zara ko d'aga mata hannu su kayi tare da yimata
alqawarin sai sun zo ranar suna,
Kallan ta sadiq yak'e cike da so a hankali yak'e driver din ciki'n natsuwa har suka Isa gida,
shi da kanshi ya bude mata murfin mota wata hadadiyar mota ta hango Lexus Toyota parke a
harabar tsakar gidan su, kallan sadiq tayi tace "Habibina munyi baqine?" d'aga mata kai yayi
tare da janta suka shige tana shiga gida ya dai ihu wasu kyalkyali suka fara zubowa a jikin ta.
da flowers kallan sadiq take da mamaki pack ya mata tare da cewa happy birthday my wifeí ¼í¾‚,
janta yayi gaban cake shida angel dan kusan ita ta h'ada komai ,sai smile fatuha tak'e tare suka
hada hannu suka yanka cake din parlour ya dau tafi, gutsuro cake din sadiq yayi ya bata a baki
itama ta amsa ta bashi Sannan angel ta bata itama ta ba angel, pics sukayi sosai yan'uwa da
abokan arziqi suka bata gift da yawa daukarta sadiq yayi tare da maido ta harabar gida a je ta
qasa yayi tare da rungume ta, ta baya tana facing din motar yace "Rufe idanuwan ki ga wani
abu?" lumshe ido tayi sadiq yace ta bude tana budewa taga car key wani irin sakewa tayi tana
kallan shi juyowa tayi tare da rungume shi tasa kukan farin cikin. shafa ta yake ta baya a hankali
tare da zame jikin shi yasa hannu ya goge mata hawayan dariya ta saki tare da yimai pack ta
ko ina. dariya su majeed suka saki shi da fatima, murfi motar ta bude sai farin ciki tak'e Sannan
suka dawo gida sadiq ya mata alqawarin kafi ta tafi university zai koya mata driven.
*Bayan kwana* 2
Shirya kaya fatuha tak'e cikin trolley yanzu ciki'n ta ze kai 4 month, sadiq ne ya janyo ta tare da
zaunar da ita shi ya cigaba da had'a kayan, sai murna take kasancewar wudil zasu d'aga nan su
wuce abuja, bayan ya gama kamala h'ada kayan cikin trolley Sannan ya janyo trolley din
parlour tare da kiran Sunday amsar kayan yayi ya kai boot Sannan sadiq ya leqa bedroom din
angel itama ta gama hada na ta kayan. smile tayi tare da yima sadiq pack ta miqa mai trolley
din, amsa sadiq yayi yace "Angel kin sa komai ko? Dan karki manta wani abu" d'aga kai tayi
tace "Yes daddy good girl in zaki fito ki kashe AC da komai na bedroom din" ok tace tare da
nufar AC zata kashe sadiq ya fita tare da ba Sunday ya kai boot komai sun gama hadawa
fatuha na sanye da atamfa an mata dinkin bubu mai kyau sai dauri da tasha tayi kyau har ta gaji
ga wani haske da ta qara , angel rike da wayar ta fita iPhone 6 tana video call da Jamal tana
sanye lace Riga da sket dan yanzu ta fara zama yan'mata kashe wayar tayi tare da biyo su
mom suka fita a tare. sadiq yaja mota sai da suka fara zuwa wajan, mom haka ta hada masu
tsaraba sosai tare da yi masu Allah ya kiyaye hanya ita da abba sanna suka fito tare da daukar
hayar wudil,
Da misalin karfe 2:00pm suka Isa ciki'n murna fatuha ta shige gida ita da angel, da gudu
angel ta fada jiki'n inna dariya inna ta saki tace "Yan'mata?" kwabe fuska fatuha tayi tace "Angel
dan kin ga kin fini sauri ko shine kika rigani?" dariya sukayi a tare Sannan suka shige parlour
haka inna ta rinqa nan da su sadiq ko tunda ya sauke su ya wuce gona wajan baffa ya taya shi
aiki sai hana shi yake amma ya qiji bari sai yama liqis suka dawo. gaishe da inna sadiq yayi sai
zuba mai albarka take Sannan ya wuce masaukin shi waka kawai yayi yana tsane jikin shi
fatuha ta shigo da kulolin abinci ta aje mai Sannan ta amshi towel din tana gogemai jiki, janyo
jikin shi sadiq yayi yana facing nata cike da so a hankali ya kai hannu kan cikinta yace "Ya
babyna?" smile fatuha tayi tace "Yana lafiya lau" da gaske? d'aga mai kai tayi rage tsawan shi
yayi tare da kasa kunne sai tin cikin yana murmushi saboda baby sai motsi yake pack yama
cikin tare da miqewa fatuha ta taimaka mai ya shirya Sannan tayi feeding nashi tuwo shinkafa
miyar kuka tasha manshanu da naman rago sosai yaji d'adi abincin.
Angel ko sai zuba ma inna surutu tak'e tana biye mata, jin tak'e kamar jikar ta h'aka itama
angel saki'n jiki take da inna.
Qoqarin fita fatuha tak'e Sadiq ya riqe ta tare da langwabe kai my love, shafa gefan face nashi
tayi tace "Na'am" shagwabe fuska sadiq yayi ce "Please ki kwana anan?" zaro ido waje fatuha
tayi tace "Tap ba ruwana nama ji da wannan kunyar ta nuna cikin ta" dariya sadiq yayi tare da
hade face nasu guru guda yace "Ai na halal ne ko kin mata?" lumshe ido tayi a hankali sadiq ya
lalubu baki'n ta ya fara mata France kiss sun Dade a haka Sannan ya sake ta yana maida
numfashi ,smile fatuha tayi tace I love u, Sannan ta fita da sauri , barbaza gashin kanshi sadiq
yayi tare da furzar da iska bakin shi yace always loving u fatuha Sannan ya kwanta.
Kwanan su fatuha biyu a wudil hada kayan su suke zasu wuce, fatuha ji take kamar karsu
tafi h'aka dai ta gama hada kayan inna sai samu albarka take tare da yi masu addu'a samun
zaman lafiya mai daurewa, sadiq ko albishir ya masu daya biya masu kujera makka murna
wajan fatuha ba'a magana haka ta rinqa zuba ma sadiq godiya haka su baffa da inna sannan ya
fido kudi masu yawa ya aje masu da kyar ya samu baffa ya amsa, Sannan itama fatuha ta baje
masu tsaraba Lace's da atamfa da shada da ta siya masu sosai su inna sun ji dadi Sannan
suka dau hanyar abuja fatuha har da har kwallata ita da angel,
Sai wurin dare suka iso abuja gidan ya hadu fadin tsaruwar gidan ma bata lokaci ne, dan
yafi na kano ko ina na gidan yaran sadiq ne sojoji da yawa kamar a barak h'aka suka shigo da
kayan su kasancewar sunci abinci a hanya sallah kawai su kayi angel ta shige dakin da sadiq
ya gwada mata a matsayin nata daki'n ya hadu dan yafi nata na kano kyau,
Haka suma daki'n su fatuha ya hadu iya kar haduwa, har kauyanci sai da fatuha tayima sadiq
dariya kawai yake mata saboda komai tayi birgeshi take.
*Washe gari*
Bayan sun kamala komai sadiq yaje da su yawo sosai sun sha yawo inda sadiq keta kulla da
fatuha yana bata kayan Gina jik,i wanda zasu taimaka mata ta haihu lafiya.
3 *month letters*
Sosai ciki'n fatuha ya girma dan har mom ta ce sadiq ya maido ta kano saboda cikin yanzu wata
na takwas,da yake ba yadda sadiq ya iya dan baya so tayi nisa da shi.
Shi da kanshi ya h'ada masu kaya Sannan ya kai masu boot itama fatuha ji take za tayi
missing nashi Sannan suka dau hanyar kano, suna Isa kano gidan mom ya wuce da su lokacin
itama fatima ta dawo gida ita da basma saboda mom ta ce baza su je gida ba a wajan ta zasu
haihu har suyi arba'in. dadi ta ji ganin su sai damuwar ta ta ragu kwana sadiq daya ya juya
abuja cike da kewar fatuha.
Akwana a tashi ba wuya wajan Allah, su fatuha yau da naquda suka tashi majeed mom ta
kira tare da driver ya wuce da su asibiti, labour aka wuce da su su uku sun Dade suna naquda,
ko da sadiq ya iso gari d'aga airport asibiti kawai ya wuce yana Isa lokacin yayi dai dai da
haihuwa fatuha ta silibo baby boy din ta Fatima ma boy ta Haifa, basma baby girl masha Allah
yaran masu kyau, musanman fatuha gaba ki daya baby sadiq ya d'ako h'aka suka rinqa murna
kankace mi asibiti ya cika,
A hankali sadiq ya qaraso tare da daukar baby yana kalla smile yayi tare da kallan fatuha
kiss din hannu ta Sadiq yayi yace "Thank u my wife da kika bani wannan farin cikin". Angel ma
murna ba'a magana kwana su d'aya aka sallame su family house aka wuce da su,
Sosai suke samu kulawa tare da wanka da shan abubuwa masu gina jiki, ranar suna anyi
shagali ba dan k'adan ba, inda dan fatuha yaci sunan abba Ibrahim ana kiranshi da aslam ,
Dan majeed yaci su baba khabir ana kiran shi da Walid, diyar Khaleed taci suna Khadija ana
kiranta da Nana,
Suna yayi suna inda aka dinga narka kudi kamar ba'a so, anyi ciye ciye da lashe lashe
Sannan taro ya watse kowa ya tafi gida cike da farin ciki aka bar masu jego,
Mom sosai ta zage tana gyaran ya'yan nata inda suke ta shan gyara jikin da tsimi wani irin
kyau sukayi ga wani sheqi da suke ta zubawa. baby's kuwa sunyi wayau gasu yan duma duma
saboda suna samun ruwan nono sosai kullan angel na maqale da aslam sai fatuha zata bashi
mama Sannan angel ke bata shi ,dan wani irin Son duniya ta daura mashi, bata da lokaci kowa
sai na aslam.
Sanye da qaramin towel ta fita d'aga bathroom tana goge gashin ta da qaramin towel
,gaban dressing mirror ta tsaya tare da janyo lotion , sadiq ta hango ta cikin mirror wani irin
lalausan murmushi ta sakar mai a hankali ya qaraso tare da rungume ta tabaya yana shinshi na
kamshi jikin ta lumshe ido fatuha tayi tana amsar sakwanin sadiq, qoqarin cire towel di'n yake ta
riqe tana kallan shi ,lumshe ido yayi yace, "Please" shiru tayi bata ce komai ba, daukar ta kawai
yayi ya daura saman bed ya fara aika mata sakwani da zafi zafi gani zasu Lola yasa na silalewa
na fice.
Shiryawa tak'e cikin atamfa riga da sket cike da shagwaba tace "Habibina gaskiya ka tashi ka
fita bana so mom ta zo ta gan ka? tana ganin ka zata gane ta ida zancan tana parking din
gashinta" smile sadiq yayi tare da rungume ta ta baya yace "Um my love baza ta gane komai ba
kinji?" da gaske daga mata kai sadiq yayi alamar eh tare da Ciro wasu takadu gada aljihu shi ya
miqamata ,wani irin tsale fatuha tayi tare da qara qaqame shi ba ko mai bane sai admission na
north west university,
Da sauri fatuha ta fita tana kwalawa mom kira, fitowa tayi d'aga kitchen ta ce na'am fatuha
fadawa tayi jikin mom tare da nuna mata admission murna mom ta tayata tare da yima sadiq
godiya sosa keya yayi angel itama fitowa tayi riqe da aslam amsarsa sadiq yayi yana mashi
wasa, haka su fatima suka rinqa taya fatuha murna.
3 *years letters*
Sosai fatuha ke maida hankali a karatun ta tana karanta law yanzu haka tana level 2, aslam
yayi wayau sosai dan har tafiya yana yi ba ida baya zuwa zai kai year 2 ga surutu tsiya komai
ya gani sai ya tanka angel kuma na SS2 an fara zama yan'mata.
Yauma kamar kullun a gajiye ta dawo d'aga makaranta tun safe taje school sai 5:00pm suka
gama lectures ,ga wani irin kasala da take ji aslam ne ya rugo da gudu d'aga jikin baba asabe
ya fada jikin fatuha, daga shi sama tayi tana chabe shi yana dariya zaunawa tayi Saman three
star tare da gaida baba asabe amsawa tayi tare da shigewa kitchen aslam zama yayi saman
cinyar ta yana zuba mata surutu, cakulkuli ta shiga yimai yana dariya tsagaitawa tayi tace "Ina
yaya ?", daga kai yayi cikin tsamin murya yace yaya na bacci ok fatuha tace tare da tasha ta
shige bedroom bata zame ko ina ba sai toilet ta sheqa wanka ta fita tare da gabatar da salolin
da ake bin ta. turo kofar da akayi ne ya sata smile angel ce tsaye bakin kofar sanye da jean n
t-shirt tace mom sannu da dawowa, yauwa fatuha tace qarasowa tayi tace mom ki zo muyi
lunch tun dazu na dawo d'aga school naqi cin komai sai kin dawo, murmushi fatuha tayi tace "
Karki qara barin kanki da yunwa kinji angel?" d'aga kai tayi tare da cewa ai nasha