Showing 39001 words to 42000 words out of 99609 words

Chapter 14 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

shi murmushi Mom tayi tace "Ai ina
tunanin wannan yafi wancan, dan wannan dan sudan ne" amma fa na gode Mom kamar kinsan
gobe zai dawo toh ai shikenan daya garin da madara ake sha duk dare shi kuma dayan da
zuma ga turaruka nan masu kamshi in kina anfani da su ko cup kika riqe sai yayi kamshi, washe
baki Anuty bilki tayi mom thanks kamar kin san abban hanan nasan kamshi sosai wallahi , ah
daughter waye baya san kamshi ?sai dai in Mutum bai samu ba kamshi na da muhinmanci
sosai daughter ko kamshi kika riqe to wallahi kin riqe mijinki à wannunki, haka Anuty bilki ta riqa
jerawa mom godiya agogo ta kalla kusan 8:30pm Mom bari muzo mu lalaba mu tafi gida dare
ya fara yi, bada'n gobe abban hanan zai dawo ba da mun kwana wallahi, ai ko ba bazai d'awo
gobe ba ban zan bari ki kwanar min gida ba, ke kullun kika zo yini sai ki bige da kwana ?ai
hakuri ake a zauna har miji ya dawo ya same ka ba wai ka kwaso kafa kazo gida ba, mayafinta
ta janyo da handbag dinta ta tura bakar ledar ciki fitowa sukayi daga bedroom din Anuty bilki
na gaba mom na bayan ta suka sauko daga upstairs sai da ta iso parlour ta yafa mayafin ta ,su
hanan da ke zaune parlour suna shan fruit Anuty bilki ta qaraso hanan ku tashi mu tafi dare nayi
,bata fuska hanan tayi tace "Momi na fa dauka sai 9:00pm zamu tafi "ai kin san bana san driven
din dare ko ?kuma ba da driver nazo ba hanan bata so su tafi yanzu ba da ba exam suke ba da
nan zata kwana fatuha ma haka bata ji dadi ba saboda in hanan ta zo tana dibe mata kewa
Anuty bilki ce ta katse masu tunani da cewa "Hanan yima baba jinmai magana zamu tafi ta baki
afra "bata ida rufe bakin ta ba sai ga baba jinmai riqe da hijabin ta a hannu afra na goye a
bayan ta washe da baki tace ah kuma har kun fito yanzu na ke cewa bari na kawo maki Afra
yau nama yi daran tafiya da yake na tsaya yima mai gida farfesu, mom ce ta ce ku dai baku ji
baby ya sata farfesu ke kuma kin miqa mata diya tana ta fama ga afra da shegen kuka ,ba
komai ai kuma ko kukan ba tayi ba Allah ya taimake ki shi kuma baby bayan yasan baki wuce
magrib shine zai daura maki wahala, murmushi baba jinmai tayi tana qoqarin miqawa hanan
afra ,dariya Anuty bilki tayi tace mom da kin bar shiga tsakanin baba jinmai da baby ko ka shiga
kai zaka sha kunya murmushi mom tayi ,to ai sai mu wuce tare sai na sauke ki gida baba toh
shikenan tare suka fito fatuha na kusa da hanan sunata zuba surutu jidda na riqe da hannu
Jamal duk suka rako su filin gida , Anuty bilki na qoqarin bude murfin mota sadiq ya shigo
tsayawa tayi tana sakin Murmushi qarasowa yayi yace "Sister har zaki tafi ?na dauka kwana
zakiyi ai ya fadi cikin zolaya, harara ta maka mai baby ka rainani wallahi dariya yayi baba har
dake zasu tafi da niyata na kai ki, ah ba komai Hanan dake kusa da fatuha sai turo baki take
sadiq ne ya kalle ta tare da aika mata harara sister na kusa fara cima hanan naga kwanan wani
rashin ji ke damun ta, ni ba ruwana wannan tsakanin ku ne, toh shikenan raurau da ido hanan
tayi tare da cewa uncle sorry harara ya kuma aika mata ganin be da niyar hakura yasa ta tabe

baki ta shige mota tana yima fatuha bye bye su duka suka shige motar Anuty bilki tace "In anyi
hutu this time around jidda a gida zatazo" toh ya ce mata ai sun kusa fara exam I think this
Monday zasu fara eh Anuty bilki tace mai tare da ja su suka bar harabar gidan sannan su
fatuha suka jiyo riqe take da hannu jidda.


Direct bedroom suka wuce sadiq kuma ya wuce dining area , ko da suka shiga bedroom
fatuha ta dire jidda tayi mata wanka sannan itama tayi kusan tare suka shirya saboda itama
yau ta gaji tasha surutu har da godema Allah, night dress suka sa sannan ta dau jidda tana
mata surutu suna haurawa upstairs a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq, a parlour
suka iske shi zaune yana kallan news da gudu jidda ta fada jikin shi ,daddy yes angel ,um
daddy ina ice cream din Anuty da chocolate din ta? laqace mata hanci yayi yace "Yana
bedroom da gudu jidda ta shige bedroom fatuha kuma na qoqarin fita har ta bude kofar, jidda ta
qaraso riqe da ledar shopping Anuty ga naki , angel har dani a tsarabar washe baki jidda tayi ta
ce eh toh na gode ta amsa ta fita.


Direct bedroom din ta ta shige tare da kunna haske, saman bed ta zauna tare da bude ledar
shopping din tun kan ta fara shan ice cream din miyan ta ya tsinke ,tana sha tana kada kai
Amma fa wannan abu akwai dadi sosai gaskiya me kyau yasan kan kwadai, sai da ta cika cikin
ta da ice cream sannan ta kwanta bacci yayi awan gaba da ita.


Akwana a tashi ba wuya wajan Allah sadiq ne janye da trolley din mom dana abba sai da ya zo
bakin kofa ya ba ola da Sunday yayi musu umarnin da su sa kayan bayan boot, ok boss fatuha
ko na parlour zaune sai tsoro take yanzu idan su mom suka tafi Allah ka dai yasan muguntar
da sadiq zai mata ranan unguwa ka dai suka je amma sai da ta dandana kudar ta, bale kuma
kwanaki duka wannan zancan a zuci take tare da kukan zuci dan tasan watan cin uban tane ya
tsaya, su mom ne suka qaraso parlour tana riqe da hannu jidda sai lisafa mata tsaraba da zata
mata take washe da baki fatuha ta tashi tana yi masu Allah ya kiyaye hanya , mom har ta kai
bakin kofa ta juyo da kalli sadiq tace toh ga amanar fatuha sauran kuma inna dawo naji ka
mata wani abu dan nasan halin, bata fuska yayi kamar qaramin yaro yana bin fatuha da harara
tuni yan hanjin ta suka fara kadawa dan tasan kashin ta ya bushe daurewa kawai take amma ji
take kamar ta daura hannu aka ta sa ihu gashi baba jinmai taje biki kauye daga ita sai rabi'a
kuma rabi'a data gama aikin ta take tafiya ,jidda ce ta katse mata tunanin datake taré da janta
tm har suka qarasa farfajiyar gidan, sadiq ne ya shiga wajan zaman driver da alama shi zai
kaisu airport tuni jidda itama ta shige motar mom ce ta juyo tace fatuha duk abinda kike buqata
kiyiwa baby magana kinji toh tace mata tana raraba ido tana daga masu hannu har motar su ta
fita daga harabar gidan.

*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com



49_50

Su sadiq na fita harabar gidan, fatuha ta juyo gida cike da tsoro raurau tayi da ido kamar tayi
kuka saboda tuntuni rabi'a ta tafi sai ita kadan kwal a gidan sai su ola, parlour ta zauna tayi
tagumi kamar munafuka tana ta raraba ido kamar wadda tayima sarki qarya, ganin tsoran ba zai
fishe ta da komai ba yasa ta kuna kallo washe da baki ta dau remote control tana canza
tashoshi Bollywood ta kai tayi shiru tana kallan film gaba ki daya imanin ta naga TV jin cikin ta
ya fara kukan yunwa yasa ta tashi dining area taje ta zubo macaroni da miya yaji kifi sosai
kasan cewa fatuha ba mai san macaroni ba ce yasa ta zuba kadan, ta dawo parlour saman
three star ta zauna ta Fara ci bayan ta kamala ta kai plate din kitchen tare da wanke wa
bedroom ta koma tare da rage kayan jikin ta ta shiga wanka bata wani dade ba ta fito ko da ta
fito lotion ta shafa tare da feshe jikin ta da turare white t-shirt din ta na aiki tasa kasan cewa
rigar ta kawo mata gwiwa sai taji bata sha'awar sa skirt din gashin ta ta baza ta sharce masha
Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba ,qarewa kanta kallo tayi a dressing mirror dariya tayi tace
"Kai dan Allah dubi yadda nayi kamar ta cikin film din dana gama kalla hhhh lol" ta kumayin
dariya tana godéma Allah da yawadata ta da gashi à haka tasa kafa tafita daga bedroom din.


Bangaran su sadiq har yana kai su mom airport , ya wuce da jidda family house dan shi yama
manta da wata fatuha part din ammi ya shiga riqe da hannu jidda , a'a wana ke gani , murmushi

sadiq yayi tare da zama saman kujera yana gaisheta sannan yace, "Matar yanaga kin qara
kyau?" washe baki ammi tayi tana gyara daurin dankwalin ta tare da amsa mai ta qaraso
parlour itama ta zauna, ohni mai gida ace min jiki yayi sauki da har na fara dakan gunba ance
min kana can rai hannu Allah ka zama dan gurgu ta ida zancan tana dariya ,turo baki sadiq yayi
yace "Haba ammi har so kike na bingire kenan ?dariya ammi tayi tare da janyo jidda jikin ta yar
nema yau ba'a amin gwalangwatsin ba smile jidda tayi kawai tare da cewa "Ammi ina gorubar
da kika ce zaki siyo min ni da jamal? yar nema ashe baki manta ba ai tuntuni na siya tana daki
na cikin drowe, da gudu jidda ta shige dakin ammi ta dan juyo tana facing din sadiq gyara
murya ammi tayi tace "Ni ko Sadiq ya kamata kayi aure? Yanzu fisabilillahi dubi yadda jidda tayi
wayau sosai yarinya na shirin zaman yan'mata, amma kai baka ko maganar aure bale nuna
sha'awar ka ko dai baka lafiya ne Abubakar sadiq?" sadiq dake zaune saman three star ya hada
gira sama data qasa kamar be taba dariya ba, kai kullun baka so a fada ma gaskiya sai ka hau
gunguni shi kuma Ibrahim ya zuba ma ido ko maganar aure bai ma, sadiq ko tunda ammi ta
fara magana ya kai wuya dan shi be da tsarin yin wani aure yanzu, Alhaji ne ya qaraso parlour
da alama yanzu ya dawo daga kasuwa ganin ammi nata fada yasa Alhaji qaraso dan yaji ba'a
sin zancan, ganin sadiq tatasa gaba ya san maganar gizo bata wuce qoqi, haba ladingo ya za
ai ki tasa yaro gaba kina mai maganar aure? eh koma me ake samu a auran nan ai ya taba yi
inya gaji da zama haka ai dole yayi aure tunda shi ba qarfe bane, ammi tabe baki tayi tace
"Malam kenan da yaranan na da wannan tunanin ta tuni yayi amma kwata kwata banga alamar
yin hakan ba , koma dai meye ba kyau sasji gaba ba kina mai fada, ba ko abin motsa baki
amma sai fada kike mai, shiko sadiq dadine ya mamaye mai zuciya sai murmushi yake, ammi
tayi yake tace "Wallahi malam abin ya tsayamin araine?" Alhaji zama yayi kusa da sadiq tare da
shafa gashin shi yi hakuri kaji Abubakar sadiq, qaqaro murmushi sadiq yayi Wanda iya qarshi
lips din shi yauwa ko kai fa, ammi kuma asiya ta kwalawa kira ta kawowa Alhaji abinci da sadiq,
sadiq sai fama daurewa ammi yake bayan asiya ta kawo komai ammi tace ya sauko ya ci, na
koshi ya fadi a taqaice, bude baki ammi tayi ta fara fada yanzu ni sadiq ban isa nama magana
ba ko na baka shawara sai ka nunamin ban isa ba ko Ibrahim ai bai isa yamin haka ba matsar
kwalla ta fara Alhaji da ke gefe ta kaici ma ya hana shi magana sadiq ganin abun ammi da
gaske ne ya sashi cin abincin tare da sakin rai sannan ammi ta ji dadi ba laifi ya dan saki jiki
amma sai wani bangare na zuciyar shi ya ke ji kamar ta famamai inda ke mai qaiqayi tabas
yasan yayi rashin kausar har abada bazai kuma samun wada zata maye gurbinta ba, amma
wani bari na zuciyar shi yaqi yadda ya cusa san wata diya mace har ta samu gurbi a zuciyar shi
numfashi ya sauke tare da miqewa tsaye yana kiran angel, mai gida kardai ka ce min tafiya za
kayi ?ko har yanzu baka huce ba? murmushi sadiq yayi haba matar ni na isa nayi fushi dake
nayi fushi dake gobe ina zan fake washe baki ammi tayi tace yauwa dan albarka , Allah yasa
ma Albarka ameen ammi , bari na kirama yar neman nasan yanzu haka ta wargaza min daki
dariya Alhaji yayi ya ce aiko data kyauta, malam har da kai masu biye ma ifiritan nan ko da
yanzu Jamal zai zo su hade biyar baka siyan part din nan dariya Alhaji yayi tare da shigewa
bedroom din shi, ammi kuma ta shige nata tana kwalawa jidda kira aiko tana isa dakin taci karo
da abin goriba duk jidda ta watsar a tsakar dakin ohni ladingo ai dama na fadi nasan za'a rina
tunda najiki shuru washe baki jidda tayi tace ammi, sadiq dake parlour ya qaraso yana dariya
laa angel waya ce kiyi ma ammi baena turo baki tayi tace "Daddy ba bana nake ba" ammi tace
gidan ku kikayi ko? dariya jidda tayi ta boye bayan baban ta , ammi bari mu qarasa part din

Umma toh shikenan saura canma ki mata barnar haqora jidda ta washe sannan sadiq yayi ma
ammi sallama suka wuce part din Umma.


Parlour ta kuma dawowa tare da kallan agogo ganin karfe 3:00pm yasa fatuha rau rau da
ido, tasan za'a rina tunda aka bar amanar ta a hannu sangami a iya tunanin ta ko wanne gari
suka kai su mom ya ci ace sun dawo gida, zama tayi saman one star can kuma sai ta tashi
upstairs ta haura sama direct part din sadiq ta shige a hankali ta murda handle din cikin sa'a
kofar ta bude saboda a tunanin ta ya kulle part din, tana shiga sanyi da kamshi suka mamaye
mata hanci lumshe ido tayi tare da mai da kofar parlour ta rufe bedroom dinshi ta shige tana ta
kalle kalle wani album ta hango ya leqo ta qarqashin gado duqawa tayi tajanyo shi da hannun
ta washe da baki ta bude album din pics din sadiq ta fara cikin karo da shi ya saki murmushi a
pic din gashi yasha kyau har ya gaji ,cigaba tayi da ganin pics din album din wani guri ta Ganshi
da kausar wani gurin shi daya ganin yadda suke pics din yasa fatuha ta dade tana kallan pics
din ko ba'a fada mata ba tasan maman jidda ce saboda suna kama da jidda ji tayi gaba ki daya
sun birge ta haka ta lalace tana kallan albums din kiran sallah la'asar ne ya sata qoqarin mai da
album din har ta turashi qarqashin gado sai ta ji wani album din janyo shi tayi tare da yin smile,
bari na tafi da wannan inna idar da sallah ya debe min kewa, tunda ni ka dai suka bari wato sun
barni a gida duk abinda zai cinye ni ya cinye ni downstairs ta dawo ta aje album din a parlour ita
kuma ta koma bedroom din ta dauro alwala.


Cikin sallama su ka shiga part din umma, Umma na zaune tana kallo tana shan fruit a hankali
da alama zaman ya mata dadi ,cikin fara'a ta amsa sallamar su sadiq zaunawa yayi tare da
gaishe ta ta amsa jidda ko saman ciyar Umma tayi masauki, yan'mata baba fari da ido jidda tayi
tace "Na'am grandma" a'a waya koya maki fari da ido haka? dariya tayi tace "Anuty mana" wace
Anutyn? Ta bata Amsa da cewa "Anuty fatuha mana" ah ni ban santa ba kam aiko Anuty fatuha
na da kirki sosai yanzu haka tana gida murmushi Umma tayi tare da yi masu tayi fruits qasa
sadiq ya sauko ya sha fruits din shi ya qoshi sannan ya haura upstairs cikin natsuwa ya murda
handle din kofar daki kwance ya hango majid yana ta sharar bacci dan gutun tsaki ya ja tare da
shiga daki fridge ya bude ya dau ruwa mai dan sanyi sanyi sai da yazo saitin face din majid ya
zuba a hannun sa ya shiga yayafa mai, firgigit majid ya miqe yana qoqarin tashi ganin sadiq
yasashi komawa ya zauna tare da zabga tsaki , kai dai wallahi mugune ,in banda mugunta ina
bacci zaka sheqa min ruwa? harara sadiq ya aika mai yanzu lokacin bacci ne kana ganin la'asar
ta wuce, mtss toh ina ruwan ka? da ruwa na sannan ya zauna saman sofa, wallahi big man
baka kyauta min ba wallahi mafarkin wata hot baby nake kawai ka zo ka katse wa mutane jin
dadi mtss tashi ka ban guri Dan iska kawai, dariya sadiq ya fashe da ita sakin baki majid yayi
yana mai kallan rainin wayau me haka wai , kaga kyale ni je kayi wanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login