Showing 75001 words to 78000 words out of 99609 words
Chapter 26 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf
tace a taqaice dan da
kyar take mai magana saboda tsanar shi da ke bin zuciyar ta, nasan na maki laifi my love naje
nayi abu bada sanin ki ba amma please kiyi hakuri wasu Sabin hawaye fatuha ta h'ade tace "Ba
komai tana qoqarin bale murfin motar, idan dai kin hakura please ki bini nayi dropping din ki?
daure fuska fatuha tayi dan bata jin zata iya bin majeed a yanzu, lagwabe kai majeed yayi yace
please ki bani dama duk da nasan bani da mazauni a zuciyar ki,Am ma Dan Allah Kiyi hakuri
kisoni koda kadane,tunda nataso bantaba samun yarinyar DA ta kwanta min a rai kamarki,
fatuha please ki bani dama na gwada maki soyayyar da nake maki haka majeed ya rinqa
magiya da kyar ya samu fatuha ta shiga motar shima sai da jidda suka shige ya ja motar.
Sadiq dake zaune cikin mota yana k'allan duk yadda suke ,da kyar ya iya saita numfashin
shi, tabas yasan ranar da fatuha zata zama malakin majeed ba abin da zai hana shi zama gawa
.da kyar ya iya bude baki ya ce ma driver ya jasu,ba musu yabi umarnin ogansa suka bar
haraban gidan.suna zuwa wajen aikinsu SadiQ ya bude motar yafito tare DA daukar jakarsa
,ahankali yake tafiya kamar kazar DA kwai ya fahema aciki. Duk inda ya wuce ma'aikata Nata
gaisheshi hannu kawai yake daga masu, domin jiyake bakinsa yayi masa nauyi. Yana zuwa
office dinsa yabude yashiga ,yayi jifa DA breekfest dinsa ya zauna bisa kujira wani kuka ne ya
subuce masa Mai radadi DA ciwo, jiyake duniyar nayi masa zafi,bai tab a sanin yana kaunar
fautuha ba sai yanzu DA yake shirin rasata. Way majeed ! Me yasa zakamin haka? Me yasa
kake Neman ruashemin farinciki na? Me yasa zakace kanason Fatuha alhalin nafika bukatarka
a yan " DA karfin tsiya ya d'aki teburin d'ake gabanshi yace nooooo Fatuha tawace insha Allah
wani murmushin karfin hal'i yayi (DA Ni Salma nakasa gane ma'anar hakan).
Majeed nayin parking a harabar makarantar Fatuha ta Kama murfin motar zata bude ,DA sauri
ya Dana wani remot ya rufe koffofin motar ,cike DA tsiwa ta dubeshi suna hada ido dashi ta
sunkuyar DA kasa, batasan meyasa majeed yake Mata korjini duk yanda taso yimasa rashin
kunya suna h'ada ido zata nemi natsuwar ta tarasa. Murmushi majeed yayi yace, "Haba My love
,ya za'ayi kifita kibar mijinki DA tsananin tunanin ki? Ya kamata kifada min wata kalma DA
zaisani tunanin ki koda Ina office plsss matata kada kice min aa". Takaicine ya lulube Fatuha
,banda iskanci gidan uban wa aka d'aura mana aure d'ashi DA har zai kirani matarsa taja tsaki
a ranta mtsss ,a fili kuma tace " Plsss oncl kabarni natafi Dan Allah ta karasa maganar kamar
zata Mai kuka" Sorry my lovely Zaki tafi amma Dan Allah Kiyi min murmushi KO Zan samu
tsuwar zuciyata?" Fatuha tace a ranta "Dan iska shege mugu kawai Allah yasa zuciyar ka ya
dawama DA bakinciki k'amar yand'a kak'e ko'kari'n sani". A fili kuma tayi murmushi DA iyakarshi
lebenta, majeed ya b'ude masu kofa'r DA sauri ta fita tayi gaba, jeedah nako'kari'n binta majeed
yaciro kudi masu yawa yaba jeedah shi kansa baisan KO nawane. tayi Mai godiya tare DA Mai
piek a kumatu ta tafi DA gudu domin har Fatuha tayi Mata nitsa, shima majeed cike DA farinciki
ya bar harabar makarantar....
*_Kuyi h'akuri da wannan page din, b'ana samun time sabod'a yanzu na k'oma skul._*
*Taku h'ar kullun salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R
*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
79_80
Ko da fatuha ta shiga class ba wani walwala, haka su nana suka rinqa tanbayar ta "Ta fada
masu meke damun ta?" amma firtaqi gaya masu damuwar ta, Nana ce tace, "Haba fatuha
kenan baki daukemu a matsayin qawayan ki ba? da har zaki boye mana abun dake damun ki"
Zara ce ta budi baki tace, "Kyale ta Nana ai dai mun san matsayin mu yanzu "Zara na qoqarin
jan nana subar seat din , fatuha ta riqe Zara please kuyi hakuri, zan fada maku damuwa ta ida
zancan hawaye na sulalo mata. duk abin ya faru haka fatuha ta kwashe ta fada masu, Zara taji
haushi ba kadan ba haka suka rinqa bama fatuha hakuri tana raira kuka da kyar suka shawo
kanta.
Bangaran majeed inbanda dad'i ba abinda yake ji ,zuciyar shi fes take d'aya lumshe ido
kyakyawar fuskar fatuha yake hagowa sai ya qara sakin smile,
Jingine yak'e saman kujera office ya rasa sukunin shi, idanuwan shi na lumshe saboda
nauyin da suka mai har wata masasara ke rufe shi ga qirjin shi dak'e mai zafi. a hankali ya ware
sexy eye's ball's din shi da suka rine sukayi jaa wayar shi dak'e ruri cikin aljinhun shi ya curo
sabuwar number ce baro baro a screen din, da kamar ba zai dauka ba sai ya daure ya dauka
tare da karawa a kunne. Cikin zazakar muryata cikin yauki basma ta mai sallama, amsawa yayi
a taqaice tare da tanbayar wake magana? gyara kwanciyar tayi d'aga inda take tare da
kankame wayar dan wani irin sanyi ke ratsata, dan gyaran murya tayi cike da shagwaba tace,
"Yaya sadiq ni ce fa basma? ko number ta ashe baka da ita? ta ida zancan cikin shagwaba"
Sadiq d'ake kishingide saman kujera, ranshine ya qara suya dan shi duduniya ba macan dak'e
birge shi ko bashi sha'awa kamar fatuha, ko wannan magana ma da take yi jiyake kamar tana
watsa mai ruwan zafi, tsuke fuska sadiq yayi kamar tana ganin shi yace, "Yanzu ina wani aiki
ne letter mayi magana in na dawo" be jira ce wata ba ya katse wayar tare da yin wurgi da ita ta
dak'i bango ta dawo watse ko ta kanta be bi ba ya sa kai ya fice d'aga office din.domin idan ya
cigaba da zama tabas kwakwalwar shi da zuciyar sa suna iya bugawa. bin wayar tayi da kallo
tare da dan bata fuska , ta aje wayar ta kwanta.
Ko da aka tashi su fatuha majeed ne ya zo daukar su ,ganin shine yasa ta had'a gira sama
data kasa dan ba abinda ta tsana kamar ganin shi. ba yadda ta so haka ta bale murfin motar ta
shiga tare da gaishe shi, kallan ta yake me cike da so da kauna , sannan yace "My love d'aga
gani yau kin sha wuya da yawa? ina fata dai kina kulla min da kanki?" dan guntun tsaki fatuha
ta ja ciki ciki sannan tace a cikin zuciyar ta "Har wani Kira kake na kulla ma da kaina mtww dan
iska kawai" muryar majeed ce ta doki dodan kunnan ta a karo na biyu yace "My love! ko duk
gajiyar ce tasa ko magana ba'a San yimin?" dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi laban ta tace
"A'a" murmushi majeed yayi tare da cigaba da driven din shin, haka ya rinqa janta da surutu
tana amsa mai sama sama sannan ya wuce da su bakery yayi masu siyaya ice cream da cake.
jidda ko sai dadi take ji dan har yanzu bata san inda aka dosaba.
Suna kunna hancin motar su. suka ci karo da sadiq wanda shima dawowar shi kenan wani irin
dogwan numfashi sadiq yaja a duk lokacin da yaga majeed da fatuha, numfashin shi sai ya
nemi ya dauke ko qirjin shi ya rinqa mai zafi. da kyar ya iya d'aga kafar sa dan baya so ko
fuskar su ya gani sun fito a tare, amma sai dai kash majeed ya riga ya kira sunan shi. lumshe
ido yayi ya tsaya chak! sai da ya kwashe yan mintina sannan ya waigo tare da sakin smile din
karfin hali, ta gaban shi fatuha ta raba ta wuce jidda nata zuba mai surutu sannan itama ta
shige, miqa mashi hannu majeed yayi suka gaisa, big man duk yau ban ganka a office ba oh ina
cikin office ina wani aiki ne gobe ma nake so na wuce Lego's , Lego's kuma ?me zaka je yi
loges? inji majeed zan je nayi 2week ne cikin ruwa na dawo , Eyya to Allah ya taimaka ameen
yana qoqarin shigewa majeed yace, "Baby!" yes yace a taqaice dama ina so muyi wata magana
ok mu shiga ciki ok majeed yace tare da bin bayan sadiq suka shiga part din sadiq briefcase din
shi sadiq ya aje tare da rage kayan jikin shi ya shiga toilet, ya dade a toilet din beyi wankan ba
yana kukan bakin ciki sannan ya tashi yayi wanka sanye da bathrobe ya fito qaramin towel a
hannu shi yana goge jikin shi. majeed na zaune saman sofa shima tashi yayi ya shige toilet ya
sheqa wanka ya fito ko da ya fito lokacin sadiq ya shirya cikin black 3 quarter din shi da white
shirt mai gajeran hannu, yana zaune saman sofa idanuwan shi lumshe, shiryawa majeed yayi a
tsanake sannan ya bude wardrobe din sadiq ya ciro riga da wando riga blue sai dark blue jeans
sannan ya bude fridge ya curo fresh milk ya tsiyaya a cups ya miqama sadiq ya amsa, zama
yayi kusa da sadiq yace, "Please ina so kamin taimako guda please?" ok inajin ka indai baifi
karfina. murmushi majeed ya saki yace "Befi karfin ka ba" gyara zama sadiq yayi yana
sauraran majeed riqe hannu shi majeed yayi cikin lagwabe kai please baby kamin hanya fatuha
ta so ni .tsura mashi ido sadiq yayi da idanuwashin da suka cika da kwalla hadiye su yayi yana
saurara majeed, baby wallahi ina san fatuha ban taba jin San wata ba kamarta ba baby karkayi
tunanin irin sanda nake ma sauran yan'mata nea nake mata a'a santa nake da gaske wallahi
inna rasata zan iya rasa rai na majeed ya fada. sadiq dai binshi yake da ido kamar sakarai
gabaki daya jikin shi ya mutu sai zuciyar shi dake ta har bawa da sauri kamar zata fito waje
,dan matse hannu shi da majeed yayine ya sasa dawowa d'aga duniyar tunanin .smile ya saki,
haba my man karka damu kaji dan jama aji take amma nasan zata so ka kaji Kasan yadda mata
suke amma nasan zata so ka har ku dai-daita .murmushi majeed ya saki tare da kaima sadiq
hug hawaye suka cigaba da yima sadiq anbaliya dan ko yasan ya rasa fatuha Dan baya fatan
abinda zai samu majeed dan uwan shi abokin shi bashi da aboki dan uwa saman da majeed.
lokaci yayi da ya kamata ya ba zuciyar shi hakuri jin majeed zai zame jikin shi yasa sadiq saurin
share hawayan shin tare da sai ta kanshi murmushi suka sakar ma junan su, fira suka fara
sama sama kiran sallah magrib ne ya tashe su,
*1week letter*
Shirye shirye aketayi a family house, kasancewa yau za'a sa rana biki duk wanda ka kalla cikin
farin ciki yake musanman basma da majeed, zaune suke cikin daki'n yan'mata ana zuba hira
muryar basma k'adai ke tashi fatuha na gefe tana matsar kwalla dan har yanzu gani take kamar
wasa ,kamar mafarki tashi tayi ta fita dag'a dakin ganin kayan da ake ta wucewa da sune yasa
jiki fatuha ya qara sanyi. fitowa tayi d'aga parlour hango qanan baban ta tayi su baba barau
wasu hawaye masu zafi suka sulalo mata yanzu ta tabatar za'a Samata rana da wanda bata so
a matsayin miji kuka ne ya ci karfin ta. fita tayi d'aga gidan gabaki daya dan ko sanin inda zata
ba dan inda zata ba. can baba jinmai ta fado mata a rai kekenapap ta tara ta shige tace "A
kaita gadan qaya" kasan cewar gidan baba jinmai kan titi yake bata wani sha wahala ba ganin
gidan. kukan da take yasa mai kekenapap din bar mata kudin saboda ya tausaya mata ko
sallama bata cika ba ta shige gidan, baba jinmai dake qoqari fita, fatuha ce ta fada jikin ta tare
da sakin kuka kamar ranta zai fita. rudewa baba jinmai tayi tana kallan ta baki saké, zaunar da
ita tayi saman kujera tana tanbayar ta lafiya? kuka take sosai, cikin shasheqar kuka tace
"Wallahi baba bana san majeed bana jin zan iya zaman aure da shi ta ida zancan tana rushewa
da kuka" sallati baba jinmai ta hauyi tare da tafi na Shiga uku ni jinmai , me nake ji haka fatuha
sokike ki ja mana abin fade ?toh in ba majeed din ba wakike so? kuka ta kuma saki cikin
shasheqar kuka bakin ta na rawa tace "Baba sadiq nake so! wallahi ina rasa sadiq mutuwa
zanyi" ta ida zancan tana kuka mai tsuma zuciya, zaro ido waje baba jinmai tayi na Shiga uku ni
jinmai. rungume fatuha tayi tana lalashi dan ita kanta ta tausayama fatuha ita kanta taso ace da
sadiq din za'ayi ,amma ya zasuyi tunda shi be ce yana so ba? d'ago da fatuha tayi tana share
mata hawayan ta kiyi hakuri fatuha kinji ki cigaba da addu'a Allah yana tare dak'e Allah zai dubi
zuciyar ki ya baki mafi alheri fatuha kisama zuciyar ki sallama kinji .ajiyar zuciya kawai take saki
tayi lamo a jikin baba jinmai.
In banda tari ba abinda yake har wani jiri yake gani ,majeed d'ake gefan shi sai sannu yake
mai. toilet ya shige da sauri yana cigaba da tarin gaban zing kallan mirror d'ake manne jikin zing
din yayi jini da ya ganine gefan bakin shi ya sashi zaro ido! hannu ya kai ya taba ganin kamar
jinine yasa gaban shi ya qara faduwa hawayan dake maqale a idanuwashi suka sulalo.zamewa
yayi a qasan toilet din yayi yana mai da numfashi sama sama miqewa yayi da sauri ya fito duk
da yana jin jiri .majeed dak'e zaman jiranshi ne ya ta shi yana mai sannu ko amsa mai sadiq ya
kasa, wardrobe din shi ya bude ya janyo trolley ya fara zuba kayan shi yana zubawa jiri na dibar
shi ga tarin sai zuwa yake tare da jini amma duk wannan abun yaki yadda majeed ya gane sai
da ya gama had'a kayan shi tsaf majid na gefe tsaye riqe shi yayi yace "Baby wai me ke faruwa
ne? naga muna lafiya lau lokaci daya ka rude" murmushi yayi yace "Karka damu tunawa nayi da
flight dina na zuwa Lego's yau zai tashi kuma gashi saura 10 minutes ya tashi" ok muje nayi
dropping naka ka barshi kawai nayi ma driver magana kaji? ok ya ce mai tare da yi mai pack
sannan ya sa kai ya fita da kyar ya iya jan trolley ya fita waje yana tafiya yana tari tunkan ya
qara so ashuru driver ya bude mai murfin mota amsar trolley din yayi yasa a boot sadiq yana
Shiga mota ya fara b'ale bottle din rigar shi saboda zafi ga numfashin shi d'ake daukewa yana
dawowa. ko da ashuru driver ya shigo mota ja yayi suka bar harabar gidan ta cikin mirror ya
fara ganin halin da sadiq yake ciki. yallabai! yace a tsorace cikin murya da kyar da kyar sadiq
ya iya furta kaini wajan Dr yakub aiko da gudu ashuru ya fisgi mota sai asibitin Dr yakub suna
Isa asibiti sadiq ya bude murfin motar duk da yana ganin jiri ga numfashin shi dake mai sama
sama office din Dr yakub ya nufa yana bude kofar ya fadi sumame a wajan...♀
Muje zuwa fan's
*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
♂
*Writing by*
*salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R
*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
81_82
Mikewa Dr yakub yayi dan kawowa sadiq taimakwan gagawa. gabaki d'aya shima ya rude
kwalawa norses kira ya shiga yi da sauran ma aikatan asibitin kafi kace me har an daura sadiq
a gadan asibiti ,ashuru driver da shigowar shi yanzu ya gani bin gadan yayi yana matsar kwalla,
ba'a zame da sadiq ko ina ba sai emergency, ashura na ganin hak'a ya ci birki bakin kofar yana
zarya yar wayar da ke aljihu shi ya zaro dan ya kira gida amma sai dai wayar ba chaji kuma bai
iya tafiya ya bar sadiq a yanzu dan ana iya buqatar wani abu. h'aka ya rinqa zarya baki'n kofar
ga baki d'aya ya rude.
Hak'a baba jinmai ta rinqa lalashin fatuha sannan tayi shuru, fatuha tashi kiga mu koma
tunda dai kin san aiki na can na jira na ? matsar kwalla ta fara cikin sanyin murya tace "Dan
Allah baba ki barni a nan wallahi bana san zuwa, bana san jin hayaniyar kowa! mudin na cigaba
da ganin abinda ake a gida ina iya shiga wani hali" duk yadda baba jinmai taso ta tafi da fatuha
firtaqi ba yanda ta iya shiya ta barta ta tafi ko da baba jinmai