Showing 36001 words to 39000 words out of 99609 words

Chapter 13 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

Advertisement

baba jan abba yayi suka shige part nashi suka dasa sabuwar hira
abin ka da yan'uwa haka Umma da mom suka bude saban shafi na hira basma ce ta fito sanye
da gown ta zo har parlour ta gaida mom ,tare da kawo masu kayan motsa baki sannan ta ja
jidda bedroom din tana mata wasa tare da tanbayar ina daddy washe da baki jidda tace yanan

lafiya lau ok good ,idan kun koma gida ki ce mai anuty basma na gaisheshi to jidda tace mata,
chocolate ta dauko a bedside drowe taba jidda sannan ta cigaba da assignment din ta da
datake yi sun dade sosai dan kusan a can su kayi dinner sai kusan 9:00pm sannan suka fito, se
da abba ya qara leqawa part din ammi ya gaishe da alhaji sannan suka fito har bakin mota
Umma da baba da basma suka rako su sannan suka juya cikin gida.


Fatuha kuwa sadiq na lulube ta bacci ya kwashe ta ,ba ita ta tashi ba sai da ake Kiran sallar
isha'i ko da ta tashi zazabin ya sauka sai dai jikin ta ba qwari, a hankali ta yaye blanket din
jikinta ta shige toilet arwala ta dauro bayan ta gabatar da sallah ta koma saman bed ta kwanta,
sadiq bashi ya fito daga gym ba sai magrib wanka yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai
bayan sallah isha'i ko da ya shigo gida yaji ba motsin kowa hakan tabatar mai da su mom basu
dawo ba, bedroom din fatuha ya leqa kwance ya hango ta jin shigowar shi yasa fatuha qara yin
lamo haskyan dakin ya kunna tuni dakin ya gwaraye da haske ,a hankali ya qaraso ya leqa
fuskar ta tare da cewa fatuha banza tayi kamar me bacci tsaki ya ja yace "Nasan kina jina ko? ki
tashi ki sha magani kona qarasa ki da bindiga, tunda dai mutuwar kike so" tuni fatuha ta tashi
zaune tana zarar ido maganin ya shiga bale mata ya bata sai da ta sha sannan ya miqa mata
fresh milk tace ta koshi wani irin kallo ya wurga mata ba arziqi ta kafa kai ta sanye, sannan ya
fita daga daki yana fita ta ce ah ashe su sangami ana da kirki har da hada ni da madara mai
dadi sannan ta ja dan guntun tsaki ta koma ta kwanta.


Bayan ya fito daga dakin fatuha parlour ya dawo ya zauna tare da lumshe idanuwan shi
kamar me bacci cikin sallama su mom suka shigo wani irin smile yayi tare da tashi zaune, ya
qaraso wajan su jidda ce ta rungume shi tana cewa daddy I miss u miss u more angel kin tafi
kin bar daddy shi ka dai a gida, turo baki tayi tace "Daddy Anuty nan bata taya Kuyi hira ko? ta
ida zancan ta bata fuska" eyya angel Anuty ba lafiya fever take, mom da zaman ta kenan
saman three star tace me ya sameta sadiq yace mom fever take dazu na ganta a parlour zaune
tana rawar sanyi shine na kira mata Dr yakub ,good baby ka kyauta bari na dubata abba da ke
haurawa upstairs ya ce kice ina mata sannu to mom ta ce tare da shiga ita da jidda, ko da suka
shiga a lokacin fatuha tayi bacci cikin tausayawa Mmy take kallanta domin sakanita d Allah take
son yarinyar d'aga karshe tayi mata Adu'a suka bar dakin.


yau ko sadiq shi da kanshi ya shirya jidda, sannan su kayi bacci jidda ko sai missing din Anuty
fatuha take sadiq ko dadi ya ji komin banza ta saitu.



*taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*
★we are the best★


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook*:www.Facebook.com/REAlHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com


45_46


*Yan uwa kuyi hakuri jiya nayi mstk maimakon nasa 43_44 sai nasa 43_45 ina fatan zaku min
uzuri yauw zamu tashi d'aga 45_46 ina fatan kungane ni Salma ina Al'fahari d'aku Nagode sosai
yanda k'uke son wanga littafin nawa Allah Ubangigi yabarmu taré Ameen....wanga pag din
sadaukarwane gaduk mai bin labarin I love you ol my fan's‍♂*


Misalin karfe 6:00am na safe fatuha ta tashi Alhamdulillah jikin nata da sauki, à hankali ta sauko
d'aga gadon ta shiga toilettes wanka tayi tare da yin arwala ,tana fitowa tasa doguwar Riga ta
shimfida daduma domin gabatar da sallah ,kasan cewar yau juma'a tana gamawa ta cire rigar
ta saka wata Riga da wando mai mai ruwan zumuwa Rigar ya tsaya mata har gwuwa ba
qaramin kyau kayan suka mata sai suka fido da ship din ta sosai veil din kayan ta dauko se yar
hoda data Murza se lipstick ta sama lips din ta , tayi kyau masha Allah direct part din sadiq ta
wuce a dai dai bakin kofar ta ci birki ta zaro idanuwan ta har ga Allah yanzu Sadiq ya fara bata
tsoro daure, fuska tayi à hankali ta murda handle din kofar, parlour ba kowa sai sanyi AC da ke
tashi da kamshi a hankali ta qarasa kofar bedroom ta murda a hankali sadiq ta hango gaban
dress mirror, sanye da bathrobe yana goge gashin kan shi cikin sallama ta qaraso bedroom din
ciki ciki ya amsa kamar me koyan magana jidda dake zaune saman bed itama sanye da
bathrobe da alamar da ya gama gyara kanshi ze gyarata washe da baki jidda tace Anuty tare
da rugawa a rungume ta bata fuska tayi tace "Anuty ashe baki lafiya shine baki fada min ba? ta

ida zancan tana bata fuska" murmushi fatuha tayi tace "Ai yanzu na warke sauki ranki Jidda ta"
toh shikenan Anuty sadiq ko harkar gaban shi yake fatuha kuwa sai binshi take da ido a sace
ohni mutun sai shegen kinibibi kamar mace dan gutun tsaki fatuha ta ja tare da daukar jidda
suka fita.

Bedroom ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta, sannan ta raba mata gashin ta gida biyu
taja hannun ta suka wuce dining area ,mom da abba na zaune a dining area cikin natsuwa ta
qaraso ita da jidda ta gaishe su mom cikin ladabi a tare suka amsa tare da yimata ya jikin,
washe da baki tace da sauki jidda ta jama kujera ta zauna sannan ta fara saving nata tana cikin
saving nata sadiq ya qaraso dining area gaishe da su mom yayi tare da yi masu pack sannan
ya samu kujera ya zauna masha Allah ya sha kyau har ya gaji, kallo daya fatuha ta masa ta
kauda kai cikin tsanar sa Amma duk da haka sai da ta yaba kyau irin na sadiq har mamaki take
anya akwai wanda ya fishi kyau kuwa musanman yau da yake sanye da manyan kaya, tunda ta
zo gidan yau ce rana ta farko data fara ganin me kyau da manyan kaya shada ce sky blue yasa
tasha dinki da dark blue zare anmai irin dinkinnan na sarauta se hula blue mai ratsin dark blue ,
hannu ya kai ya dau cup ya fara hada tea dan shi mutun ne ba mai san yawan cin abinci ,
bayan ya gama hada tea ya fara sha a hankali mom ce ta kalle shi tare da cewa baby karka ce
min yau ma tea kadai zaka sha lagwabe kai yayi yace eh, haba baby wai me yasa baka san cin
abinci ne eh abba da ke gefe yace "Sai kace ba soja ba sojoji da aka sani da cin abinci ,
shagwabe fuska yayi ya cigaba da shan tea din ganin mom nata magana yasa shi cin chips din
kadan fatuha sai da tabatar jidda taci ta koshi sannan ta kyale ta bayan sun kamala cin abincin
sadiq ya dau jidda fatuha na biye da su da lunch box har bakin mota , sannan jidda ta mata
pack ta shige mota juyowa tayi ta shigo gida da abba ta ci karo mom ta rako shi riqe da
briefcase din shi wuce su tayi ta koma dining area chips ta Zumaba da farfesun kifi bata wani ci
da yawa ba saboda har yau bakin ta ba dadi bayan ta kamala ta fara kokarin kwashe kwanikan
,mom ce shigo washe da baki tace "Haba fatuha ke da baki da lafiya ina ke ina aiki ki ?zauna ki
hutu" washe baki fatuha tayi tana qoqarin yin magana mom ta hanata kwalawa rabi'a kira tayi
cikin ladabi rabi'a ta qaraso tayi ta d'urkusa har kasa ta gaishe da mom , yawa rabi'a
kwanikanan zaki kwashe sannan yau ki je ki gyara part din sadiq saboda fatuha bata jin dadi
har cikin zuciyar rabi'a bata so mom ta ce ta gyara part din sadiq ba saboda basa wani shan
inuwa daya jiki ba qwari ta kwashe kayan dining area din fatuha kuwa daki ta koma tasha
magani bata wani dadi ba bacci ya kwasheta.


A cikin school yayi parking din motar shi tare da zagayowa ya budewa jidda murfin mota ,ta fito
lunch box din ya miqa mata tare da yi mata pack ,daddy am going to miss u , I now angel karki
damu anjima in an tashi ni zanzo daukar ki kin ji angel murmushi tayi tare da yi mai pack ta
shige class yana kallan ta har ta shige ,shi kuma ya wuce wajan aiki taré da kaunar diyar tashi.

Ba ita ta tashi daga bacci sai karfe 11:30pm ita kanta tayi mamaki baccin da tasha, toilet ta
shiga tayi wanka ta fito tare da shafe jikin ta da lotion wardrobe ta bude ta ciro atamfa brown

me ratsin black n white atamfar ta hadu riga da skirt dinkin ya mata kyau qarewa kanta kallo
tayi ta cikin dressing mirror murmushi ta saki tare da cewa gaskiya birni tayi dubin yanda na
koma kamar ba fatuha inna ba duk wannan zancan tana yinshi ne a zuciyarta, murmushi takara
yi tana qoqarin kama gashin kanta bude kofar da akayi ne yasa ta saurin waigowa a tunanin ta
Jidda ce sai taga hanan washe baki tayi tare da cewa "Hanan cikin fara'a" hanan ta qaraso
dakin sanye take da lace sky green mai ratsin black se veil din ta white ba qaramin kyau tayi ba
ta fito yan'matan sak, zama tayi saman bed tare da cire veil din wash na gaji wallahi dariya
fatuha tayi wai kin gaji, aiki me kikayi da kika gaji? murmushi hanan tayi tare da cewa "Kai
fatuha karki ce min wannan uban gashin naki ne?" fari da ido fatuha tayi tace na hanan ne bugu
hanan ta kai mata cikin wasa kai Amma fa kin ji dadi murmushi fatuha tayi tace "Ina Jamal da
afra?" suna parlour tare da grandma nima tanbayar ki nayi sai grandma ke ce min baki ji dadi ba
shine fa na shigo na maki sannu toh ashe har kin warke kin fara make up ta ida zancan cikin
tsokana, dariya fatuha tayi ta ce "Wallahi naji sauki danma mom bata barni nayi aiki ba" ai ta
kyauta wallahi amma yau baki je school ba eh exam muke na JSCE shiyasa ban je ba yau bani
da paper Jamal kuma fever yake shiyasa, murmushi fatuha tayi ni wallahi ina san makarantar
nan se ma na shirya jidda zata tafi sai naji kamar na bita, ai karutu akwai dadi akwai wahala kiyi
ma mom magana mana smile fatuha tayi tare da cewa toh jidda ce ta shigo bedroom din ta fada
jikin fatuha murmushi tayi tace "Yan makaranta har andawo kenan?" daga mata kai jidda tayi ta
eh Anuty kin ga daddy ya siyo min ice cream da zamu dawo har da chocolate da yawa kuma fa
naba daddy naki ya aje mana murmushi fatuha tayi ta ce toh ,a zuciyar ta kuwa cewa tayi tap
wannan daddy naki ai sai ke hanan ce ta katse mata tunanin da cewa bari naje wajan uncle
nima na amshi nawa tana fadin tana qoqarin daukar veil din ta zata fita , fatuha inkin gama
shirya jidda ki same ni a parlour muyi lunch toh tace mata to bawai dan tasan me hanan ke nufi
da kalmarta na qarshe ba daukar jidda tayi ta shige da ita bathroom ta wanke ta tas sannan
suka fito ta shafeta da mai tare da Samata gwon pink me qaramin hannu se gashinta da ta
gyara mata tayi kyau sosai masha Allah.


Direct parlour suka fito Anuty bilki na saman two star zaune, mom na zaune saman three star
suna kallo gaishe su tayi mom tayi mata ya jiki ita da Anuty bilki da gudu jidda ta koma wajan
Jamal da ke zaune saman daya daga cikin kujerin dining area itama ta zauna cikin fara'a fatuha
ta qaraso ta fara saving din su , hanan dake saukowa daga upstairs tana zunburo baki gaba
cikin bacin rai ta qaraso dining area din fatuha ta kalle ta tace, "Lafiya naga kamar an bata maki
rai ?"dan guntun tsaki taja wallahi uncle ne ya bata min rai shi kullun cikin bakin rai maganar
arziqi ba taba hada ku dashi, murmushi fatuha tayi tace "Yi hakuri kinji zauna mu ci abincin mu
in mungama mu fita farfajiya shan iska" yawa tawa abinci suka ci cikin nishadi bayan sun gama
fatuha da hanan suka kwashe kwanikan sunka kai kitchen sannan suka fita farfashi jiyar gidan
domin shan iska.

Saman resting chair suka zauna ,suna dan taba hira fatuha ba qaramin jin dadi gurin take ba
saboda har da yan shuke shuke lumshe ido tayi ta ware su, kai fatuha karki ce min wai bacci
kike ji ah ba bacci nake jiba kawai wajan yamin ne ina san guri kamar haka, shiyasa sanda
nake akauye kullun muna bakin rafi ni da fatsima murmushi hanan tayi sun dade sosai a filin

gida suna hira kiran sallah magrib ne ya tashe su a wajan suna tafe suna hira ,sadiq da ke
qaqorin fitowa zai je masallaci sanye da jalabiya milk fatuha bata lura ba ta fada mai dan ita
bata gani tana rike da hanan wata iri tsawa sadiq ya daka mata Wanda yasa yan hajin ta
katsawa hanan ko take ta kama gefe jikin fatuha ta rabe, harara ya aika masu su duka stupid
girl's kuna tafiya kuna kalle kalle baku kallan gaban ku mtss sannan ya sa kai ya fita. sauke
ajiyar zuciya hanan tayi ta ce ba dai jaraba ba mtss sannu indai uncle ne haka yake kullun cikin
bakin rai da hargowa, murmushi fatuha tayi tace ni zan fada maki haka sannan suka shige cikin
gida.


*Fan's kuyi hakuri da wannan page din am to busy shiyasa nayi shi ba yawa*

*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.comBayan su idar da
sallah parlour suka dawo suna kallo , kitchen fatuha ta shiga anan ta iske baba jinmai tana
farfesun yan'ciki gaishe ta tayi cikin sakin fuska ta amsa mata tare da yimata ya jiki ,da sauki ta
bata amsa tana qoqarin bude fridge fruits ta debo ta zuba a ball na glass tare da wankewa
sanna ta dauko wuka parlour ta koma hanan da ke zaune saman one star ta duro qasan carpet
tare amshe wuqar,t ace "Bari ni na yanka fruit din? kinga ke bakida lafiya" harara fatuha ta aika
mata waya ce maki bani lafiya? lafiya ta lau inda za'a auna mu qilama na fiki lafiya dariya hanan
tayi ta ce "Wasa kenan" tare da cigaba da yanka fruit din sai da ta gama yanka fruits din sannan
ta maida wuqar ta dawo parlour suka fara cikin fruit din cikin jin dadi suna kallo suna taba hira.


Anuty bilki ce zaune saman sofa mom na saman bed zaune, mom yanzu sai yaushe zaku
dawo? wallahi ban sani ba amma nasan sai mun kai 2week tunda shi wancan zuwan da yayi se

da yayi kusan 3week, shagwabe fuska Anuty bilki tayi amma fa gaskiya mom zamuyi missing
naki wallahi, murmushi mom tayi tare da cewa ah kanku bazan zauna ba naqi bin tsohon mijina
ba akan Wanne dalili zan barshi kullun yana zuwa uk ni ina Nigeria ni mai ya'ya, ya'yan da
suna gidan miji, dariya Anuty bilki tayi kai Mom harar ta wurga mata kinga in ta kuramin zakiya
tashi ki ban gu kona samu na cigaba da hada shirgi na, ah Mom wato kaya zaki kwasa da yawa
kenan? laaaa yau Allah ya kawo mu ya' na tirtse uwar ta Dan zatayi tafiya da uban ta , toh kaya
zan diba da yawa kika bata min rai wallahi har wata sai muyi ta ida zancan tana bude bedside
drowe baqar leda ta curo ,yauwa ga wannan tun wancan satin na so na aiko baby ya kawo
maki, to ban samu dama ba washe baki Anuty bilki tayi kai Amma fa mom naji dadi Allah yasa
wannan maganin irin wancan ne gaskiya wancan naji dadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login