Showing 27001 words to 30000 words out of 119109 words

Chapter 10 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5459

ba, shi yasa na dauketa ranar aurenta.  Domin nima na rama tijarar da tayi min.
          Kayi hakuri! Sunana Dr Mujaheed Harisou Agla! Don haka ga Yarka nan zaka iya kaita asibiti a kara bincika maka ita!"
. Yana gama fadar haka ya mike abinshi.
                     "Jay! Don Allah karka tafi"
"Ke manta dani! Zan tafi can nayi rayuwa ta, ki zauna kiyi aurenki amma ina son don Allah idan kin haifi mace! Ki ajiye min ita zan dawo na dauketa kuma ta faɗa soyayya ta."
."Jayyyyy!" Na kira sunan shi.
"Don Allah ka tafi dani! Wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimake ni, ban san lokacin da haka ya faru dani ba!"

        Juyawa yayi gaban jama'a yana kuma kallona, ya tako gabana.
"Ke zaki iya rayuwa mana, Insha Allah mijin ki zai zama mutum mai kamala."
.rufe mishi baki nayi cikin wani irin kuka, jini na zuba ta hancina ..
"Jay Ina sonka!"
Cike da mamaki yake kallona, sabida shi duk abinda nake bai fahimci cewa soyayya bace....
#Mai_Dambu....
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA HUDU
"Da gaske! Ina sonka ne? Don Allah karka ka min shiru."

   Dariyar da ban tab'a ganin yayi ba, ita ce yaƙe yi tare da nuna ni da yatsar shi.

"Meye amfanin cin fuska?! Idan baka sonta a bayyane yake tayi hakuri! Amma mu a halin babban gida mun san dajarar kanmu Yace da Mahaifinta ya zab'e ta sama da mutanen shi, zaka iya sadaukarwa haka, don Allah ka tafi Allah zai bata wanda take so." Inji Ummi Rahil,

     Daga haka ta riko hannuna tayi zata ja ni.
"Jay!"

      Na faɗa cikin kuka, bata dube shi ba, ta ja hannuna.

  Cire hannunta nayi, da sauri na sha gaban shi.
"Kace wani abu! Don Allah kayi wani abu! Karka tafi ka barni. Kai kace bazaka tafi ka barni ba. Me yasa zaka karya alqawarin da kayi min!

           Don Allah kayi hakuri kaso ne!"

      "Kinga ni bana jin kome akanki! Asalima Ni bana kaunarki! Wallahi bana sonki! Kinga ne kiyi hakuri ki...."

Kifa mishi mari nayi, kuma sai tsoro ya kamani, naja da baya.
"Kayi hakuri! Bazan kuma ba kawai ina ganin abinda idanun ka suke faɗa ne! Jay karka manta ina sonka! Ka fahimci sakon da zuciyata tazo maka dashi."

       "Yayi kyau! Amma bari na gaya miki! Ni bazan tab'a auren yar ashirin da biyar ba, balle ke da kika kusan haihuwa na,  talatin da hudu fa, ji min cutar kai! Ke bani hanya. Tsabar rashin tsoron Allah ina zan kai ki bazawara."

   . girgiza mishi kai nayi tare da riko hannun shi.
"Wallahi ba yadda kake tsammani bane, Jay"

    "Ke bani hanya na wuce, na kawo ki gidan ku ga iyayenki da danginki, kiyi zaman ki."

          "Babu inda ka! Ka dawo! Idan kuma kana ganin karya ne kafi daga gidan nan Mu gani! Jalaludeen D'an Jannart! Baka isa ka fita daga cikin zanen kaddarar mu. Ina sonka kuma ba zaka tab'a."

     Jini ne ya shiga zuba min, daga kowani kafa ba.  Juyawa naga cikin gidan yana min, a hankali na tafi zan zube yayi maza ya tare ni.

                          "Ku taimaka min! A kai ta asibiti."

           "Babu inda zamu kaita! Kai kuma mun gode! Amma ba zaka bar gidan nan ba, sai Har Mahaifinka yazo."

Inji Rahil!
"Ban gane ba? Wallahi tafiya zan yi! Tunda na dawo muku da Yarku!"..

        "Idan kasan darajar iyayenka zaka iya tafiya."

Shiru yayi kamar ya fasa ihu, tare da zama yana hararar kowa a falon, karban ta suka yi tare da kwantar da ita. Maganinta suka dauko aka fara shafa min..

      A hankali jinin ya fara tsayawa matse bakina suka yi zasu bani maganin, na watsar da su.
           Duk yadda suka so su bani maganin na sha, naki asalima guduwa nake son yi, sai da ya taso ya matse ni sosai, tare da amsar maganin ya bani da karfin tsiya.

        "Lallai!  Baka san wacece ni ba? Kuma dole itama ta mutu!"
           Ga baki daya ji yayi tsigar jikin shi ya mike me haka yake nufi.
         Addu'a ya fara tofa mata, wani irin ihu take tare da kai mishi duka, ina yakushin sa.

     Can na koma nayi likus, ban kuma fahimtar kome ba, sai da asuba.da ba tashi sallah.

       Ganin bakona ya sani komawa na kwanta, ina me jin haushin abinda na aikata na kasa b'oye son da nake mishi, yaro karami ya chaza min lissafi.

      ---
"Ni da na gama abinda zan tafi tunda mun fito sallah, ina son gobe na wuce Canada!"

      "Kayi hakuri! Mahaifinka yana zuwa! Dan tunda na ganka a Canada na shiga bibiyarka, sai gashi kai Khatoon kake bibiya.

                     Ban san me yasa na kasa daukar mataki akan abinda kayi min ba, sai dai nasanin soyayyar da nayiwa Janny gaskiya ce! Shi yasa ban ga laifinka ba.

  ..bazan maka dole akanta ba, tunda baka sonta, amma ka sani abinda kayi kusan kuskuren da Mahaifinka ya kwantanta kenan!"

      "Nifa ban fahimci abinda kuke nufi ba. Na bar iyayena a Canada! Akan me zan damu da wasu iyayen."

             "Ta yaro kyau take bata karki! Mu shiga ka karya sai kayi Sallama da Kanwar  mahaifiyarka zaka iya tafiyarka."

   Bazai iyawa Aaryaan musu ba, amma gaskiya yana jin Fad'uwar gaba, akan halin da yake ciki.

            ---
Karfe goma na safe, Jaamal da Sarah suka sauka tare da Aswad. A hankali suka karasa inda Motar da Aaryan ya turo musu, suka shiga.

     Basu san dalilin kiran su da Aaryan yayi ba, amma tsabar faduwar gaban da Jaamal ya shiga kamar zuciyar shi zata diro daga kirjin shi.

          Koda suka isa cikin gidan, wani shashi na daban aka kai su, har cikin falon Aaryaan suka isa, wanda yake zaune tare da Rahil. Tayi kuka har ta godewa Allah.

        Magana take a hankali, tana fada halin da suke ciki.

     Cikin sanyin jiki, Sarah ta nime guri ta zauna, tana kallon su. Abinci aka shiga jera musu.

      Daga bisani yace.
"Fulani Maryam ko zaki shiga daga ciki, sai su karya suma anan."

           Mik'ewa Sarah tayi ita da Rahil, suka shiga.
Tunda aka ajiye mata abin karyawa ta kasa ci.
"Hussainah zuciyata a tsora ce take! Don Allah gaya min meke faruwa! Ina Fatimah take."

          Riko hannunta yayi suka nufi d'akina, dai dai ba fito wanka kenan,ina zaune Hanisah tana busar min da gashina.

            "Alhamdulillah! Yaushe aka dawo da ita!?!"
"Jiya ta dawo da d'an uwan ta.

     Abin da mugun daure kai,.taya aka yi suka haɗu.?" Inji Rahil,

  Cikin kasaita wanda yabi jikinta da jininta, ta tako har cikin dakin. Tana kallona,
"Fatimah! Ince babu abinda ya faru.da aka dauke ki?!"

   Cikin jin nauyin abin na sunkuyar da kaina, kasa nace.
"Hum-uhum!"

"Ummin su waye d'an uwanta da ya dawo da ita haƙa?!"

    Jan hannun ta Ummi tayi, suka shiga d'akin ta, ta nuna mata abin karyawa, sai da suka gama karyawa sannan ta amsa kiran Baabi.

     Sun sami Jay a zaune tare da su Baabi, yaki magana. Duk yadda suka so yayi magana, yaki cewa kome.

.... Karshe Mamah Sarah ta zuba Mishi ido, cikin kaduwa tace.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangiji talikai! Jalaludeen!"

Ta faɗa a raunane, tare da tasowa zuwa gaban shi, ta zauna.  Hawaye na zuba mata, yau gani take kamar gata ga Janny.  Kuma rike hannun shi tayi cikin nata, kwalla ya d'aga cikin hannun su.

   Ta kuma d'ago kan ta, shima kuma ya d'ago nashi kan. Abubuwan da suka gabata suka shiga dawo mata, wani irin kuka na taso mata.
"Jay! Rabon ka shine ya salwanta da farin cikina, samun ka shine ya maye gurbin farin cikina, Jay don Allah kayi magana. Dani da Jannart guri guda muka zauna.

Abu daya muka so! Gashi nan a gabanka. Da nayi hakuri na bar mata Kawunta da yau tana raye cike da farin ciki, da nake fatan samu da itama ta same shi nima na same shi.

         Don Allah kayi min magana, kaji Yarona, kayi min magana. Idan ta kama na baka labarin amintar mu, tare da soyayyar mu. Duk zan gaya maka amma kayi hakuri kace wani abu mana."

    ...... Kamar ba zai magana ba yace.
" Toh me zance? Iyayena suna Canada! Yarinyar da na dauka na dawo da ita! Don Allah ku bar ni nayi tafiya."

     Daga haka ya mike tare da ce musu, "ni na tafi yallabai"

          Cikin wani irin kuka, tace mishi.
"Don Allah ka dawo mana, wallahi ba dan na raba mahaifinka da Mahaifiyar ka ba, da yanzun kana cikin jerin masu daraja da sa'a don Allah ka dawo."

   Muryan Mamah Sarah ne ya sani fitowa, ganin yadda take kuka tare da, bin shi.
"Magajin Izzah!"

Cak ya tsaya, nabi Abban shi da ido, ba iya ni ba hatta Baabi da Baba Aswad zubawa sarki Jaamal ido suka yi.

"Maryam! Dawo barshi yayi tafiyar shi, idan har Mace jaruma zata iya sadaukar da Rayuwar ta, domin masalaha, zai dawo. Idan har Jarumin Uba irina zan kasa na kuma tsare na mallaki Uwar shi a duniya akwai adadin tafiyar da zai yi, bar shi yaje."

         "Abba bazai tafi ba! A ranar da na fara shiga Makarantar Alberta, naga fuskar shi abinda na fara shine nazarin a ina na san wannan fuskar, sai da na b'ata lokaci me yawa, ina tunanin meye yasa nake damuwa da Jay!

                   Sai da na dawo gida, na duba computer na, naga kamar da yake da Mai Martaba sarki Jaamal, abin ya dame ni. Dan haka sai na shiga niman hanyar da zan sami kusanci da shi, har ta kai mun fara rigima, ban kuma sarewa da al'amarin shi ba, sai ranar da ya turani cikin kazamta, abinda yazo min shine yadda yayi min ranar da muka je addu'ar Umma Jannart! Daga nan na fahimci shine na gane shine amma taya yazo Canada?! Nasan zai biyo ni.

             Shi yasa ranar da muka gama makarantar, na mare shi. Abba Wallahi ban tab'a jin soyayyar kowa sama da nashi ba, a kansa na fahimci girman Soyayyar da nake mishi, Abba bazan iya rayuwa babu shi."

           Shiru falon yayi, sabida kuka na.
Cikin zafin nama ya tawo tare da had'a ni da bango.
"Akan me zaka cutar da ni? Wato ba ni na shirya sace ki ba, kece kika shirya min haka domin nazo ku b'ata min lokaci. Bana sonki! Bana kaunar ki? Ko me zaki yi sai kiyi!

      Mayya kawai, idan sona shi zai yi ajalin ki, gwara ki mutu, a rage mugun iri. Kuma babu shakka zan tafi makira Kawai."

      Ya juya zai fita na rike hannun shi.
"Kayi min alqawarin zaka tafi dani! Don Allah ka tafi da ni! Wallahi ba zan zauna dasu bane."

             Ture ni yayi cikin fada tare da jin haushin abinda nayi Mishi.

         Kuka nake kamar raina, zai fita.
"Jayyyyy! Don Allah karka tafi don Allah ka dawo. Jay"

       "Wallahi ko zaki mutu bazan soki ba."

Daga haka ya saka kai ya fita, wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da zuɓewa a kasa, hankali kowa ya tashi, musamman Baabi.

             Cikin tashin hankali, aka nufi asibiti, nan aka shiga bani kulawa. Tare da saka min ruwa.

Ga koshi ga kwana yunwa, suna ji suna gani yayi tafiyar shi.

             "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji ka kawo min dauki! Yau naga samu naga rashi!"
"Jamal ka kwantar da hankalinka!  Insha Allah zai dawo."

             Shiru yayi  kowanne su da abinda yake damun shi. Har dare suna asibiti, can suka samu shiga.
                  Juya musu baya nayi, naki magana. Duk yadda suka so min magana min kula su nayi, duk yadda suka so na kula su naki magana, karshe ma kuka na saka musu dole suka hakura tare da barin d'akin, tare da fita. Sun jima suna tattaunawa, kafin suka tsayar da Magana.

..... A daren Jaamal da Aswad suka bar Sokoto har da Mamah Sarah.

                  ---
Damagaram
      
Ubangiji ne ya kai Jay gida, domin sai yana tuki, zai ga wani baƙin hayaki yana bin shi da gilashin motar, yana tsayawa zai Baje, karshe ya saka kira'ar mashawi,  shine ya samu sauƙin al'amarin.

                    Amma kuma kallon kan shi yake tare da tunawa da wanda aka ce shine mahaifin shi, ganin zunzurutun kaman dake tsakanin su, yasa shi jin yana son sanin waye shi?

               Kwana yayi yana juyi, tare, zubawa kofar dakin shi ido yana ganin wani bakin mutum a tsaye kofar dakin shi.

       Mik'ewa yayi tare zira kafar shi kasa, yaji kamar ya saka cikin ruwa, dubawa yayi ya ji shi cikin ruwan tsundum, leka ruwan yayi cikin mamaki.

   Ya ganta jawur.

"Tabbas! Zubda jini bai kare ba. Kuma dole ka nesanci inda suka kai ka, musamman ita Yarinyar dan rai ce ga rayuwata! Garkuwa ce ga rayuwata. Idan kace zaka iya shiga tsakanin mu, zan kashe ka."

          A firgice ya farka dai-dai kiran sallah farko, ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon kofar dakin shi, yaga ashe mafarki yake.
  
Tashi yayi zuwa ban daki, yayi wanka tare da alola, sannan ya fito ya nufi masalacin dake gidan su, bayan ya idar ne ya dawo ya shirya kayan shi ya nufi inda motar shi yake ya dauki abinda zai dauka ya bar key din motar a dakin shi bayan ya saka motar a gareji.

              Duk da a dame yake, amma ba zaka fahimci haka ba, amma kasar zuciyarshi a cunkushe yake da damuwa..
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA BIYAR.

Sam baya cikin nutsuwar shi, har yazo zai wuce yaga wata mabaraciya tana niman sadaka.
Shafa jikin shi yayi ko da karamin canji, cirowa yayi ya saka mata sannan zai wuce. Tace mishi.
"Janimal! Kalma ce ta gamayyar soyayya! Ka rike a matsayin wani abinda zai taimaka maka wata rana, d'an baiwa."

    Bai saurari zantuttunkar ta ba, dan bai mata kallon me cikekken hankali ba.  A dame yake sosai. Kawai yana tafe ne amma zuciyar shi tana aina Mishi abubuwa dayawa akan Iyayen Aanih.

     Zama yayi zuciyarshi tana kokarin neman dawo Mishi da tunanin Yarinyar da babu ruwan ta, bai tab'a sanin ya shaku da ita ba, sai yanzun da yake zaune a cikin jirgin, shigowar daya daga cikin masu kula da matafiya ta juya tana Magana cikin French, kawai sai ya ga tayi mishi kama da Aanih.

        "Khatoon!!" Ya faɗa da karfi, sai da ta juya, dafe goshinsa yayi tare da lumshe idanunshi, dan ya shiga ruda ni.    Wata yarinya ce tazo ta zauna kusa da shi.  Idanu shi a lumshe.
"Sannu!" Bude kyawawan idanun shi yayi akanta.

.... Kallonta yayi kawai tare da janye idanun shi akanta. A hankali kwanakin da suka yi ya shiga ƙoƙarin dawo mishi.

       Ya kasa goge kwanakin a cikin rayuwar shi, ya kasa manta yadda ya farka ya same ta, damanmakin da ya samu a cikin kwanakin da yawa. Ranar ce ta kuma dawo mishi a hankali.

      Dare lahadi, tana kwance ya shigo ya same ta tana rawan sanyi, shine ya janye bargon ya shiga ƙoƙarin ganin ya dai-daita mata yanayin da take ciki, zare rigar jikin shi yayi, duk da ran shi bai son haka amma yana jin dole ne ya taimaka mata.
.
   Dan haka yayi ƙoƙarin, cire doguwar rigar jikinta, a hankali ya janyo ta jikin shi,  a sannu yake juyata tare da goga jikin shi a nata, lokaci guda yaji notinan kan shin suna niman kuncewa.

      Tunda ya san kan shin, bai tab'a mu'amala da mace ba, asalima jin kan shi bai bar shi ya kalle mace ba.

    Domin tunda ya karanci shashin mata a likitance, yake jin babu abinda mace zata iya boye mishi, amma ina ranar khatoon ta gigita mishi hankali, domin duk yadda yaso ya taimaka mata, zazzaɓin ta ya sauka sai da takai shine ya sauka ya barta, domin ji yayi halittar shi ta d'a namiji ta hana shi sukuni, kafin wani lokaci wasu sinadaran na musamman sun koma mishi marar shi, dole ya hakura da taimakon dan ba dan ya nime tsarin Ubangiji ba, da wallahi babu abinda zai hana shi afka mata ba.

              Domin tunda ya haɗa jikin shi da nata, tudun kirjinta ya hana shi fahimtar me yake shirin yi, a hankali ya shiga ƙoƙarin tab'a kirjinta.

           Tunda ya fara, ta bude ido ta cikin na shi, rike hannunsa tayi tare da girgiza mishi kai, jikinta yana rawa tare da bakinta tace.
"Kaji tsoron Allah! Bani da karfin da zan kwaci kai na, amma ba zan tab'a barin shaidan yayi galaba a kai na ba.

       A sani na da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login