Showing 3001 words to 6000 words out of 119109 words
Chapter 2 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
hakuri! Tana da kawaici, Janny tana da mugun zurfin ciki, zai yi wuya ta gaya maka abinda yake damunta, amma a hakan kuma tana sona tare dake da Ummana, haka yayi matukar min dad'i a rayuwata, domin bata rasu ba sai da ta nima min auren Rahil! Kinga bazan tab'a mancewa da ita ba.
Sabida macen arziki ce, me matuƙar mutunci da sanin Yakamata."
Shiru nayi sannan nace.
"Baabi kuma bata tab'a Haihuwa ba ko?!"
Fuskar shi ce ta koma wata iri, daga tambayar.
D'ago kai yayi, tare da zuba min ido, dai-dai lokacin da jini ya digo min daga hancina, wani irin jiri ya kwashe ni ban kuma sanin abinda ya faru ba, sai cikin dare.
Naji muryan Ummi tana kuka tana magana.
"Yallabai! Wannan halin da take ciki! Tsoro yake bani! Domin kusan abinda ya faru Rahilah kenan! Tayi karama da ɗaukar wannan kasadar, ba ita ta fara ba taya ita zata zame abin tuhuma."
"Kinga babu kome! Jarabta ce! Kuma zan amsheta hannu bibbiyu. Sannan nafi ganin kamar canfe ne, da zaran munyi imani dashi wallahi itama zata iya tagayyara kamar Janny! Dan haka bamu yi imani da canfe ba, Allah ya bata lafiya."
Lumshe idanuna nayi, ina kallon wasu mutane da suka saka wani yaro a cikin buhun hatsi, mika hannuna nayi zan rike buhun, naji kamar yana kara min nisa.
Kara mikawa nayi, Baabi yazo ya rungume ni.
"Baabi na! Sun tafi dashi ko? Ka gamsu can suna saka shi a cikin buhun hatsi! Zasu tafi dashi."
Addu'a ya shiga tofa min kafin wani lokaci, barci ya kuma ɗaukata, ina ta surutu.
...."abinda ya faru! Ranar yake yawo a ƙwaƙwalwarta, sannan kuma takan manta dashi, amma yawan bata labarin Jannart shine yake taso mata da nata Ciwon dan haka babu wani abu, Allah ya bata lafiya."
Haka suka kwana a kaina, Ummi tana gaya mishi gundarin Labarin abinda ya faru, a ranar. Sake baki yayi cikin mamaki yace.
"Akan me zaki dake shi? Kome yayi mata ina ruwanki? Wato kece ma kika yi sanadin barin shi gidan? Kai Amma wallahi banda wani dalili da na mare ki! Wallahi kin bani haushi fiye da kima.
Gashi nan kin saulawantar da rayuwar d'an YAR UWARKI, ki barshi da Matar Uban shi, Mahaifin shi yaga min cewa.
Yarinyar zata iya bada rayuwarta akan Yaron, shine kika mata gori akan dan ba ita ta haife shi ba? Toh ke da kike uwa daya Uba daya da Uwar Yaron, Kinga abinda kika aikata.
Ita da bata haife shi ba, tayi abinda kowa ya gani babu me zaginta, shi yasa mana take kallon ki ranar da muka koma addu'o'in Allah ya dawo mana dashi, ashe kin san abinda kika aikata mata shi yasa take miki kallon abin.
.toh wallahi ki shirya muje ki gayawa Jaamal abinda kika aikata ba shi ba, hatta Appa sai kin gaya mishi, domin kin zalinci zuciyar kowa! Kuma kin samu zubda kwalla sabida sakarcin ki na banza, nayi imani tayi hakuri ne sabida tana miki kallon Jannart ce a gabanta, da babu abinda zai hana bata miki rashin mutunci ba, kin bani mamaki.
Aiko dan tarbiyyan da ta bashi, ya kamata ki d'aga mata kafa, bawai kice ta mishi tarbiyyan mugunta ba, dan haka ki shirya muje ki bata hakuri, tare da Uban Yaron, dan babu abinda zaki kuma yi nan gaba, sai dana sani mara iya ka da amfani..
#MI
#HWA
#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!
{CIGABA KWARKWARAH}
*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*
Mallakin
Mai_Dambu
Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️
Godiya sosai Maman Abba Allah yabar zumunci!🌹😍
UKU..
Haka Baabi Yasaka Ummi a gaba da fada har karshe ya bar mata d'akin, tana kuka da dana sanin, abinda ta aikata, a cikin daren ta haɗa kayanta kala daya.
Da asuba ta barni a hannun amintacciyar baiwarta, sannan suka nufi Daura.
Sun isa da wuri, dan haka sun sami ganin Sarki Jaamal. Bayan sun gaisa Sarki Jaamal yace musu.
"Amma kun fito wani guri ne? Dan naga kamar daga tafiya kuke?"
Sunkuyar da kai Baabi yayi sannan yace.
"Mun zo baka hakuri ne! Akan b'atar Jay! Shine muka zo domin mai d'akinka tasan kome!"
.gyara zama yayi sannan yace.
"Dan Rahil tayiwa Jay fada ya fita, shine zaku zo bani hakuri!
Rahil! Kanwar Jannart ce, kuma uwa ce mishi, koda me tayi bazan tsawatar mata ba, sabida tafi ni kaunar shi, kai jinka da Jannart tana raye zata yarda na dibo jiki kazo bata hakuri ne bata borance muku ba, wallahi ban tab'a jin kome akan b'atar shi ba.
Sai dai ina kyautata zaton cewa! Allah yayi hikimar haka ne dan wasu dalilai, da yana tare damu, bazai iya rayuwa babu kalubale na, dan haka babu komai."
Shiru duk suka yi sannan Aaryan yake gaya mishi, ai ga halin da nake ciki, shiru Sarki Jaamal yayi sannan yace.
"Karku canfeta, ku dauka jarabta ce! Domin yin haka dai dai yake da wasa da rayuwarta. Don Allah karki bari wani ya camfeta"
Wannan abun da ta gaya musu, yayi matukar tasiri a zuciyar su, har suka dawo gida, sun sanya dokar kar wani ya kuma cewa akwai wani abu a tare dani.
----
A hankali rayuwa take Gara mana, har na kusan gama jami'a, a lokacin na hadu da wani soja, muka makalewa juna, a waya dan a lokacin Waya ta shiga hannun kowa, idan muna wayar nan kamar zamu cinye juna, tun ina b'oyewa har na hakura kowa ya sani.
Aikuwa Adda kishiyar kakata, ta sani a gaba da Tsokana. Sai na gaya mata.
"Ke yar doguwa waye ne kuke magana dashi a wancan manta sabo."
"Addah ki fita idanuna na rufe ina ruwanki da darling dina, jeki gurin dattin ki, kuyi ta lallaba juna"
Maka min mahuhuci, Innono tayi kamata, na tura mata baki cikin jin zafi nace mata.
"Wallahi koda Baabi ya sayo miki maganin zafi ya bani, bazan kawo miki ba tunda kika buge ni!"
Ina tura mata baki.
"Yar kwaila kawai, dube ki don Allah waye zai yi asarar kudin shi ya auri mace ba kirji."
"Innono! Wallahi ki daina wannan maganar, zaki sanya ni dai na shigowa wallahi, ai haka Allah yayi ni"
"Karki kuma saka mana mijin mu" sake baki nayi tare da kallonta sannan nace.
"Yanzun don Allah sabida wancan takwarkwashen mijin ku,.kike min wannan wulakancin, na zata sabida kawai na tsokani yar uwanki! Toh wallahi sai na kuma!"
Make ni ta kuma, na tura baki na karar wayata ne ya katse ni, na dauka tare da sakawa a kunne na.
Gyara kwanciya nayi, sannan na lumshe idanuna, tare da bude shi nace.
"Barka hasken rayuwata! Muhid"
Murmushi ya sake, wanda naji sautin shi har cikin jikina, lumshe idanuna nayi tare da narkewa a cikin kujerun falon.
."farin cikina! Ya yau? Da fatan kina lafiya."
Juya idanuna nayi sannan na sauke ajiyar zuciya nace.
"Alhamdulillah! Da fatan kai ma haka;"
"Gamu nan muna fama zamu tafi gurin wani meetinga da fatan Kema haka!"
Nan muka tsinke da hira, kamar me, har Addah tana dukana, ban ce mata kome ba, sai yar kukan da na saka, muhid yayi ta min dariya.
Mun hadu da shine lokacin zamu aikin Hajji, shima zai tafi da Yan uwan shi da Maman shi, tun daga lokacin muka fara gaisawa sama sama, har muka dawo daga nan kuma soyayya ta bude Muhid Nasir Arkilla shine cikekken sunan shi, yana aiki da hukumar soja na kasar nan.
Yanzun haka yana garin Makurdi..shine yaro na uku a gidan su, yana da yayu mata biyu a gaban shi sai shi na uku sai kanen shi biyar.
Muna gama waya dashi na katse kiran na mike ina mita tare da shafa inda Addah ta zabga min duka.
Shigowar Kanin Baabi, Baba Annuwar, ya sani mik'ewa da sauri, sabida ban san me nayi mishi ba, yana dan jin zafina.
Tunda na gaishe shi, na sa kai zan fita. Ya bini da ido, da sauri na fice dan shine Ɗan Addah na biyu, dan haka shima yana son kujeran da Baabi yake Kai.
Akwai wasu abubuwan da yake faru a cikin masarautar mu, amma bai da wani damuwa, kawai dai abin ya kasance kome sama-sama ne, kuma ana ƙoƙarin b'oyewa sabida mu yara.
Baabi yana da hakuri kuma duk abinda zaka mishi bai tab'a d'aga ido ya kalle ka.
......
Muhid ya gabatar da kanshi ga gidan mu, da ahalin gidan mu baki daya, sai kuma aka yi dace shima mahaifin shi, dan yana da sarautar a cikin masarautar mu,
Dan haka ba tare da wani tsawaitawa ba, aka saka komai cikin mutunci da girmamawa, domin anyi tunanin gwara ayi bikin nayi bautar ƙasa a dakin mijina.
Wannan tsarin yayi mana dad'i, dan haka na mai da hankalina guri guda, lokacin bikin mu na karatowa Kakanina na gurin Uwa suna ƙoƙarin gyara ni, ga matan Baabi, suma matukar ƙoƙarin na fito Matar so.
....
Haka aka yi ta shiri babu kama hannun yaro, har lokacin bikin yazo, aka fara duk wata shagalin da ake na al'ada, da sauran su a aure.
Sai dai a bangarena, tun saura kwana uku bikin na soma wasu irin mafarkai, masu mugun ban tsoro.
Ban damu sosai, ba har aka daura auren, ranar hankalin kowa ya tashi domin kuwa kin fita nayi ina kwance sai da Baabi ya saka aka b'alla kofar dakin, koda suka shigo sun same ni ina zaune, na cusa kaina a tsakanin cinyoyina, ina kuka sosai.
Zama Baabi yayi tare da cewa.
"Na zata zaki fi kowa farin ciki, dan zaki tafi gidan Muhid, Sai gashi kina zubda kwallarki masu daraja! Fatimah gaya min baƙi son auren ne? Idan baki so yau za a raba auren, dan nayi alqawarin bazan tab'a barinki, ki zubda kwalla ba."
Ciro kaina nayi cikin kuka nace.
"Baabi! Tsoro nake ji, tsoron kar wani abu ya faru."
Riko hannuna yayi sannan yace min.
"Kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru sai Ikon Allah, Insha Allah bazan tab'a barin ki, kiyi kuka ba, maza shirya an jima zasu zo su tafi dake! Khatoon ki taimake ni naji a raina na sauke nauyin da Allah ya daura min ne. Don Allah ki rike mijin ki da kima, yin amfani da hakan zai sani jin na cika Burin Fareeda."
Gyada kai nayi cikin zubda kwalla nace.
"Insha Allah Baabina!"
. Bai fita a dakin ba sai da yaga na shiga ban daki nayi alola sannan ya fita, yacewa Ummi.
"Ku lallabata."
Ina sallah ina kuka, har na idar, sannan na zauna naci gaba da kuka, ina tausayin kaina da Baabina, Shigowar Mama Sarah da Umma Raihanah, da wasu mata dai da suke da daraja, duka shiga shirya ni cikin liffaya, tare da min wanka da turaren zamani da na hadin Maiduguri, aka kaini shashin kaka na, inda Baabina yake, tunda na shiga na matsa jikin Baabih na daura kaina a bisa cinyar shi, ina sauke ajiyar zuciya.
Haka suka min nasiha sosai, sannan aka zo za a fita dani na rike shi, nace.
"Wallahi bazan biku ba, shi zai kai ni!"
.dayawa yan uwan shi, sun ji haushina amma ban damu ba, sabida bani da kowa sama dashi, Haka ya riko hannuna ina kuka ya amshi keyn mota ya saka Ni gefen shi, bai dauki kowa ba, muka nufi gidan su Muhid, tun kafin mu isa aka kira Muhid aka gaya mishi ga Amaryan shi babanta yake kawo ta.
Yan rakiya na, sun biyo bayan mu, koda muka isa. Har cikin gidan ya kaini ya zauna a babban falon gidan yayi ce a kira mishi Maman Muhid! Cikin shigar kamala ta iso.
Bayan sun gaisa, sannan yace mata.
"Toh ga Fatimah Khatoon nan na kawo miki ita, Bata san mahaifiyarta ba, amma tasan Baabinta, Amma daga ganin Muhid nasan cewa! Yayi sa'an Uwa, ko babu kome zaki riketa a matsayin yar da ta taso babu uwa, nagode sosai."
.ya faɗa a raunane, cikin damuwa da kewata. A hankali ya mike na kuma rike hannun shi. Cikin kuka ina cewa.
"Baabi! Don Allah!"
Rikon da Muhid yayi min itace ta hanani karasa abinda zan fada, haka baabi ya tafi ya barni a cikin su, Ummi da Sauran mutanen suka kai ni dakin Naman Muhid, kowa sai magana yake akan irin shakuwar da take tsakanina da baabi.
Dakyar nayi barci me cike da ban tsoro da firgitarwa, cikin dare, naji ana ta hayaniya, buɗe idanu nayi naga Maman Muhid tana share kwalla, hannunta rike da calbi, tashi nayi zaune tace min.
"Koma ki kwanta kinji!"
Shigowar Tayar shi tana kuka wiwi, ya sani tashi zaune ina raba idanuna.
"Allah ya jikan Muhid!"
Wasu irin taurari naga suna yawo a kaina, daga nan yadda na bude baki zanyi magana, kawai sai bushewa nayi a gurin. Hankalin su yayi mugun tashi.
Akan lokaci aka wuce dani asibitin kwararru na nan Sokoto, aka shiga duba lafiya, kafin asuba Baabi ya iso, cikin farar jallabiya.
Ina kwance, zama yayi a gabana yana me tausaya min, har na farka rike wuyana nayi ina son nayi magana amma ya makale.
Dakyar nace mishi.
"Baabih ruwa!"
Babu ruwa a dakin dole ya fita, aka nimo ruwan ya dawo ya bani nasha, wani irin kuka ne ya kwace min, ban san ya akayi ba nayi aman jini. Abin ya d'aga hankalin Baabih akwai Kanwar shi da take aure a Canada, tazo itama , dan haka zama tayi a jikina.
Haka na zama kamar mahaukaciya, bana hum bana hmm! Har tsawon kwanaki bakwai aka sallame ni, daga nan gidan Mu aka wuce dani, a lokacin Ummih da Ammih suka ke kula dani, na sha matukar wahala, sabida bana iya magana da kowa, mutuwar mijina. Ya dake ni.
Ashe rungume Ni da yayi shine kawai abinda zai hada mu dashi, haka nayi ta jinyar zuciyata. Na tsawon watanni sannan na koma makaranta dan saura kiris na tasa jarabawar karshe.
Muna gamawa na samu damar tafiya, bautar ƙasa, har zuwa lokacin naki sake jiki da wani namijin dan gani nake kamar abinda ya faru da Muhid zai kuma faru dashi.
Koda na gama bautar ƙasa, na samu koyarwa a cikin wata makarantar kwana da take nan Sokoto.....
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!
{CIGABA KWARKWARAH}
*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*
Mallakin
Mai_Dambu
Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️
Fatan Alkhairi gare ki Mame na group ɗin Bagudu 😍🌹
HUƊU
Cikin lokaci ƙalilan na fara koyarwa, bawai dan albashin ba a'a, sai dai haka yana matukar rage min kewar Muhid, sosai na maida hankali na sosai akan abinda nake.
Shi yasa sam ban kuma damuwa da kowa ba, sai dai haka kawai muna cikin wannan yanayin Sai ga Baraq ya shigo rayuwata.
Tun daga ranar da na ganshi, a daren na kwana ina mafarkin shi, inda nake ganin shi kwance cikin jini.
Washi gari haka na tashi babu walwala, tunda na nufi makarantar na daure fuskana tam, duk yadda naso kauce Mishi sai da ya shige min.
Haka muka tashi ban sake mishi fuska ba, duk yadda naso kar na shiga rayuwar shi, ina Baraq ya gama shigewa rayuwata. Shi yasa naki shi yayi juyin duniyar akan naso shi naki.
Yakan sani a gaba yana kallon tare da ce min.
"Fatimah meye laifina?! Ko dan bamu da arziki ne?!"
Girgiza kai nayi, sannan na zuba mishi ido, kafin na bude baki nace.
"Kawai bana jin kome akan ka ne! Kuma da zaka taimaka min ka daina damuna zai fiye maka Alkhairi."
"Toh an tab'a kin mutum babu dalili ne? Ki gaya min meye matsalar ki da ni?!"
Mik'ewa nayi ina duba agogon hannuna, sanan nayi wuccewa ta na barshi a gurin tsaye. Yana mamakin yadda nake gudun shi.
---
Baraq Nafi'u! Ya addabi rayuwata, yadda ya kai kanshi gurin Baabi ya bani mamaki, dan haka ba iya gurin Baabi ba, sai da ya gama zage dangin mu, na cikin masarautar, da nuna musu yana kaunata.
Su kuma suka mara mishi baya da taimakon Baabi, zama nayi a gaban Baabi, ina kuka wanda tun rasuwar Muhid ban kuma haka ba, kallona yayi sannan yace.
"Toh Mamana meye na kuka haka indai Baraq ne, zan ce me ya hakura, kuma zan nima miki wanda ranki yake so! Amma ki duba dakyau yaron yayi kokari domin kowa a cikin zuri'ar mu, ana son shi dan haka kiyi hakuri ki amince ayi abin."
Cire kaina nayi cikin kuka nace.
"Baabi! Tsoro nake ji! Ina tsoron abinda ya faru da Muhid don Allah baabi na kayi wani abu."
Jikin shi ne yayi masifar sanyi, tare da kura min ido, yana me jinjina maganar da nayi, amma da ya tuna. An hana shi camfin abinda zai faru, dani sai ya zuba min ido na wasu lokuta kafin yace.
"Za ayi auren ki daina sakawa a ranki wani abu zai faru saboda babu kyau canfe!"
Da haka Baabi ya kashe bakin maganan ya kuma hanani cewa kome, na cigaba da zubda kwalla, ba tare da na amince ba Baraq ya shiga niman aurena, tare da goyan bayan Baabi na, sabida lokacin, na kai shekaru ashirin da biyar, dan bayan na gama bautar ƙasa, nadan zauna na shekara daya, toh yanzun fara aikina ma yana niman shekara biyu.
..tun ina nunawa bana so, har ta kai na hakura, sabida Baraq akwai son sanya mutum a walwala. Haka kuma Iyayen shi, suma sunyi godiya sosai da irin karb'an da aka yiwa ɗan su.
Tunda aka fara hidimar na fara mafarkin ya mutu, har aka daura auren, a tsora ce nake, kasancewar ni bazawara ce yasa aka kayi kome a ranar, sannan aka watse.
Bayan ya samu rakiyar abokan shi, tare da mana yar nasiha. Sannan ya raka su.
Bayan ya dawo, ya fara nuna min wasu abubuwan da gaskiya tunanina bai kai nan ba, kunyar shi tasa na shige ban daki nayo..ina cikin ban dakin naji yana magana a waya, ina fitowa ya janyo ni, tare da