Showing 63001 words to 66000 words out of 119109 words
Chapter 22 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
ana sonka, amma ba a son haihuwar ka.*
Ban san wani irin yanayi muka shiga daga ni har Jay da Baba Aswad ba, sai dai lokaci guda kome ya tsayawa Jay cak.
Kurawa Saif ido yayi, cikin kaduwa da tashin hankali, ya taka har gaban Saif.
"Kace me? Maimaita min naji?"
"An gaya maka d'an."
Toshe mishi bakin shi nayi, cikin tashin hankali, sannan na koma bayan Jay na tsaya.
"Jay ina tare da kai. Ka rabu dashi kawai."
Janyo ni yayi tare da ture ni, gaban Saif.
"Gata nan amma baka da rabo a jikinta kai. Na yarda ni jinin Kwarkwarah ce! Amma sai na nuna maka Ni ban tab'a niman abu a gurin Ubangiji ya ki bani ba! Dan na yarda da shi.
.....zan nuna maka yadda ake Kwarkwarah yake amsar abu a hannun d'an halak."
Daga haka ya juya abin shi bai kuma magana ba. Bayan shi zan bi Baba Aswad ya yace min.
"Dawo!" Kallon shi nayi zan sake kuka.
"Saifullah! Kayi Kuskuren, ba Jalal kad'an bane Kwarkwarah daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, nasarar su daya ne. Tun da ya dawo muke niman hanyar da zamu gaya mishi maganar amma yau kad'ai ka ruguzama mana, tanadin mu akan shi.
Ka fita a masarautar nan kafin Mahaifin shi ya hukuntaka,"
Yana gama fadar haka ya sani a gaba muka bar Saif ya tsaye, cike da Mamaki.
Muna shiga falon Abban Jay muka same kowa a tsaye sunyi jim, suna kallon Jay da ya sunkuyar da kan shi kasa.
Jikina ne yayi wani irin mutuwa, a sannu na taka har gaban shi, na dauki ruwan da aka zuba mishi yasa yaki na mika mishi. D'ago fuskar shi yayi ya zuba min ido.
"Tashi ki bar nan!"
Muryana yana rawa, nace mishi.
"Jay ban san kome ba."
"Ki fita yace! Mayya mata zuciya, an ce ba a sonki dole ke sai ya soki ko kunya baki ji ba, kanin bayanki, kike likewa mara zuciya kawai ki tashi min a gaban mijina kafin na nuna miki abinda zai baki tsoro." Inji Munih.
"Ke dalla kiwa mutane shiru, banza matar cushe, Hamma Jay baya son wata mace Sama da Addah Aanih, idan kuma kina musu na gaya, Ka bar boyewa duniya SOYAYYAR da kake mata.
Sau nawa kana gayawa mutane matar kace ita! Kana yaudaran kanka baka sonta. Wata biyu da suka wuce sabida ceton rayuwarta kai ma aka yanka ka a ciki duk wannan kiyayya ce?
A yayinda Allah baya bamu dama a rayuwar kama ta yayi mu gode mishi ba butulce mishi ba.
Kowa ya kalli Addah Aanih yasan tana haukar sonka bata da zab'i ne tsayar da wani dan ta nisance ka.
Har yau Abba yakan saka hoton Umma Jannart a gaba yana kallonta ba dan kome ba, sai dan abinda kake aikatawa shi ya aikata.
Idan ka gadama ka fadawa kowa kana son Aanih Fatimah, idan kaso kayi shiru. Wanda haka shi zai sanya ka zubda kwalla na tsawon karshen rayuwarka. Amma tabbas Zuciyarka nata ce." Inji Jannart karama.
Har zata fita yace mata.
"Noorie! Dama Ni din Mahaifiyata Kwarkwarah ce?"
Juyawa tayi sannan ta sake mishi murmushi wanda ya sanya ta zubda kwalla, ta tako a hankali gaban shi.
Ta durkusa, a gaban shi. Tana kallon shi sannan tace mishi.
"Mamah Raihanah da Abba dukkan su y'ay'an Kwarkwarah ce, Ummin sokoto da Umma Jannart duk Y'ay'an Kwarkwarah ne.
Su wad'ancan matan sabida masalaha aka samar dasu, ita kuma ta samar da daidaiton zaman lafiya ne da fahimtar juna, ta kuma warware matsalolin rayuwar wasu!"
"Indai haka ne, toh ki ce mata ta je bana sonta."
Mik'ewa tayi sannan tace.
"Hamma yayi maka haƙan."
. Kauda kan shi yayi, dan baya son ma ya kalle ni.
A sanyayye na bar falon, jikina ba karfi, hmm Jay kenan na barshi har Abada, na rabu dashi kenan, idan son shi shine ajalina gwara na mutu na huta.
.....
A sanyayye kowa ya bar falon, Kawu zai mishi magana Mamah Raihanah ta d'aga mishi hannu tare da cewa.
"Zuru, ta ishi ɗan kunya.! Kyale shi barin gado asara ce."
Babu wanda bai ji zafin Jay ba, sai aka kyale shi.
..... Ina kwance kowa na barci amma ni idanuna biyu, juyi nake a hankali, karshe na mike tare da nufar ban daki nayi alola nazo na gabatar da sallar dare.
Na jima ina kaiwa Allah kuka na, har zuwa wani lokaci, kafin nayi sallama, tare da mik'ewa. Na nad'e abin sallah. Kwanciya nayi ban cire hijab din jikina ba.
Na gyara kwanciya ta.
"Aanihhhhhhhh! Shiiii." Naji kamar ana kirana tare da jin karar matan nan, a hankali na mike na sauka a gadon, na fita daga d'akin, sannan na nufi hanyar fita daga gidan baki d'aya.
Har na isa bakin kofar fita na sami kofar a bude, a hankali na saka kai na fita daga cikin gidan baki daya na hango ta tsaye, gurinta na nufa tare da bin bayanta har can karshen gidan.
Yana dakin shi bai yi barci ba, sai ganin wuccewa yayi dan haka yayi maza ya d'aga labulen tagar shi, sai hangota yayi tana tafiya kamar wacce aka tura ta.
Da gudu ya fito daga cikin gidan ya leka dakin yaga duk suna kwancen, tsawa ya daka musu duk suka mike ya gaya musu ga Aanih can ta fita, sannan shima ya fita da mugun gudu, suka biyo bayan shi Rumana da Aliyah.
Bayan shi suka bi, yayi musu nisa, har ya cimma. Lokacin da suka iso, sun same shi da ita, suka dambe, lallai ya kyaleta ta tafi.
Yadda take kai mishi duka tare da yakushi, sai dai ƙoƙarin janyo ta daga jikin itacen da ta makalewa, ita sai ta isa jikin ganuwar gidan, ga gurin ya zama sunkuru.
Lokacin da ya fincikota har su Mamah Sarah da Raihanah sun iso, tare da Kawu.
Da shi da Kawu suka janyo ta da karfin tsiya, suka nufi cikin gidan tana ihu tare kuka tana faɗin.
"Wallahi sai ta mutu! Sai na kashe ta. Sai ta sadaukar mana da rayuwarta."
Share zufa Jay yayi, tare da kallon Kawu, sannan yace.
"Idan na fahimta akwai abinda kuke boye min, meke faruwa a cikin masarautan nan?!"
Ajiyar zuciya Kawu ya sauke sannan ya mike tare da shiga dakin shi sa ya dauko wata ruwan addu'o'in ya kawo ya shafa mata, da taimakon Raihanah aka dura mata ta shanye.
Bayan sun bata ta watso musu tare da komawa ta kwanta sai barci.
"Abba me kuke nufi dani da ba zaku gaya min me ke faruwa ba?!"
... "Idan kana son sanin meke faruwa sai dai ka auri Yarinyan haka ne kawai zai taimaki rayuwar ta, in ba haka ba toh kuwa mutuwa itama zata yi." Inji Kawu.
...."kamar mutuwa zata yi? Kenan akwai bashin da kuka ci, wanda sai ita da bata ji ba bata gani ba? Me yasa kuke ruffenfen sirrin boye?
Ku gaya min abin da yake faruwa"
Shiru yayi sakamakon kallon da Rahil tayi mishi, dan yasan bata sakewa kowa fuska.
"Babban Rumah ina ga tunda ta sami barci, ku koma cikin Ni zan zauna da ita."
"A'ah muma zamu iya zama ai. Sauran su shiga cikin gidan, mu sai mu zauna."
Shiru kowa yayi, dan yan matasan sun razana, kawai sai suka zauna a gurin dan tsoro ya hana su shiga dakunan su.
...... Tsura mata ido yayi, yana juya amsar da Abban shi ya bashi akan ta, shi dai baya sonta amma a duk lokacin da zata shiga wani irin yanayi sai yaji ba zai iya jurewa ba, shi yasa baya kaunar yaji wani abu ya same ta, amma ba damuwan shi bane yayi ta kirb'a mata rashin mutunci, koda kuwa zata na kuka yana masifar kaunar kukan ta, dan burge shi take. Baya kaunar macen da bata da raki, ya na son mace me raki.
Musamman wacce take da saurin fansa tare da fada, yana son mace me addini da ibada, Aanih kuwa yaga har tabon Sallah ce da ita, shi duk da ta haɗa abubuwan da yake so.
Sam baya ra'ayin bazawara, duk abinda zai mata yana mata ne dan tana ramawa.
Ya jima yana nazarin wasu abubuwan akan ta, wanda suka mishi amma shi baya kaunarta ko kadan.
Har aka kira sallah farko sannan ya mike ya nufi shashin sa, yayi alola tare da saka jallabiya ruwan toka, sabuwa kal.
Haka ma Abban shi, ya fito sanye da farar jallabiyar, suka nufi masalacin tare.
Karfe bakwai saura Kwata na farka tare da dafe goshina, ina ƙoƙarin tuno abinda ya faru amma ya tafi kamar mafarki, tashi nayi Ummi ta rike ni muka nufi ban dakin dake dakin da muka kwana.
Ita ta haɗa min ruwan wanka, na shiga nayi tare da alola nazo nayi sallah, sannan aka kawo min abinci na ci, kadan ina kallon Ummi ta hada mana kayan mu, sannan aka fitar da shi waje.
Bayan an shirya mana, na mike a sanyayye, na saka hijab dina. Ina gyara zaman shi yana shigowa cikin ɗakin, wani irin bugawa kirjina take kamar zata fashe. Sunkuyar da kaina nayi kasa.
Jikina a mace. A hankali ya tako gabana, tare da zura hannun shi a cikin aljuhun rigar shi. Shiru yayi na wani lokaci sannan kalle ni a karo na biyu.
"Ban san me yasa haka ke faruwa damu ba, amma ina miki fatan Alkhairi." Ya faɗa min , da sauri na d'ago kaina na kalle shi da idanuna wanda suke cike da kwalla.
A sanyayye na raba gefen shi zan wuce, ya rike min hijab.
"Bana jin zan iya samun damar maimaita abinda ya faru a cikin rayuwar mu ba.
Daga jiya zuwa yau, Zuciya ta ta haneni da na barki kiyi rayuwarki kamar kowani me Yanci, nasan na baki wahala,. amma ina niman haka ya zame mana abinda zamu tuna muyi dariya da farin ciki.
Nasan na sanya ki kuka, amma ba zan iya baki hakuri ba, amma zan iya ce miki ina miki fatan Alkhairi.
Ki fahimci..."
"Toh me yasa kake fada ni matar kace? Me yasa kake son kare martabata da sunan matar ka ce ni, Jay da zaka zauna dani ba zan tab'a barin ka kamani da laifi ba. Da zaka zauna dani, ba zan tab'a barin ka kayi korafi ba.
..... Jay shin son ka da nayi laifi ne? Meye kuskure na? Gaya min meye laifina? Meye baka bukata a tare dani zan gyara, saura kwanaki ƙalilan."
Takawa yayi har jikin tagar dakin, yana me d'aga labulen yana kallon waje.
"Ba zan iya baki abin da kika bani ba! Ba zan iya tisassa zuciyata kaunar abin da bana son shi! Zan iya kome amma banda dolantawa kaina abinda bana so? Kije Allah ya baki zaman lafiya da mijinki. Tare da zuri'a na gani."
Ji nayi kamar nuna juya na rungume shi, ina sake wata irin kuka. Ji nayi kamar na bude mishi kirjina yaga yadda sunan shi take rubuce jikin allon zuciyata.
Bana ɗebe tsammanin koda zan rasa kome, indai zan same shi zanyi maneje da shi a haka, koda zan iya samun tawayya daga dangina zan rungume Jay a matsayin abokin rayuwata.
Zan yi hakuri akan shi kuma zan kauda kaina akan shi, bazan tab'a zama mishi azzalumar mace ba.
Iya abinda zan iya yi akan shi ya hadda har da sadaukar da Rayuwata da farincikina akan shi, amma ina lura da yayi ina mutuwa akan soyayyar shi itace makulin rashin mutuncin da yake min, lura da yayi ina kassara zuciyata akan shi itace zaren azabarin janyowa yake azabtar dani ta hanyar cewa baya yi na.
Me yasa mace bata da kima a duk lokacin da ta cewa namiji tana son shi! Me yasa mace bata da wata daraja dan tace tana son namiji, wannan al'amarin yana matukar damuna, a duk lokacin da mace ta furtawa namiji ina sonka toh daga ranar duk wata kima nata ya kare.
Koda kuwa yarinya ce qarama, toh da zaran ta fadi haka toh magana. Ya ƙare sai na miji ya bijiro da wulakancin yayi ta mata gashin kuma,.yana wulakanta ta, yana mata abinda ya gadama...
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi*
Ban kuma tsinkewa da Jay baya yina ba, sai da na fito matar shi ta tsare ni zata min rashin mutunci, Rumah ta dakatar da ita.
"Kina wani abu kamar Jahila! Kina hauka akan mutumin da ya kusan kare minti arba'in a cikin d'akin ta.
Haka bai ishe ki ba? Haka bai nuna miki ita ce abin da yake bukata ba."
"Rumah! Bana son damuwa, mata ta zo muje." Ya mika mata hannu! Cikin dauki da murnan ta mika mishi hannu. Yadda ya rike ta sai da ta kalle shi.
Suna barin shashin, ya makureta a jikin bango, tare da zare mata idanu.
"Wallahi Munih kina kure hakurina, idan na kuma ganin kin zagi Aanih sai na karya miki hannun ki. Wacce bata san ciwon kanta ba."
Sake ta yayi ta fadi kasa, sannan yayi wucewar shi, sashin sa. Yana shiga dakin shi ya d'aga labulen da yake kallon inda su Aanih take, a sanyayye yake kallon yadda take niman shi. Tana duba ta inda zai ɓullo amma har ta shiga cikin motar babu shi babu alamar shi.
.... Har ta zauna ta kuma fitowa, domin gyara zama. Kamar ance ta d'aga kai ta hango shi yana kallonta, sake labulen yayi tare da juya bayan shi, ga tagar.
---
Tunda na gan shi yana leke na abin ya bani mamaki da al'ajabi, kawai na shiga motar tunda ba zai min amfani ba.
Tunda muka dauko hanyar gida, na shiga damuwa sosai. Domin naga sakon Saif da ya turo min akan gashi a gaban Dangina, ya kawo ƙara na akan abinda muka mishi ni da Jay.
Tunda naga sakon jikina yayi sanyi, na rasa yadda zan gaya mishi abin da min bai kyau min ba. Haka nayi shiru, can naji Ummi tana magana a hankali. Tare da bawa Baabi hakuri.
Can ta kashe wayar sannan ta juyo gare Ni tace min.
"Meye amfanin abinda kika yiwa mutumin da zaki aura? Kin ja min Bankad'a a cikin danginki. Sunce nice nake sanya ki abubuwa saboda d'an yar uwata meye yayi zafi da Mahaifinki yake min barazana akan aurena?"
Shiru nayi tare da sunkuyar da kai na ƙasa, har muka isa sokoto.. Ummi waya take cikin harshen kanuri, ban san meke faruwa ba, amma naji Hanisah tana ce min.
Baabi ya haɗa Ummi da Babanta ne shi yasa take ta magana tana faɗin gaskiya.. har muka shiga cikin gidan. Inda na samu yan uwan Baabi da Saif ana jiran mu, Ummi bata tsaya ba tace zata yi sallah idan zasu iya jiran mu toh.
Tsoto ya kamani musamman da naga dangin mu baki d'aya, har da kakata Ummi.
Bayan mun idar muka nufi inda ake tattaunawar,.ina bayan Ummi. Dake ranta ya b'aci sosai zama tayi tana kallon kowa a wajen tarr.
"Assalamu alaikum jama'a Barkan ku, ba wani abu ya hada mu anan ba, sai magana akan abin kunyar da Fatimah take shirin aikatawa a cikin masarautan nan! Jiya da dare Saif ya kirani yana gaya min Ya kama Fatimah da D'an Sarkin daura da ita suna masha'ar su."
Ba iya Saif ba hatta ni sai da muka kalli Bana Annuwar, jikina ya dauki rawa sosai, kamar wacce aka jona min lantarki.
Kallon Baabi nake kam shi a sunkuye, tare da kallon Saif shima na shi a sunkuye, wani irin kuka ne ya kwace min. Na shiga rantse rantse.
"Wallahi babu abinda ya haɗa Ni da Jay, asalima fada suka yi Saif ka fada musu gaskiya mana"
..shiru yayi, sannan Baba Annuwar ya shiga fadar wasu abubuwan masu daure kai da muni, wanda sam ban aikata ba, kallon Baabi nayi tare da son