Showing 111001 words to 114000 words out of 119109 words

Chapter 38 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5469

bane, wasa wasa. Har muka kwana, washi gari ma muka tashi da fushi da juna.

...... Kwana uku da suka biyo baya na sauko na fara gaishe shi, wai nan na kuma ganin rashin mutunci sosai. Domin kuwa tsakanin shi da Allah ya dauki fushi.

       Dakyar da sudin goshi na samu kan shi ya sauko, tare da gaya min maganar da yafi na da muni, ba dan yace baya sona bane yaki tab'a ni sai na k'iyayye kome nashi, a cikin kwanaki da muka yi a Amurka nayi kokarin koyawa kaina hakuri dashi, domin na kasance ina gani naki gani, ina ji naki ji. Haka yayi mugun sanya samun nutsuwa. Satin mu biyu aka sallame shi muka koma hotel din da yake kusada asibitin, anan muka cigaba da kulawa da lafiyar shi, kullum zamu shirya mu fita, tare da shi, muyi ta daukar hoto. Mutum kamar me aljanun. Yana ganin wasu mazan suna bina da ido zai rufe ni da fada, sai fushi yau ma haka ce ya faru. Tunda wani baƙin fata ya kafe ni da ido, mutumin nan ya shiga masifa karshe dai, muka dawo gida sai ya fara fushi, da dare na matsa kusa da shi, na kwanta.

... .... Tare da rungume shi, ta baya, amma ya cire hannuna, a hankali nake wasa da gashin kanshi. Ya juya a fusace, kawai na tura mishi, bakina dole yayi shiru. Daga nan kuma ya shiga shagalin shi.

  Kome ya tuna sai gashi nan ya ture ni, tare da juya min baya, dariya ya bani sabida ya iya bori, a cikin Jay babu iya ka, kai jama'a.

          A cikin kwana biyu muka shiga tattarowa zuwa gida, dan dukkan mu, mun yi kewar gida, a hankali yake gaya min yadda yayi kewar Najim da Fahad, kuma Nima na fahimci haka daga yadda yake jidar musu tsaraba, nima ya sani dole na kwashi kaya da kudin da yake hannun mu, turarruka da kayan kwalliya kawai na diba.

     Sai kaya masu kyau na zamani wasu Rumah da Hanisah da Jannart da Raihah. Na sayawa Iyayen mu maza suma turarruka tare da matan.

Sai Husnah da Munin suma na diba musu, har muka bar kasuwar zamanin.

        .... Washi gari muka bar garin, kaina na kafad'ar shi, muna hira har muka gama kome, sannan muka shiga jirgin mu.

             ---
Ranar juma'a muka iso garin Abuja, da karfe tara na dare, a gajiye muka fito, daga gidan Minista Dr Bulama, aka zo daukar mu. Tare da wasu yan mata fannah da Ammah, Sun hadu ba laifi tun da muka shiga gidan.

    Matar gidan jikinta yake rawa,tana hidima da mu, ta kawo wannan ajiye min wannan.

   Sabida ganin Jay a cikin gidan kawai, Yaran matasa da yan mata na gidan sun saka shi a tsakiyar su ana hira dashi. Ni kuwa matar nan bani kulawa tayi ta hanyar sani nayi wanka ta bani wannan naci na shafa wannan sannan take ce min.
"Zahrah! Duk cikar mace matukar ta gaza daukar nauyin cikin mijinta sunanta sakarya!

   Kiji a ranki ki macece, kiji a ranki ke zaki iya sarrafa abinda mijinki zai iya ci, bawai wanda ba zai iya  ci ba.

Karki yarda wata mace ta hango kasawar ki, ki nuna mata ko a gidan giya akwai babba, bana son naji ace akwai wacce zata iya karban matsayin ki, Mu Ahalin Jannart, Uwar mijinki muna matukar kaunarki da kuma girmama duk wani abinda ya shafe ki, karki ji kome duk abinda kike bukata ki gaya min, za mu miki."

Kwalla ne ya cika min ido, zuciyata ta kuma cika da kaunar Jay, Kaf dangin Mahaifiyar shi suka matukar kaunata. Na rasa wani irin so suke min, suna matukar girmama alamarina, kamar su goye ni suke ji, bani da Uwa amma Allah ya bani su ta sanadin Jay.

     Daga nan ta bani wata lafayya, na saka bayan na shirya cikin riga da skirt, na atamfa sannan na nad'e kaina da laffayar ta ja hannuna zuwa. Babban Falon Dr Bulama..da sallama muka shiga cikin.
"Ango ba cefene, yau kaine a garin mu, na zata ba zaka tsaya anan bane!"

Shafa kan shi yayi sannan ya sake wata lallausar murmushi, sannan yace.
"Uwargidan Amaryan, duk ke daya. Babu me kwace miki fadar ki."
"Aikuwa na iya kishi Dan wannan jaja amaren ka, waka zan mata da ruwan sanyi."

Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina, sannan muka gaisa da baba Dr, muna cikin gaisawa yace min.
"Maamah! Baki ba shi labarin yadda yayi jinyar shi bane!"
Kallon juna muka yi da Jay ya sake min murmushi, nima na maida mishi, tare da gyad'awa Baba Dr kai nace mishi.
"Idan na fada ba yarda zai yi ba, shi yasa na bar maganar, dan zai ce ba gaskiya bane"

  Gyada kai yayi sannan ya shiga bamu labarin, rikicin da muka yi ta yi, akan ya kirani Maamah, murmushi kawai yake, yana kallona, ganin har lokacin yana me kafe ni da ido, kawai naji a raina da zan iya jin abinda yake ran shi nasan yabo ne da jinjina...
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:21 AM - Ummi Tandama: *Allah, ya maida ƙoƙo masaki.*
_Ke Alkhairi ce duk namijin da ya same ki a rayuwar shi, yayi sa'a_ yace a ranshi, yana murmushi.

    *Akwai sa'ar da mutum zai yi bayan ya sami nagartaccen mutum irinka? Ai kai ne sa'ata baki daya* na fadi haka  a raina, ina me sunkuyar da kaina, hira sosai aka bude tare da tattaunawa akan asibitin shi da za a bude mishi, amma kuma naji Baba Dr yana cewa.

" Bai zama dole a bude maka ba, dan naji suna wani batu akan ka Allah ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin Ya Allah,"
Muka amsa baki dayan mu,

  Dakin abinci muka nufa, anan muka ci kad'an sannan muka fito,  ina kallon yadda yake bina da ido, kin kula shi nayi. Har muka nemi kwancin mu, daki daya aka bamu, dan haka muna shiga.

   ..Na shige ban daki, na watsa ruwa, ina fitowa na same shi, ya rage kayan shi zai shiga wanka, janyo ni yayi tare da kallon fuskana.
"Ki shiryarwa daren yau! Dan ina ganin zan rage za...."

"Yallabai! Kwantar da hankalinka, Ni hutun sallah ma nake, yanzun na gani." B'ata rai yayi wucewar shi abin shi. Bai kuma kulani ba.

    Har ya fito ya samu na fara barci, shiryawa yayi sannan yazo ya kwanta a bayana, tare da janyo ni jikin shi, a hankali barci yayi gaba dashi, sabida mun rigada mun gama gajiya, shi yasa bai dame ni ba.

         ---
A can daura kuwa, sun san mun sauka a Abuja, dan haka Abba da kan shi, ya saka aka kira su Husnah. Bayan sun shigo suka gaishe shi, kallon su yayi sannan yace musu.

"Allah yayi muku albarka." Ya fada a sanyayye, sannan ya kuma cigaba da cewa.
"Gobe Insha Allah, Mijinku zai dawo suna Abuja ne, da yayarku!"

      "Allah ya dawo dasu lafiya, muna jiran su." Inji Husnah,

Kallon su yayi sannan yace musu.
"Ko kuna da bukatar wani abu ne?"
"A'.."
"Eh! Muna da bukatar kudi." Inji Munih, bayan Husnah tana son cewa a'a, murmushi yayi tare da dauko wata takarda me kunshe da kudi ya mika musu.

Suka amsa suna godiya, sannan suka mishi sallama, tare da barin falon, murmushi yayi yana jinjina qarfin halin Munih, yana kuma girmama hakurin Husnah.

  ... .. Yadda take murmushin mugunta bayan sun fito.
"Insha Allah saura kiris naci qaniyar wata, idan na gama da ita na dawo kan farar angulu." Daga haka tayi wucewarta, Husnah bata kulata ba, dan tasan da ita take.

......
       Washi gari
Farkawa yayi ya kalli yadda gashina ya rufe mishi fuska, yana fitar da wani daddar kamshi, shafa kaina yayi sannan yace min.
"Nanah Fatimah!" Tura mishi baki nayi tare da gyara kwanciya ta a jikin shi, sake shafa fuskana yayi zuwa wuya na yace.
"Zuhruyyah! Tashi zan tafi sallah ne!"
A hankali na d'ago kaina  sannan na janye daga jikin shi, cire matashin kan shi yayi ya cusa min a jikina, sannan ya daga gadon, kallon yadda na k'amk'ame matashin yayi.

   Murmushi yayi sannan yazo ya sumbaci bakina, zuwa goshina, kafin ya shiga ban daki. Sai da ya watsa ruwa, sannan ya dauro alola tare da saka jallabiya ya nufi masallacin da yake cikin gidan.

                    --- Kafin ya dawo nayi wanka, ina fitowa yana shigo min d'aki, zama nayi a gaban  mudubi na shiga gyara jikina, ina gamawa na dauki kayana, ina sakawa ya matso kusa dani.  Rungume ni yayi tare da cewa.
"Kina da jiki me kyau! Shi yasa baya nuna tsufarki"

    ..... Gyada mishi, kai domin Jay bai iya magana ba, kuma duk abin da zai fito bakin shi, Alhamdulillah Nagodewa Allah, kawai yankota yake.

     Ina gamawa na shirya cikin doguwar rigar yadi me tsantsi, duk da na saka wando da rigar mama, amma haka Jay ya hanani sukuni da surutu.
"Wallahi baki isa ki fita gidan nan da dan jinjirin mayafin nan ba, sabida rashin sanin ciwon kai, toh wallahi naga kafarki  a waje zan zane ki kinji na rantse da Allah."

  Zuba mishi ido nayi,  gaban madubi na duba kaina naga dole yaji Babu dad'i, domin kuwa duk inda na juya jikina sai ya girgiza,  dake ina da ƙaruwar jiki ne, cire kayan nayi sannan na nimo wata atamfar riga da zani, na saka amma dake yau yana jin rikici ne, nan yace bai iya ji ba.

   Na nimo doguwar rigar na saka, na atamfa, na saka ina sakawa ya kare min kallo, kauda kai yayi sannan yace min.

"Shima ai ya fidda kirjin ki, Ni kam na shiga uku, wai ke dama haka kike a hanaki sata ki koma sane, toh cire rigar ki saka riga da zanin can." Kwalla ce ta zubo min, dole na cire na saka. Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya matso kusa da ni, idanu shi akan kirjina.
"Wannan ma an mutu ba a tsira bane toh amma da sauki tunda ya.. kai ina zo nan daga yau zaki daina saka rigar mama masu fitar da mama nan!" Ya faɗa haka tare da fita.

   Har ya isa bakin kofar yace min.
"Kuma ki saka babban mayafi irin na juya, yawwa."

   Banza nayi dashi, a hankali na gama shiryawa na fito, muka karya, muna hira har kusan karfe  goma sannan muka dawo shiryawa, ina cikin shirya kayan ya shigo, a zafaffe ya juyar dani. Tare da bina da wasu zazzafar sumbata. Kamar zai cinye ni.

Tun ina kau da kai na, har na kasa na shiga biye mishi, kamar ba zamu bar juna ba, ban da ina hutun salla da babu abin da zai hana Jay karb'an hakkin shi domin ban tab'a ganin shi  cikin damuwa da kumar bukata irin na yau ba,

       Ture ni yayi gefe, tare da rike hannu na gam, ina mamakin abin da ya kawo mishi sauyi, lokaci guda. Dan haka wuta wuta ya fitar mana da kayan mu, dan yana fama da ruwan kashe gobara ne koda kuwa ta kwata ce zai iya watsawa.

.....idan har wutar zata mutu toh bukata ta biya shi kenan, dan haka muka shirya sai filin jirgin sama. Kamar zai yi hauka. Sabida yadda yake jin shi.

              --- karfe sha biyu muka sauka a Katsina, ba tare da ya gayawa Najim mun taso ba, haka ya kira. Murad karamin yaron Sarkin Katsina ya gaya mishi isowar mu, mota biyu aka turo suka kwashe mu zuwa daura

     .......
Karfe biyu yayi mana a cikin masarautan, ko cikin gidan bai shiga, ya nufi cikin gidan shi. Wani abu naji ya tsaya min a rai. Take na fara niman taimakon Allah.

   Kafin na shiga cikin gidan, na nemi kome na rasa sai ma nutsuwar da zuciyata ta samu, shi kuwa yana zuwa.

Ya taradda Husnah tana lalle, afujajjan ya kwace kome ya cire sannan yaja ta zuwa d'akin ta.

       Anan ya gurje ta son ran shi, tare da sauke nauyin da ya kwaso baki daya akan ta, ajiyar zuciya ya sauke, lokacin da ya fahimci ya sauke gajiyar shi akanta, yana kallon yadda take sauke numfashi. Tausayi ta bashi,  duk da haka yayi fatan ina ma Da Fatimah ce zata kasance haka da yafi kowa amfana da ita, Husnah ma ba laifi dan ta haɗu.

     Ban ɗakin ta ya shiga yayi wanka sannan ya fito abin shi ya shiryawa ya barta kwance, bayan yace mata.
"Ki tashi kiyi wanka bana son kazamta."

Yana fita,ya nufi cikin gidan su anan ya taradda ana ta hira yaushe gamo, zama yayi cike da kunya, dan alamun wasu abubuwan da yayi suna bayyana, kasa magana yayi duk da tambayar shi lafiyar shi da ake, Ni Ko ban kalle shi ba, dan na san juyen bakin mai yayi, dan haka ban koma sha'awan kallon inda yake ba balle na kula shi.

            Mik'ewa nayi na Barsu a falon na shiga dakin su qarama na rufe kaina na fashe da kuka, sai da nayi me isata sannan nayi kwanciya ta a d'akin.

  A gidan na wuni,naki yarda na koma gidan shi,ina jin shi yana kaiwa da komowa, akan mu tafi nace bazan koma ba yayi tafiyar shi.

           Har dakin ya biyo ni, ina kwance, juyar dani yayi tare da zubawa fuskana ido.

"Kinyi kuka? Me aka miki?" Wani kukan ne ya tawo min, na kuma rushewa da shi, ina yi ina shasheka, nace mishi.
"Don Allah yaushe zaka kaini gurin Baabina?"

Zuba min ido yayi sannan yace min.
"Babu rana! Balle wata. Indai dan haka kike kuka toh ki shirya domin kuka yanzun kika fara, kuma babu wanda ya isa ya juya ni baki isa ba, dan haka ki taso mu tafi ko raina ya b'aci na miki abinda baki zata ba. Tun dake baki da burin kome sai na sanya Ni a b'acin rai.

       Ban san me na miki kike aikata min wannan mugun abin ba,daga ki sanya ni cikin damuwa sai ki sanya ni cikin b'acin rai, abinda kananun yaran da kika samu basa min, shine ke bari ki min, wallahi baki isa ba.

Kin kasa, kuma babu wanda ya isa ya juya min baya a wannan lokacin. Ki fito ina jiranki."

Daga haka yayi ficcewar shi, kuka nake har da shasheka, ina ji ina gani bai damu da alamarina, ba, koda na fito na same shi suna magana da Mamah Sarah, tana mika mishi wata littafi, tana faɗin.
"Ina ga akwai wani a hannun Kawu, kuma tun shekarun baya naso buɗewa, na kasa amma tace min a wani takarda dole sai na nimo Jakadiya Sahurah, ka duba yadda zaka bude Littafin yana da amfani.

..... Naso baka tuntuni sai wannan hatsarin ya faru, toh yanzun kuma naga kasami lafiya kuma ina jin Kawu yace wata me zuwa zasu baka sarautar bana son abubuwa su maka yawa, ba tare da ka duba ba."

  Amsa yayi tare da kallon bangon littafin an rubuta, kundin tarihina! Me kunshe da al'ajabi. Murmushi yayi sannan yacewa Mamah Sarah.
"Rubutun Ammih na, irin nawa ne. Tun ban karanta ba, naji ina kewarta."

Murmushi Mamah Sarah tayi, sannan ta goge kwallar da ya zubo mata, tace.
"Idan kuma ka karanta, sai kaji dama zata dawo ne, sabida Jannart tayi min kome!"

                Girgiza kai yayi sannan  yace mata.
"Toh Mamah zamu tafi."

     Daga haka Yasaka kai muka fita, tunda muka nufi gidan yake duba yadda zai bude Littafin, wanda aka rubuta cewa.
*Sunan Kawu da Nawa ne, mukulin bude littafin, sunar da ya bani ranar da muka rasa junar mu! Kalmomin masu Harafi bakwai*
Har muka shiga gidan, zama yayi a falo ya mika min, tare da cewa.
"Sunan Ammih da Abba! Ki hada ya baki ma'anar kuma kalmomi masu Harafi bakwai. Tayani dubawa."

Duk da ina jin haushin sa, amma haka muka raba dare muna duba  cikakken sunan da zamu bude Littafin.

    Wasa wasa muna gurin, har kusan asuba, sanan ya jani zuwa d'akina, anan muka kwana. Da asuba muka daura har kusan karfe ɗaya na rana babu karya ba.

         Abu kamar wasa sai da muka dauki kwanaki, dan Munih bata nan, ranar da Abba ya bata kuɗin suka yi tafiya da safe da zamu sauko, ina kallon Yadda ya gama shan wahala sannan. ya ajiye Littafin.

Yana me cewa.
"Wallahi na gaji, Littafin babu wani abun da zan iya buɗewa."

      "Ka dai tuna da kyau! Babu mamaki tasan zaka san sunan ne ko kuma kaje ka tambayi Abba!"

         Aikuwa ya fita zuwa gidan Abba, ya sashi a gaba ya bashi daya kundin tarihin Maman shi, sannan ya bashi ya kuma makelewa Abba sai ya gaya mishi Mabudin, ya rasa meye kalmar da Zata bude littattafan guda biyu...
_Kuyi hakuri mura ya dame Ni_
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba*

"Kai amma abin yayi kyau,Yanzun aiki ne babba a gurin ki, kiyi hakuri da halin shi da duk wani abinda zai miki,  ki daina kuka domin shima zai yi duk abinda kika yi dashi zai cigaba hakuri kawai yi kina nuna mishi abin da ya dace a rayuwar shi."

Yayi bayani sosai, sannan ya kuma yi gargadi kar a kuskura abar shi yayi wani abin da zai shafi jima'i, dan bai cikin hankalin shi, kuma matukar aka ce zai yi jima'i da mace toh akwai matsala. Domin zuciyar shi  ba zata iya sarrafa sakonni Ƙwaƙwalwar shi ba. Dan haka ayi takatsantsar dashi. Idan kuma haka ya faru.

         Toh tabbas karfin shi da lafiyar shi zasu rubayya zuwa kashi tamanin cikin dari, kuma idan hakan ta faru.

   Likitan yayi bayani sosai, kafin ya fita. Kallona Abban shi yayi a raunane yace min.
"Ina ga zaki..."
"Ina ruwanka? Meye matsalar ka dasu? Fatimah zaki iya zama da Jalal?" Inji Baba Aswad,

Gyad'a mishi kai nayi, wasu siraran hawaye na zuba min, nace..
"Don Allah ya bar kirana da Mama!"
          Murmushi Baabina yayi sannan yace min.
"Ciwo ne ya mai da shi haka, Insha Allah ya warke bazai kuma kiranki Mama ba"

  Gyad'a kai nayi, shi kuwa ganin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login