Showing 30001 words to 33000 words out of 119109 words

Chapter 11 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5456

kai, baka tab'a kama da maha'inci ba, toh yau guda me zai sanya kayi Kuskuren da zai tabibiyar ahalin ka, tunda kasan bashi ce kuma sai an biya shi.

         Don Allah ka bari, zan iya jure kome amma ban da wannan abin sabida kimata tana tab'awa tankar ta mahaifina ne ya tab'a. Amma idan kaga yadda yayi maka shi kenan."
Ta faɗa a sanyayye, shi kan shi sai da jikin shi yayi mugun sanyin, dole ya janye tare da fita a d'akin.

         "Yallabai da abinda za a taimaka maka ne?!" A hankali ya bude shanyayyun idanun shi akan matar ya girgiza mata kai! Tare da juya kan shi yana kallon tagar jirgin.

                A iya sanin shi bai tab'a kusantar matsala irin ta kwanakin nan, Aanih ta haifa masa da damuwa, gani yake jirgin ma bata sauri.

         A hankali barci yayi gaba dashi. Cikin abibds bai fi minti biyar ba, sai gashi yana jin shashekar kukanta, a hankali take kusanto shi, har ya iso dab dashi.
"Ina sonka Jay!" Bude idanu yayi cikin sauri.  Tare da dafe goshin sa.
        Suna tafiya har dare yayi, a lokacin ya mike tare da nufar wasu musulmai suka gabatar da sallah. Bayan sun idar ya dawo mazaunin shi. Jikin shi na kuma sanyi.

       ----
"Mamahna! Amshi abincin mana!"
        A sannu na bude bakina ya saka min! Ina taunawa hawaye na zuba min, kallon shi nayi ina hango juriya da jarumta mahaifina, karb'an kwanon nayi tare da gyara gashina na fara ci, hannu baka hannu kwarya.

               Rike hannuna yayi tare da ce min.
"Ki nutsu! Don Allah kin ji."

    Kallon shi nayi tare da kai abincin bakina, a nutse?
"Yace baya sona! Baya kaunata! Kuma Baabina, ina son shi. Baabina me yasa kaddarata tazo a hade da nashi bayan bazan iya jurewa ba, me yasa halayyar shi suka bambanta da sauran Mazan?

.... Baabi kirjina kamar ta fashe! Baabina! Me yasa ka ajiye sarautar ka?!"

      Murmushi yayi, sannan ya shiga bani abincin kauda kai nayi tare da mik'ewa. Na nufi tagar dakin ina kallon yadda garin yake.
"Ban san Mahaifiyata ba? Kamar yadda shima bai san Mahaifiyar shi ba!

       Mun rayu a mabanbanta duniyoyi!  Sai dai nasan bazai tab'a kaunata ba."

   "Inji waye? Ai tuni ya kaunace ki? Tuni yaso ki? Ki bani aron lokaci idan bai dawo ba, ni da kaina zan dawo kawo.."

          "Rahil! Ki bar maganar Jalal, Ni na miki miji!" Juyowa nai a firgice tare da rike kirjina, na fashe da wata irin kuka, ina me durkusawa a gurin, da gwiwata dukka biyu. Jan hannun ta yayi suka fita basu kuma bin ta kaina ba. Anan nayi kuma har na godewa Allah da ya halicce ni.

               Kamar wacce aka yiwa fada na had'iye kukan tare da yin alqawarin idan Son Jay itace ajalina gwara na mutu na huta da bakin cikin rayuwa.

        ---
Daura...
Tunda suka isa Mamah Sarah take kuka, kamar ranta zai fito. Janny ta shiga a hankali, tana me kallonta tare da Raihah sai Rumah.

       Tsayawa suka yi daga bakin kofar, suna share kwalla, ganin yadda mahaifiyar su take zubda kwalla, haka ya kashe musu jiki musamman Rumah da taki komawa gidan Mijinta! Khalid dan gidan Mamah Raihanah, shekara daya kenan da auren tazo daga Kaduna.

  Dake anan suke da zama, a hankali Janny ta karasa kusa da ita, ta fara zare mata takalmin kafarta, tare da matsa mata kafar.

          "Ita rayuwa tana bamu damar fuskantar matsalolin mu, bawai mu kasance cikin damuwa da rashin nutsuwa bane! Da matukar wahala, a fahimci banbancin Ra'ayin tare da juyewar wata dab'ia, amma a yadda tsarin zanen kaddarar take.

    Dole sai anyi rashi kuma anyi samu, haka ce zata damawa zukatar wasu mutanen adalci, Mama karki tilas zuciyar ki! D'anki zai dawo gare ki!"

         Shi yasa take masifar kaunar Yarinyar domin gani take kamar Jannynta ce ta kuma dawo mata, hakuri kawaici zurfin ciki. Duk ta gado me sunanta.

           ---
"Abba! Ba zai tab'a yarda ya biyo mu ba! Sannan kuma bazai tab'a amincewa da bukatar mu ba, A wannan lokaci nake bukatar shi,  amma bazai tab'a zama damu ba,

       Asalima abinda muke kokarin yi kamar tursasawa ce, shi da kan shi, zai biyo sawun mu."

      Murmushi Abban Jaamal yayi tare da kallon shi wato hali a jikin rai tace.

"Hmm! Mahaukaciyar Kasuwa! Sa gabanki inda kike dosa, itama Kuma Faɗimah fa? Ko ba zaka bata wata tukwaicin kaunar da ta nuna maka bane?  Ko da yake! A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari. Ba  wani sabon abu bane, domin kuwa idan muka duba."

    Sunkuyar da kai Kawu yayi cikin nutsuwa ya shafa kan shi sannan yace.

"Abba kenan! Karka min. An yi min sagegeduwa, halin Jalal ya sha kaina, ni ban tab'a."

    "Amma wa. Dodo ɗaya ake yiwa tsafi. Idan shi bai tab'a kawowa kai ne ka haife shi ba, amma shi ya nunawa duniya abinda kayiwa Jannart! Ya nuna halin. Kaje ka sami Magaji duk yadda kuka yi ka same ni, amma bazan iya barin jini na a wata duniya domin yace bai samun ba."

             Ajiyar zuciya Kawu ya sauke tare da cewa.
"Toh Abba!"
    Tashi yayi tare da mishi sai da an jima.
           ----
Karfe shida na safe!
Ya sauka a garin Calgary! Cike da son sanin abubuwan da suka boya daga ganin shi.

. Kallon Asood da Hikmi yayi, tare da mika musu hannu suka gaisa.
"Ya kome ya tafi yadda ya dace? Ka same ta?!"
Shiga yayi Bayan motar su ya kwantar da kan shi a jikin kujerar, tare da lumshe idanun shi.

Ya kasa fahimtar kome akan kan shi, amma yana jinjina qarfin shigar da shi da Fatimah tayi.

"Jay! Kayi mana shiru? Jay ko baka same ta bane?!" Inji Asood,

Ajiyar zuciya ya shiga saukewa sabida yadda.yake jin ya barta kenan, ba ita ba hatta mutanen da suka gabatar da kan su a gare shi!! Yana jin kowacce motsin da zai yi da mutane biyun nan yake motsawa.

Sarkin Daura! Sai Ummin Fatimah! Yana jinta a ran shi sosai, sama da yadda yake jin mai martaba sarkin Daura!

"Amma kai wallahi anyi d'an iska! Ka mana bayani kayi shiru sai share mu kake!" Bude idanu yayi shanye da toka, kamar bazai magana ba yace.
"Ka dame Ni!"

Kura mishi ido Asood yayi tare da gyara zaman shi bai kuma ce mishi kala ba, asalima tsoron kuma mishi magana yayi.

Har suka iso Unguwar su Jay! Ya fita a hankali daga cikin motar, ya kura musu ido.
"Don Allah ku kyale Ni!"

Daga haka ya shige gidan su, bayan tafiyar Jay! Asood ya kalle Hikmi.
"Hiky me kake ganin ya faru? Jay Ya sauya daga yadda yake a baya, ko dai ya fara soyayya da Aanih ce?!"

."toh laifi ne? Dan ya fara soyayya da ita? Ni ban ga kome ba, sai tashin hankali da dimauta da take cikin ƙwayar idanu shi! Sai tsantsar damuwa da take cikin ƙwayar idanun shi! Yana cikin matsala sosai! Dan haka mu barshi na wasu lokuta kafin ya samu nutsuwa."

"Toh ko yayi mata fyade ne?!" Juyawa Hiky yayi cikin mamaki!
"Me yasa kake danganta shi da aikata hakan? Abokin mu ne! Sannan dan kai kana ganin kana aikata laifuka bai zama dole ni dashi mu aikata abin da kake zargi ba."

Cizon bakin shi yayi tare da rintsa idanun shi, tun ranar da Aanih ta mare shi, yake niman mafita da zai rama, amma bai samu ba, shi yasa ya d'aura Jay akan yaje ya mata fyade.

Idan kuma bai mata ba, tabbatacciya ce shi zai mata hakan koda kuwa akan mutuwar shi ce.

....
"Assalamu alaikum warahmatullah!" Kallon shi suka yi cike da mamaki.
"Jayyyyy! Zo nan."

A hankali yake cire kafar shi, har ya isa gaban su.
"Ya mutanen gidan?!"
"Ya Jay! Zauna mana!" Inji Munih.
"Yarona zauna mana!" Kura musu ido yayi kawai ya nufi sama abin shi, yana shiga ya rufe dakin shi, tare da sulalewa ya zauna.

Abinda ya dawo kan shi, shine kamar shi da Sarkin Daura, babu kamar da yake da Baban shi na nan Canada, amma me yasa suka mishi haka?

Waye shi? Me yasa suka raba shi da dangin shi! Me yasa suka sami damar nisanta shi da ahalin shi.

Shi yasa yake jin cewa, akwai abinda ake boye mishi, musamman idan Kaka tana mishi kallon bai cika ba? Ashe itama bata amshe shi a matsayin jikarta bane.

Shi yasa Munih take son sakar mishi jiki dan tasan babu wata alaƙa a tsakanin su! Lumshe idanunshi yayi tare da kwanciya a kasar dakin shi.

Me yasa shi kaddarar shi tazo mishi a kaikace!? Me yasa kome ya lalace mishi lokaci guda? Taya Haka ta faru ba tare da ya fahimci cewa shi din d'an wasu ne?....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

   *HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA SHIDA.
Dafe goshin sa yayi tare da fadin.
"Nayi hauka!" Ya kuma mik'ewa daga kwancen ya shiga ban daki, cika ruwa yayi a cikin abin wankar ya shiga ciki.

   Ya kwanta ruwa na ratsa shi, kamar yadda yake takura Ƙwaƙwalwar shi da zurfaffa tunanin halin da yake ciki. Ya jima a cikin ruwan kafin ya cud'e jikin shi ya fito. Yana shiga dakin shi yayi arba da Munih.

  Kauda kan shi yayi kamar baya Dakin, takowa tayi har gaban shi ta mika mishi madara mai zafi tayi tana kallon hadaddiyar surar jikin shi, wanda yake cike dam da gashi, sun kwanta luf luf.

          Saukar da idanun ta tayi kan k'uguna shi, tare da d'ago kai.
         Amsar madarar yayi tare da ajiyewa a saman mirror din shi. Sannan ya juya mata baya tare da goge jikin shi. Ya jima sosai yana gyara jikin shi kuma tana d'akin.

    Yasan tana kallon shi dan yana jin haka a jikin shi.
Bai gama ida tunanin shi ba, sai jin hannun ta tayi tana me rungumo shi ta baya, rintsa idanun shi yayi tare da janye ta daga jikin shi, ya nuna mata hanyar fita.

                 Ba musu ta fita tana murmushi, tun da ya zauna a bakin gadon, yake kuma jinjina qarfin hakurin Aanih! Yarinyar tasan darajar kimanta ta kuma san hujjar da zata kawo maka dan ta kare kanta, duk da tana ganiyar matantakar ta.

           Amma ba tab'a d'aga kai ta kalle shi da wata manufa ba, asalima idan ta ga yana saka kaya juya mishi baya take.

        Fatimah tana da mugun kunya da kawaici, amma soyayya ta sata bude baki ta gaya mishi sirrin zuciyarta.

      Bayan ya gama saka kayan shi ya dauki madarar ya sha, sannan ya tattara kome na d'akin ya gyara sabida Allah yayi shi mutum me mugun tsafta, baya son kazamta ko na miskala zarratin.

       Yana gama sha ya kwanta, abin shi a d'akin.
Bude kofar d'akin aka yi, ya d'ago kan shi, ya zuba mata ido.

  Juya mata baya yayi dan bai shirya tambayar su,  abinda suka adana mishi ba.

          A hankali ta shigo, tare da zama a gefen gadon, tana kallon shi.
"Jaheed!  Meke faruwa ne?!"

Rintsa idanun yayi kamar zai nutse cikin matashin ya furta da huci me zafi! Sannan yace.
"Babu!"
"Jay! Nasan kan! Na kuma san halin ka! Me zaka iya boye min bayan naga dimauta a kwaryar idanun ka! Bayan naga tarin tashin hankalin da suke cikin idanun ka. Ba a b'oyewa uwa ko uba tashin hankali."

       Tashi yayi zaune ya kura mata ido, idanun shi suna kyalin kwallar da suke cike fam da ruwan hawaye. A hankali ya bude bakin shi zai magana sai kuma ya fasa tare da mik'ewa ya shiga daukar yar falmarar rigar shi!(Jacket top)

   Sannan ya dauki takalmin shi na sawu ciki. Ya juya tare da barin d'akin.
"Jay!"
     Cak ya tsaya yana jin hawaye na sauka akan fuskar shi, ya d'an juyar da kan shi kad'an yana me d'an wai-waiye kad'an, dafa kafadar shi tayi ya sashi jin wani irin b'acin rai.

"Shin ban cancanci jin meke damun D'an nawa bane?!" Ta faɗa a sanyayye.
"Kiyi hakuri!" Daga haka ya saka kai ya fice daga gidan ma baki daya, yana zuwa inda ya ajiye motar shi ya sami Munih a cikin motar tana kallon shi.

  Shiga yayi  tare da kwantar da kan shi.
      "Ina zamu je namijin Zaki!"
Kwantar da kan shi yayi tare da lumshe idanunshi,  ya d'aga mata yatsun shi biyu.

        Sosai take jan motar bata tsaya ba, sai gidan Asood! Wanda yake Alberta town south.

         Wata irin kasala yake ji, tare da tsintar kan shi cikin wata irin buƙatar mace wanda bai tsammaci haka ba,. Buɗe ido yayi cikin nutsuwa yaga ta koma Mishi Aanih.

      Hannun shi ya kai kan cinyarta tare da matsawa, a cikin wata irin bugawa zuciya.

           Murmushi Munih tayi tare da bin shi da wata yaudararriyar murmushi. Fita tayi ya biyo ta, har zuwa cikin gidan.

      Tunda ya shiga, suka zube a falon, sam bai jin ya aikata abinda zuciyarshi take muradi! Amma halin da yake ciki ya wajaba akan shi ya sauke ajiyar da take jinin shi.

  .....matse cibiyar shi yayi zuwa marar shi, ya zuba mata ido.
"Jayyyyy! Ina sonka!"

      Lumshe idanunshi ya kuma yi a karo na ba adadi. Ya sauke wata irin ajiyar zuciya.

         Mika mata hannu yayi tare da b'alle rigar jikin ta, ya rungume ta.

      Jin wani irin yanayi yake kamar ba zai. Amma yana ƙoƙarin ganin ketare iyakar shi, kamar wanda aka watsawa wani abu, ya fara wani irin barci. Me dauke da mafarkai.

                   Yau ma ri ke da hannu. Shi take har bakin kofar da kullum sai an bude mishi haske yake hana shi ganin mutanen cikin su. A hankali aka bude kofar yana me addu'ar Allah ya bashi sa'ar kallon meke cikin gurin, kawai yaji an rufe kofar tare da cewa.
"Babu wani magajin Izzah sai Zulum! Doly na cigaba da mulkina ko na sake aikata abinda zai zame muku mafarin bala'i."

          Kamar giftawa sai tsintar kanshi yayi a wata masarautar na daban wanda shi kan shi ba zai iya cewa ga abinda yake gani ba, zuɓewa suka yi a gaban shi tare da bashi hanya matar tana rike da hannun shi har bisa wata kataga da akayi ta da d'anyen azurfa, sai kambu da aka sanya mishi. Akan shi wanda ya haifar mishi da wata irin yanayi na musamman, bude idanun shi yayi ya kafe shi akan ta, sanye cikin kaya me launin ruwan ja, kanta sanye da wata irin kambu duk inda ta wuce sai ka ga mutanen sun zube akasa rigar jikinta ja ne.

    ....kuma yana haifar da jini sabida jikewar shi, tana nisa gaban shi ta kalle shi tare da zare siririn jar igiyar da take gaban rigar ta. Taja rigar ta zube daga jikinta kyakyawan surar jikinta me cike da kyau da kuma haiba.

       Suka bayyana mishi.
"Jalaludeen! Karka kuskura ka amince da shi ba Ziryana bane Zulum ne!"

             Juyawa yayi tare da lek'awa yana kallon su, a daidai lokacin da ta dauki hannun shi ta sanya a k'ugunta, kallon fuskar ta yayi, tana murmushi tace mishi..
"Jayyyyy! Baka yarda Aanihn ka bace?!"

             A hankali ya shafa k'ugun shi, jin wani abu yayi tare da fidda shi, kafin ta fahimci kudirin shi, tuni ya soka mata sai da ya biyo ta bayan ta, daidai shigowar wasu wanda ba zai iya cewa gasu waye ba, kawai sai ganin yayi Fatimah ta yanki jiki zata zub'e ya riketa a kirjin shi, gefen shi kuwa matar nan ce ta fashe da Dariya bayan ta rikid'e zuwa wani baƙin bamaguje tare da girgiza jiki ya b'ace yana faɗin.

      "Indai zaka iya kashe Macen da kake so tabbas Ni d'aya zan cigaba da mulki tare da...."

             "Jayyyyy! Dole kai.... Har olau  baka kaunata?!" Tayi mishi tambayar hancinta yana zubda jini, haka ma gefen bakinta yana zubda jini.

         "Rayuwata! Farin cikina! Sadaukarwa ce a gare ki, Aanih kar ki manta i...."

A firgice ya farka daga mafarki da yake, tsintar Munih ba yayi a kirjin shi tana wani irin barci me cike da nutsuwa tare da jin dadi, d'agota yayi tare da ganin babu kome a jikin shi, daga shi har ita.

    Mamaki ce ta kama shi ya daki kanshi tare da tir da abinda ya faru.

        Hankad'e ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login