Showing 6001 words to 9000 words out of 119109 words
Chapter 3 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
matse ni a jikin bango, ga baki daya dauke wuta nayi, sabida jin yana min abinda yafi karfin tsayuwa.
Lokaci guda naji kamar zan zube, haka ya kuma matse ni kamar zai yi kome dani a tsaye, duk da a shekaruna bai dace na razana da shi ba, amma ga baki daya sai nake ganin kamar yana wuce iyakata.
.... Ganin kamar zan zube a kasa ya sashi mana masauki a gadon, daga nan ya nime kome ya faru, sai dai buga kofar gidan da ake yi yasa Allah ya kwace ni a hannun shi, har zai fita ya tsaya yana murmushi sannan yace.
"Da dai kin buɗe idanunki, domin yau zamu raya daren ne!"
Jan bargo nayi tare da rufe fuskana, ina me juya mishi baya. dan ban san ya akayi kayan jikina suka watse ba, gidan da muke hade yake da na iyayen shi, suna dan ciki damu. Dan haka naji muryan yayar shi mace da namiji suna magana da ƙarfi.
"Yo kwaɗayin abin duniya Yasaka auri mutuwarka ita din ba macen aure bace, sabida akwai tsinuwar mutane da aljanu akanta kazo muje cikin gida, kaji a cikin mutanen da suka zo daga kauye iskar wata ya tashi take gaya mana, wallahi kazo."
Koda suka shiga abinda matar tace.
"Ayya! Ina baku hakuri sabida sun kashe shi, kuma itama yasan ya mutu, tunda tana yawan ganin shi cikin barcinta an kashe shi, dan haka kuyi hakuri ku koreta a gidan dan zasu iya yin komai."
Kawai ganin Baraq aka yi ya yanki jiki ya zube tare da anan jini, dan haka kanen shi da mugun gudu suka yi d'akina, tare da rufewa zasu dake shi, sai dai abin mamaki sunyi bugun duniyar nan yaki buɗewa karshe haka suka hakura.
Har zuwa asuba, sai ga Baabi da Ummin suka zo, tare da zama akayi jana'izar Baraq sannan aka kai shi ina kwance ina barci me hade da mafarkin ya rasu, har ina cewa karya ne a mafarkin yanzun yanzun ya gama.
Buɗe ido nayi ga yan uwan mu, da sauran mutanen. Tashi zan yi na tuna babu kaya a jikina cikin kunya.
"Ummi kayana!"
Mik'ewa tayi ta bani nasaka, sannan na sauko da kafana daga gadon, kawai naga hatta bargon jini ya b'ata, shiru nayi ina nazarin abin da ya faru, su kuma ganin haka. Sai suka dauka ai jiyan, sai da yayi tarayya dani kafin ya rasu.
Ban fahimci abinda yake faruwa ba, amma yadda naga suke kallona ya ɗan sani tsarguwa da kaina, a hankali na shige ban daki nayi wanka da alola nazo na gabatar da sallah, bayan an dawo daga kai Baraq makwancin shine Baabi ya nemi tafiya dani, sabida yadda yan uwan Baraq suke faɗa zasu kashe ni.
Tunda na zama makara, duk wanda ya aureni mutuwar shi ya aura. Babu wanda ya gaya min abinda ya faru, sai da naga suna hada min kayana, anan na fahimci akwai wata matsala. Dan haka na shiga tambayar su, ko ya sake ni ne.
"Ba sakinki yayi ba, Allah yayi mishi rasuwa ne!"
Kurawa Ammih ido nayi, na kama dariya dariya kamar mahaukaciya, ina nuna su da hannu, zuwa wani lokaci na zube a gurin. Na fara ihu tare da kuka, dakyar Aka fitar dani a gidan, zuciyar Baabi ta karaya da alamarina.
Dan haka koda muka isa gidan na kule kaina a daki, sai da Baabi ya ɓalle kofar, shi ke bani abinci a baki. Shi yake kula dani, har na sami watanin da zan gama takaba, daga nan ban kuma sha'awar fita kofar gida ba, kai ko bikin sallah ake bana fita waje.
Balle kuma wani sha'anin bana zuwa, sabida bayan rasuwar Baraq, anta yawo dani wai mayya ce ni.
Har takai a cikin Zuri'ar mu, ana zargin na da hakan sai na daina shi, duk da wasu na zuwa gidan mu dan ganin halin da nake ciki,sai Allah ya nuna musu bani da wani damuwa a fuskar sai a zuciyata.
Akwai Yayar Baabi hajiya Amina,.tana auren Wazirin sokoto, dan tane ya fara nima na, kamar da gaske, dan na fara gudun shi, kawai tasaka aka kirani, koda naje gidan, ina zaune a falon kasa wasu yan mata biyar suka fito, biyu yaranta ne, daya kuma yar kawarta ce. Biyun Kawayen su ne.
Kasancewar muna wasa dasu, suna zuwa suka zauna.
"A'ah makara kece a gidan?!"
Wani irin muzanta nayi domin a kiraka da makara ba abin dad'i bane.
Ciro kaina nayi ina kallon su, sai kuwa suka kwashe da dariya, sannan suka ce.
"Ban da rashin adalci! Taya kin san baki da lafiya zaki amincewa Ya Hisham! Dan ki kashe mana shi ko? Toh wallahi idan baki rabu dashi ba. Kai ku tashi muje, ga mace har mace ta zama matar mutuwa! Kowa ya aureta sai wani bashi ba."
Shiru nayi ina me wasa da zoben hannuna, har Yayar Baabi ta sauko Hajiya Amina, kaina a sunkuye, ta zauna.
"Da fatan su Khareema da Loloh sun miki kashedin kar na kuma jin labarin Hisham a cikin gidan ku! Idan kuma kina son a tozarta zumunci ne toh zamu yi hakan."
Girgiza mata kai nayi, sannan na mike tare da ce mata.
"Sai an jima!"
"Ki dai k'iyayye abinda nace miki"
Tunda na fita, dakyar nake takawa, har na isa gidan daki na wuce na rufe kaina, duk sai naji Sokoto tayi min girma, dan haka nayi kuka nayi kuka a ranar, kamar babu abinda zanyi bayan shi.
A hankali rayuwata ta zama abin yayatawa, yau saurayi zai zo gobe zai gudu bani kuma ganin shi, haka ya sa. Shiga kunci sosai.
Domin har nayi dana sanin rayuwata, bani fita bani da kowa sai kanwata Hanisah, wacce muke matukar kaunar juna da ita.
Sai Muhammad Kabir, shi ke bin Hanisah, shi kuma yaron Ammih ce, sai Janny ita ke bin shi, kafin Kuma Kazeem, dan Ummi da Hassan da Hussaini, duk yaran ta idan aka cire kabir, Yaran Ammih biyu ne Kabir da Husnah.
Dan haka idan na shiga damuwa kanena, zagaye ni suke suna masu kwanciya a jikina, suna kuka, yawan damuwar da nake ciki yasa Baabi shirya min kayana zuwa Canada.
Haka yayi min dad'i sabida inda Zani a Canada, Yan uwan mune! Aunty Fouzia, da mijinta shima Kuma Yayan Mana na ne.
Suna zaune a jahar Calgary na kasar Canadan, sani a gaba kanena suka yi, wannan yace kaza wannan yace kaza.
Karshe ni dai kallon su nake ina murmushi me hade da kuka, sabida zanyi kewar su. Tunda muka fito, dayawa wasu sunyi farin cikin tafiya na, saboda kar na zauna y'ay'an su. Suce suna sona.
Cikin shekaru talatin na rayuwata, na fuskanci damuwa har nake ganin kamar dan ni matsalar take karuwa, sai dai tunda na bar sokoto naji matsalar ta ragu min.
Baabi da kan shi, ya kaini Canada, mun isa garin Calgary da safe, tun a filin jirgin na fahimci haduwar garin, sannan muna tsaye Aunty Fouzia da mijinta suka zo daukar mu.
Cikin farin ciki, Yanayina bani da jiki sosai, amma ina da tsayi masha Allah, sannan ina da dan karamin kyau, dai-dai gwargwado, amma ni wankar tarwada ce, bakina yana da dan fadi. Sai dogon karan hanci, bani da manyan idanu, amma yanayina ba laifi.
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!
{CIGABA KWARKWARAH}
*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*
Mallakin
Mai_Dambu
Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️
Fatan Alkhairi Fans din KWARKWARAH da MAGAJIN IZZAH ga Pagen ku nan gaisuwar taku ce😍🙈
BIYAR.
Idan nace zan baku labarin yadda garin calgary yake zamu kwana mu wuni ban gama bada labarin yadda garin yake, dan matuƙar haduwa ce, koda muka. Isa gidan wanda yake.
Preston town, anan motar su Kawu Muddam ya tsaya, a hankali ya karasa jikin kofar gidan ya tsaya, sannan muka fito. Ina kallon Unguwa, yayi min kyau, musamman iskar da take kad'awa.
Cikin gida suka mana jagora shi da Umma Fouzan, tunda muka shiga nake kallon yadda tsarin gidan yake, bayan munci abinci muka yi wanka na kwanta kenan Baabi ya turo min yar Karamar yarinyar Umma Fouzan me suna.
Ablah, da sauri na mike na fita gurin shi.
"Baabi na gaji ne! Na kwanta na huta."
Murmushi yayi sannan ya kalli agogon hannun shi yace.
"Zamu shiga jami'ar Alberta ne, mu gama miki kome zuwa nan da jibi na koma gida!"
Gyada kai nayi, sannan nace mishi.
"Baabi ko nazo muje ne?!"
"Idan zaki iya muje mana!"
Murmushi nayi dukda na gaji sosai, amma bana son rabuwa da Baabi na ya sani shiryawa zan fita sai ga Umma tashigo.
"Ba fa inda zaki domin nace su tafi! Ko kunya baki ji ba, ƙatuwar Uwar mata, zaki bishi zokai-zokai toh sai ki kwanta ki huta"
Tura baki nayi idanuna suna kawo ruwa nace.
"Ni wallahi mutum ba yazo ba, a hana rayuwar shi sukuni."
Dariya tayi, abinta dan mun saba fadar mu da ita. Fita tayi yanar ni, nayi kwanciya ta..
---
A cikin kwanaki biyar suka gama min, kome sannan Baabi yayi min nasiha. Tare da ja min kunne kar naga bana gida nace zanyi abinda rai nake so.
Naji nasihar shi, amma bazan iya bari a ci min mutunci na kyale ba, dan haka ranar da na cika sati daya, ya koma nima kuma a ranar zan fara zuwa makarantar. Da wuri na shirya cikin doguwar rigar, tare da nad'e kaina. Da farin mayafin.
Sai takalmina baki shigen kayan jikina. Tare da jakar da nad'ebi abinda zanyi amfani dashi. Na nufi waje inda Kawu Muddam ke jira na, sai danna ansakuwar shi yake.
Koda na isa waje, na kalle shi a hankali. Nace mishi.
"Kayi hakuri!"
Kallon agogon shi yayi, na shiga tare da gyara zaman agogona, ina son agogona domin gadon Mahaifiyata ce, dan agogon ta zinari ce hadi da Lu'lu'u, Baabi yace shi ya sayawa Maaminah, lokacin zuwan su, Madina bayan auren su.
Shi yasa nake son agogon dan yace min, na rike shi da kima. Mun isa makarantar, shi da kanshi ya kai ni har cikin ajin bayan mun biya wani ofishin mun ajiye bayyanan na fara karatu, har kofar aji ya ajiye ni tare da bani wata takarda da zata kaini unguwar da muka fito.
... Bayan tafiyar shi na shiga ajin na zauna, duk da kowa harkan gaban shi yake. Nima na zauna tare da nutsuwa guri guda. Ina kallon yadda suke hidimar gaban su. Dake nima ba ma'abociyar son magana bane, ban kuma kallon kome da suke yi ba.
Shigowar wani bature, wanda zai dauke mu a darasin lissafi. Ya gabatar da kanshi. Sannan ya fara abinda ya kawo shi, yana gamawa ya fita, a hankali naga daliban nata fita, nima daukar jakata nayi na fito.
Dandazon dalibai na gani, maza da mata, ana ta tafawa tare da kiran.
"Jay!Jay!"
Ban damu da naje gurin ba, na zauna na fara abinda ya kawo ni.
"Oo shit!" Naji an Fada tare da cewa.
"Sarkin mu! Ka buga wasan mana, karka bari Lucky ya kwace kwallon"
Ban d'ago ba, sai da naji suna cewa.
"Wowwww! Sarki Juyo kaga wata yar tsanar barbie! Dubeta don Allah, daga gani itama yar Afirka ce."
A lokacin na d'ago idanuna, tare da kallon gurin, da suke maganar sai naga dayawan mutane ma nice na zame musu abin kallon.
Bai juyo ba, sai sharb'e gini yake.
Ya kuma buga kwallon a kasa, tare da cigaba da wasan, a hankali ya juyo tare da kallon inda suke magana ta, ban san me ya faɗa ba tunda kaina a sunkuye yake. Sannan kuma bani tunanin ya faɗa wata kalma mai ma'ana, sai ta rashin d'a'a sam babu alamar yayi magana kawai naji sun kwashe da mugun dariya har da buga inda suke.
Sosai sai da naga wata yarinya tazo inda nake ta zauna tace min.
"Barka dai!"
"Yawwa!" Nace mata ina rubutu, gyara zama tayi sannan ta fara da cewa.
"Dake fa Jay yake magana baki sani ba!"
Kallon waye Jay nayi mata, ta nuna min inda suke wasan ƙwallon kwando, cikin Sa'a idanun mu suka haɗu da juna, kauda kaina nayi tare da cigaba da cewa.
"Idan ya isa yazo gabana yayi maganar shi, ba ya tsaya a can yayi magana ba, sanan ni karatu ya kawo ni ba fitina ba, karatu ya kawo ni!"
..ina gama gaya mata haka, na mike ba barta dan dama ina magana tare da tattara kayana ne.
Kallon juna suka yi dashi tare da d'agawa juna kafad'a. Ina aji na shiga na zauna zuwa wani lokaci aka dawo malami na biyu ya shigo inda zai dauke mu, kimiyyar lissafi.
Mun mai da hankali, kawai sai ga yaran nan sun shigo cikin ajin, koda suka shigo. Kallon Malamin suka yi, tare da hana shi yin komai, yana kallon yadda kowa yake shan jinin jikin shi, bayi magana ba sai wani takaddarin yaro irin shi yace.
"Karku damu! Shugaban dalibai! Ya shigo ya duba yadda kuke karantunku sannan kuma, yaji hujjar da ya hana d'aya daga cikin ku zuwa gaida shi a matsayin shi na shugaban ku."
Juyawa suka yi, suna kallona. Shanye da toka, na zubawa abinda nake ido, ban ko kalle inda suke ba.
Buga kujeran da nake yayi da kwallon hannun shi, ban d'ago kai ba, amma na razana, sai dai ban nuna haka ya dame ni ba, sai ma kauda tsoron da nayi naki d'ago kaina, cikin jin haushi.
Dan koran shi yayi watsi da kayana, ban san lokacin da na tattaro duk wani jurinta na kifa mishi mari ba, sai da yayi taga-taga zai fadi cikin zafin rai nace.
"Kwashe min kayana! Ko na kara maka!"
"Ni kika mara?!" Ee e
Ya faɗa a fusace, zai yo kaina.
"Abeel!"
Yana kiran sunan shi, ya kwashe min kayana, yana huci tare da cewa.
"Ki fara kuka daga yau!"
Sannan suna fita, ban damu ba dan iya haukar da zasu yi kenan.
Suna fita, malamin yace min.
"Kiyi hakuri gaskiya, kin lakato rigimar da tafi ƙarfin ki, domin zasu miki abinda baki tsammani ba, dan haka dabar su take."
Gyara zama nayi sannan nace.
"Meye amfanin hukumar makarantar da bazata hukunta su ba."
Murmushi yayi sannan ya cigaba da abinda yake, yana fadin.
"A wannan duniyar! Idan zaka mu'amalanci mutane kayi nazarin wata gudunmawar suke bawa al'umma, shi yaron da kika mara, kwararre ne a fagen lissafin kimiya, wanda nake muku, shi kuma Uban gayya su, jajjurtacce ne a kowani ɓangare, likitane yanzun haka digiri na biyu yake shida abokan shi.
Sai sauran suma muna kiran su, dan ba iya kwallon kwandon ba, jami'an mu tana alfahari da Mujaheed Harisou Agla, sabida kwazon shi. Likitane da yake da matukar tausayi, da kuma son na kasa dashi, matsalar da aka samu da tun zuwan ki, kika gaishe shi. Tabbas da haka bai faru ba."
Kallon Malamin nayi sannan nace.
"Kenan abinda nayi shine kuskuren! Na taso inda aka san daraja d'an Adam ne, taya zasu shigo lokacin darasi sannan, kuma su ce zasu yi abinda suka gadama."
Daga haka ban kuma magana ba, na shiga hada kayana tare da mai da hankali na, kan abinda nake yi. Har muka tashi wajen karfi biyu da rabi, ko ta inda wad'ancan jakunan suke ban kalla ba, nayi gida abuna.
Koda na isa gidan watsa ruwa nayi, tare da sallah na kwanta.
---
"Jay! Marina tayi ga!"
Watsa mishi ruwan coffee din bakin shi yayi, tare da daka hannu a bakin shi alamun yayi mishi shiru. Ya cigaba da shan coffee din shi, wata yar karamar mage ya gani tana son tsallaka hanya, ya tashi da sauri ya tsallaka ya tsuguna sai ga wata dattijuwa, ashe itace me magen..idan tana son tsallaka wa sai ta tura yar magenta, murmushi yayi tare da mikawa tsuguwar hannu, ta taso yana tafiya a hankali har suka tsallaka yana rike da magen.
Bayan sun wuce, ya dawo ya zauna, yana kallon Abeel da Mas'ud tare da Hikmi sai murmusawa yaƙe yace.
"Da alamu yau kasha yatsu biyar!"
Kurb'an shayin yayi, da bai yi dariya ba, sai yanzun da yake tunawa ya fashe da dariya, kuma dama sun san dabi'ar shi kenan, matukar aka yi maka abu amadadin ya tayaka jin haushi da mita a'a bazai yi ba sai da ya sakoka a gaba yayi ta maka dariya. Wannan dabi'ar bai hana shi idan ya gama ya fashe maka da mugun dariya ba.
Sai yayi sannan ya daure fuskar shi, haka ce ta faru sannan yace.
"Gaya min me kake son kayi mata idan na kawo maka ita har dakinka na gidan hutawar mu"
Zaro ido yayi yana mamakin yadda za ayi ya dauko ta.
"A'ah ba sai ka daukota ba, kawai abinda nake so ka bata wahala a cikin makarantar idan kayi min haka shi kenan ka kare min kimata, ka wulakantata daga gobe ka nuna mata izzarka don Allah Jay, don Allah gobe ka mata sanadin da zata shiga matsala a cikin makarantar."
.gyara zama yayi sannan ya daura ƙafan shi daya akan daya ya maida hannun shi baya, sannan ya kura mishi ido.
"Amma kasan