Showing 54001 words to 57000 words out of 119109 words

Chapter 19 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5465

Yarabawa da Gobirawa. Kuma za ka ga irin wannan wasa yana dada dinke zumunci ne, ba yana batawa ba ne.

Wannan dai duk a zamanin mulkin Habe ne aka yi ire-iren wadannan hare-hare. Amma yayin da aka sami shigowar daular Usumaniyya, back kasashen suka zama daya, addinin musulunci ya hade su. Saboda haka, wata kasa ba ta kai wa wata kasa farmaki ba a cikin titocin da Shehu Usumanu Danfodiyo ya kafa. Sun zama abokan aiki, abokan hulda, kuma abokan shawarar juna.






*Girman kasar masarautar Zazzau a halin yanzu*

Sauyin da aka samu bisa sabon tsari na gwamnati, a yanzu a kowacce karamar hukuma ana da gundumomi ashirin da uku wadanda hakimai suke mulki a karkashin Mai Martaba Sarkin Zazzau. Kamar dai yadda gwamnatin jiha mai ci yanzu ta mayar da su.

Amma gwamnatin baya ta nunnunka wadannan gundumomi, saboda ana shigo da harkar siyasa a cikin masarautun. Wata gwamnatin ta zo ta kara gundumomi, har sun kai tamanin da shida, ita kuma wannan gwamnati da ta zo sai ta rage su zuwa ashirin da uku.

A zamanin mulkin soja an yanke wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Kaduna, wadanda ke lardin Zazzau, wadanda suka hada da Kaciya da Zonkwa. Ta yankin kudu, sai aka bar lardin na Zazzau da kananan hukumomin Igabi da Kaduna ta kudu da Kaduna ta Arewa. Ta arewa akwai kananan hukumomin Giwa da Kudan, ta gabas kuwa akwai Makarfi da Ikara da Kubau. A yankin tsakiya kuwa akwai kananan hukumomin Soba da Sabon Gari da Zariya. A yanzu kananan hukumomi goma sha daya da gundumomi ashirin da uku kenan suke bin masarautar Zazzau a yau.

A da kuwa tun daga karamar hukumar Kaciya, zuwa Chikun, har zuwa Kagarko, duk suna bin Zazzau ne. Amma daga baya aka sami wata gwamnati ta soja ta yanke wadannan kananan hukumomi, ta yi wasu sababbin masarautu, abin da ya sa aka sami masarautu kusan talatin da biyu. Saboda ra’ayin siyasa na son a ba kowacce kabila ‘yancinta, kar a ce an Dianne wa nice yanki a jihar.

----
Mu koma labari...
Saifullah.......
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....

  *Ma sha ruwa.. magirbi*

*Saifullahi Ahmad sullubawa*

Shine d'a na biyar a gidan sarautar Zazzau, mahaifin shi sarki Ahmad Abdullahi Sullubawa, shike mulkin Masarautar Zazzau a yanzun, sarki me matukar adalci, Sarkin da talakawan shi ke matukar son shi da kaunar shi.

      Mutum me kawaici da rikon amana.

    Sarki Ahmad yana da mata hudu russ, da yara Kimanin goma sha biyar.

            Maza da mata kuma, Saifullahi shine d'a na biyar, kafin shi akwai hudu a saman shi biyu mata biyu maza, Abdullahi shine na fari, sai takwaran Sarkin Kano wanda ake kiran shi San kano, Adamu. Sai Mariya, sannan Asma'u.

  Sannan Saifullahi, dakin su Saifullah su maza uku ne da mace daya ne sai sai sauran goma sha daya, sun kasance dakunan. Inda me bin mamansu Saif tana da yara uku mata biyu namiji ɗaya, sai me bin ta tana da yara maza biyu rak.
.sai amaryan da take da mata uku namiji ɗaya.

     Duk da ana zazzafar kishi amma haka bai hana kasami hadin kai a gurin Yaran su ba, domin su saif sune manyan, dukda akwai wasu a gaban shi.

     Amma a halin yanzun anfi mishi kallon shi zai gaji mahaifinsu. Sabida hakuri da juriya,

         Sannan masarautan tana da wani irin tarihin al'ajabi na rasuwan tsohon sarki, Shehu dan idrisa.
Yakasance sanda uwarshi ta haifrshi a ranar kudan Zuma sukazo gidan har kofar dakinta sunata yawo daga sama zuwa kasa daga baya suka rankaya suka tafi,
Haka ranar da aka bashi mulki na sarautar kasar zazzau ma wannan kudan zuman sunzo mashi suntafi,
Ana jibi ze rasu Dan kadan sunzo ana gobe zai rasu masu yawa sukazo sunata shawagi suje sama su dawo kasa kamar masu Kai gaisuwa za a kashe su girgiza kai yayi sannan yace.

" kowacce rayuwa tana tafe ne da mahadin ta, a'' a barsu  suma iya wannan shine wa adin da ya rage tsakanin mu, muyi sallama. Dan haka kar a cutar dasu idan sun tafi ba lallai bane su kuma dawowa"haka  suka zo .
Daga bayan sun tafi seya girgiza Kai kawai ya cikin matsanancin jin jiki ya kalli  uwargidansa yana  cewan.

"Nifa  lokaci yayi Daman inata ganin wasu halittu daban masu cutarwa Amman basumin komai harda maciji.  Dan Allah bai nufa zasu cutar dani ba, kome na rayuwa yana da iyaka, dan haka zan tafi."
(Wannan labarin da na bada na Sarkin Zazzau! Gaskiya ne domin nima haka aka turo min sakon, kuma Alhamdulillah naga ya shiga cikin labarin)

.....
"Aanih Fatimah! Baki cewa zararre irina kome ba!"  Da wutsiyar ido na kalle shi, sannan na kauda kaina, tare da kallon gefe na.

          Shiru yayi bai kuma magana ba, tunda yaga naki magana,  juyawa nayi na kalle shi. Murmushi yayi sannan yace.
"Na zata zaman kurame zamu yi."
              Juya idanu na nayi, sannan na mai da kaina inda nake kallo nace.
"Ka tsaya daga bakin kofar gidan tunda ka fahimci inda na fito."

           ...
"Duk inda kike fito! Ya nuna min cewa an shuka bishiyar zinariya ce ta bada Lu'ulu'u, dan kinfi karfin jauhari ko azurfa."

        Muna shiga kwanar gidan, na nuna mishi inda zai sauke ni.

        Bai kula ni ba, har cikin gidan ya shiga dani, bud'e motar nayi zan fita najita a rufe, juyawa nayi muka kalli juna.
"Koda baki magana ba, zan isa sokoto na gabatar da kaina."

      Shafa kan shi yayi cikin nutsuwa, sannan ya lashe bushashen lebban shi, yace.
"Balle kuma nasan kina yina!"
Sake kallon shi nayi a karo na biyu, kaifin idanun shi ya sani sunkuyar da kaina.

           Na shiga wasan dole. Saif ya haɗu, babu karya ya kai a so shi, kawai zuciyata bata yin shi ne, tana can manne da Jay. Bude baki nayi zance mishi yayi hakuri, sai na kasa magana. Kawai nace mishi.

        "Allah ya tabbatar da Alkhairi!" Daga haka na fito daga motar da sauri, zuciyata tana harbawa.
    
             Ba wai ina son shi bane, amma ko babu kome ya dace na amshi tayin shi, tunda wanda nake dawainiyyar so yace baya yina.

     Sai da yaga shiga na cikin gidan, sannan ya juya kan motar shi yayi tafiyar shi,   ina shiga cikin na sami Aunty Aina'uh, na zauna muka tab'a hira sannan na wuce daki har na shiga sai naga bai dace naki gaya mata Saif ne ya dawo dani ba.

         Dawowa nayi ko zama banyi ba na gaya mata, zuba min ido tayi kafin tace min.
"Amma ya zanyi da wasilah?"
  Dariya ta bani sannan nace mata.
"Ai hakuri zaki bata tunda bana son D'anta."

Bata zata da gaske nake ba, sai da aka kwana biyu, lokacin wakilan shi sun isa gurin Baabi, ya amshi tayin su, amma ya basu hakuri tare da ce musu, zai kirani yaji ta bakina.

             Duk yadda muka yi zai musu magana, dan haka suka tafi tare da Alkhairi, bayan tafiyar su ya kirani, mun jima muna magana, bani da zab'i haka na nuna mishi ina son Saif. Shima kuma Baabi yasan na amshi tayin Saif ne kawai, amma bana son shi. Dan haka bayan sati biyu Baabi ya kira Sarkin Ahmad ya gaya mishi zasu iya turo duk wani abinda ya dace.

       Haka yayi musu dad'i, tun daga ranar muka shiga ƙwarya ƙwaryan soyayya, wanda ya shiga jan hankali na, da kuma nutsuwa ta, Saif yana da kirki. Yana da mutunci sosai.

            .......
"Kaga abinda nake ta gaya maka, kaje ka sami yarinyar nan kuyi magana, gashi nan ta tura wani gidan su"

     A razane ya d'ago kan shi, daga cin abincin da ya mik'e, tsaye bai kuma wani abu ba, ya bar gidan.

                     A hankali ya shiga duba wayar shi, hotunar bikina da Ikrama ya shiga dubawa, kafin ya shiga niman inda zai samu Ikrama, sun jima suna magana kafin ya kashe kiran.

               Huci yayi tare da shafa fuskar shi.
          .......
Daura.
Yana kwance a dogon kujera, wayar shi tana gefe yana sauraron tafsirin din malam Jafar Muhmood Adam, wanda yayi na hadisin Ummu Zarr.

      Zama Jannart tayi tare da kallon shi, tace.
"Hamma!"
Bude ido daya yayi, tare da d'aga mata gira.
"Ka sami labarin wata me zuwa za a yi baikon  Addah?"

           Bude idanu yayi tar akan ta yace.
"Toh Noorie me zanyi? Ina ruwana da Addarku, ko gatari ce bata gaba na."

    Zare ido tayi tare da rike baki tace.
"Hamma!"
"Noorie!" Yakira sunanta a gajiye, sannan yace.
"Don Allah jeki d'akina zaki ga ipad din da kika ce kina so"

     Rau-rau tayi da idanunta, sannan tace.
"Ni wallahi bana son Husnah da wancar buzuwar, ni nafi sonka da Addah."

      "Wayyo Allah na!" Ya fada a hankali.
"Kina son ipad din ko na bawa Raihah."

      Da sauri ta mike tare da nufar dakin, tana murna ganin sabuwa ce dall, ta fito da gudu, tana murna.
       
       Ajiyar zuciya ya sauke,  ya cusa hannun shi dukka biyu cikin gashin kanshi, yana yatsunawa, kamar ya fasa ihu tsabar rashin sanin cikakken fahimtar abinda zai yi, shi bawai sonta yaƙe ba, kawai bai ga wani dacewar tayi wani aure a yanzu ne idan duniya da gaskiya ai bari zata yi yayi aure tukun tayi nata.(🙄🤔🤦🏽‍♀? Sonkai)

       Shiga dakin shi yayi tare da kwanciya ya zuba kafar shi a kasa, sannan ya saka hannun shi kasar matashin sa, ya ciro wata yar karamar wayar kirar nokia.

             Dan danne danne yayi sannan ya kira. Sai da yayi shiru na wasu lokuta kafin ya iya buɗe bakin shi yace.
"Ke wacce irin mutum ce da bata da cikakken hankali, aure zaki yi? Ko sanin ya kamata baki yi ba, yaushe kika tsarewa aurenki da har zaki so wani auren?"

       Kashe wayar aka yi, ya kuma kira yaji taki shiga nan haushi ya kama shi, ba tare da ya kuma wani abu ba, ya rufe wayar.

......
Abuja.
Ina aiki a kicin kawai naji kiran waya ina dauka, ya fara gaya min magana. Da na fahimci cewa zai b'ata min rai shine na kashe wayar baki daya, na cigaba da aikina.

Indai halin jay ne babu bukatar na damu kaina, ba yau muka saba ba. Kuna wayar na kuma yi dan nasan ya hakura ba zai kira ba.
Dan haka na ajiye na cigaba da aikina.

Sake kira aka yi na share, karshe ina na kuma dauka, ina sakawa a kunne na, ya shiga masifa.

"Kaga Ni bana son shirme da yaranta, dan na fahimci baka san ciwon kan ka ba, don Allah karka kuma kira na, mayye mara zuciya, kaje kayi rayuwar ka mana, Asood kafita harkokina."

Daga haka na katse kiran Asood, na cigaba da abinda nake. Dan da farko na zata Jay ne ashe ba shi bane. Asood ne.

----
Wasa wasa, aka saka bikin Jay, yana cika yana batsewa aka fara kai kayayyakin auren daya gidan Galadima, daya kuma aka wuce dashi Damagaram, cikin wata uku da aka saka bikin anata hidimar gidana sabon Asibiti dan baban shi na Canada ya kawo mishi takardun shaida karatun shi.

Dan haka aka shirya mishi tafiya Maiduguri, sun zo su amma shi bai samu damar zuwa ba, sabida ana tunanin kar a kuma dauke shi.

... Tunda ya shigo garin, aka karb'e shi cikin gata da farin ciki, ga uban dangin Maman shi da kuma gidan sarautan da aka shiga mishi hidima da biki.

Anan Ministan harkokin lafiya Dr Bulama yake tambayar shi matsayin Karatun shi.

"Yallabai! Na karanci ɓangaren mata da yara ne," gyada kai yayi sannan yace.
"Zaka yi aiki da mune ko zaka gina naka na kanka?"

Gyara zama yayi sannan ya sunkuyar da kanshi..
Yana faɗin.
"Nafi son nayi aikina da kaina, amma naji ance sai naje Nsukka nayi jarabawar gwaji."

"A'a mun dawo da ita gwagwalada, zaka iya zama a cikin gidana na can kayi jarabawar a can, idan ka gama sai ka dawo gida. Sannan kuma asibitin zan so kayi mana anan, amma nasan mahaifinka yana kewarka kuma zai bukaci kayi a daura, dan haka ga zamu bada gudummawar mu."

Nan ya dauko takardan cheq ya rubuta mishi kudi masu yawa, yayi godiya sosai.. lokacin da ya shiga sauran gidajen, dangin Maman shi haka suka yita bashi gudunmawar su na Asibitin da za a gina mishi karshe ya nuna musu kudin yayi mishi yawa.

Nan suka shiga ba shi labarin, rayuwar Mahaifiyarshi, tun daga kakar shi da tafita da Jannart, har zuwa irin sadaukarwa da mahaifiyar shi tayi, sannan suka zuba mishi ido.

Yana kallon su bai ce kome ba, a hankali ya sunkuyar da kan shi, kasa, sannan yace.
"Kenan masarautan zagaye take da ruffenfen sirrin da suka kasa cimma matsaya akan shi?"

"Masarautan cike take da tsinuwar mutane da aljanun." Inji Umma Kaltum, kanwar Mahaifiyar Jannart,

Sun jima suna tattaunawa kafin yayi mata sallama, ya nufi gidan kakan shi, ya same shi. Shida wasu malamai, juyawa yayi zai fita wani Dattijon a cikin malaman, ya kira shi.

Shiga yayi ya zauna tare da sunkuyar da kan shi Sarki Kazeem yace musu.
"Shine Jikana na fari, dan gurin Jannart Hassanah, bai jima da dawowa kasar ba."

Gyada kai malaman suka yi sannan suka zuba mishi ido kafin suka ce ya tafi, yana fita babban cikin malaman yace musu.
"Wannan yaron yazo rusa tarihi ne! Bayan shi kan shi tarihin ne, karfin hali da juriya duk yana da ita, kafiya da naci ya dauke kome. Sai dai kuma ban san wani irin yanayi zai kasance ba, daga ranar da taurarin su ya hadu guri guda.

Domin duk matan shi babu wacce zata iya daukar nauyin kasadar da take cikin rayuwar shi. Idan kuma aka samu toh tabbas tarihi zai iya mai maita kan shi, domin masu fushi da fushin wani suna fusace akan shi, sannan wata duniyar tana niman shi domin dai-dai mata alkaryanta, kada ku sake yin wasa da rayuwar shi, koda kuwa yanayin tafiya ce ta kama shi, yayi ta Addu'o'i. Domin akwai matsala ba akan shi zata faru ba kan duk wacce tsautsayin...
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: *Ba domin tsawo a kanga wata ba*

"Duk wacce tsautsayin ƙaddara ya shiga tsakanin su da shi, dole itace zata maye gurbin da aka rasa amma muna namu Allah yana nashi.'"

       Cikin tashin hankali, Sarki Kazeem ya zuba musu ido, had'iye yawu yayi sannan yace.
"Babu yadda za a dakatar da al'amarin?"

       Mik'ewa babban yayi cikin nutsuwa ya taka a hankali zuwa bakin kofar fita yace.
"Idan guguwa ta taso ka tab'a ganin an dakatar da ita? Idan ruwa zata yi ambaliya ka tab'a ganin an sanya mata shinge, toh kamar yadda mutuwa take zuwa babu sanarwa haka kaddarar su ta haɗa lokaci guda.

        Dan haka Allah shi yafi mu sanin abin da dace."

     "Sheikh Muhammad, a yanzun haka shirin auren shi ake, mun zab'a mishi mata, ya amshe su amma daya daga cikin su yaki amsar tayinta ." Inji Kazeem.

   Girgiza kai Sheikh Muhammad yayi sannan yace.
"Karku manta, tunda ya amshi tayin sauran haka yana nufin kaddarar su da ita wacce yaki amsar d'aya ce. Haka yana nufin tarihin masarautar su zata kuma mai-maita kanta kenan"

Daga haka suka ficce, daga gidan. Shigowa Jay yayi jikin shi a mace dan ya hadu da su Sheikh Muhammad suka mishi wani irin kallo. Sannan zasu wucce Sheikh Muhammad yace mishi.
            "Tauraron ka yafi nata karfi! Ka nisanceta domin kusantarta dai dai yake da tab'a karfin haskenta, daga ranar da kayi gangancin tarayya da ita. Toh daga sannan kome zai iya faruwa da ita. Ka rabu da ita tayi rayuwarta domin ta hanyar zata kuɓuta daga kaddararku"

        "Kai waye da zaka dakatar da ni abin da ban damu dashi ba? Wacece kake tunanin ta isa nayi rayuwa da ita?  Idan ina son Mata dubu zan iya mallakawa kai na, amma mace bata gabana zaka iya tafiyar ka"

          Yayi gaba yana jin babu dadi, murmushi Sheikh yayi sannan yace.
"Tabbas rayuwar wannan Yaro cike take da Izzah, shi yasa yake jin kome akan shi."

    Daga haka suka bar masarautan baki daya.

    ----
Cikin sauri na fito daga cikin gurin wanke kai, da nazo yi. Ina kallon wayar dake hannuna naga kiran Saif ne, murmushi nayi zan dauka naji an rike hannuna.

                 D'ago kaina nayi naga wata tsohuwa, tana rike da sanda. Ajiyar zuciya na sauke tare da zuba mata ido tsigar jikina yana mik'ewa.

           Murmushi nayi mata a sanyayye na zare hannuna daga nata, na bude jakata zan dauki kudi ina kawai naji wani abu zummm, naji jikina yayi min wani mugun sanyi. Kallon matar nayi kamar zanyi kuka nace mata.
"Me kike bukata?"

Dariya tayi idanuna yana fidda wani irin yanayi shi ba kore ba, shi ba shuɗi ba, shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login