Showing 45001 words to 48000 words out of 119109 words

Chapter 16 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5448

ba Lallai bane kowa ya fahimci bashin da ba kaine ka ci ba.

Taya duniya zata fahimci girman Soyayyar da Sadaukarwa? Taya duniya zata gane halin da zuciya take ciki? Maza ki dakatar da wannan Kuskuren da ake shirin saka shi a ciki, idan ba haka ba.

Daukar nauyin kasadar yana jingine bisa kafadarki!"

Bude idanu nayi, tare da tashi zane. Jini ne ya digo daga cikin hancina, ga kaina yayi wani dum.

Da sauri na fita daga lambun dan ina iya hango abinda yake shirin faruwa a filin nan da wasu mintuna masu zuwa.

Ganin shi nayi yana ƙoƙarin hawa doki, na rike shi hancina na saukar da jini.

Girgiza mishi kai nayi cikin zubda kwalla, sabida jin wani irin karfi da nake ji a jikina, tare da wani irin yanayi me tadda hankali.

Zuba mishi ido nayi dakyar bakina ya iya furta.
"Jay! Karka tafi."

Cikin ganin yafi karfin ya saurare ni yace min.
" Koda zaki ya zamma wulakantace, ba ya yi wasa da khinzeri ba! Dan haka ki sa kai ki bar nan kafin na miki abinda baki zata ba."

"A'ah Jay, Bera yana gani'n raminshi, bazai yarda wuta ta cishi ba. Me yasa?"

"Ke bana son shirme da yayyafi kogi yake cika, ke kin isa ko dakatar da ni ne?!"

Murmushin takaici nayi tare da zuba mishi ido, sannan nace.
"Allah ba ya ba gwanni'n tona tsaba.! Ai ya fishi sanin dalilin da ya hana shi, don Allah karka tafi."

Ture Ni yayi tare da hawa dokin shi...

Paid before read 🕊?
10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.....

*Jiki Magayi... Duka da d'anyen kara*

   Da gudu ya zaburi dokin, ji nayi kamar ance min.
"Ki dakatar dashi!"

      Da sauri na mike na nufi hanyar wajen.
"Karku sake tafito!"

Ya fadawa Fadawa masu tsaron kofar shiga filin, ina zuwa suka hanani shiga, kamar zanyi hauka haka nake kuka.

"Don Allah ku barni na je, wallahi akwai abin da zai faru mara daɗi ne!" Na fada musu ina rokon su.

Juya min baya suka yi, alamar ba zasu saurare ni ba, sunkuyar da kai nayi, dai dai fitowan Abban shi dasu Baba Aswad, suna zuwa aka bude musu kofar kafin suyi wani yunkuri, na shiga filin da sauri.

Tattaro alkyabar jikina nake, tare da niman in da yake. Hango sahun farko nayi nasu Fahad, tare da Mijin Rumah sahu na biyu kuma shine akan doki, wata irin guguwa ce ta taso tare da mamaye filin baki daya.


Kafin ya lafa, tawagar farko suka fara suka juya da gudu sannan suka koma, tawagar Jay suka tashi amma dokin shi yaki tafiya sai mik'ewa take, abinda ya d'aga hankalin Iyayen shi.

Kowa so yake ya kai mishi dauki, shi kuma yana hankoron ya jan linzamin dokin yake, amma dokin yaki sai ma mik'ewa da dokin yake.

Ban san lokacin da na cire alkyabar jikina ba, babu takalmi a kafana, nake keta dandazon mutanen da suke kokarin ganin sun dakatar da mutane shiga.
Tsalle yake tare da walagigi da shi, kamar wacce ake cilla ni cikin filin.

"Hasssss! Kunba nuba! Jiyya hiyya, huuuuuuuuuu, ja hass bam da..." Na daka mishi tsawa, wani irin tsalle dokin yayi suka zube a gabana, durkusa nayi a hankali tare da riko hannun shi.

Jini na d'iga a hancina tare da idanuna, dakyar ya mike tare da fisge hannun shi, yana harara na. D'igin shi ya fara a hankali lokacin da su Abban shi suka iso filin.

Guguwa ce ta kuma tashi da karfin tsiya zata sure shi.

"Zulum! Ka Raf ka, atɓa di na, fass haya mi ro, fur ab fuuwa"

Cak guduwar ta tsaya tare da zuwa ya kuma dungulewa da karfi ya sure ni a guje.

Hankalin kowa ya tashi, sabida ganin yadda iskar take kwantawa dani,.kafin ta watsar dani can gefe. Dakyar na cire kaina na mika Mishi hannu.

Kallona yayi sannan ya kauda kan shi, kamar bai ga halin da nake ciki ba.

"J...a..y!" Na Kira shi a gajiye da kuma wahalar da nasha.

Banza yayi kamar bai sanni ba, sai da Baba Aswad ya nufoni da sauri tare da Najim,

Suna isowa Najim ya kai hannun shi da niyyar dauka na, ai kuwa Jay ya doke shi sai da ya fad'i, sannan ya durkusa ya dauke ni, tare da b'ata rai da fuskar shi, sai ka rantse mugun abu ya dauko.

A hankali ya nufi cikin gidan, ina hannun shi sai aman jini nake, tare da mik'ewa ina kokuwa da numfashi na,


Kai tsaye shashin Mamah Sarah yayi da ita, inda aka shiga bata kulawa, yana tsaye a kanta. Har ya juya zai fita ta rike hannun shi.

Cikin tausayawa kanta ta bude ido, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta sake shi. Ya fita da sauri yana me jin ɗacin abinda tai a gaban jama'a, babu dan mayafi, ai haka bai dace ba.

Tsaki yaja tare da tunawa toh meye matsalar shi da ita, haka yayi ta sakawa yana warewa, har Najim yazo ya zauna kusa dashi sannan ya kalle shi kafin ya kauda kanshi, yana me kallon sama.

"Inji Baban Sarki wai kazo!" Inji Najim.

Mik'ewa yayi, sannan ya mike tare da barin gurin, Najim yana bin shi.
"Amma Fatimah tayi kasada da rayuwarta fa?" Cewar Najim,

"Toh ina ruwa na, meye matsalata da ita."

Murmushi Najim yayi sannan yace.
"Amma kamar naga wani abu na daban a cikin ƙwayar idanun ka"

Shiru yayi sannan yace.
" Ganin ka ya gano karya! Malam Lauya"

"Malam likita me yasa bazaka amshi batuna ba!"
"Ban iya dogon magana bane!"
Da sallama suka shiga falon, kowa kallon shi yake, sai a lokacin ya kalli kan shi da jikin shi sun yi butubutu, sunkuyar da kai yayi cikin nutsuwa, dan bai lura da suwaye a falon ba, sai da yayi an ce mishi.
"Jaheed!!"
Da sauri ya d'ago kan shi da sauri, yana kallon Baban shi na Canada.
Kau da kan shi yayi sabida har yanzun yana jin zafin abin suka mishi.
Kallon kasa yayi cikin nazarin meye ya kawo su Daura.

"Jalaludeen! Ga Babanka na canada, tare da sauran iyalan shi suna cikin gida.

Abin mamaki ashe ma d'an ne ga Yayan Rumanah kakarka, matar shi kuma kanwa ce ga Balkisu. Kai dai Allah ya dauke ka ya kai ka cikin dangi da yan uwa."

Shiru yayi kamar ruwa cinye shi, ya rasa abinda zai ce bai kuma firgice ba, ya d'ago kan shi yana kallon su.
"Gashi ya baka yar shi Munubiya! Sannan mun nima maka auren Fatimah."

"Wallahi bana sonta! Bana kaunarta don Allah karku haɗa mu, dan zan zalince ta."

"Baka isa ba, idan an daura maka ita ka mutu."

Kamar wani karamin Yaro. Ya b'ata rai mik'ewa yayi zai fita Najim ya zaunar dashi yana kallon fuskar shi.
"Ahalin masarauta an samu da kamewa da kuma ɗa'a yin haka sam bai dace ba."

Kallon iyayen su Najim yayi cikin nutsuwa sannan ya cigaba da cewa.
"Ku iyayen mu ne, sannan kun fimu sanin dalilin da yasa kuke son a nima mishi Aanih Fatimah Aryaan, mu bamu sani ba. Amma ko a musulince, shi yake da ikon nimawa kan shi mata, dan shi waliyyin kan shine! Dan haka don Allah ku dakatar da nima mishi ita, tunda ya ce baya yinta a barta kowa ya hakura tunda ya amince da sauran zab'in ku."

Jikin kowa yayi matukar sanyi sabida abinda Najim ya faɗa.
"Kuje!"
Mik'ewa suka yi, ba tare da anyi wani magana ba.
Har suka fita babu wanda ya tanka musu.
"Abba haka zamu bar shi babu wanda ya isa dashi."

"Kai ma haka kayiwa uwar shi, ai gado ba karambani bane!"

Shiru suka yi ba tare da cewa wani abu, ba. Har dai suka watse.

---
A hankali maganar ya watsu a cikin gidan, kamar wutar daji. Jay kan babu abinda ya dame shi. Koda aka ce ya samu Husnah shareta yayi ya cigaba da abinda ke gaban shi, Munih ce ma tayi ta shige mishi.

Tare da nunawa ai ita ana sonta.
Ina kwance a dakin Mamah Sarah Hanisah tana hada min kayana, Munih ta shigo cikin wani rawan kai tana kiran.
"Janna!!!!"

D'aga kai muka yi tare da zuba mata ido, kamar taga kashi haka ta kalle mu, shigowar Jay ya mai da hankalin shi kan mu, fuskar shi babu fara a ya shigo. Har gabana ya iso, kaina a sunkuye, zama yayi a kujeran dake gaba na ya zauna.

"Assalamu alaikum! Abba gata nan!"
Ajiye min wayar yayi akan cinyata yayi tare da tsare ni da ido, mun jima muna magana ban gama magana da Baabi ba, wayata da take cikin shiru tayi haske, ina dauka naga Asood Buba Yaro, dake data na yana kune.

Domin na cusawa Jay Haushi cikin sakalci na kashe kiran Baabi ina ce mishi.
"Baabina zan kiraka an jima."

Da sauri na dauki wayar ina me sake murmushi.
"Sahibi na! Ya kake? ya kwana biyu?"

Sake murmushin jin dadi nayi tare da mai da kai na jikin matashin ina sauke yar karamar dariya nace.
"Hmm! Toh me ka shirya min idan na dawo daga daura wanda zai zame min na musamman?"

Wani shegen shewa na saka, nan kuwa bakar magana Asood yake gaya min.
"Kasan yadda nake kokarin na dawo mu hadu! Ayya Asood tun a Canada kak...."

Jikin shi na wani irin rawa, ya fauce wayar hannu na, ya shiga gayawa Asood bakar magana,.karshe suka yi fada kaca-kaca.
"Malam bani wayata! Kuma wallahi sai na kai karar ka gurin Ummi."
Kallon Hanisah da Munih yayi cikin nutsuwa, take suka fita, kasa magana yayi yana kallona.
"Wallahi idan baki rabu da yaron can ba!"

Daga haka ya shiga ya kulle hanyar da Asood zai dame ni, kasa hakuri yayi ya fita da wayar, ban kuma ganin shi ba. Sai da aka gama hada min kaya a mota yazo ya same ni a falo ya cilla min kwalin sabuwar waya, tare da sabin layi.
" Ki Cigaba da kwashe kwashe!"
"Idan nayi akan ka nake? Ina ruwanka dani? Wai in tambaye ka Jay zaman ka nake da ba zanyi kwashe kwashe ba. Ince nan kace min baka sona Ina ruwanka da samarina!"

Duk kanen shi sun zuba mana ido, ran shi ne ya b'aci.
"Uban me kuke jira da bazaki bar falon ba!"

A tsorace suka bar falon, yana zuwa ya dauke ne da mugun mari, sai da bakina ya fashe rike kuncina nayi! Kuka ya kwace min.
"Allah ya isa min! Mugu kawai."

"Kika kuma gaya min magana sai na zane ki!"
"Sabida kai ne Ubanta? Wallahi Deen ka fita hanyar Fatimah ina ruwanka da ita, baka ce baka sonta ba? Uban me tayi maka da zaka mare ta!"Inji Rahil Kanwar Jannart,

"Wai meke faruwa Rahil?" Inji Mamah Raihanah tare da Sarah.
Cikin b'acin rai take nuna musu ni, ina kuka sosai.
"Kawai ya bani wayata da layinka!"

Na fada, banza yayi dani.
"Baka ji bane? Ina wayarta da layinkanta?"

"Na wurga a rijiya!" Daga haka Yasaka kai ya fita, kuka nake ina fadin.
"Allah sai yabi min hakkina, lokacin da aka saya min waya babu shawarin wani banza balle ya dauki wayata ya wurga min, wawa kawai."

Su kan su basu yi tsammanin zai dawo ba, sai ganin shi muka yi ya kamar zai rufe ni da duka.
Da karfin tsiya ya janyo ni zai fita dani, Mamah Raihanah ta tsinka mishi mari, sai da ya sake ni.

"Ta gaya maka wawa! Wanda bai san inda ke mishi ciwo ba, wani shegen ne yace ka yarda mata wayarta, ina ruwanka da ita? Toh wallahi ahirr dinka Ubanka ma bai isa yazo gabana yayi min rashin kunya ba, balle kai sakarai kawai kuma na kuma ganin ka daki wata a cikin masarautan nan sai na baka mamaki."

Yana fita ta juye kaina ta balbale ni da fada, sannan ta dauki wayar da ya kawo min, ta mika min, dukda tafi rawa tsada da kyau amma bai burge ni ba.

Da wuri na bar garin daura, shi kuwa uban yan ɗacin rai, haka ya wuni cikin dakin shi, fita masalaci yake sanya shi fita.

Dayawan mutane, sun watse su Ummi ma sun koma Sokoto.

Yana zaune, rike da yar na'ura me ƙwaƙwalwa, yana dube dube. Yaga sakon Munih.
_Barka Jay😍_

Share ta yayi tare da cigaba da aikin shi, sake turo mishi wani tayi.
_Ayya Jay kayi hakuri mana😭_
Bude sakon yayi tare da cigaba da abin aikin shi.

_Jay ina sonka☺️_

Murmushi yayi sannan lashe bakin shi ya kashe wayar baki daya.
.....
Abuja
Bayan na dawo gida, sai da na kuma rashin lafiya, kamar bazan rayu ba, sannan naji sauki.

...... Yau muka yi da Rumah zan zo gidan ta, dan haka da wuri na gayawa Aunty Aina'uh, ita kanta taji dadin ganin na cire Jay daga cikin rayuwa ta.

Da sauri na fita ina ce mata.
"Uwata sai na dawo!"

"Allah ya k'iyayye hanya, ki kula sosai don Allah."

"Amin Ya Allah."
Da sauri na nufi inda motar take, sanya driven ya kai ni Unguwar su.

.... Karfe biyu na isa gidan, a hankali na fito daga motar nayiwa driven sallama, sannan na nufi cikin gidan, cikin nutsuwa.

A farfajiyar gidan, na hango Khalid da wani mutum bayan shi kawai na iya hangowa, ban kuma kallon su ba, har na iso inda suke, gaishe da Khalid nayi ya amsa.
"Gimbiya Aanih Fatimah! Kece a gidan mu?...."

#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.....

*Yariman Zazzau*

Cikin zazzakar muryana nace Mishi.
"Abban Maam nice ya aiki dasu Maam da Mamanta?"

            Murmushi yayi sannan yace,
"Alhamdulillahi, ya gida da jikin ki da fatan kin ji sauki ko?"
"Gyada mishi kai nayi,.ina murmushin takaici.
"Toh ki shiga tana cikin"
    
A sanyayye yayi wucewa ta,.ina ji a jikina ana bina da kallo, bayan na shige ya kalli abokin shi su cigaba da hirar su, ya ga yana bin bayana da ido.
"S. Yarima! Ya dai?"
Khalid ya tambayi abokin shi, lumshe idanunshi yayi wanda suke kamar yasha wani abu na maye.
             "Kayi shiru kuma? Bayan kana bani labarin." Inji Khalid,
"Wannan yarinyar daga wata masarauta take?" Tambayar yayi tare da kafe Khalid da ido, zuciyar shi tana wani irin rawa. Lumshe idanunshi yayi na wasu lokuta kafin ya bude ya kuma mai maita tambayar da yayiwa Khalid.

       "Yar sarkin sokoto ce!" Ya bashi amsa a takaice,
     Zubawa Khalid ido yayi sannan ya taɓe baki tare da shafa kan shi, sannan yace.
"Ok wacce ta gudu  ranar aurenta?"

Yayi tambayar tare da zubawa Khalid ido.
"Ba gudu tayi ba! Sace ta aka yi."

          Basar da zancen yayi kamar bai damu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login