Showing 99001 words to 102000 words out of 119109 words

Chapter 34 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

8138

basu son gaskiya. Gashi nan suka son nasara mu.

Ina da yakinin zaki taya shi kafa gaskiya, don Allah."

..... "Mama irin wannan maganar kamar kina rokona ne, Ni kuma kunyar haka nake ji. Zan bawa Jay goyan baya har ya kafa adalci Insha Allah "

A hankali take gaya min, sakon Maman Jay, kallonta nayi da jajjayen Idanuna nace mata.
"Kiyi hakuri! Ba zamu rusa Ganuwar ba! Yin haka dai dai yake da zunubi domin akwai shugaban mu a gurin,.kuma kar mu kuma jin maganar rushe ganuwar nan,?"

Wani irin tsoro e ya kamata, daga haka na juya mata baya, kuka ya tawo min, ina gaya mata cewa.
"Zan iya miki kome amma bazan rushe ganuwar ba, domin akwai masu ibadar su a gurin, yin haka zunubi ce Babba."
.haka na fita na barta, har Jay ya shigo..

Kwananta daya, aka sallame ta, tunda muka dawo Jay ya saka ni a daki ya hanani fita ko falo sai ya biyo ni, maye ya hanani sakat, tun da yaji yadda na koma akwanakin da nayi a Sokoto, sai wani rawan kai yake shi nan wani ango.

........ Tsakanin shi da Galadima rikice ne ya girmama, dan Galadima ya sako Jay a gaba, nan ya fita hayacin sa, sai da na tafi har gidan Galadima da kaina.

Ban same shi ba, wai bayan na, ina tsaye a gaban wasu lambobin girmamawan da ya samu a shekarun shi na aiki ya shigo falon shi.
"Da alamu dai kaje ta'aziyar abokin cin mushen ka ne? Koda yake kai da kake da yakinin saka yaro karami gaba, ina kuma shi da yake da goyan bayan Sarauniya irina da."

"Aanih Khatoon! Idan da zaki bani hadin kai, me zai hana na ture wancan yaron ai naga ba wani abu zai iya miki ba?"

Juyawa nayi gaban shi ina kallon yadda yake bina da kallo.
"Me yasa baku iya tsayawa ga abin da yake naku sai kun tab'a rabon wani?"

"Fatimah! Kin yi min laifi, amma a hakan nayi shiru, idan na fadawa manyan mutanen cikin masarautan nan cewa Jalal ya auro mace mafi hatsari a cikin masarautan nan ba zaki sha da dadi ba, amma sabida ina yin ki, ba zan fada ba."

"Aikuwa zaka mutu baka samu abin da kake bukata daga gare ni ba, dan Ni sabida Jay aka halicce ni, idan kuma kayi kuskuren shiga inda babu hurumin ka, zaka bakunci lahira, domin ba zan tab'a barin ka ba, ka kyale Yaro yayi aikin shi yadda ya fara."
"Ziryana ki hada kai dani muyi tsayayya mulki tare!"
"Da Aanih Fatimah Khatoon kake magana ba da wata can ba, ka sakewa mijina mara yayi fitsari idan na haka ba, wallahi abin da zai faru ba zan maka kyau ba." *Don Allah kuyi hakuri bamu da wuta ne chajina yayi kasa sosai!*
10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *_Rijiya ta bada guga ya hana_*


*ALHAMDULILLAHI MUN GODE SOSAI ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI JIKI YAYI SAUKI...

"Baraxana kike min?" Ya tambaye ni, yana me karasowa inda nake, wani irin kallo nayi mishi ya tsaya cak. Ya kasa motsawa, sai zare idanu yake.

"Meye nufin ki? Rike ni da kika yi! Toh sake ni Nima zan rabu da mijinki! Ki sake ni nace Ziryana." Juya baya nayi dan a iya zuwa yanzun bana jin kome idanuna sun kad'a jajjur, jini yake d'iga a hancina.
   
             "Ranki shi dad'e! Nayi mubayi'a!" Juyawa nayi na ganshi duke akan gwiwar shi, dan dukawa nayi ina kallon fuskarshi.
"Idan na gadama, zan iya sanyawa a kama min d'an iskan da yake tare da kai, idan kuma naso zan Barka nayi ta matse bakin ka, Kana sake magana kowa yasan halin da kake ciki.

          Amadadin gidajen ku ya samu zaman lafiya sai a iya samun tashin hankali da rashin zaman y, ka sani bana da zab'i a rayuwata sama da na bada rayuwata domin Jalal, idan na kuskura na kuma samun wani shirme har naga canji a fuskar shi.
           Na rantse da karfin kujeran da na gada, sai tsuntsaye sun tsatsagi namar ka, a samar sahara kamar yadda ka kai shi ka ajiye shi a gurin."
Cikin wani irin bala'in sauri ya ke kallon da fuskana, tare da ganin gaskiyar maganar da nayi, Uwa Uba, jinin da yake fita daga hancina.
  
     Cikin tsantsar rashin yarda da abin da yake gani, yace min.
"Toh Ziryana ki kashe ni mana!"

"Ba zan kashe ka ba! Domin nasan kai ka saka Abdul kashe Ubanshi! Ka kuma kashe Gamji! Ka kuma kashe Abdul din, Kayi a hankali ni ba zubda jini nazo ba.dan haka ka kiyayye abin da zan ce maka.  Kafita harkokin shi"

Daga haka nayi feccewar zan bar gidan yace min.
"Ya tsawon shekarun yake?"
"Dai-daiton da tunaninka!"
"Me yasa kika fusata?"
" Bazlah ki sanya a mishi horo na musamman bakin shi yana nan!"
Ina fadar haka na bar gidan.

               ----
Allah ya taimake ni, Jay baya gida dan haka nayi kwanciya ta.

     Kwanaki sunyi tafiyar bazata, sati sun koma watanin, watanin sun shuɗe, Shakara ya kuma sako jikin.  Muna dab da fara azumin watan Ramadan. Na fara wani irin ciwon ciki, kasancewar Munih tana dauke da wani cikin, kusan wata biyar, sai ni da nake fama da ciwon ciki.

      Ranar da na fara, kamar ba zan rayu ba, haka nayi ta juya. Bazlah kuwa haka suka yi ta kawo min saiwa,ina ganin shi zan fara amai. Data ga haka sai ta dakatar da kome.  Duk suka zuba min ido,  Jay baya gari ya tafi Maiduguri. Dan haka zan iya cewa kamar jira ake ya bar gidan suka dauke ni.

......... Shigowar wani tsoho cikin dakin, ya gama dubani sannan ya cewa bazlah.
"Ba zai yi tasha maganin mu ba, domin ita bani Adam ce, kuma Sarauniyar mu, dauke take da juna biyu, iya abin da na gani kece Uwar Fada!" Ya gayawa Bazlah, cikin wani irin farin ciki. Ta kalle ni ina barci wahala sannan ta kalli tsohon tace mishi.

        "Ka gama naka,kuma masarauta tayi maka kyauta, kaje kofar taskar masarautar nan a baka zinari da lu'ulu'u."

  D'an dukawa yayi sannan ya mata.
          "Ranki shi dad'e! A kula da cikin domin zai iya samun matsala, idan da hali a bar bayyana mata masarautan nan, shima cikin a adana shi yadda babu wanda zai san dashi har sai ya kai matakin da ba zai iya salwanta ba.". Jinjina mishi kai tayi sannan tace mishi.
"Na baka damar haka, ka gwada sa'arka."

        Daukar wani magani yayi ya shafa min akan cikin, sannan ya dauko wani abu ya shafa min a goshina,  ba zata kuma ganin masarautan ba, amma zata na yawan kawo shi a cikin ranta. Idan ta haihu sai mu bar musu abin da ta haifa, ita kuma mu dawo da ita duniyar mu. Amma ki nazarci abinda nake nufi."

          "Kaje zan duba abin." Godiya yayi sannan ya bar d'akin, Ni kuma bazlah ta shafa fuskana, sannan tace.
"Ranki shi dad'e! Zamu yi kewar ki, muna tare dake domin bawa baki kariya."

          Mai dani d'akina suka yi, sannan takira wasu manyan bayinta tace musu.
"Ku kula da cikin jikin ta! Sannan ku saka ido, akan wani a cikin gidan. Idan kunga abin da bai muku ba, ku gaya min."
Daga haka suka b'ace.

           Wuni nai ina barci, har zuwa lokacin sallah, sannan na farka dakyar babu ciwon yanzun, ban daki na mike zan shiga naji motsin ruwa, ina shiga na samu an cika min ruwa har da wasu fure akai, ga kamshin turaren da yake fita a dakin, tunani na ne ya tsaya cak ina niman inda na tab'a jin kamshin..
   
Wanka nayi sosai, sannan na hada da alola na fito. Lokacin da na fito, naga kayana har da abin sallar, sam ba zan iya cewa nice na ajiye ba, amma kaina ya daure. Kawai na share tare da sakawa na gabatar da sallah.

Ina cikin addu'o'in barci ya dame ni ga yunwa. Mik'ewa nayi zan fice falo Zabba'u ta shigo, kallon ta nayi sannan nace mata.
"Zabbah ina jin yunwa! Nima min wani abu koda dan wanke ne, domin Allah, a saka yaji da kayan lambu. A dafa min kai a saka a kai."

            "An gama ranki shi dad'e!" Ta fita da sauri, ji nake kamar bata sauri dan haka na nufi kitchen ɗin na shiga aikin nima,.tunda muka tsame na farko, na juye a yar kwanon tangaran na fita waje, na cinye shi tass,  na kuma tasowa lokacin har ta gama, tana fitowa na zauna a kasa, hada min tayi sannan na shiga ci a hankali. Ina lumshe idanuna, ga wani abun dad'in da yayi min, ina gama ci na fara yunkurin amai, a hankali naji yana sauka, sakamakon jin ana min fita tare da jin wasu abu kamar ana shafa bayana.

             Kallonta Zabba'u nayi sannan nace mata.
"Baki ji abinda nake ji ba?"

Cak aka bari, "A'a ranki shi dad'e!" Turo kofa aka yi Munih ce da cikinta, zare ido ta fara yi kafin idanunta ya sauka akan kwanon abincin dauka gama ci, dan na saka Zabba'u munci tare.

       Allah Sarki kamar wata mayunwaciya tazo ta ɗauki kwanon har tana had'iye yawu, dariya ta bani nace mata.
"Ranki shi dad'e! A miki zaki ci ne?" Murmushi tayi wanda ya janyo zuba kwalla daga idanunta, na kalli Zabba'u, nace mata.
"Tashi ki hada mata itama, irin namu da muka ci "

     "Toh uwar d'akina." Ta nufi hanyar kitchen, kallon yadda Munih take zaune a dame ya sani kallonta a fisge, ba laifi Yar buzayen akwai kyau, kome nata me sanyi ce, kawai matsalarta bata da mutunci ne, ba a bin damuwa bane tana gama ci ya kafta mana rashin mutunci, amma dan nutsuwa akwai shi.

         "Aanih Khatoon! Kamar kina da ciki?" Murmushi nayi mata zan ce mata eh sai ji nayi kamar an rufe min bakina, na girgiza mata kai, nace.
"Babu kome!". Shiru tayi sannan ta cigaba da jana da hira ina biye mata, har aka kawo dan wanke ta zauna taci sosai. Sannan ta mike zata fita.

Naji bana son ta fita sake janta da hira nayi har can wani lokaci, sannan muka sauko tare, ganin mu tare da Husnah tayi ya sanya mata wani irin tsoro, dan haka ta kasa boye b'acin rainta. Zama muka yi a falon muna tab'a hira dasu Zabba'u, Haka tazo ta wuce mu, fuu. Kota kanta ban bi ba.

          ...... Ranar da Jay ya dawo a dakin Husnah ya sauka, ban mu san meye ya faru ba, sai kawai ganin shi nayi ya hauro yana huci.
"Meye Husnah tayi muku da kuks hada ta da bayinki suka mata barazanar cewa zasu kasheta?"

Tashi nayi zan mishi magana, ya dakatar dani, haka yayi ta masifar shi, tsabar ya bani dariya, juya mishi  baya nayi, tare da fashewa da dariya. Fincikoni yayi tare da kallon fuskana.
"Ga mahaukaci nan ko?"

    Rike dariyar da nake nayi, sannan nace mishi.
"A'ah Hamma!"
Na faɗa ina dariya.
"Wai meye matsalar ki ne? Dariyar me kike min?"

"Dalla sake ni, kaje an baka aji garau, tare da tafiya birnin dad'i shine zaka zo kana min ihu, Ni babu abin da nayi mata, kuka babu abinda suka mata, idan baka yarda ba ka tambayi Munih!"

"Wacce Munih? Bayan an gaya min kun hade mata kai, keda Muniba, kuka ci mutuncinta."

    "Ka godewa Allah, iya mutuncinta muka ci fa." Na faɗa mishi ina kauda kaina, dan na fara jin haushin sa.
"Ni kike gayawa magana!"
"Toh kayi hakuri!"
Tsaki yayi min sannan ya bar d'akin, zan  ci qaniyar Husnah, dan  gidan su.

...... Fushi Jay ya dauka wai yazo yana magana na mai dashi dan iska, har da kai karana gurin Ummin, kirana tayi cikin fada wai na bata kunya, tayi ta min faɗa akan Jay. Haka bai mishi ba ya kuma hada ni da Mamah Sarah, ita kan bata bi bayan shi ba sai ma tambayar shi da tayi akan me ya faru, yana gaya mata, ta harare shi. Sannan tace masa.
'baka da hankali har yanzu, A madadin ka tara su kaji ta bakin kowa shine zaka yanke musu hukunci kai tsaye.

Ba ayin haka domin ba adalci bane, kuma zan je gidan naci mutuncin kowacce ce munafukar zan mata diban albarka."

      Fadar da tayi mishi ya sashi jin wani abu a ranshi har yake tuninanin dan ba ita ta haife shi ba, dan ko da tayi fadar sai da fuskar shi ta nuna bai gamsu da haka ba,  bayan ya bar gidan ne ya nufi namu..ya sami Munih da Husnah suna faɗa.

            Har suna tana gaya mata cewa.
"Kiyi fatan ki haihu lafiya! Sai kiyi tunanin fada akan mijin ba wai kina nan miji yana juya muku bayan.."
Shiru tayi naja hannun Munih, kawai bazata yarinyar nan ta fashe da kuka, tare da ɗaukar yarta me sunan Mamah Sarah, zata fita daga gidan, kallon ta yayi. Sannan ya zuba mana ido..
"Nagode da kuka ci mutuncin Yarinyar da babu ruwanta."

"An cin kaci namu!" Inji Munih, dariya ya bani, nacewa Munih.
"Muje kici dan wanke, zan yanka miki har da gurji da ganyen latas."

    Juyawa yayi kamar wanda aka aiko shi kaina, zai mare ni. Sai kwashe shi aka yi ya zube a gurin.
"Kafin kayi fada dani, ka shirya da kyau."

Na rike hannu Munih muka haura sama, muna dariya, tun daga lokacin muka manna musu hauka, bawai na jone da Munih dan na cutar da mijina bane, a'a itama tana fada ne akan mijinta, dan haka ba wani shirin azo a gani bane, kawai abin da Bature yake fada nan ne (Fight for Survive) shine abin da muke tsakanin mu da Husnah, ita dan ta bakanta mu a gurin shi. Mu kuma sai muka hada har dashi muka bakanta musu, idan ya ga ina mishi dariya haushi yake ji yayi ta masifa kafin wani lokaci sun sussuta shi, ya zama wani mara hakuri.

Idan aka mishi a fada anan gidan kuma Husnah ta hada shi damu, ba zan mata wani mafarki da nayi ba akan shi, tun da na farka, na taka har dakin Husnah tana ganina ta fara kame kame, sawa nayi Zabba'u, ta daure min ita. Na shiga tambayar ta.
"Meye kuke mishi haka? Me ya same shi kuke sanya shi haushi."

"Ya rabu da kaka na! Idan na haka ba, iya haushi yake yi? Gaba hauka tuburan zaiyi."
" Saketa Zabba! Kika ce hauka tuburan ko?"

     Daga haka na fita a dakin hankalina a tashe, shiga d'akina nayi Zabba'u zata bini nace mata.
"Jeki!"
Juyawa tayi tare da cewa..
"Allah ya huci zuciyar ki!"

  Yana fita na zauna kamar mareniya.
"Ranki shi dad'e! Ciyar dashi suka yi, ta cikin gida can. Saboda nan an zuba nasa an kwashe, ki bamu izinin mu sanya ta tayi magana mana."

    A hankali na d'ago tare da zuba mata ido, sannan na sunkuyar da kai na kwalla na cika min ido.
"Bazlah kina ganin babu matsala."

   "A'ah akwai! Sai dai zaki yi hakuri ne, dan domin kayi nasara sai ka fadi a gaban abokan gaba! Domin ceton rayuwar shi! Dole ki fuskanci tozarci! Shine makarin...."

😪😓😭😭😭 Alqur'an labari ya sauya ku bani shawara Oum Nass na datse musu na gudu 😜🤣  naji ance Dambuje buje 🤨🙄
10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *An san da Allah bai hana damo shan sanda ba*

Tunda na shiga cikin gidan, na sami Munih a tsaye, kallona tayi a sanyayye, har zan wuce ta rike alkyaba ta, had'iye yawun b'acin rai nayi sannan na juya na kalle ta.
"Na san ba zaku dawo ku same ni ba, Aanih ga shi abin cikina bai kai na Haihuwa ba da na bar miki, don Allah ki taya ni, niman gafaran Jay, kuma ki gaya mishi ina son shi sosai, Aanih domin kawo karshen wani labari dole sai an gina wani labari."
Saukowa nayi daga matakalar, na zuba mata ido, tausayi ta bani. Rike hannunta nayi muka wuce d'akinta, na shiga hada mata kayanta. Har na gama sannan muka fito tare ban iya mata magana ba, zan haura sama tace min.
"Kina jin haushina ko? Na san da haka ai, amma idan kika yi hakuri zaki ga rayuwar duniya babu kome a cikin shi sai hakuri da nasara, kafin mutane suyi nasara dole sai sun fad'i, kiji a ranki nasarar da kike son Jay dashi ne ya zo!"

Murmushi nayi sannan nace mata,
"Babu kome! Insha Allah zan dawo na same ki, kin sauka lafiya."
Daga haka na haura sama, ina gama abin da zanyi na dawo na shiga dakin shi na zubawa hotuna na, ido "yaushe aka yi su? Ta ina ya same su?" Abin mamaki bani da mai bani amsa, wasu a Calgary, wasu a Sokoto, wasu ban masan ta ina ya same su ba, yayi yan rubuce-rubuce a jikin shi a hankali na isa jikin wani wanda nayi ana ruwan sama a Calgary, ina rike da lema.
Kasan hoton ya rubuta wata yar karamar kalama.
*SAU DAYAWA BAKA SANIN WAYE ABOKIN RAYUWAR KA, SAI DALILI ME KARFI YA GIFTA KE ALKHAIRI CE AANIH BINT AARYAAN.*
A hankali na shafa rubutun ina kallon yadda yayi wasu rubuce-rubuce a gaban wasu, dama ina haukana ashe shi yafi ni haukacewa taya? Kwalla ce ta cika min ido, a hankali na gama hada kayan, idan nace zan karance wasu kalaman soyayya shaukin soyayyar shi ba zai barni na gama ba, haka na tattaro abun da zan iya na fito muka fita da cikin gidan, juyawa Munih tayi sannan ta kalli gidan, kwalla na zuba daga idanun ta. Rike hannunta nayi sannan fadawan da suke jiran mu, suka kwashi kayan mu. Muka nufi cikin gidan. Na sami Jay kamar yadda na barshi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login