Showing 102001 words to 105000 words out of 119109 words
Chapter 35 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
Jay ya gama da kowa da renin hankali, haka Najim ya kama shi zuwa mota, muka wuce katsina.
---
Bayan kwana uku, ban fahimci shiga da fitar shi ba, sai dai na lura da yau yake son barin Maiduguri, kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Ba dai tafiya zaka yi ka barni ba?"
"Me kika gani?" Ya dawo min da tambayana,
Jim nayi sannan na kuma kalle shi nace mishi.
"Bana ganewa jikina ne, jina nake a daudaure!"
"Alhamdulillah! Baki fara shan ruwan addu'o'in bane, kuma kin ce kina son ki haihu, shine aka baki addu'a ko zamu dace da rahamar Ubangiji."
Daga haka yaja jakar kayan shi, zai fita.
"Tafiya zaka yi?"
"Aanih!" Ya kira suna na a gajiye da tambayar da nake mishi.
"Ki zauna zan dawo."
"Shikenan!"
Nace mishi,sannan ya fita da sauri. Tunda muka shigo gidan ake yawan sauka da sadaka, tare da bani addu'o'in, ban kawo kome ba amma na fahimci kodan cikin jikina ne da nake yawan jin naushin.
.kafib zuwan su Aanih Maiduguri, Jay ya dauki Munih ya kaita gidan Baba Magaji ya bata ruwan addu'o'in, har zasu fito sai yace Jay ya tsaya. Shine ta fita,
Kallon Jay yayi sannan yace mishi.
"Na samo mafita! Amma yana da hatsari!"
Cikinr zakuwa ya kalli Baba Magaji yana jiran me zai ce mishi.
"Ka nisanta Aanih da Daura, Insha Allah za'a dace, idan akayi addu'o'in ranar jumma'a, yau Litinin, gobe ya kamata kubar garin nan, amma kuma idan ita ta rayu kai zaka mutu! Idan kuma kai ka rayu ita da abu cikin sun zama fansa daga abinda aka yiwa Ziryana!"
Wani irin zufa ke karyo mishi, kafin yacewa Baba Magaji.
"Na amince?"
Da haka ya fito, daga cikin gidan suka dawo gidan su, Jay ya kasa barci domin sintiri yake tsakanin dakin shi da falo.
Shigowar Husnah dakin Munih yasata mik'ewa, tana kallon ta. Murmushi Husnah tayi, sannan ta ajiyewa Munih wani abu tace mata.
"Ranar jumma'a, zaki yi amfani dashi, domin raba Jay da Aanih. Idan kika ki kuma kece zaki rasa shi ne na rigana da na same shi!" Daga haka ta fita, Munih bata tab'a abun ba, kawai dai ta cigaba da kallon abun har gari yawaye, daga nan ta samu ta fita da abun zuwa gidan Baba Magaji.
Ta samu bayanan, dan haka ta dawo dashi, sannan ta maidawa Nanah abinta, yawan ganin Jay yana cikin damuwa yasata bin shi har falon shi ta zauna a kusada shi.
"Jay! Nasan nayi maka laifi amma ka gaya min halin da kake ciki ko zan iya taimaka maka?"
Ajiyar zuciya yayi sannan yayi wani miskilin shiru, kafin ya shiga gaya mata halin da suke ciki, rike hannun shi tayi cikin nata, tace mishi..
"Bafa abin damuwa bane! Kawai kai ka dami kanka, Insha Allah Ubangiji zai kawo mana mafita, ai kun dace da Aanih, kawai ka ji a ranka kana tare da Aanih ka."
Daga nan ta koma d'akinta tayi ta kuka, sabida tana jin abun da zata yi shine zai iya bawa Jay da Aanih daman cigaba da rayuwar su, dan haka ita ta kasance a tsakanin su babu wani riba sai faduwa, haka ta kifa hannun ta akan fuskarta tayi kuka kamar ranta zai fita,. Washi gari da zasu bar garin ta sami Aanih tana rokonta ta nima mata yafiyar Jay..
Bayan koma gidan su Mamah, tana kwance tana shafa cikinta, tana kallon agogon bango, takwas, da rabi na safiyar Jumma'a, dan haka ta mike tare da shiryawa cikin doguwar rigar fari, ta cewa Mamah Sarah zata taza ta gaida Baba sarki da Umma.
Tana fita ta wuce gidan Baba Magaji, inda ake ta Addu'o'i. Tana zuwa ta wuce dakin Baba Magaji tasamu yana ta Addu'a,
A can gidan sarautar kuwa manyan motar rusa gidaje ne aka shigar dashi tun daga shashin bayi ake rusa gidan har zuwa kan tsuhuwar bishiyar tsamiyar da take gidan, duk da ana aikin amma motar suna tsayawa, suke tsayawa sabida motar su haka kawai zata kashe kanta dakyar suke aikin.
---
A can gidan Baba Magaji kuwa, wasu abubuwan da ake Munih ta dakatar tare da bashi damar ayi sadaukarwa da ita, duk da yaki amma haka yasa ta bashi hakuri tare da kafewa tace.
"Kayi hakuri kawai kayi dani,".
.duk yadda yaso kar a sami matsala, dole aka samu sabida bukatar da ta bada, ana sakata cikin addu'o'in kuwa inda suke gidan ya shiga zubda jini sosai, kamar ana yanka dabba, Jay yace su cigaba.
----
A dakin Nanah itama kokuwa take da numfashinta, sabida rashin wadatar shi, karshe duk yadda taso fahimtar da mutane halin da take ciki babu wanda ya gane domin mutuwa tayi, .
Haka Zalika Galadima shima a dakin shi ya rasu.
"Zan tafi ba zan kuma wai-waiyar Zuri'ar ku ba, Sai dai kaucewa Aanih Fatimah ta rike Gaskiya ta kuma tsayawa mijinta, dan ya tsaya mata. Ya kuma sota, ina kuma baku hakurin tafiya da Munih. Amma ga yarinyar da ta bari dan bazan iya tafiya da rai biyu ba."
Daga haka Ziryana ta koma cikin madubin da ta fito, tare da ɗaukar wani abu tayi tafiyar, kafin tayi magana lokacin da aka mai da aikin Kan Munih, nakuda ya taso mata gadan gadan, dole aka mai da ita cikin gidan, inda tasha wahala, sannan ta haifi yarta mace yar karama da ita.
Sabida bata kai watanin Haihuwar ba, bakwai kawai takai. Yarinyar tana faduwa ana rufe ganuwar tare da fitar ran Mahaifiyarta. Dama ta faɗa tace.
_Domin karshen wani labarin dole a kuma gina wani labarin_.
Labarin ta ya tafi, shima Jay yankar jiki yayi ya fadi, tare da aman jini.
Zulum kuwa kama shi Ziryana tayi sannan ta saka shi a cikin wani sunduki, suka kai shi karshen wata rijiya da take can karshen Dafur dab da iyakar Madinatul Noor, iyaka da Birnin kisra, aka saka shi a ciki sannan aka rufe shi, sawa Bazlah tai aka dinga zuwa duwatsu a cikin rijiyar tare da shafe bashi labarin.
Sannan itama Ziryana suka baje a iska, dama ita fansa haka take. Sabida buri yana zama a zuciya, da zaran aka samu wanda yaji zai iya tayaka yakin da ka gaza yakan shiga zuciyarka yaji meye kake bukata, meye fatar ka! (Wannan shi ne abinda masana tarihin aljanu da dangogin su suka tabbatar, fansan yana rayuwa ne akan muradin ramuwa.)
Daga nan Dafur suka nime d'aya daga cikin jinin Sarautar birnin suka bashi rikon kwarya kafin a fidda sarauniyar su, dama dayawa basu son Aanih sai gashi an musu iyaka da ita...
---
Ina wanka a ban daki nima na yanki jiki na zube a gurin, ina aman jini, babu wanda ya sani. Sai da Ya kaka taji shiru yazo duba lafiya, suka shigo bude ban dakin tayi ta hango ni kwance babu b'ata lokaci ta fita tare da kiran Gimbiya Zainab, aka tafi da ni asibiti.
Tun da aka kai ni, nake kwancen ban san waye a kai na ba, abun ya dame su, ga jinin da yake zuba. Sheikh Amin Kawu yakewa Jay, yana zuwa yaga irin yadda fatar jikina yake tattarewa ina kara komawa ruwan rawaya, yasa aka yi maza aka mai dani gida. Anan aka cigaba da kulawa dani ana min magani.
--
Daura
Anyi Jana'izar Munih, cikin tashin hankali Jay yake kallon Jaririyar da aka bar mishi, hawaye na zuba mishi, ta tafi ta bar masarautan shikenan haka ya rike yarinyar yayi mata huduba da sunan Munubiya, wanda asalin sunan ta A'isha ne suka boye shi, lokacin da iyayen ta suka ji mutuwar sun dimauta, sosai dan haka suks tawo daga Canada, aka yi addu'ar rana bakwai dasu, da zasu tafi ne suka roki Jay ya basu yarinyar idan ta kara girma ya amsheta, bai hana su ba dan shima zai so haka. Dake da aka yi rasuwar bai shiga gidan shi ba, sai da aka ji kukan Maryam yayi yawa aka shiga aka samu uwarta itama ta mutu, har ta fara lalacewa, amma Allah da ikon Allah inda yarinyar take shan nono, babu matsala, haka itama aka tattara bayan an yafa mata ruwa..aka mata yar Sallah dan wasu sunki yi mata sallah.
Aka suka kai ta, makwancinta..yana dawowa ya dauki yarinyar Jaririyar ya bawa Mamah Raihanah, ta tafi da ita akan idan ta cika shekara biyu zai amsheta.
Haka gidan yayi mishi fad'i babu Munih babu Husnah, Aanih Fatimah Khatoon kuma tana can itama a halin jinya, a lokacin da kome ya faru, dayawa sun fito sun yi korafin abin da Galadima yayi musu tare da barazanar da yayiwa rayuwa su.
Jay ya amsa musu da cewa zai saka a duba Alamarin, Insha Allah zai musu adalci, bayan kowa ya watse a fadar ya rage daga shi sai Najim, kallon Najim yayi sannan yace mishi.
"Aanih tayi kokari! Amma Munih tayi Jahadi! Duk wannan abun ya faru ne sabida kujeran mulki.
.. kowa nason shi, gashi anyi fadar soyayya an kuma yi fadar akan kujeran, Yau gashi bani da damuwa da kowa,.kasan me ya kawo haka, sabida rashin bawa kowa damar yayi abin da yake so! Dan haka zan bawa kowa damar yayi yadda yake so..kasaka hannu a wancan takardan Zan bawa Fadah Waziri na amsa a hannun mahaifin shi.
Kai kuma na baka galadima, na amsa daga cikin gidan su. Sai wani abu da ban sani ba ko zaka amsa, Yar uwata Raihanah da fatan zaka amshi amshi aurenta.
Hikmi na bashi Hanisah, Insha Allah zaku ji dadin haka"
Murmushi Najim yayi, sannan yacewa Jay.
"Amma kai ma zaka."
"Na sani! Akwai Inam! Yar Mamah Jamlah, zasu dawo daga Germany. Yarinyar tunda taga Hotona, take kuka. Har ta kai an nima mata Number na,.yarinya ce karama sha biyar ce, na kuma san Aanih zata fahimci ni."
*Barka da sabuwar gabatarwa Inam🤣*
10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *Kowa ya daka ta wani! Tabbas zai rasa turmin daka tashi*
Sake baki Najim yayi yana kallon Jay, jikin shi a matukar tsora ce, ganin babu karya a maganar da yake yi ne, yace mishi.
"Ni babu ruwana! Kaje ka sami su Baba sarki, da Abban ka. Kai ko wata guda ba ayi da mutuwar matanka ba ka fara tunanin aure, irinku ne suke jawo mana iftila'in rayuwa a gurin matan mu, ban isa ba kaje can kuyi yadda kake so."
Dariyar mugunta Jay ya saka, sannan ya mike suka bi ta kofar baya zuwa cikin gidan, tun da suka shiga falon suka kuma gaida iyayen su, sannan Jay ya Zungure Najim, Najim ya girgiza mishi kal.
Jay ya kuma tab'a Najim, ya kuma girgiza mishi kai, duk suna kallon su, can dai Jay ya ce musu..
"Najim ya zo da magana!"
"A'a bani bane kai ne!"
Sosa kai yayi, sannan ya gaya musu abin da yake bukata,mik'ewa Jaamal yayi tare da Aswad suka bar musu falon da Baba Sarki, wani irin kallo Baba Sarki yayi musu. Sannan ya musu zagin kare dangi kana ya gargad'i Jay da ya bar maganar nan tun a gurin, sannan ya rabu dasu.
.........
Yau wata na shida, ina jinya zuwan jay hudu kuma duk yana fushi,ban san laifina ba. Sai dai haka ya matukar tab'a ni domin ciwon kai da jini ne ya sako ni a gaba, kafin wani lokaci na fara kumburi. Dalilin da yasa aka kira shi. Amma Jay bai zo ba sai da ya gama abin da yake gaban shi sannan yazo, yana gani na yace zamu koma, babu wanda ya hana shi tafiya dani tunda Alhamdulillah na warke sosai.
Koda muka biyo jirgi, haka yayi ta cika yana batsewa, share shi nima nayi, har muka iso daura. Inda na samu Mama Jamlah sun zo da yarta me mugun rawan kai.
Kallo daya yayiwa yarinyar ya shiga cikin nutsuwar shi, sam bata mishi ba. Duk da bai so Munih ba sai dai baya jin zai auri me rawan kai, dan haka ina lura dashi ya fara kaf kaf dani, lokacin da muka isa gidan mu ne naga yayi min fili, babu Munih babu Husnah ko babu kome ai zaka so ka sani abokin sa'in'sa.
Share kwalla nayi d'azun Mama ta bani sakon Munih. Tunda nayi wanka na shiga kitchen na girka mana tuwon shinkafa miyar kuka. Wanda yaji daddawa. Habbatu sauda. Curry da sauran kayan hadi. Namar miyar ma daketa nayi sannan na burgeta a miyar kukan.
Ni daya na a cikin gidan babu kowa, haka na gama aikina na nufi ban daki nayi wanka sannan na fito, ganin shi nayi zaune ya zuba min ido, shi kan shi yayi kewata amma tsabar shariyar ta motsa, kauda kai yayi sannan ya cigaba da latsa wayar hannu shi, ina budar da gashi kaina, kawai naji an karb'a ya shiga busar min.
"A ina ka koyi gyaran gashi?"
Na tambaye shi, daukar mai yayi yana shafa min a kaina, a sannu Yaren shi ya shiga sauyawa. Karshen shariya dai ya tafi domin kamar zautacce haka ya koma min.
Sai da ya gamsu dani sannan ya koma gefe ya rungume ni yana shafa bayana, dan ma cikin jikina ya takura shi, amma ya samu nutsuwa sosai.
"Kin san me?"
"Sai ka faɗa!"
Wani shiru ne ya gifta a tsakanin mu, sannsn yace min.
"Wallahi naso kara aure!"
Wani abin naji ya tsaya min, a makoshi na shiga kokuwar cire numfashina sai da ya fahimci haka ya d'agani, tare da jinginar dani a allon gadon.
"Ban fa yi auren ba! Irin wannan kishin! Don Allah rufa min asiri babu aure a yanzun tunda wancan tsohon sarkin yana raye toh baki da matsala."
"Idan ya mutu ina da matsala kenan?" A rud'e ya mike tare da rikicewa, ya ma rasa yadda zai min bayani. Kafin ya min bayan yadda na yarda.
.... Yarinyar tana zuwa tayi ta min hauka da shirme, amma ban tab'a damuwa ba, saboda yarinya ce karama, kuma tana fama da fallin balaga, kanta hayaki yake, idan ta shigo kitchen ta dinga min bude bude.
Irin dai abun da mutum zai maka ya gundure ka, haka tayi ta min, ni kuma ina jin kunyarta.
---
Yau za a saka ranar bikin su Najim, na shirya da wuri, zan tafi gidan sai gada sanye da wata fitinannen gown, ta zuba kwalliya ni kuma ina daman taimaka mishi da links yana tsaye, kawai Yarinyar nan ta danno mana d'akin.
Juyawa nayi ma watsa mata harara, nace mata.
"Dan gidan ku, haka ake zuwa cikin gidan mutane? Fita idan na gama mishi..."
Rike hannuna yayi, na d'ago kai ina kallon shi, a hankali ya zare hannun ya kai tsakanin cikina zuwa k'uguna, tare da kara janyo ni jikin shi, cike da mamaki kawai naji bakin shi a saman nawa, wata irin ajiyar zuciya na sauke tare da rike kwalar rigarshi, muna kallon idanun juna.
..... Kafin kace me yarinyar ta gudu, dama yau ina lura dashi niman hanyar da zai turmushe ni yake sai ga Inam ta kawo mishi sauki, yau naga kayan haushi kamar zanyi kuka, bayana ciwo yake tun jiya kuma na gaya mishi, sai duba ni da yayi yace wai ba Haihuwa bace da sauransu, aikuwa yana gama ikon shi ciwo na danno min kai.
A daddafe na samu na shiga ban daki nayi tsarki, har shima ya shigo, ganin ina durkushe ban tashi ba ya taimaka min mik'ewar da zanyi kawai naji abu ya tawo min baƙi daya a hankali nace mishi.
"Bari ga wani abu zai sauko min!"
A hankali ya kyale ni aikuwa, na rarrumi kafar shi na matse gam, ina kiran sunan Allah, yana son ya taimaka min amma na rike shi.
"Yawwa yi nishi," ya faɗa min kamar wanda ya zage ni naji kalmar. Haka ina fama yana kira min nayi nishi, karshe da ya ishe ni nace mishi.
"Fita fita! Bana son ganinka, maza waje." Ture shi, a hankali ya riko ni,.muka fito dakin sannan ya dauko matashi ya jera min a bayan, kafin ya fita zuwa dakin shi.
.... .sai da ya gama shirya duk abinda zai bukata, sannan ya dawo dakin, yana kallona. Sai nayi yunkurin zan fita ya koma, yana dawowa ya shiga duba ni a hankali, yana cikin dubawa yaji na fara nishi, lokacin su Karama sun zo kirana wai nazo inji Mamah Raihanah. Zasu shigo ya daka musu tsawa suka juya da sauri.
Suna isa Karama tace.
"Hamma yace mu tafi!"
"A'a koran mu yayi,matar shi tana nish..."
Rufe mata baki Karama tayi, cikin jin haushi. Sannan ta bangaje ta tare da barin falon, dake bata da hankali sai da ta gaya musu abin da muka mata da kuma wanda suka ji.