Showing 114001 words to 117000 words out of 119109 words

Chapter 39 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5470

daina kuka, yazo ya mannu da jikina tare da saka hannun shi a bakin shi, yana kallon su Baabi.

                 
          Gani yake kamar, sune suke bata min rai dan haka ya narke a jikina, kamar wani mara lafiya, karshe haka Baabi yayi min nasiha, sannan suka tafi.
"Maamah!"

Cikin shashekar kuka, na kalle shi.  Kwantar da kanshi yayi  a kafad'a na, yana shafa cikin shi. Jan hannuna yayi tare da daurawa akan cikin shi, janyewa nayi da sauri. Sakamakon jin gargasa har saman cikin shi..

       Zamewa nayi daga gadon, zan nima mishi abinci shima kuma ya sauka daga gadon, ina d'aga kafana yana saka nashi, ina juyawa kawai muka yi karo da shi.

            Shafa cikin shi yayi, tare da kallon abincin. Zama nayi a kujeran jikin gadon shi kuma na nuna mishi bakin gado, nokewa yayi. Naga ya fara kokarin zama akan cinyata. Zubur na mike tare da zare mishi idanu, na nuna mishi bakin gado.

         Kamar yadda nayi mishi haka yazo ya zauna tare da kwaɓe fuska zai min kuka, na shiga bashi abincin yana ci yana tura min baƙi.

      🤦🏽‍♀? Dakyar ya karbi abincin, sannan na tuna ko wanke mishi baki banyi ba, tsawon kwanaki yana kwance.

    Barin shi nayi na wuce ban daki, ina shiga yana bina, a fusace na juyo. Kwantar da kan shi yayi, na juya ina hada mishi ruwan zafi wanda zai yi wanka, Allah yaso ni da arziki, ruwan babu wani zafi sosai.

Jin ina ta haɗa ruwan tare da saka hannuna ina tab'awa, kafin na fahimci me ake ciki sai ji nayi ya jefa ni cikin ruwan.

       A razane na kalle shi, na fita da sauri, tare da Zungure mishi goshi.

      "Ka cire kayanka, wanka zaka yi" na fada mishi.

        "Ka cire kayanka wanka zaka yi" ya mai-maita, takaici ya bani na shiga kukuwar cire rigar, karshe da yaga zan takura mishi ya ya galla min cizo, a hannuna idanuna ne suka cika da kwalla.

    Na kalle shi yana rike da hannun, da hakoran shi.
.wani irin tausayin kaina ne ya kama ni, na zare daga bakin shi ya ture shi ina duba gurin, jingina nayi da bango a hankali na sulale kasa, tare da sake wani irin kuka mara sauti.

           Shima zama yayi a gaba na, yana kallon yadda nake kuka. Shima kuma ya kama kukan.

Haushi ya bani, na mike tare da kallon shi kamar na daka mishi tsawa, sai kuma na shiga kiciniyar cire mishi rigar jikin shi.

       Fisgo ni yayi tare da kallon fuskana, yana murza idanun shi.

      Kallon juna muke, na wani lokaci. Sannan na kuma mik'ewa, na saka cire kayan shi na bar shi da yar gajeren wando.
Nasha wahala kafin nayi mishi wanka, da na gama kuma. Na rasa yadda zan mishi bayanin ya cire wandon shi.  Karshe dai haka na kauda kaina na zare mishi wandon shi, da sauri na daura mishi tawol idanuna a rufe.

              Riga da wando, ruwan sararin samaniya na saka mishi, kalar kayan marasa lafiya,

      Ina gama shirya shi malamar jinya tana shigowa da maganin shi, tana bashi yaki amsa sai da na karb'a na bashi.

        Can ya saka mana rikici, dakyar ya tsaya na bashi ya sha, zuwa wani lokaci ya kama barci, akan cinyata.

        ......
Washi Gari.

       Ya rigani ya tashi, hannun shi ya kai, yana lallubar hannu na. Tare da kaiwa cikin shi yana shafawa, a bisa kuskure na ya kai hannuna saman marar shi, wani irin yanayi muka ji babu shiri na bude  idanuna, ina kallon shi.

    Shima Ni yake kallo, sa sauri na ciro hannuna daga cikin wandon.

               "Hmm!" Ya furta yana kallona.
        Da sauri na mike ba kalli agogon dakin, ban daki na shiga ban kai ga rufe kofar ba sai gashi nan ya shigo.

                 Takaici ya kamani na ce mishi.
"Jay don Allah fita."

"Jay don Allah fita!" Ya faɗa min.
Tsaki naja shima kuma yayi.
Mik'ewa nayi tare da turo shi waje, na rufe kofar.

     Ina tsaki, sai da na gama uzurina, sannan na fito.

           Kallona yayi har da sauke ajiyar zuciya, idanun shi yayi jajjur. Alamar zai fara kuka..
   Kai shi nayi tare da zare mishi wandon shi, na nuna mishi yadda zai zauna, kamar wanda zan daura shi akan mugun abu na gudu haka ya ririke ni.

   Kwalla ce ta cika min ido, domin hannun shi ya damki, kirjina. Kallon juna muka yi da sauri na buge hannun shi, kallona yayi tare mai da hannun shi kirjina, na kuma make hannun. Kamar zararriya haka ya manna min hauka, nayi ta faɗa. Ni daya na.

        Ko ya fahimci bana son ya tab'a min ne, aikuwa sai da ya barni na manta, kawai naji hannun shi a gurin, cikin wani irin yanayi yake tab'a min su. Zabura nayi dan yadda yake tab'a min ko lokacin da yake da cikakken hankali bai min irin wannan tab'awar har cikin jinin jikina nake jin hannun shi a gurin.
     Dakyar na kwace kaina a hannun shi.

   Na juya mishi baya, kwalla na zubo min. Hannun shi ya kai tare da dafa kafad'ana, cire hannun shi nayi tare da cewa.
" Ka rabu da ni! Tunda baka jin magan...."

      Cak ya na had'iye maganar, rungume ni yayi tare da saka kan shi a kafad'ana zuwa wuyana, ina jin saukar hawayen shi. Tausayi ya bani na janye jikina daga gare shi, na matsar da shi gefe.

.a hankali na nuna mishi abin da nake bukata, bawai yayi bane, domin kuwa ya sani kuka yafi sau goma, kafin muka fito.

    .kuma bai yi kome ba, muna zaune dashi kawai naga yana matse cinyar shi, kallon shi nayi, cikin fargaba, a hankali na kai hannuna tsakanin cinyar shi da sauri na cire, sabida wani abu na daban da naji, na zuba mishi , mik'ewar da zai yi kawai ya fara saka fitsari a jikin shi. Kai shi ban daki nayi. Tare da jan kunnen shi na zaunar dashi bayan na cire mishi wandon shi nace.
"Idan kana jin fitsari kace min zaka yi wiwi! Idan kuma zaka yi!"

      Shiru nayi sabida ya taso ko gama bukatar shi bayi ba, na zuba mishi ido, garin diban ruwa na wanke mishi jikin shi, muka fara kokuwa, sai da ya buge ni,  dakyar ya wanke jikin shi muka fito bayan nayi alola shima yayi, sallah kan Sai godiyar Ubangiji.

        Domin kuwa, bayan na idar haka yayi ta bankauran shi, muna idarwa ya kamo hannuna zai kai cikin shi. Nayi maza na kwace tare da dalla mai shi harara. Sunkuyar da kan shi yayi,
Na mike tsaye..kamar jirana yake ina mik'ewa ya mik'e.

       Yana biye dani, har na hada mishi ruwan zafi, na ajiye na fara kokarin cire mishi maganin da zai sha. Ban san me ya faru ba sai ji nayi an watsa min ruwan zafi a jikina ya sake kofin a kasa ya fashe, shi kuma ya rike bakin shi da hannun shi.

Juyawa nayi na kalle shi, takaici ya hanani magana, haka na tattara kofin, haushin sa yasani kin bashi maganin, na cigaba da hada nawa, ina gamawa na koma gefe ina sha ina kallon yadda yake wangale bakin shi, hawaye na zuba mishi.

.. sai da na karya da ruwan shayin sannan shima na hada mishi nasa. Ina bashi yana zubda rabi a jikina yana shan rabi. Koda ya gama sha, nazo bashi magani nan ya kwara min amai, dai dai shigowar su Baabi.

            Tashi nayi na shige ban daki raina yana kara b'aci, dakyar na fito,  na same shi ba zaune a bakin kofar, yana jin na buɗe ya mike da sauri zai sure ni na. Dakatar da shi da sauri, dan dole ya koma gefe tare da rab'ewa. Yana kallona a sace.
.. can ya kama kuka, irin kukan nan me shegen ban haushi, dakyar na samu yayi shiru, bayan na zauna ya daura kan shi akan cinyata, can ya fara barci.

    Fita suka yi ban san ya aka yi ba, sai gasu da takardun wai nan da wata uku za a kuma mishi aikin, amma an sallame mu.

            Kamar na daka tsalle dan murna, na shiga hada kayan mu, duk inda nayi yana bina, har na gama muka fito, dan sun ga dacewar mu koma gida, babu amfanin zaman nan ɗin, tunda aikin sai nan da wata uku..kuma za'a ta kashe kudi ne.

          Masaukin su Baabi muka koma, tun a bakin kofar mashigar yaga wata mata, sanye da irin riga me bayyana kirjin nan, Allah yasa idanuna suna kan shi, kawai kafin su Abban shi ya taro shi ya kaiwa matar nan cafka nayi maza na buge hannun.

    Kallona yayi tare da saka dariya, dakyar muka shiga otel din.

     Abubuwan ban haushi Jay yayi shi cikin rashin damuwa, tunda na lafiyar ce ta ishe shi ba.

           WASHI GARI
Tun asuba, muka bar ƙasar, yana barci na tashe shi, dan bama kwanciya guri guda, gudun faruwar wani abu.

     Tunda na samu yayi uzurin shi, muka fito. A tashar jirgin yaga wata yarinya da yar dolinta aikuwa ya saka min rigima sai na saya mishi, haka Baabi suka shiga cikin kasuwar tashan jirgin suka sayo mishi, aka bashi.

       Ana bashi ya saka dariya ya mika min.
"Maamah!" Ya miko min, kamar bazan amsa ba na karb'a na duba, matsowa yayi jikina ya daura yar dolin akan cinyar mu dake manne da juna, sannan ya daura kanshi a kafad'ana.

     "Maamah!" Kallon shi nayi, ya kuma kirana "Maamah"
"Ki amsa mana, mahaifin shi bazai ji dadi ba."
.d'ago kai nayi na kalle shi nace mishi.
"Meye ne Jay?"
"Ki amsa mana mahaifin shi ba zai ji dadi ba"
"Toh kayi hakuri, ba zan kuma ba."

     Dariya yayi sannan yace min.
"Toh kayi hakuri bazan kuma ba"

Jan kumatuna shi nayi tare da cewa.
"Yaron kirki"

Ja min kumatu yayi sannan yace min.
"Yaron kirki!"

       Share shi nayi ina zaune can sai ga wata yarinya da roban guguru, tana ci. Yana ganinta ya fauce.
"Bata kafin na maka bulala!"
Na daka mishi tsawa, tare da zare mishi idanu. Da sauri ya mika mata, kamar na had'iye zuciya ta na huta da ban haushin jay, can muna zaune Baba Aswad ya fita, sai gashi da gugurun, ya amsa yaki yana kallona.

Amsa nayi nacewa Baba Aswad.
"Mun gode!" Shima kuma yace.
"Mun gode!"

       Bude mishi nayi ya kalla, a hankali nasaka hannuna na diba, na fara ci, da sauri ya diba ko nace ya dunbula, ya kai baki. Yayi na farko duk ya watsar a kasa, zai kuma na biyu na rike hannun shi. Tare da nuna mishi yadda ake ci. Babu musu ya shiga duba shima yana ci a hankali. Tausayi yake bani.

  Har jirgin mu ya taso, karshe biyar na safe, muka nufi Dubai daga can kuma muka nufi gida.

  Kafin mu iso gida, raina ya b'aci...
Paid Before read
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *Alhamdulillahi*

Cikin tashin hankali suka nufi Jay, tare da jijjiga shi, ina yayi nisa.
A rikice Najim ya riko wuyar Dr Fatihu, cikin b'acin rai yace.
"Gaya min me ya faru da Anih Fatimah?"
Cikin mamaki yake kallon su, kafin shima ya kuma tambayar su.
"Me kuke nufi? Matar lafiyar ta kalau, yanzun za a fito da ita. jariran biyu aka cire mata, dayan bai fito da rai ba, daya kuma Alhamdulillah lafiyayyen ne. Shine nake shirin muku bayani da."

"Toh ai sigar da kake bayani bai bada ma'ana ba dan ga Jay can sume,"
Dole aka kai Jay dakin da aka dauko Aanih aka shiga bashi kulawa, (Romeo and Juliet) bayan wasu mintuna aka fito da Aanih.

Dai dai shigowar Baabi da Ummin. Suka nufi dakin da aka kwantar da Jay san sunji Jikin Aanih da sauki, shine dai ake tsoron kar wani abu ya same shi.

Sai da aka kwana aka wuni, dan ita Aanih ta farka, Jay ne dai a cikin tashin hankali, sosai suka damu da halin da yake ciki, har zuwa wani lokaci..kafin likitoci suka dukufa akan shi.
......
"Ummi ina Jay? Bai zo ba,"
Na fada a hankali, shafa kaina tayi sannan tace min.
"Yana nan lafiya akwai abinda ya tsayar da shine."

Shiru nayi kafin na kuma kallonta nace mata!
"Jikina yana bani akwai matsala, meke faruwa dashi?"

"Babu komai!" Ta bani amsa a takaice tana goge kwallar dake idanunta, shiru ne ya kuma gifta tsakanin mu. Har Abban Jay ya shigo cikin murmushi ya dauki Yaron, yana jijjiga shi yace mana.
"Allah yasa yayi gadon sunan Takwaran shi, Aswad."

Had'iye yawu nayi tare da kallon yaron, da yake hannun Abba. Ni na zata zasu ce sunan Baabi zasu saka sai kawai naji sunan Abokin Abba.
Share batun nayi dan kar shaidan yayi tasiri a zuciyata, sannan ya kuma cewa.
"Alhamdulillah shima sai da sauki, dan ya farfaɗo yana barci!"
Hannuna nakai baki nace..
"Waye?!"
Dafe goshi Ummi tayi sanan tace mishi.
"Kawu! Baka san yar taka bata san mijinta babu lafiya bane, ai sai ka mata bayani,"
Daga haka ta fita tabar mana d'akin, kallona yayi cikin nutsuwa sannan ya min bayanin halin da Jay yake ciki, goge kwallar idona nayi, sannan nace mishi.
"Allah ya bashi lafiya!"

"Amin Ya Allah," kallona yayi sannan yace min.
"Kingan shi kamar mijinki ranar da aka haife shi, amma shi bai ji dumin jikin uwa ba, don Allah kiyi hakuri dashi, Insha Allah zaki yi nasara a rayuwarki.

Ina miki kallon Jannart ne, banbantata soyayyar ki da ta Jay ba, sabida dukkanku abu daya a gurina, Fatimah zanyi farin ciki idan kika rike min Jay bisa amana da gaskiya, har Abada ba zan tab'a barin shi ya kuntatta miki ba, koda kuwa haka zai sanya nayi fushi dashi.

Fatimah Nagode. Nagode sosai da kawo min shi har gida."

Wani irin kukan farin ciki ne yazo min, cikin jin dadi. Wai ni ake bawa Jay, lallai mata zasu buga mulkin mallaka. Wani dad'i naji tare da sake murmushin mugunta.

Har na shiga duniyar tunani, gani nan dashi yana shiryawa zai tafi fada. Na shigo rike da Yaron nace mishi.
"Saraki!"
"Na'am!" Ya amsa min,
"Toh yau bazaka fada ba!". Cikin wata irin soyayya yace min.
"An gama ranki shi dad'e!"

"Karbe shi!" Naji muryan Abba da sauri na amshe shi, na ajiye shi a kusa dani.

Har Abba ya fita, wani dad'i ya kuma kama ni.

..... Jay bai farka ba sai dare, yana tashi ya zuba musu ido. Cikin karaya yace musu.
"Ta rasu ko?"
Zama Najim yayi kusa dashi ya dan kalle shi yace mishi.
"Toh baban soyayya, kayi wanka kaci abinci sai na kai ka makabarta kaga."

"Zan saɓa maka Najim! Saraki kayi wanka Fatimah da Takwara lafiyan su lau, kaji."

Ya rasa abinda zai ce musu, amma maganar gaskiya yana cewa wani irin yanayi, dakyar yayi wanka da alola, sannan ya gabatar da salollin kan shi, yana idarwa Najim ya haɗa mishi shayi me kauri, ya sha. Ko hutawa bai yi ba, ya mike babu wanda ya hana shi, suka nufi dakin da Aanih take. Cike dakin yake da Iyayen su mata.

Yana shigowa ya tsaya a bakin kofar, cikin nutsuwa ya kura mana ido, ina shayar da jaririn, sai nuna min yadda zan rike kan Yaron Ummi take, farin cikin da yake ran shi ya gaza boye shi, sunkuyar da kai yayi, Duk da yana da wasu yaran Amma yaron da yafito jikin Aanih fansar kaunar su ce.
"Saraki shigo mana."
Kamar wanda aka doke kafar shi ya shigo d'akin, ya zauna. Tare da kura min ido, a hankali kowa ya watse daga d'akin, zama yayi sannan ya rungume ni tare da yaron.
"Nagode!"
Kwalla ce ta cika min ido, nace mishi.
"Shine zaka tafi ka barni!"
Shafa hannuna yayi sannan yace min.
"Gani nan ai babu inda zani, tunda kaunarmu daya ce."

Wasa wasa, Jay ya hana kowa zama a d'akin. Shi ya makale mana, har aka sallame mu. Inda muka koma shashin Mamah Sarah, nan aka shiga bamu kulawa har muka cika sati daya aka yiwa Yaro raɗin suna, ranar inda muke kiran shi da Jaish, kowa sai da yayi ta magana wai da fatan sunan me kadari ne, shiru muka yi bamu kula su ba.

... Bayan suna akaso mai dani Sokoto Baabi yace a barni kawai, kyauta kayan alfarma tare da kyautar arziki na same shi a hannun dangin Maman Jay, har kuka nayi, sabida kayan har mu shekara uku muna amfani dashi, tsabar wasa da kuɗi har da motar wasa wanda sai ya kusan shekaru biyar yana fama dashi ga keken zama, abubuwa dai gasu nan kayan suna nawa da na samu ba a cewa kome.

Domin suna min Son so ne, musamman da suka ga ina son jinin su, kuma bani tab'a ganin laifin shi, haka ya kuma kara min kima a idanun su, koda aka bawa Jay kyautar mata daga gidajen sarautar Hausa bakwai.

Kakan shi sarki Kazeem ya hana su, yace jikan shi ya gode ba zai kara aure ba, dan tsiya yayiwa Jay tare da tambayar shi ko bana wadatar dashi ne da zai amshi wasu matan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login