Showing 42001 words to 45000 words out of 119109 words
Chapter 15 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
na dawo Noorie!"
Cikin wani irin murna tare da ihu tace.
"Ya ce min Noorie."
Aikuwa take masu shela suka fara kara bisa suna fadin cewa.
"Saraki ya kuma kiran Gimbiya Jannart da Noorie haka ya sata farin ciki."
Aikuwa dake ana son karawa magauta haushi aka shiga sake ganguna, jan shi tayi har babban falon tsohon sarki Jalaludeen.
Tare yake da yaran shi tare da jikokin shi, ga kuma Aminan shi, a hankali ya shiga dakin tare da sallama, ya tsaya zai cire takalmin shi.
"Barka da Zuwa Amale!"
D'ago kan shi yayi cikin nutsuwa ya kalle ta, murmushi yayi tare da zubar hawayen, sannan ya cire takalmin ya isa gaban Jaamal ya zuba gwiwar shi a kasa, tare da sake wata irin kuka.
Wanda ya kuma saka kowa a falon kuka, sunkuyar da kai Jaamal yayi tare da tuno Jannart din shi, shekaru Ashirin da bakwai.
Rungume shi yayi tare da ce mishi.
"Ban san yaushe mutumin nan ya koyi kuka ba, dan a sanina baya kuka sai dai ajiyar zuciya."
Murmushi tsohon sarki yayi sannan yace.
" Idan gora tana rawa ba a cika bane, dan haka ban ga jarumi a gabana ba Ragon mata na gani, wanda mace ta sanya shi biyota."
Janye jikin shi yayi daga na Kawu, sannan ya share kwalla da take fuskar shi, ya sake murmushi. Yana shafa kan shi. Tare da kallon kakan shi ya matsa kusa da shi, ya zauna ya kasa magana sai shafa yalwatattacen gashin kanshi yaƙe cikin wani irin farin ciki mara iyaka.
"Yanzun ina Iyayenka na can?" Kakan shi ya tambaye shi.
Kallon Jama'ar dake falon yayi sannan ya sunkuyar da kan shi kasa.
"Nayi rashin adalci, har na dawo basu tsaya nayi sallama dasu ba." Ya faɗa a sanyayye,
Share batun kakan shi yayi sannan ya kuma mai da hankali gurin tambayar shi.
"Me ka karanta?"
Murmushi yayi sannan ya shafa kan shi yace.
"Likitan mata da yara ne Ni!"
"Matakin digiri ko ka kara gaba?"
Gyara zama yayi sannan yace.
"Zuwa mataki na biyu na digiri."
"Kana da ra'ayin aiki ne ko zaka..."
"Yallabai! Bako ne kamata yayi a bar shi ya tafi ya huta da iyayen shi sauran tambayar ya biyo baya."
"Toh Rumanah!"
A hankali ya sallami kowa har Jay wanda Sarah da kanta ta shirya mishi abinci, bayan ya wuce dakin Kawu ya zauna Kawu ya dauko mishi hotunar Mahaifiyarshi. Tare da wasu abubuwan da yake mata hatta Littafin da ta bar Mishi. Sannan ya kuma dawowa dashi wani daki dake can sama kusa da na Sarah ya bashi key din dakin.
Sannan ya bude kofar ya shiga, kome na d'akin a shirye yake.... Ban daki ya shiga,
.---
Buga cinyar shi Ajiya yayi cikin jin haushin kowa, yana huci kamar zai tashi sama.
"Amma!"
"Me zaka ce Sa'i? Amma me? Bayan ka san Yaron nan takaddari ne, sannan mara jin magana ba ma zai tab'a kyale mu ba, bana rena kankantar allura."
"Ajiya me kake son nayi bayan ka gaya maka nima ban san kome ba! Kawai naji labarin zai dawo ne, kuma."
"Kuma ka tura sakarkaru su tare su a hanyar zuwan su ko? Sabida an ce maka Wancan shadanin lauyan zai taso babu sanin abinda ya dace. Kaga bamu da lokacin da zamu ɓata, akan wannan al'amarin kawai kaje zan nime ka."
..jiki a mace sa'i ya mike tare da kad'e babban rigar shi, sanan ya nufi hanyar fita.
---
Abuja...
Zaune nake ina ƙoƙarin shan tea, kiran Hanisah ya shigo min.
"Ke yan mata! Ina Baabi da Ummin tare da Ammih na,"
"Addah ba shi ya kawo ni ba, albishirinki"
Juya ido nayi sannan nace.
"Katon farin goro!"
"Wayyo Hamma Jay ya dawo Wallahi, yanzun haka yana daura."
Idanuna ne suka cika da kwalla, kamar zanyi kuka nace.
"Hanisah ina wasa dake ne?"
Dariya ta saka tare da cewa.
"Malama Addah kin fada soyayyar Hammana, ki min magana cikin da'a in ba haka ba, zan iya."
Hawaye ne ya zubo min kashe wayar nayi tare da sake wani irin kuka, na rasa meke damuna akan shi.
Bude data na nayi tare da duba Hanisah a Whatsp, na tura mata da cewa.
_Bani Number Ummu Rumanah!_
*🤣🙄 akan me zan baki number ta? Kinga malama Addah kiyi hakuri kawai dan na lura*
_😒😠 Ina wasa dake ne wai?_
Na tura mata,
*😡😜🤭 Gayawa keya labarin! Bazan bada ba sai an bani cin hanci*
_🙆🏽♀️🤦🏽♀? Abinda ya kashe kasar mu wannan cin amanar kasa ne! Bazan bada ba_
*🙅🏼♀️Tun muna shaida juna nemi wacce zata baki ba dai Jikar Shehun Borno ba*
_🤔🤔🤔 Yau naga abinda yafi zare tsayi, toh wallahi duk ranar da muka jone dashi Hammanki sai na gaya mishi hassadar da kike mishi dan kar ya sami kyakyawan mace irina_
*Haba? 🙄🤣 Toh maza gaya mishi Addah ina son zoben hannunki nan, shi kawai nake so, sai na tura miki number*
_🤦🏽♀? Kaico kin dage sai na baki cin hanci dai? Toh na baki amma ki duba yana nan a cikin dakina ban tawo dashi ba_
Turo min Number tayi cikin sauri na ajiye shi a wayata, sannan na kuma kirata zuciyata tana bugawa, tana dauka murya na yana rawa nace.
"Hmm! Hmm! Dama ina son magana da Kanin ki ne"
"Toh dan kashe bari na bashi yana falon Abban mu ne"
Cikin sanyin jiki na kashe ina jin wani irin tsoro, yana kamani, can ta kira ki da sauri na .kashe kiran sannan na kirata,
"Gashi nan!"
"Waye kuma Ummu?!"
Naji muryan shi me matukar daɗi ta daki kunne na.
"Jayyyyy"
Sauke numfashi yayi, sannan yacewa Ummu.
"Kinga ban san me wayar ba jeki dashi!"
.kamar na fashe da kuka, na kashe kiran.
Sake kirana tayi, cikin damuwa tace.
"Aanih kiyi hakuri, wai bai gane ki ba!"
"Ba damuwa Rumah ya oga Khalid,"
Dariya tayi sannan tace.
"Muna lafiya,kina Abuja amma baki son zuwa gidana, idan na dawo don Allah kizo"
"Insha Allah, zan zo....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.....
*Kamar Kombo kamar kure!*
"Insha Allah idan kin dawo zan shigo miki da Yardan Ubangiji."
Haka tayi ta jana da hirar, ina kaucewa. Amma babu yadda na iya, har zuwa wani lokaci. Sannan muka yi sallama.
Kifa fuskana nayi a tafin hannuna, na fashe da kuka, me mugun cin rai, sai da nayi ya ishe ni sannan na mike na wanke fuskana.
Sannan na cigaba da zama a dakin dan nafi son zaman dakin sama da zaman waje.
---
Daura.
"Saraki! Baka da kirki amma kasan wacece ta kiraka, amma kake nunawa baka santa ba, Toh Aanih Fatimah!"
Cigaba yayi da cin abincin shi ba tare da ya kalli inda take ba.
"Amma baki da hankali, mutum yana cin abinci kina cika shi da suturan banza." Inji Mama Sarah,
"Kai Mama! Meye laifina dan na tuna mishi ita, Yau kina gani. Shine ta sanadin ta, da bata yi dalilin zuwan shi ba, da babu ku babu labarin shi.
Mama ko da yaushe kamata yayi kina abu babu wani fifiko, sabida shi aka fasa auren ta, yau ta kira tayi mishi Jajjen ya dawo cikin dangin shi sai yaki kulata. Shegen girman kan shi nan zai janyo mishi asara wata rana."
Tana gama fad'ar haka tasa kai zata fita, Mahaifin su ya shigo.
"Mamahna keda waye haka?"
Cike da jin haushi, ta gaya mishi abinda ya faru.
"Amma Ni banga laifin Khatoon ba, dan yarinyar tayi kokari sosai. Kuma ina sha'awan ta shigo gidan nan a matsayin surukata!"
Da sauri ya d'ago kan shi yana kallon Abban shi kafin ya ajiye cokalin. Shiru yayi bai ce wani abu ba. Sai mik'ewar da yayi abin shi.
....... A cikin kwanaki ƙalilan ya saba da kowa, sannan Raihanah tazo daga Abuja ita da sauran yaranta har da Aliyah da yaran ta.
"Yawwa Mamah don Allah kice Abban Jannart ya kara min kwanaki."
"Ina ruwana, lokacin da kika zo kunyi shawara dani ne? Kawai kika bar min wannan janny da shegen farin idanun ta, tayi ta saka min kuka, dauketa kafin nayi mata."
Shigowar Jay tare da Najim yasata zuba musu ido, cikin farin cikin da ta kasa b'oyewa.
Suna shigowa sai ga Jaamal da Aswad suma sun shigo, a hankali tace.
"Alhamdulillahi, naga wanan amintar yau gashi Ƴaƴan ku ma suma sun haɗe kan su. Allah ka jikan Jannart da Rahama, duk wannan aikinta ne."
Shigowar Sarah tare da bayi mata dauke da manyan ture har uku, yasa ta zuba mata ido. Ta zauna a hankali bayan an ajiye tiren, kar'ar wayar Sarah yayi ta dauka tare da cewa.
"Alhamdulillahi barkanku da zuwa."
Mik'ewa tayi tana gyara zaman Alkyabar ta, tana kallon Raihanah karama tace.
"Maamah tashi maza ga Ummin ku na sokoto sun iso, maza kuje ku gyara mata d'akin dake shashina, tare da ke Maman Kawa."
Mik'ewa Aliyah tayi suka nufi shashin Sarah aka shiga gyara, duk sai jikin su yayi sanyi. Sakamakon abinda Jaamal ya faɗa.
"Yau shekaru talatin da bakwai, haduwa ta da Jannart! Ranar da bazan manta ba, mun fito cikin gari daga aikan Baba. Muka same su tana kuka, lokacin da muka tsaya Domin taimakon sun muka kalli juna."
Murmushi yayi sannan ya zuba idanun shi akan kofar shigowa falon yana kallon Rahil tare da Hanisah da Jannart karama, buɗewa Jannart karama hannu yayi, ta shiga tafiya a hankali tana kallon kowa, a hankali ta shiga jikin shi.
Ya mai da idanun shi kan Jikar shi ta fari itama Jannart ce ya kirata, ta mike da sauri. Sai Yar gurin Aliyah itama Jannart ce, ta isa jikin shi sannan ya shiga duba Jannart babba yar aurar shi.
"Aura!" Ya kira ta.
Shigowa tayi tare da Fahad, sai nokewa take.
"Zo nan." Da sauri ta isa gare shi.
Dukkan su, sunan mutum daya suka ci, kallon Rahil yayi cikin kulawa yace.
"Ina Yar Jannart?!"
Murmushi tayi tana goge kwallar da ta cika mata idanu, tace.
"Tana abuja, gurin Kanwar Mahaifiyarta."
Da sauri ya zuba mata ido, kafin ya mai da idanun shi kan Jay wanda jikin shi yayi mugun sanyi kafin yace.
"Me yasa ta tafi can?"
"Tun bayan fasa aurenta, Ikrama yace matukar tana Sokoto, zai ya tozarta ta."
Da wani irin yanayi Jay ya kalle ta, bakin shi na rawa yace.
"Akan me?"
"Kan abin da kayi mata! Dauke ta da kayi ranar auren ta."
Jan numfashi yayi tare da kau da kan shi, tare da mike yana me tauna bakin shi yace.
"Ita ce ta shirya ni kuma na gabatar." Daga haka ya bar falon.
"Kamar kumbo kamar kure! Halin uban halin d'an." Inji Mama Raihanah,
"Toh itama tazo nan ayi bikin dawowar d'an uwanta da ita."
Ba tare da sanin Jay ba, Abban shi ya turo Najim suka tazo da Aani.
.....
Da yamma muka iso Daura, dan haka yan matan suka ja ni zuwa dakin su, yayinda Rumah da Aliyah suka ce na fita cikin su ba zan zauna a cikin yara ba.
Murmushi nayi kawai, nan muka shiga hira, akan wasu abubuwan har lokacin cin abinci yayi.
Sanye nake da jar doguwar riga, muna shigowa suma suka shigo tare da Kamil Mijin Aliyah, sai Khalid dan Mamah Raihanah, mijin Rumah, suka shiga.
Sai Najim, Fahad, Da Shi kan shi Jay din. A hankali yake tafiya suna biye da shi, har inda aka zuba abincin, babban teburin cin abincin.
Tunda muka zauna nake kokarin b'oye yanayin da nake ji a raina, har muka fara cin abincin. Kallon shi nayi lokacin da naji kamar shi tana yawo akan nawa, sai da na kware, murmushi yayi ya cigaba da cin abinci.
"A ci abinci a hankali bazai kare ba."
Kura mishi ido nayi, cikin bakin ciki,, idanuna na cika da kwalla. Mik'ewa nayi yayi maza ya hard'e kafarshi da nawa.
Komawa nayi tare da zama na kasa cin abinci.
"Kici kar ya kare!"
Toshe baki na nayi, tare da barin gurin da sauri kuka yana zuwa min, a hankali nake tafiya. Dake nafita daga gidan, duhu ne a gurin.
A hankali nake tafiya ina kuka, daga nesa na hango wata mace tsaye, tsigar jikina ne ya mike.
A hankali ta fara tafiya, kamar wanda aka sani dole sai na bita, har muka kusan barin masarautan, ji nayi an dafani wani irin tsoro ne ya kamani tare da sake wata irin kuka da ajiyar zuciya.. kamshin galaxy naji na juya da sauri na fada jikinshi ina me rufe fuskana a kirjin shi. Kuka na saka me mugun karfi jikina yana rawa.
Kasa cire ki yayi a hankali yana kallon yadda na razana,
"Me ya kawo ki nan?!"
Fincike hannuna nayi tare da zabga mishi harara nayi, ina kuka tare da cewa.
"Ba kallon yunwa kake min ba, ace mutum yazo gidan ku kana wulakanta shi."
Juyawa yayi tare da barin na a gurin yana fadin..
"Toh ki koma gidan ku mana"
"Ai ba kai ne ka kawo Ni ba!"
Juyowa yayi tare da takowa gabana, ya zuba min ido.
"Ina son a rayuwata, idan nayi magana kar a maida min!"
"Sabida ka girme kowa? Toh ka tambaya da kyau na baka shekaru shida!"
Takowa yayi ina ja da baya, har na dangana da wata bishiyar durimi.
"Haka nake son naga tsorona a cikin idanun ki, baki girme ni ba! Sabida zan iya sarrafa ki a kowani ɓangare."
Ture shi nayi tare da cewa.
"Tir! Ni ba yar iska bace."
Na rab'a zan.wuce daga gurin shi.
Fisgo ni yayi jikin shi tare da matse ni, ya saka kan shi ta wuyana yana faɗin.
"Waye d'an iska?!"
"Wanda ya tsargu!"
Na bashi amsa.
"Toh bari na nuna miki Iskanci."
Lokaci guda ya saukar min da kasala, cizon shi nayi da mugun karfi sai da ya sake yar nishi, sabida zafin.
Kwace rikon da yayi min nayi zan gudu, ya samun kafa ai kuwa na zube akan kafaffuna. Tare da sake kuka. Kallon hannun shi yayi tare da shafa gurin sabida zafi da azabar da gurin yake mishi, a hankali na mike ya kuma saka min kafa, cikin kuka.
Na fara magana, ina cewa.
"Allah ya isa min! Tunda ban san abinda nayi maka ba, kake ta samun kafa ina Fad'uwa, ba zan yafe maka ba.".
"Ban nemi yafiyarki ba! Kuma sai na rama cizon da kika min."
Zaro idanu yayi cikin tsoro, yadda ya murtuke fuska zaka dauka da gaske hakan ne a ran shi, sunkuyowa yayi Allah ya bani Sa'a na ture shi na kwasa da sauri sauri gudu gudu.
Mik'ewa yayi tare da kwafa, akan sai ya rama abin da nayi mishi.
.....
A cikin kwana biyu mun zama wasu irin abokan fada, kamar wuta da auduga, yana gani na zai ce zai rama cizon shi. Ji min Iskanci sai kace Yaro.
Ranar Juma'a aka yi walimar dawowar shi, bayan an gama nasiha da fadakarwa, kawai Galadima ya tashi yayi sallama tare da godiya, sannan yace.
"Ina farin cikin dawowar Abokina, Jalaludeen ina kuma kara mishi wata kyauta ta musamman, na Jikar da nafi so yar wajen Umar, wato Husnah. Tana gurin Nanah Khadijah. Ku dai-daita kanku."
Zufa ne ya shiga sauko min ina kallon shi daga can sanye da alkyaba ruwan madara wanda yake sirke da zaren gwal.
Kurawa juna ido muka yi, sannan na kauda kaina,
Sunkuyar da kaina nayi hawaye na zuba min, sabida bakin ciki. Kusan har aka tashi ban iya kallon kowa ba. Sai dai an shirya wasan dawakai ne. Kuma shima zai hau dokin.
Bakin ciki ya sani ko zuwa gurin kallon dawakan ban yi ba, na nufi can bayan gidan, na zauna a lambu.
Ina kallon ruwan da ya taru a gurin da wasu manyan agwagi ke wasan ruwan dasu.
"Shiiiiii!" Na juya ina kallon inda nake jin karar, matan nan ce sanye da jajjayen kaya, jini na zuba a jikinta duk inda ta wuce jinin na b'atawa, hannunta rungume a kirjinta, ga kudar zuma bakakke da suke shawagi a kanta.
Kukan doki naji, ya shiga wani irin mik'ewa.
Da gudun gaske yayo kaina, tun kafin ya iso, naja zuwa zuciya tare da zuɓewa a gurin, ban san lokacin da na dauka ba, sai dai na kuma ganin matar ne, a kusada ni tana shafa fuskana.
"Wani lokaci bayyana cutar da take ran mu, itace igiyar farko da take fara illatar mu, ko da kuwa zaka fadawa duniya girman halin da ka wanzu a cikin shi