Showing 21001 words to 24000 words out of 119109 words
Chapter 8 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
inda yake sai ka samu ana girmama shi.
Ina zaune maza keta kawo min hari, ban kula su ba.
"Manyan a ina ka samu iri me kyau haka? Gaskiya ta haɗu."
Bai magana ba, haka suka yi ta magana, yana jin su. Mik'ewa daya daga cikin su yayi zai zo inda nake ya rike mishi hannu.
"Karka fara!"
Komawa yayi ya zauna,
"Toh wacece ita?!"
"Ita din kamila ce! Daga gaban iyayenta na daukota."
Shiru yayi sannan ya mike, tare da mika musu hannu, sannan yazo inda nake ya riko hannuna muka fita, kallona yayi sannan yace.
"Me yasa kike daukar hankalin su?!"
Banza nayi dashi dan bani da amsar bashi, can yace.
"Ina magana kinyi banza dani ke wacece!"
Dake kaina a sunkuye yake, yana tab'a ni ina dungurawa, abin ya dame shi.
Yana kuma mamakin yadda nake wannan abin. Har dawo dani gidan, ya zagayo tare da saka hannun shi zai dauke ni, aikuwa sai ga hannun shi ya sauka a kirjina, cike da mamaki. Ya kalle yadda nake sume ga jinin nan yana d'iga daga hancina...
. Janye hannun shi yake son yi, amma shaidan na mishi huɗubar tsiya, kara tabawa yayi yaji yadda suke, wani irin yanayi yaji lokaci guda, d'ago fuska na. Yana kallon yadda zubda jini hanci da idanu.
.janye hannunsa yayi tare da kaini d'akina, yafita.
Tunda daga ranar, ban kuma ganin shi ba, shigar da yake yi ma, ya daina baya zuwa inda nake.
Sosai na damu akan rashin ganin shi, ga wani irin yanayi da nake tsintar kaina, na tashin hankali.
......
Yau kwana bakwai kenan, ina kwance ya shigo min, hasken wayar shi ya dallara min, sannan ya coge a gefe..idanun shi a kaina.
.."zaki raka ni!"
"Gaskiya indai gidan rawa ne bazani ba, sabida ba tarbiyyar gidan mu bane!"
Takowa yayi gabana, cikin izza ya durkusa tare da haska fuskar mu yace.
"Kalli cikin idanuna! Nace zaki raka ni!"
"Ni bazan."
Fincikoni yayi har jikin shi na rawa ya kura min ido, cikin jin haushi yace.
"Ki tashi kafin nayi.amfani da baiwar da Allah yayi min, na gyara miki zama!"
... Babu shiri na mike ya watsa min kayan ya ficce a d'akin, kuka ne ya kwace min.
Sai da nayi ya ishe ni, sannan na saka kayan, doguwar riga ce har kasa, a hankali na fito daga dakin. Wannan karar da naji na ranar can.
"Shiiii!"
Tsintar kaina nayi da bin inda kar'ar yake fitowa, kawai naji ya fincikoni. Tare da ja na,.muka fita.
Sai da ya jefa ni cikin motar, sannan ya dawo yaja mu, tun a hanyar nake aman jini. Kaina kamar zata yi bindiga, buga motar yayi bayan ya tsaya, cikin jin haushi yace.
"Duk abinda zaki yi, sai kin rakani party nan!"
Babu yadda na iya haka muka nufi, inda suka shirya, shirmen su. Bana jin dadin shigar da nayi.
... Tunda muka shiga, abokan shi suka ja shi can gefe. Wani cikin su yazo ya takura min da surutu. Karshe da na gaji, na silale zan gudu. Ashe sun ga fita na daga dakin party wani daga cikin abokan shi yace mishi.
"Yarinyar da kuka zo ta fita fa! Kuma naga su Ghali sun bita."
Mik'ewa yayi, yaji gabaki daya, bazai iya dogon tafiya ba, komawa yayi ya kwanta a kujeran. Tare da buga kanshi, yana faɗin.
"Yarinyar kamila ce! Ni ne na daukota domin daukar fansan abinda tayi min, taya zan su min haka."
Dakyar ya mike, yana buga kanshi sannan ya fito. Can nesa yaji ihuna, da sauri ya shiga niman inda nake, nan kuwa kokuwa suke dani, daya na kokarin yaga min rigar jikina, daya kuma yana me rufe min bakina.
.... Wani irin kuka ne ya kwace min, cikin tashin hankali na kwala mishi kira.
"Mujaheed!" Sake toshe min bakina suka yi, tare da kai ni kasa.
Allah ya bani Sa'a wanda ya rufe min bakina, na gantsara mishi cizo, sai da yayi ihu, a lokacin Jay ya iso, tare da zama a gaban su.
"Karku mata kome! Domin mata ta ce!"
. Da mamaki suka zuba mishi ido, Ghali ya dauki wata sanda a gurin ya make mishi kai, tare da cigaba da dukar shi, sannan ya tura wanda na ciza, ya dauko musu ruwa.
Zuba mishi ruwan suka yi, sannan suka mike tare da cewa.
"Karka kuma gigin kawota gidan casu, domin wallahi gobe zamu kuma farmata."
... Gyada musu kai yayi, suna tafiya na iso gurin shi da sauri, tare da kallon shi, dake abuge yake mika min hannu yayi da sauri na rarrafa jikin shi ina kuka sosai.
"Jay! Ka kai Ni gurin Baabina, bani da lafiya! Idan baka kai Ni ba wani abu zai same ni!"
D'ago kaina yayi, giya tana gaya mishi wani abu na daban, kafin nayi wata yunkuri sai jin bakin shi nayi cikin nawa, duk yadda naso kwace kaina, na kasa.
Hancina da kunne ne, suka fara zubda jini, kafin wani lokaci, idanuna sun rufe da jinin, saukar da bakin shi yayi wuyana, tare da Binta da wata zazzafar sumbata.
Sai ganin kaina yayi yana reto.
Dakyar ya mike tare da lallubar makulin motar shi, ya kunna, sannan ya nufi motar tare da daukata, shi kanshi bai san inda zai kai ni ba.
Tunda ya ajiye ni a cikin motar, ya nufi gida dani, dakyar ya isa konace Allah ya nufa muna da nisan kwana.
Daukata yayi zuwa dakin da ya bada na zauna, ya kwantar dani, sannan ya fita. Dakin shi da yake da taga ta wajen d'akina, ya shiga. Ko cire kayan jikin shi bai yi ba, ya kwanta.
---
Washi gari! Koda ya farka, a hankali abinda ya faru daren jiya ya shiga dawo mishi.
Ganin har yayi Sallah tare da wanka bai ji muryana ina wasa da Yar Jinjirin Rakumar nan ba, ya sanya shi fitowa. Har tsakar gidan.
Gama kewaye tsakar gidan yayi kafin ya koma inda Innaih take aiki, yace.
"Innaih ina wancan Yarinyar?!"
Cike da mamaki take kallon shi, kafin ta maida kanta, izuwa aikin da take sannan tace.
"Faɗimah ba yarinya bace! Magajin Izzah, kawai jikinta ne da bai nuna alamar girma."
Tanke fuskar shi yayi cikin jin haushin abinda Innaih tace.
"Innaih! Tambayarki nayi ina take?!"
"Allah ya huci zuciyar ka! Barden Damagaram."
Nuna mishi dakin tayi, cikin wani irin Izzah da jin kai, ya nufi dakin, daga shi sai 3 qrt. Ya iso bakin kofar.
Yana turo kanshi sai da ya razana, sabida yadda gashin kaina yayi buzu-buzu, ga Idanuna da suke fidda jini.
Mai da kaina nayi kasa ina gogewa.
"Dama baki da lafiya ne?!"
Banza dashi nayi, na cigaba da goge jinin.
"Ina miki magana kinyi banza dani.!"
...
"Don Allah ka kyale ni! Ka mai dani gurin Dangina, idan ba haka ba. Mutuwa zanyi."
Fita yayi daga dakin, ya nufi dakin shi. Ya shirya ya bar gidan,
Bayan wani lokaci, ya kuma dawowa d'akin. Kwalayen allura da ruwa ya ajiye har ya durkusa zai sanya min karin ruwan. Kawai ya juya abinshi can ya kuma dawowa ya taimaka min tashi nayi kuma na koma zan zub'e da sauri ya rikoni kaina yayi baya.
Cikin tashin hankali, ya dauke ni zuwa dakin shi, ya shiga had'a min, maganin da alluran.
Yana gamawa, ya haɗa min ruwan sannan ya zuba alluran, ya koma gefe yana kallon yadda nake fidda numfashi, jikin shi yayi mugun sanyi. Yana ji a ranshi bai kyauta ba. Sam yana ganin rashin dacewa da ya daukota a gaban ahalinta. Duk halin da ta shiga shine silah
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!
{CIGABA KWARKWARAH}
*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*
Mallakin
Mai_Dambu
Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️
Wannan shafin gaisuwar shi takuce Aunty Mamie da Sister Safiya 😍🌟🤗
SHA BIYU.
Zuba mata ido yayi cikin sanyin jiki, dole ya bata kulawa kamar yadda ya daukota, dole ya ji da lafiyarta, kamar yadda ya daukota.
A hankali barci yayi gaba dashi wanda yake dauke da mafarkai daban daban.
"Zo muje na kai ka, kaga yadda al'ummar da suke jiran ka! Taso kaga yadda kowa ya jima yana jiran zuwarka."
Riko Hannun shi aka yi, ana bude kofar haske ya cika mishi idanu, karewar da yayi kenan ya farka daga barcin.
Jin tarina ya sashi mik'ewa, koda yazo na gama b'ata mishi zanin gadon shi da jini. A rud'e ya kai hannun shi ya riko ni.
"Don Allah ka mai dani gida! Kaji a can suna da maganin da suke min idan ciwon ya tashi kaji Jay!"
Na faɗa cikin wani irin kuka,
Wani allura ya janyo tare da cikawa sannan ya ga yadda nake zare mishi idanu ina shirin kuka, fincikoni yayi tare da matse ni, ya tsikara min alluran, ajiyar zuciya na sauke, tare da janye jikina, zan kwanta.
"Gaya min! Meye ke damunki!"
Shiru nayi ban amsa mishi ba, can ya kuma ce min.
"Me yasa kika zabi rayuwarki sama da ta iyayenki musamman mahaifinki?!"
A hankali nake bashi labarin, yadda na taso tare da kulawar da nake samu, a gurin Baabi, har zuwa lokacin da nayi ta samun rikicin aurena.
"Abinda yasa naki auren Ikrama, ba kome bane sai dan ya kasance, yana niman abinda zai hada auren mu, shi da mahaifinsa tare da kanin Mahaifina, idan suka bashi aurena, zan zame musu wani abinda zasu na aikata mugun nufinsu."
Shiru yayi sannan na cigaba da cewa.
"Nasan Baabina yana cikin damuwa, damu kuma nasan yan uwan shi zasu mishi caaa! Jay "
Na tashi a hankali, tare da matsowa gaban shi nace.
"Shekaru na talatin da uku! Zuwa da hudu! Gashi kaje ka sato ni, yanzun me zan gayawa Baabina, bana son yayi fushi dani!
Kuma bana son ya zarge ni, Jay kana da mugun hali, amma kuma kana da tausayi, ni Yanzun bana son na koma gida ma, nafi son na zauna kayi ta ce min aljana, idan haka zai sanya kasami farin ciki. Jay bana son kana kula...."
Zuba min ido yayi, tare da gyara min gashina.
"Jay! Wai da gaske ni mummuna ce? Don Allah gaya min meye laifina."
"Ban tab'a ganin mummuna irinki ba!"
Ware shanyayyun idanuna nayi kafin na mai da su na rufe, tare da b'ata rai, na tura mishi baki.
"Jay! Baabina yace! Babu kyakyawa irina, ina da kyau kamar Umma Jannart. Sannan ina wasu abubuwa irin nata."
Daga haka na zube a jikin shi, na fara wasu maganganun kananu, saka kunne shi yayi, yaga naja yar bakina nayi shiru, d'ago kaina yayi, yana kallon baki. Mai dani yayi kwance.
Tare da zuba min ido, jikin shi a mace. Har zai mike na rike hannun shi.
"Jayyyyy!"
Komawa yayi yana mai da min gashina baya, kamar zanyi kuka, na riko hannun shi. A kirjina na cigaba da barci, sai da yaga barcin yayi nisa dani, sannan ya zare hannun shi.
Yana me komawa kujeran hutawa, ya zauna yana me nazarin maganar da nayi.
Dole yana bukatar ya mai dani gida, amma taya!
---
Sokoto.
A.S.P Habib Samim talba.
Mari ya kwad'awa Ansaar, sai da bakin shi ya fashe.
"Gaya min! Ina kuka kai Fulani Aanih?"
"Wallahi! Yallabai, ban kaita ko ina ba, asalima ita ce ta nime na sace ta, ko kaza ban tab'a dacewa ba, wallahi iya gaskiyar kenan! Muna cikin haka wani yanayin wani mutum yazo daga kasar waje.
Shine ya bani kudi tare da cewa na bar mishi aikin zai karasa, shi kuma ya cigaba da gaya mata yadda zai shigo gidan da fari ta amince, amma daga baya ta turo min sakon karshe ta fasa, ashe shi bai fasa ba, shine ya shiga cikin gidan a matsayin me gyaran panpo. Iya abinda na sani kenan!"
Shiru Habib yayi tare da gyara yar gemun shi da take kara tsirowa.
Fita yayi daga dakin horon
...... Bayan b'atar Aanih Me girma Gwamnan ya saka aka kawo Habib yazo yayi bincike, garin binciken ne ya samu sakon da aka turo a wayarta, da kuma Whatsp ɗinta, daga nan suka shiga niman Ansaar, suka kamo shi yau sati biyu kenan, suna mishi mugun duka.
---
Lokacin da ya fita daga ofishin su, Fada ya wuce, inda ya samu sarki akan maganar ko yana sane da cewa Yar shi wani tabi ta gudu.
Sunkuyar da kai Aryaan ya, cikin matsanancin kunya da jin tozarci.
.... Mik'ewa kanin shi da suke ciki d'aya yayi zai kaiwa Habib mari.
"Barshi ya fadi gaskiya! Akan yarinyar da ta gama gantali, zaka fara kokarin daukar shi, toh bari na gaya maka, wallahi ba zaka dake shi ba karya yayi muku?
.kawai Aryaan yayi murabus, mulkin a matsayin sarkin Musulmai bai dace dashi ba, sai sarkin mata, tunda bai iya lankwasa yar shi ba, waye zai lankwasa ya biyu.
Dan haka ya sauka daga muqaminsa, dan bazamu cigaba da bin jagorancin sa ba."
Mik'ewa Naufal yayi Aaryaan ya dakatar dashi, cikin murmushi, me cike da tawwakali.. mike daga kujeran da yake, ya sauka a kai.
Ya kasa cewa kome, sannan ya juya ya bar fadan baki daya. Kallon kallo aka yi tsakanin Habib da Najim wanda Sarki Jaamal na daura ya turo shi domin taimakawa, Sarkin Da wasu bayyanan da ya samu.
Sai kuma yazo ya samu kome ya lalace, cikin mutuwar jiki ya bude bakin shi dakyar yace.
"Habib! A dokar kasa ka taka doka sosai, domin amadadin ka nime shi cikin nutsuwa, kuyi magana kazo ka tadda husuma wanda dokar kasa ta haramta haka."
"Malam Lauya! Bazaka koya min aikina ba, dan haka abinda doka ta bani nayi, dan rashin Imani an samu mun kama wani na daban, bayan yasan Yar sh...."
Kifa mishi mari Najim yayi, cikin fusata yace.
"Dan sanda ka mara?!"
Ajiye jakar shi yayi yana nade hannun rigar shi yayi cikin b'acin rai yace.
"Ni a matsayin abokina nake maka magana, dan abu kazan ka, idan aka sami mahaifinka da wannan batun ya zai ji? Kasan wutar da ka hura kuwa! Ina ma da Jalal yana raye, nasan sai yaci Ubanka laada a waje, banza wanda bai san aikin shi ba."
Daga haka duk suka watse a cikin fadar, har da sauran mutanen.
......
Tsaye yake ko kayan jikin shi bai cire ba, yana kallon hoton. Aanih cikin rauni da tausayin wani irin yanayi take ciki, yana yawan jin kewarta da shashekar kukanta.
A baya bayan nan. Yana yawan mafarkin ta, tana mika mishi hannu. Ko kuma tana kwance cikin jini.
Shi yasa tunda ya shigo ya hana kowacce mace ta shigo mishi daki dan bai nutsuwar zuciya.
Kafe hotonta yayi da ido, sannan ya dauki takarda da biro,ya zauna ya rubuta takardan murabus din shi sannan ya koma ya zauna a kujeran hutawa, yana jijjiga kan shi.
Yayi imanin duk inda take, tana cikin kariyar Ubangiji, bai lalata na kowa ba, yayi Imani Allah bazai tab'a barin a lalata mishi na shi ba.
Sake bude ido yayi sakamakon, jin muryan Hanisah tana kuka,. Kallonta yayi tare da mika mata hannu, a hankali ta karaso ta daura kanta a bisa cinyar shi, tana wani irin kuka.
"Baabi kayi hakuri! Insha Allah Didih zata dawo muna da yakinin sace ta aka yi."
Shafa kanta yayi, sannan ya fara magana yace.
"Me yasa kika canza abinda ya faru! Bayan kin tabbatar itace ta gudu da kafarta?!"
"Baabi! Kimar kace na kare! Taya zan yarda a zubda maka ita! Sannan kuma zai iya shafar masarautar? Nasan idan nace musu nasan da kanta ta nime a sace ta, aure zai mata wahala, amma idan na nuna ban san kome ba akan haka, duk ranar da ta dawo.
Ba zata rasa mijin aure ba, Baabi, yaranka maza bi, mu hudu kuma mata,. Baabi dole mu koyi boye sirrin gidan mu, dole mu rufawa kan mu asiri."
"Allah yayi miki albarka! Amma idan ta dawo me kika ga ya dace nayi mata? A matsayin ki na uwa mace!"
D'ago kai tayi cikin damuwa da tashin hankali, tace.
"Baabi! Sabida a wanke ta daga zargi za a iya kaita asibiti ko likitan yazo ya dubata a cikin gidan, a tabbatar da lafiyarta! Shi kenan."
. "Toh madalla da shawarar ki. Jeki zan huta!"
Ya sallame ta, sannan ya cigaba da zurfaffa tunanin shi, da kuma Halin da Babbar Yar shi take ciki.
---
Daura...
"Kawu! Ka rage tunanin nan haka! Don Allah, Insha Allah nima ina ji a jikina abubuwa suna dab da faruwa!"
Juyawa yayi cikin nutsuwa ya kuma dawowa gabanta ya zauna yana kallon ta.
"Sarah! Yaron da na gani ya sace Aanih! Ƙwayar idanun shi sak Na Janny! Kuma babu abinda ya bari, da yanayin idanunta.
Cikin idanun shi, sun kasance irin nata zaiba, sai girman su sak nawa, Ina tsoron kar."
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, don Allah ka daina fadar haka, domin wallahi bana jin kome akan haka, Ni dai karka sa a fara zargin Yaron da bai san kome ba da aikata wani abu."
"Ba haka bane! Abinda nake son."
Mik'ewa tayi ta bar Mishi dakin, haka kawai kullum sai ya nanata abun daya, sai kace akan shi aka fara ganin abu me kama daya, tana fama da ciwon zuciya akan sace Mata Yaronta tsowon shekaru ashirin, amma dare daya ya wurgata da wata damuwa, duk ya diririce ya koma wani irin mutum.
Dan abu kadan sai ya mai