Showing 117001 words to 119109 words out of 119109 words

Chapter 40 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5471

Dariya yayi kawai, dan yasan babu abinda zai cewa yar Guzumar shi(🤣🤦🏽‍♀?)

Watan mu biyar aka fara bikin Yan mata, na rasa inda zan tafi gashi Jay da masifa dan ina cika wata uku ya tadda rigima wai a dawo mishi dani ko yayi aure. Baba shiri aka mai dani.

Fitinanne daren ranar na fadi gaskiya na dan Mamah Sarah ta gyara ni yadda ya dace, nan yayi ta shagalin shi..

Batun Haihuwa kuwa, da kan shi ya saka aka sanya min abun hana daukar ciki, haka yayi matukar bani haushi. Da nayi magana yace wai dan lafiya ta yayi haka.

Dole na hakura aka yi bikin ina domin Hanisah Lebanon aka wuce da ita, Raihanah kuma aka kai ta gidan Najim. Jannart karama kuma aka wuce da ita Kaduna.

Allah Sarki Fahad, kamar yayi hauka, dan ma wanda ya auri Jannart din Habib ne dan gidan Baba Samim, an yi bikin sosai.
..... Juyi nayi sabida gajiyar biki, na zabgawa Jay harara. Sai murmusawa yaƙe hankalin kwancen.
"Tashi ki hada mana ruwan wanka!"
"Jay Ni gaskiya a cire min wannan roban wallahi damuna yake!"
Ajyar zuciya ya sauke, sannan yace.
"Karki damu! Insha Allah gobe zasu cire miki!"

Gyada mishi kai nayi cikin farin ciki, dan Allah ya gani bana son tsarin iyali, shi kuma yace bai shirya rasa ni ba a rayuwar shi. Shi yasa takura aka zo gida ka kwafkuma min (implant) ranar da aka saka min yaga rashin kirki dan fushi nayi dashi sosai na kwana biyu, kafin na sauko.

Dake yasan bai da gaskiya rimi rimi yayi ta bina,ana haka Jay ya tsiro da wata hali, baya zuwa Fada da manyan kaya, sai da suit, anyi magana yace zamanin shi ne, a barshi da sabon tsarin, haka aka barshi yayi ta mulkin shi babu wanda ya damu dashi tunda bawai zai fasa ba ne.

Dangin Galadima ya hana su mulkin anyi juyin duniyar nan ya bada yace suyi hakurin sai yi a gaba amma ba a mulkin shi.

Masarautan ta sami zaman lafiya, da kwanciyar hankali yayi da y'ay'an masarautan suka kasance wasu jigogin jagorancin al'umma, sosai Jay yake amsa lambobin girmamawa daga ƙasashen waje, musamman members na ECWAS, sannan tarayyar Turai sun bashi lamban yabo, na gwarzon Sarki me zaman lafiya a cikin yankin shi.

Jay yana da matukar kokari wajen bawa talakawan shi lokacin shi, yana amsa kokensu. Wanda haka ya karawa mishi soyayyar shi a zukatar mutane.

Har yanzun Ina da yaro daya, nabi Jay akan Yasaka a dubani da kanshi yace min.
"Yan matana lafiyarki lau, nine nake amfani da abin hana daukar ciki, dan haka abar tambayana ko bani da lafiya. So nake Jaish ya cika shekara bakwai, sai ki dauki wani."

Takaici ya kama ni nace mishi.."da girmana zan ta Haihuwa? Kasan wahalar da zan sha nan gaba idan na samu cikin? Dake ba.."

Shiru nayi sakamakon bakin shi ya daura akan nawa, cikin kwarewa da iyawa yake sumbatar, kafin wani lokaci har na manta da fadar da nake mishi, ba laifi ina samun nutsuwar shi, amma ba shi zai hana idan na bashi haushi ya kafta min rashin mutunci ba.

Kai Jama'a Jay sai hankali, Jaish yana niman shekara biyu da rabi, Yaron yana da Hakuri, tun bai da wayo nake barin shi a gurin Mamah, ita take gaya min wai halin Ammin Jay yayi tana da hakuri bata da kwaraniya.

Gata da bata cika son mutane ba, haka Jaish shima baya son mutane.

Bayan shekara biyar cif, Yau ake sunan Raihanah ta haihu sai hidima muke, mu shiga mu fita har mun gama shiryawa Ya shigo min, zai kwanta nace mishi..
"Saraki lafiya?"
"Zazzabi nake ji!". Tab'e baki nayi abin mamaki, yau kusan sati Daya Kenan, kullum sai ya dawo ya kwanta bai da lafiya, abin tausayi da al'ajabi Jay baya. Son warin girki, baya son kamshin turare.

Bayan son magana, ga tashin zuciya. Yayi ta yunkurin amai, ranar nayi dariya da yake lissafo min halin da yake ciki, nace mishi.
"Gaya min gaskiya yaushe nayi maka ciki!"
Duk da yana fama da zazzabin sai da yayi dariya yace min..
"Da alamu kai tunda kece kike lafiya ni ne akwance gaskiya kin gama haihu indai Ni zan cigaba da ɗaukar nauyin laulayin ki, gaba zaa iya cewa Ni zanyi nakudar. Allah hudu sun isa babu Allah yayi musu albarka."

Tausayi ya bani, Jay bai son hayaniyar yara, kota mutane ne sai ya bar gurin, balle ta gidan, tunda aka dawo da Munih ya tattarata ya mikawa Mamah Sarah, Dama Maryama tana hannun Mamah Raihanah. Sai gidan yarage Jaish.

---
Tare da Jay mukayi renon cikin jikina, ko nace cikin mu. Tunda tare ake laulayin,(🤣😹)

Shima tun kafin na fara nakuda aka cire min shi, inda samu Y'a mace, ana bashi bai amsa ba, ya nuna musu kofar ni yake jira. Yana ganin Dr Fatihu ya juya mishi baya, har ya wuce. Yana tsaye bakin shi dauke da suna Allah aka fito dani, ina barci maganin.

....
Bayan kwana bakwai.
Yarinya taci sunan Ammin Jay, muna kiran ta da Jal Pharih, kyakyawar mu, dan kusan ta dauko Jay da Abban shi, har da Umma Rumana, tsohuwa.

Haka dayawa mutanen sun zo suna, (Yo nima dai naga Yan Group din MI! Da Fans din KWARKWARAH! Ana ta dambe da kaza! Lekowa nayi nace kai mata dai ba a barin mu a gurin diban Gara! UmNass tace kedai bari Ai naga sunan har dasu Aaryaan Sultan! Da Neemrah, nace mata Eh ga AMIDUD da Matar Shi tayi Takwara Jal Pharih, Mommy Kautharh ta tab'e baki tace. Oni y'asu Addah Ramlat, Allah yasa karta musu halin Pharih! Kamar kin sani! Inji UmNass! Yan fitilar Hikayata suka ce! Addar mu, don Allah wacece wancan zinariya sai kyalkyali take, dariya nayi nace musu daya me alkyabar itace SAFINAH Ashraf! Wancan me doguwar rigar itace Amrah Sadeeq, Addah Amrah. Zasu kuma tambaya ta nace musu don Allah Mommy Sayyid kiji da Aunty Fatimah Mom Abul, sanan ki taimakawa Sister Maryama kolo da Maman Ummita da ruwa, idan zaki wuce akwai Mama Mai Voice ita da Aunty Sa'a mika musu wancan ruwan sanyi! Sannan na juya gurin Mommy Kautharh nace taimaka min kibawa Naman Abunah wannan kayan sunan)

Anyi shagali sosai, sai dare aka watse duk na gaji wallahi, niman guri nayi zan kwanta, Jay ya shigo wai yana son shayi, haka na wuce dakin girki na dafa mishi, ina kaiwa ya wani langwabe min, ajiyewa nayi zan fita yace min.
"Yan mata! Ko irin na yan gayu bazaki min ba, ki dan rungume ni sama sama!"
Dariya ya bani, nazo na rungumo shi tare da shafa kan shi ina dariya sosai, d'agowa yayi sannan yace.
"Kece sa'ata! Kuma nasara ta yana hade da taki, ban tab'a gani. Mace me kirki irin ki ba Nagode Binta!"

Da wayo da hikima na gudu na barshi,
---
Watan mu uku muka je Sokoto,duk da Jay yana matukar kokarin zuwa duk bayan wata shi, idan bai zo ba ni zan zo da Jaish.

Hanisah tana nan Daura, sabida nan Hikmi yake aikin shi, kuma itama ta haihu yaranta biyu tana renon cikin na uku.

Karama itama yaranta biyu, ne tana goyon na biyun kenan, Matar Fahad itama ta haihu, kuma muna zumunci dashi sosai, karshe naji ana cewa zai Auri Inam, Barka dan har yau bata hakura da Saraki ba, Yarinyar tasawa Dan jinjirin mijina ido,

.... Tunda na isa sokoto, dayawan Yan uwan Baabi da na Mamana kasa hakuri suka yi inda suka fito da halin su a fili, na hassada, wai ai bana zaman dad'i maneji nake, wanda suka zo sunan Jal Pharih suka ƙaryata su, dan sun zo sunga yadda Jay yake makale ni idan na kai mishi abin karyawa ba.

Ban san me yasa mutanen mu. Suke son ganin mace ta samu damuwa a gidan mijinta ba, sun fison kayi ta gayawa duniya mijina bai kyauta min ba, mijina ya cutar dani, Eh akwai haka amma muna biye Alkhairin su mu fidda sharrin su, ban.yabi maza ba amma dayawan mutane suna son jin mace tana kawo korafin mijinta, ba burgewa bane. Akwai damuwa a tsakanin mu, amma bana jin zan iya gayawa kowa. Allah yana sane dani.

Haka na gama kwanaki na na dawo, suna son na gaya musu aibun Jay. Ni kuma nak'i sam, haka ya basu mamaki. Dan dai baki gaya musu kome akan mijina, duk wacce ta matsu ta biyo ni gidana.

***
Bayan kwanaki da dawowa na, muna kwance yake gaya min ai Baban Munih bai da lafiya zai je duba shi a Nijar ko zan je. Cikin jin dadi nace eh.

A cikin kwanakin muka dauki hanyar nijar har da Munih karama, muka je muka gaishe shi, daga nan muka shiga wannan kauyen da muka zauna da ya satone. A dakin muka kwana.

--- bayan mun dawo ne ya dauke mu, muka tafi Umrah.. kwanan mu goma, muna gurin cin abincin, Sai ga Saifullah da matar shi tare da yar shi. Wani saka fuska Jay yayi tun da suka gaisa na kuma gaida matar ya sani dole muka mike, Jay akwai zafin kishi.

Bayan mun dawo daga Umrah. Al'amuran yau da kullum sun cigaba da tafiya yadda ba'a tsammani. Kuma budi yana samu mu, dan Allah ya wadata mu da samu dai-dai fahimtar mai karatu.

Dai dai gwargwadon, akwai bude kuma babu laifi. Ina samu a ta ko ina , musamman haihuwar Jal Pharih, na samu abin da bai tab'a zato ba, dan a ranar Jay ya mallaka min asibitin shi.

......Shi kuma Bana Bulama, ya bani kyautar fili a garin Abuja, tare da wani katafaren gida a garin Lagos, mai martaba sarkin borno ya bani gida da fili, yace a tambaye ni me nake so da filin, nace makaranta a ginawa marayu, Allah yakai ladan ga Iyayen mu mata.

Filin Abuja kuma aka gidana asibitin JaiPhari, Baabina ya kuma bani shawara na fara kasuwanci, inda ya tambayi izinin Jay, akan tunda ina da dukiya ko za a fara min kasuwan ce daga ƙasashen waje, Jay yace ai duk abinda yayi duk me kyau ne.

Haka kuwa aka fara kasuwancin cikin Yardan Ubangiji, sai ga Albarka ta ko ina.

...... Allah ya albarkaci rayuwar mu, ya inda Ni kaina ban yi zato ba, mijina dangin shi na gurin Uwa da na gurin Uba, kamar su lashe ni, dan ban iya son kaina ba, ina Alkhairi sosai.

Mijina kuma ina alfahari dashi, tako ina rayuwa ta mike mana shima mulkin shi babu zalinci....
Yarana sun girma, kuma rayuwar su gwanin ban sha'awa.
Alhamdulillahi nan na kawo karshen Kwarkwarah ( wato magajin Izzah) kuyi hakuri nasan wasu zasu ce bai musu ba, nima wallahi bai min ba.... Amma Insha ALLAH mu hadu a wasu musamman zanen kaddarata... Idan na samu lokaci na fara muku Insha Allah december, idan ban da lokaci zan ajiye Insha Allah mu shiga sabon shekara lafiya kuyi hakuri bana iya rike mutane, duk dadin labari nakan rabu dashi na huta kai ma ka huta... Thank You 🙏🏼💝
Thank You....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login