Showing 96001 words to 99000 words out of 119109 words

Chapter 33 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5468

da yaga na barshi yayi yadda yake so, sannan ya janye daga kaina, yana me sumbtar goshina, riko hannun shi nayi cikin damuwa nace mishi.
"Baka ce min kome ba?"
"Toh Aanih Haihuwa dai ta Allah ce ban isa na baki ba sai idan Allah ya baki.. kiyi hakuri da sauran lokaci."

Haka nayi hakuri tunda bani da abin da zance mishi, amma maganar gaskiya ina son haihuwa sosai.

---
Ana gobe suna da dare, muna kwance shi kam yana dakin Husnah, sai ihun Munih naji da sauri na sauko rike Yaron tayi tana jijjiga shi, Ya rasu.

Ihu ta kuma zata fadi na rike ta.
"Aanih d'azun na bashi nono na shiga ban daki kafin na fito na sami gawar shi, bayan barci nake don Allah waye yayi min wannan aikata min wannan rashin Imani?"

Kallon Jaririn nayi abin tausayi, kai ma sun tab'a ka, kallon yaron nayi sannan na taka har dakin na zubawa kome na dakin ido, a hankali na juya na kalle ta sannan nace mata.
"Baki ba shi ruwa ya sha bane?"

"Wallahi a'a ban bashi ba!" Karb'an yaron nayi..na kalle shi na kuma kallo matan da suke daki, bugawa su Jay kofa nayi dan dole suka bude na gaya musu.

Ina jin kamshin wacce ta kashe yaron amma wallahi babu ita cikin gidan. Juyawa nayi zan fita, ina jin raina na b'aci, har na kai bakin kofa nace mata.
"Kiyi hakuri! Jinin shi ba zai tafi a banza ba sai abin miki hakkinki."

Daga haka na bar dakin,ina shiga na yanki jiki na fadi babu kowa sai Zabba'u da ta biyo bayana, da sauri ta sauka ta kira Jay, lokacin da yazo ma bana cikin hayacina, abu goma da ashirin. Shi abin mamaki ya bashi taya aka yi aka shigo gidan shi aka kashe mishi Yaro ne bayan shi da kan shi ya rufe gidan.

.... Addu'o'in ya fara min, har zuwa lokacin da na sauke ajiyar zuciya. Yana ganin na fara barci ya mike ya fita, haka yayi ta sintiri har asuba, inda ya samu.an shirya Yaron.

Allah Sarki, ba yi sunan yaro na sai Jana'izar shi aka yi. Yaron da yaci sunan Sarki Kazeem, aka kashe shi. Bayan anyi sallah aka tafi kai shi makwabcinsa, suna dawowa suka sami Munih ta fita hayacinta, tayi kuka har ta godewa Allah. Abun tausayi ta kasa magana, gashi ta wahala a haihuwar, shi kan shi sai da ya kusan kuka.

........ Lokacin da ya shigo ina zaune kallon shi nayi ya zabge kisar mummuke ake mishi, sun kasa fitowa su mishi gaba da gaba. Kwantar da kan shi yayi akan gwiwata, yana sauke ajiyar zuciya. Shafa kan shi nayi a hankali nake jin kaunar shi na kara huda duk wata kafar dake jikina.

A sannu na share mishi kwallar da ta cika mishi idanu, nace mishi.
"Saraki! Karka yi kuka! Idan kayi haka nima zan ji babu dad'i."

"Aanih ya zanyi? Bana ganin mutanen da suke min wannan rashin Imani, yanzun zuciyata ta gama karayewa a cikin masarautan nan, kema gaki ba lafiya."
"Karka daka ta tawa! Domin ni na riga da na.." kallona yayi sannan ya rike hannuna ya zauna, buga kofar aka yi, nace.
"Waye?!"
"Ranki shi dad'e! Zabba'u ce! Mai Martaba yayi baki ne."
Mik'ewa yayi sannan ya kalle ni yace min.
"Ina son hutawa amma jama'a ga kuma."
"Kaje don Allah!" Haka ya fita, kawai ina zaune naji kamar ance min naje, babban mayafi na dauka sannan na fita ina sauka naji Baba Galadima yana fad'in.

"Matsalar ka ai tamu ce, da ka gaya mana halin da ake ciki da mun baka shawara domin ina tunanin masu baka shawara basu baka dai dai, sannan ka janye idanun ka da jikinka akan wasu alamarin da suke cikin gidan sarauta domin haka zai iya tab'a kimarka, tun..."

"Tunda mai magana ya san yadda kome yake tafiya ko? Ba laifi bane dan an ba shi shawarar ya janye daga cikin matsalolin masarautar, kuskure a dubi idanun shi ace mishi kimar shi zata zube! Yin haka idan ya kuma faru harshen mutum zan saka a yanke mishi." Na fadi haka ina daga tsaye! Kallona Jay yayi zai min magana na dakatar dashi..
"Ta'aziyar rashin d'an shi kuka zo! Ku tattara ku bar gidan nan ƙafin fushina ya kwace."

Na daka musu tsawa, lokaci guda idanuna suka sauya daga fari zuwa jajjur. Kallon kallo muka yi da Galadima! Ya taso zuwa gabana yace min..
"Sarauniyar Ziryana! Tana tare dake. Tabbas dole ayi ta ta ƙare, baki isa ba!"
Ya fada kasa kasa, dafe hannun matakalar nayi tare da sake murmushin mugunta, yayi yayi ya taka ya kasa, yana tsayar a gabana, karshe durkusawa yayi cike da bakin cikin yace min.
"Nayi mubayi'a,"

"Ku sake shi. Amma kasan da cewa Ni garkuwa ce ga Jalaludeen, ka cigaba da bashi wahala. Idan na fusata ba zai maka Kyau ba."

Da sauri ya fita, zuwa gurina Jay yayi. Jini ya digo daga cikin hancina. Goge min yayi da hannun shi, yana kallon fuskana.

"Fatimah! Duk meye amfanin haka?" Juyawa nayi zan bar gurin ya rike hannuna.
"Me yasa?" Ya kuma tambayana,
"Jay kenan!" Jinin ne ya kuma digowa daga kofar hancina, na juya zan bar gurin ya hauro shima, ya fisgoni na fada kirjin shi kamar zamu fadi.
"Ban cancanci sanin kome ba?"

Sunkuyar da kai nayi sannan na sauke ajiyar zuciya, nace mishi.
"Ina son ka saka ido sosai akan Baba Galadima! Jay zan tafi amma ina son nayi maka abin da zaka tuna dani."

Daga haka na juya da sauri na bar gurin shi, ban san lokacin da kwalla suka zubo min ba, jin hannun shi nayi a cikina, tare da saka kan shi kafad'ana.

..."me kike bukata?" Ya tambaye ni, juyawa nayi na kalle shi. "Ina son ganin Baabina da kanena."

Zuba min ido yayi sannan yace min.
"Bayan su fa?"
"Ina son zuwa Maiduguri."
Hade goshin mu yayi guri guda, yana kallon cikin idanuna, yana faɗin..
"Kece kwarin gwiwa ta, taya ba zan tsaya miki ba, ina tare dake!"
Janye kaina nayi na saka akan kafad'arshi na sauke wani irin ajiyar zuciya, tare da rungume shi sosai.

A hankali ya janye ni, muka koma daki hira da muka bude wanda kusan dukkan labarin mu ne da abun da yake faruwa damu, har muka gama, zan tafi madafi ya biyo ni. Ina aikin yana me kara rikon cikina da hannun shi.
"Jay! Haka zan rayu babu ɗa ko ƴa da kai." Yadda nayi maganar ya sanya shi jin wani irin tausayina juyo ni yayi sannan ya kalle ni cikin damuwa yace.
"Kina son Haihuwar ne?" Murmushi nayi sannan na gyada mishi kai.

"Fatimah! Haihuwa a tare dake akwai mugun hatsari ne! Shi yasa amma zan duba abin da ya dace." Yadda yake a dame ya sani fahimtar akwai matsala, sai na barshi a haka.

.........
Bayan sati biyu, ya shirya min tafiya sokoto, tare da rakiyar jami'an tsaron har tashar jirgin sama.
Bayan tafiya na ne, aka fara shirin aikin ganuwar, wanda Baba Galadima yace ba za a ture ba.

Yadda ya kawo dalilan shi Yasaka mutane suka yi na'am da ra'ayin shi. Jay kamar zai yi hauka, haka ya kirani, bai gaya min ba amma daga yanayin Muryan shi na fahimci akwai matsala, dan haka na shiga bashi hakuri da labari.

Karshe haka ya share batun, nima haka naji batun.

.... Kwana goma nayi a Sokoto, na bi yan uwan da dangina tare da kawayena, dayawan su gani na, ya kashe musu baki, sabida yadda suka ga na sami nutsuwa a rayuwar aurena, babu birkicewa wanda zai nuna damuwa a jikina.
Sai tambayana suke meye Jay yake bani nayi kiba haka, murmushi kawai nake, bana cewa. Sabida Allah ya kawo min mafita a rayuwata, naje gidan su Muhid na gaida Mahaifiyarshi, sannan na dawo gida.

Ana gobe zan tafi Umman Baabi yayi tasaka aka bani maganin mata, (🙈🙊) kamar me ta kuma koda min na sha, sannan ta bani wani na dawo dashi. Gidan mu nan ma Ummi tasaka min gyaran jiki, sai da Ammih ita kuma ta haɗa min duk wani abun da uwa take haɗawa Yarta idan yazo ganin gida.

........ Washi gari aka kuma hada min kome Baabi ya bani kuɗin wai kar na tambayi Jay, naji kewar su Sosai, kasa boye kuka na nayi SOSAI..
*Kuyi hakuri! Insha Allah mun kusan kammalawa!*
10/23/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: _Ansan da wuyar biri ake daure shi a k'ugu_

Tun da muka fito, daga gidan mu za a kai ni tashar jirgin, na fahimci ana bin mu, lumshe idanuna nayi na kwantar da kaina, haka kawai naji wani abu yana haurowa daga kafana zuwa kaina. Bude idanu nayi cikin wata irin murya nace.
"Barde! Tsaya." Kafin mu tsaya sun wuce mu da mugun gudu, "Bazlah, a kona motar da mutanen cikin su"  da sauri Barde ya juya yana kallona, ban d'ago na kalle shi ba nace mishi.

"Muje ko!"  Jiki na rawa ya tadda motar muka bar gurin, muna isa gaba kadan muka ga motar ta kama da wuta,.kauda kai nayi tare da mai da hankali na kan wayar hanuna na turawa Jay sakon abin da ya faru.
     *Wasu sun biyo ni! Amma nasaka an kona min su*
Kira na yayi na .kashe wayar baki daya domin idan bana hayacina bana son a min magana, sai dai Ni na yi maka. Muna isa tashar jirgin sama, Barde da yake tsorace dani ya kwashe min kayana zuwa cikin tashar, daga nan yayi komawan shi gida, tun a hanya ya manta da duk abin da ya faru.

                 .... Bayan jirgin mu ya tashi, naga wasu mutane suna kallona, sau daya na kalle su. Na kauda kaina, har muka iso katsina, na samu Najim yazo dauka na, mutanen nan suna biye damu, kallona daya nayi musu naga sun firgici, haka muka dauko hanyar katsina, suna kallona Najim yayi cikin damuwa yace min.
"Akwai matsala!"

"Kyale su! Zasu mutuwa zasu yi!" Kafin yayi min magana motar ta kwace musu, duk da idanuna a rufe suke sai da nace mishi.

"Ka yarda da abin da na gaya maka?"  Cikin wani irin azzaben tsoro yace min.
"Eh..eah e.h"
"Ka nutsu babu abin da za a maka! Duk wanda yake tare da sarauniyar mu yana cikin kariyar mu." Aka fada mishi haka dai dai kunnen shi. Kamar kan motar zata kwace a hannun shi nace mishi.

"Kiyashin gidan ku ba zan tab'a barin a cutar dashi ba balle kuma kai."

.... Mun iso daura lafiya, cikin nutsuwa, har kofar gidan ya kai ni na fita. Kallon gidan nayi nace mishi.
'"bari a gyara gidan domin akwai ƙura da Datti, zan karasa cikin gidan."

   Gyada kai yayi, sannan ya fito zai bude min kofar na hana shi na bude abuna. Na fita, cikin gida sun yi murnan dawowa ta, kowa yaji dad'in ganina, ni kuma ina kewar mijina, kamar yasan ina nan sai gashi nan, tashi nayi na nufi dakin Karama, sai gashi ya biyo ni yana shigowa na rufe kofar tare da rungumo shi ta baya, juyawa yayi yana kallona.
"Aanih Fatima Khatoon!"
"Na'am Jay dina." Juyo ni yayi yana kallon fuskana, yace.
"Nayi kewar ki!"
Dariya nayi sannan na rike hannun shi na saka a fuskana nace mishi.
"Nafi ka!"
"Anya kuwa? Dubi yadda kika kara kiba! Ni kuma fitinar mutane yana hanani sukuni!"

     "Sabida ka kasa tunkarar Galadima ko? Shine damuwar ka, ba kowa ba, ni bana jin kome, amma babu ruwanka akan abin da zan yi tunda kai ba zaka iya ba."
"A'a! Ke mace ce ba zaki iya dasu ba" kallon shi nayi a nutse, sannan na janye jikina. Zan bar dakin.
"Kace ni mace ce? Toh bari na nuna maka wani abu!"  Fitowa nayi dashi har shashin masu girkin su Mamah amintacciyar baiwar su, da take musu abinci ita na je na tsayawa, nace mata.
"Umma Hari! Bani ladan kisar da aka saki kika aikata?"

A razane ta juyo tana kallona zufa na karyo mata jikinta yana rawa, nace mata.
"Zan kyale ki idan kika gaya min suwaye suka saka ki, idan kuma ki ka ki. Tabbas zan sanya ayi ta zane ki har sai kin daina numfashi."

          Jikinta ne ya dauki rawa, ta mike a hankali hawaye na zuba mata, na kalle ta wani irin tausayi ta bani, saboda bana tunanin kwadayin ne yasata ta aikata haka sai dalili mai karfi.
"Me yasa kika yarda da aikin kisa?"
  Kanta a sunkuye ta zube a gabana ta kuma fashe da kuka, tana fadin.
"Bani da hanyar taimakawa yarinyar da nake rike da ita bata da lafiya, shine na sami Fulani Nanah na gaya mata, ita kuma ta bani aiki ita da Gimbiya Husnah."

                 Kallon Jay nayi wanda yake bayan mu can, naje na same shi, yana kallona nace mishi.
"Mutanen nan sun yi nisan da koda ka kama su baka da hujjar, koda bamu mata kome ba, ina tabbatar maka  gobe ba zata kai labari ba, domin ana bibiyarta, idan namu son faruwar wannan al'amarin dole mu tafi da ita cikin gidan mu."

  ..."ban fahimci abin da kike nufi ba?"
"Hamma Jay!" Karama ta kwala mishi. Da sauri ya juya gurinta kasa magana tayi tana nuna mishi hanya, juyawa nayi gurin Umma Hari, ta kuma sake wani irin kuka, tana me rokona tana faɗin.
"Ki cewa mijinki ya hakura da fada da Galadima, sabida taurin kan shi matar Uban shi matar da ta rene shi itace aka sani na zuba mata gub..." D'aga hannu nayi zan mare ta aka rike hannun.

"Ki godewa Allah da bata mutu ba, sannan gubar ba me tasiri bane, tana shan danyen madara zata amayar dashi, ban da haka."
A fusace na juya ga Mamah Nana, kallon ta nayi. Zan yi magana ta saka min hannu a baki.
"Ki bar ni na d"aga muryana, domin Tass nake na aikata kome. Da alamu kina son dan yaron mijinki, dan haka kiyi kaf kafa dashi kafin fushin mu ya ta'azara akan shi, ke kuma hari. Kamar yadda kika sake bakin ki, haka zaki karasa rayuwarki babu harshen magana."

"Karki kuskura ki mata wani abu dan zan iya sakawa a.."

"Ayi me? Toh bari naga idan kin ji labarin na tura mijinki da uwar goyan shi duniyar mutuwa ya zaki ji, kiyi maza ki dakatar dasu tafiya asibiti domin sunan shi gaw." Rike mata wuya nayi tare da jingina ta da bango.
"Duk wanda ya Kuskura ya taba min miji, sunan shi gawa kuma ki jira dawowa na."

Da sauri na bi hanya da zata kai ni, gurin Mama Sarah na samu ya bar gidan da sauri. Komawa cikin gidan nayi. Na kuma kowa waje da sauri. Kamar Mahaukaciya. Tsayawa nayi na takarkare na fashe da wani irin kuka, tare da zuɓewa a kan gwiwa ta, Bazlah ce ta bayyana da wasu da ban san su ba.
"Sarauniyar ki gaya mana me kike bukata."
D'ago jajjayen Idanuna nayi, wanda jini ya kwanta a cikin su.
"Husnah! Nanah, Galadima! " Ku kai min su baitul azab, karku rangwata musu, ku shayar dasu madarar azaba, ku horasu babu dare babu rana. Kuyi musu mafi munin azaba, wanda zasu Fahimci girman laifin su.

Idan ta kama ayi ta yanka namar jikin su, ana bawa dabbobi suna ce a aikata."

"Mun bi umarninki mun kuma tabbatar zamu aikata."

Daga nan wasu suka suka tashi zuwa cikin gidan, suka dauki Nanah da Husnah, can wasu suka dawo, tare da Galadima.

"Baki son su rayu ne? Ko baki son mahafinki da yan uwanki su rayu? Tunda kin zabi haka bari na tabbatar miki da abin da zan iya aikatawa. Ziryana ki hada hannu dani. Na amshi masarautan. Ni na cigaba daga inda na tsaya."

"Bakin Azzalumin ba zan tab'a baka wannan damar ba, zan saka a sake ka sabida Aanih amma ba zan kyale ka ba."

Daga nan na mike zan tafi, rike hannuna yayi ina juyawa na wanka mishi wani marin da sai da bakin shi ya fashe nace mishi.
"Kul!"
Daga nan na juya abuna.
"Ranki shi dad'e! Zaki iya rufe idanunki, yanzun haka Yariman da Mamar shi sun isa Asibitin kema idan kika rufe idanunki zamu kai ki can."

Gyada musu kai nayi tare da rufe idanuna.
"Mun iso!" A kofar shiga asibitin na ganni, sannan suka tsaya a gurin ba iya su ba, wasu ma dayawa suna. Nan a bakin kofar asibitin, har dakin da aka kwantar da Mama Sarah, a bakin kofar naga Jay a tsaya, a hankali na isa gare shi na kwantar da kaina abayan shi, na sake Mishi kuka a hankali nace mishi.
"Jay naji tsoron kar wani abu ya same ka." Janyo ni yayi sannan ya riko hannuna, yana faɗin..
"Babu abin da zai same ni facce Allah ya rubuta min a zanen kaddarata dan haka ki daina damun kanki Insha Allah kome zai zo da sauki."

Har likitan ya fito, yana kallon mu yace mana Jay yaje, ni kuma na shiga d'akin, na sameta hawaye na zuba daga gefen idanunta, rike hannunta nayi, ta bude ido a hankali ta zuba min su..sannan na tace min.
"Aanih kin zo kema? Aanih masarautan Akwai fitinannu dayawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login