Showing 69001 words to 72000 words out of 119109 words

Chapter 24 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5472

kwailolin ka, ku cinye kanku. Yaro karami da kai sai tsageranci, da rashin kunya."

   Dukar motar yayi, tare da sako kan shi zai fito, na juya da sauri ko tsayawa ban yi ba, dan nasan ba kunya ce ya wadace shi ba.

Ina shiga falon, na sami yan uwan Baabi, suna jirana, ban tab'a fuskantar cin mutuncin irin na yau ba, tare da yan uwan Maamana, sun zage ni tare da min mugun fata, Baabi kan bai ce musu kome ba, burin shi kawai gobe a daura min aure na bar gidan shine fatan shi. Nayi kuka kamar me kusan kwana nayi a zaune sai da asuba na kwanta, shima ban jima ba. Aka tashe ni da wani mugun zazzaɓi na tashi.

Wanda yayi sanadin dole aka hakura da kwalliyar da za a min,

         Na cigaba da kwanciya, ina kwance Ummi ta kawo min abin karyawa sai da ta sani na karya dole ina ci, na fara kwara amai. Lokacin, Aunty Aina'uh ta shigo ita da Aunty Barakah, ganin ina amai kamar hanjin cikina zai fita ya sasu tsaki.
"Abin da ake gudu, gashi nan ta sake mishi jiki ya gama da Ita!"

         "Zazzabi ne kuma haka take zazzaɓin ta, Yarona ba FASIKI bane kamar yadda itama ba fasika bace, kuna da Yara maza da mata me yasa baku tunanin goben su? Me yasa baku tab'a tunanin Fareeda sai kanku?."

Nan suka shiga gaya mata magana, ita kuwa bata kula su ba, ta mai da hankalinta kaina.

        ----
Karfe sha daya aka fara shirin daurin auren, wanda sai da aka fara karanto siga, sannan kuma aka kuma sanar da kuma daurin.

    Kallon Juna Saif da Jay suka yi, kafin Jay ya matso kusa da shi yace.
"Na gaya maka ban tab'a niman abu a gurin Ubangiji ya hanani ba, saboda nayi imani dashi, karfina bashi zai bani ba, da naso bar maka ita! Amma da nasan cewa kana tare da wancan munafukin Kanin Babanta ya sani dawowa na maka dukar da zaku fadi har kasa, ya kaji sigar Jalaludeen D'an Jaamal! Jaamal d'an Jalaludeen, har zuwa kakana na biyu. Ko bazan ya kome da ita ba, zan ajiye ta kamar fitila a cikin gida na. Alhamdulillahi na mallaki Fatimah, na gaya maka baka da rabo a jikinta. *D'an karamin su! Babban su nake*

Daga haka ya wuce gurin mutane, yana mika musu hannu, ana gaisawa, fuskar shi sai fidda annuri yake, kamar wanda aka bashi wata abu bayan Fatimah.
Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *Abokin damo, guza*

Murmushin sa kawai zaka kalla ka fahimci yana cikin farincikina, yana tsaye dasu Najim da Hikmi wanda ya samu labarin auren Aanih Fatimah.

       Daga nan aka suka wuce, wata yar karamar wani Baabi ya haɗawa Jay. Na daurin auren, sosai aka yi wa'azi sannan aka taso.
.....
Ina kwancen Yayar Baabi ta shigo Hajiya hafizah kallon banza tayi min.
"Kinyi asarar rayuwa! Kanin kannin bayanki kika dage aka baki. Toh ki shirya dan matan shi babu jahillai irinki bane, wacce bata da aiki sai son zuciya."

Haka ta gama zage ni tass, tare da mugun nufin akan auren da aka min, wallahi ban fahimci sabida Jay take min wannan diban albarkan ba.

     Bayan fitar ta, na kumshe idanu na, ina jin d'aci a rana. Tare da jin zafin abin da suke min, can naji an rangad'a gud'a tare da kirari, tunda naji haka na fahimci tabbas an shigo da Sadakina ne, kuma tunda naji haka.

    Da gudu Hoor suka shigo dakin tare da janye min bargon suka yi tare da d'aka min duka, suna fadin.
"Sisih gwal na miliyan daya da rabi. Wai waye Mijin nan baki da ya rikita miki lissafi.

          Lallai kin haɗu, waye ma angon ne haka?" Suka tambaye ni lokaci guda.  Wani irin sanyin nake ji wanda ya tilasta ni jan bargon na rufe kaina, ina rawan sanyi.

        Kallon juna suka yi sannan suka fashe da dariya, jin ana buga tambura tare da kakaki, can kuma aka fara busa algaita, ya sasu da sauri, Ni kuwa wani irin kuka ne me ban tausayi ya kamani, tare da sabon zazzaɓi.

                .... Suna sauka kasa, Jay da abokan shi suna shigowa, zuga guda. Domin wasu da safe nan suka iso daga nijar. Dan bai gaya musu auren shi na Daura ba, amma wannan ya gaya musu tun sati daya da ya wuce.

                Aikuwa suka tawo, yanzun haka wasu zasu wuce Daura sabida akwai liyyafan da za ayi a can.

      Tunda ya shigo falon, duk yan uwan Baabi sai da jikin su ya mutu, musamman yadda ya shigo da abokan shi wanda suka kasance yan boko ga samartaka, uwa uba, kyau da haduwa.
Wannan yasa yan uwan mu, shiga hankalin su.

       Haka suka gaida kowa, aka kai su falon Ammih da Ummi, suka yi gaisuwa, kafin suka wuce cikin gida, inda anan suka yi wasa da kuɗi kamar basa so. Domin kakanina da abokan wasa suka tambaya.
"Waye Jay din nan ne?!" Nuna shi Najim da Fahad suka yi.

            Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai yana gyara babban rigar shi.

    "Ai dole Yarinya tayi hauka! Toh munji ka biya sadaki da sisin gwal! Mu kuma bazamu baka ita ba sai ka biya mu, ladan mu."

    Murmushi yayi bai ce kome ba, take Hikmi da Fahad, suka yi magana. A hankali Hikmi ya ciro musu bandiri na dollas, ya ajiye musu.
   
Wani irin guÉ—a suka yi tare da jinjina musu, har zai mike Umman Baabi tace.
"Jalaludeen!!"
... A sanyayye ya d'ago kan shi. Tare da saukewa a kan Umma, sannan ya kuma sunkuyarwa yana sauraron ta.

        "Kayi hakuri! Kayi hakuri!! Kuma nasan Takwara tana da hakuri da nutsuwa,  nasan zaka yi dace da samunta, zai yi wuya ta botsare maka, amma Insha Allah zaka same ta a macen rufin asiri. Macen da zata boye laifin mijinta, zata zame maka garkuwa, a yayinda Duniya ta juya maka baya, nasan halinta ba zata tab'a ketare iyakar da ka shinga mata ba. Ga Fatimah nan ka riketa amana, Allah ya baku zaman lafiya."

        "Amin kowa yacee."  A hankali Najim ya isa gabanta ya ajiye mata yan dubu dubu, har uku. Sannan yace.
"Gashi nan ki kunsa lalle, inji angonki."

          "A'ah Ni bazan amsa ba dan mutum na baku, bance ku mai da.."

  "In dai nida Batul d'aya ne toh babu amfanin ki dawo mana da shi." Ya faɗa a sanyayye. Albarka aka shiga saka mishi,  basu fita daga gidan ba, sai da sukawa yan uwan Baabi da yaran su Alkhairi. Wani abin mamaki kamar yasan basa kaunar shi. Amma yayi ta sawa ana basu kudi.

     Bayan sun fita yaji wayar shi tana kara, dubawa yayi yaga Ummin dauka yayi tare da sakawa a kunne yace mata.
"Barka!"
"Abbalawan kazo Fatimah bata da lafiya fa"
Shiru yayi sannan yace.
"Toh ai gidan.."
"Matar kace da bamu da matsala akan..." Katse kiran yayi sannan ya kalli abokan shi tare da kallon agogon hannun shi yace musu.
"Bari na duba wancan matar." Dake sun fishi Iskanci suka juya tare da cewa.
"Wacce mata??"
Banza yayi da su, ya juya a hankali yana shafa fuskar shi, dan matuƙar ya tsaya zasu mishi maganar banza ne.

           .....koda ya shiga ya samu falon a cike da mutane, cikin tsananin kunya ya koma tare da kiran Ummin shi, turo Hanisah tayi suka haura dakin, ina kwance na dunkule sai rawan sanyi nake.

    .... "Assalamu alaikum!" Yayi sallama, duk da ina son d'aga bargon amma babu karfi a jikina, dan dole na koma tare da rufe idanuna.

   .  A hankali ta ajiye maganin tare da abincin da tasa Habisha ta kawo min, yana tsaye Baabi ya shigo.
"Jay! Kai ma ka shigo ne?"

Cike da kunya ya sunkuyar da kan shi, yana sosa keyar shi. Fita yayi kawai.
"Toh ka duba ta mana, idan kuma za a mata karin ruwa ne sai kayi magana."

   Gyada kai yayi sannan ya matsa jikin gadon, yana ganin sun fita ya koma jikin kofar ya rufe, a hankali ya cire babban rigar shi, sannan ya isa bakin gadon.

   Zama yayi  tare da yaye bargon yana kallon fuskana, a sannu ya kai hannun shi kan fuskana. A hankali na bude idanuna, muka zubawa juna ido. Hura min iskar bakin shi yayi, na kumshe idanu na.

       "Yan mata! Meye na kwanciya haka? Ko baki son Saif ne?" Lumshe idanuna nayi tare da mai da kaina cikin matashin, murmushi yayi sannan ya kuma tab'a wuyana, zuwa kirjina da yake bugawa.

            Kallon shi na kuma yi, kafin na janye hannun shi daga jikina, a hankali ya zare rigar jikin shi, bayan ya cire aninin rigar shi, sannan ya janyo ni jikin shi tare da had'a jikinmu. A hankali yake zame min rigar jikina.
            Cikin sauri na d'ago kaina, tare da kallon shi, sunkuyar da kaina nayi. Sumbatar goshina yayi cikin jin tausayina, yana shafa bayana.

                       Rabani da rigar jikina yayi sannan ya ja bargon ya rufe ni, sannan ya shiga ban daki ya haɗa ruwan zafi tare da dauko karamin tawol ya fito dashi.

...... Yazo ya shiga goge min jikina, tare da kallon jikina. Yana goge min wayar shi tayi kara, dauka yayi tare da sakawa a kunne, sannan ya cigaba da magana yana goge min jikin. Cak ya tsaya.
"Muniba! Idan kika Kuskura kika min rashin hankali, wallahi idan na dawo sai kin koma Canada, ina gaya miki."

       Shiru yayi tare da wurga wayar saman gadon, sai da ya gama goge min jikin sannan ya dauko abincin ya fara bani, ina yunkurin amai, dole ya mike tare da fita.

             Can ya kuma dawowa, ya sanya min ruwa sannan ya ajiye min sauran maganin da zan sha, kafin ya kalle ni, barci na shirin dauka na, yace.
"Bakin ce min wawan Yaro ba? Ki shirya daren gobe zamu raba reni!" Daga haka barci yayi gaba dani.

   Ban farka ba sai karfe uku, lokacin har an gama tattara min kome nawa, sannan aka fita dashi.

        Ina tashi na wuce ban daki nayi wanka da alola, dakyar nayi sallah, ina idarwa na shiga ɗura abincin kamar wacce ta shekara bata Ci ba.

          ----
Tunda ya gama kula dani, ya isa gurin abokan shi, ya uzura musu lallai su wuce Daura, bai tab'a jin son kusantar matan shi ba, sai yau da ya goge min jikina, anan yaji lallai ya dace da zama angon gaske.

      Tunda suka biyo jirgi suka nufi Daura, yake ɗokance da Husnah dan baya ta Munih.

     Koda ya isa, ya sami gidan a cike mutanen borno sun zo, masalaci ya nufa yayi sallah, sannan ya nufi gidan shi, kiran Husnah yayi suka shiga shashin sa.

      Hmmm! Sai da ya zama angon gaske sosai sannan ya fito, suka haɗu da Munih zata shiga dakin shi ya dakatar da ita.

             "Zan shiga naga Uwar me..." Buge mata baki yayin sannan ya nuna mata hanyar fita.
"Allah zai saka min!"

    Bai kulata ba yayi ficcewar shi, tana ganin ya fita, ta shige dakin shi, taga meke faruwa. Aikuwa hango Husnah tayi tana barci tare da sauke ajiyer zuciya. Tsaki tayi tare da barin d'akin. Kamar ta fashe da kuka.

              ........
Yau jikin shi yake a nitse, sabida yaji abin da kowa yake ji, wani gani gani yakewa abokan shi.

    .---
Hudu aka shiga dani shashin Umman Baabi, tayi min nasiha akan zaman aure shiru tayi bayani akan rayuwar aure da ma'aura, musaman yanda aure ya koma a wannan zamanin,
Da tazo magana akan Matar So, kuwa har wani take tayu musu...
MATAR SO SUNANE DA KOWACE KE SON AKIRATA DA SHI
. Babban gishirin Zaman aure Wanda zai kaiki da mallakar zuciyansa tamakar kin wanke kin bashi ne.
1.Hakuri,
2 .juriya,.
3. ladabi da biyayya. Sai kin jure Zaki Iya hakuri Sai Kuma kinada hankuri zakiya may Ladabi da biyayya.
Babban makamin mace agidan miji Kuma sune
ADDUA ADDUA ADDUA DA MIKA LAMARINKI GA ALLAH.
*BABBAN HANYAR MALLAKA KUMA*
1. Iya girki (ba indomie ko spaghetti ba nope
2. Iya sarrafa Shi a shimfida (Iya jima'i) karki/ka zama lusari
3. Iya Magana. Kisan irin kalaman da Zaki dinga furtawa. Iya mu'ala da mutane. Yin adalci kyautata zato da Kuma yin uzuri.
Ta cigaba da cewa.
"A wannan zamanin iyaye muna sakaci da yawa yarinya ta girma har tayi aure baki nusar da ita rayuwar aure da rayuwar da zatayi anan gaba ba, maxan ysnzun basu damu da ki musu, wani abin azo a gani matuƙar zaki riƙe girki iya sarrafa harshe, ya sarafashi a gado, mutunta danginshi maida damuwarshi naki, ki kambama alamarinshi fiye dana kowa,

Karki ce ya cika fushi ko yana da miskilanci a'a ke zaki koya mishi sakewa dake dakuma sauran mutane, Matar fari itace ke fara lalata alamarin namiji duk yanda kika É—aurashi haka zai mike, sannan akwai kura kuran damuke aikatawa, rashin yin kwalliya a gidajenmu sai zamu fita unguwa, zan muku misali dani kaina, na zauna a cikin gidan nan dadda tun kuruciyar mu har girman mu ko jagira banyi nafita dashi toh waye zanwa a waje ? bayan ina da wanda ya ajiyeni namishi,! wannan É—abi'ar tasamu mazauni a cikin zukatar Yarana baki É—aya, idan mace takai mace kuma ta amsa mace babu malamar da zata zauna da ita tace mata ga yanda zatabi da namiji, sabida rayuwarshi kamar na É—an shekara uku ne, da zaran ya tada rigimar shi, sai ki duba dabi'ar karamin yaro ki gani, da zaran ya fara kuka zan faÉ—i a kasa yayita shureshure, a lokacin zai baki haushi kaman ki jibgeshi amma idan kika tuna da, cewa kukanshi kara miki zafin kai zaiyi, niman alewa ko wani abu zaki fara dan ku rabu lafiya,

Toh namiji ma haka yake shi bazai faÉ—i ba, amma zai koma gefe yayita huci idan kina da wayo, a lokacin sai ki saukar da kai ki bashi hakuri, idan kika ga yaki sa shi a gaba kita rarrashinsa, wanda idan kinga zaki iya saka mishi fitinanne kuka shi akawa laifin tuni zai manta da wani rigima ya sauko, toh a lokacin sai kiyi amfani da damar haka ki bashi hakuri dan zai damu shi akawa laifi ke kuma kike kuka, Mata muna da matsala a rayuwarmu sosai bazamu iya rarrashin miji ba amna zamu iya rarrashin mai saida É—an kunne dan yayi mana sauki,, haba mata ina hikimar tamu take ina kwarewar tamu take, tunda Asiyah ta iya bawa fir'auna shawara ya É—auka waye ne mijin naki da bazai É—auka ba,

Ummu Salma an karɓo daga gare a hadisin da buhari da musulin suka rawaito.

Tace manzon Allah yana zama yayi shawari dasu, akan alamuran addini ko, kuma wani yaki, indai manzon Allah zaiyi shawara da matarshi ke wacece da bazaki bawa mijinki lokacinki ba, ina kira gareku mata yan boko karki ce aiki ya hanaki kula da miji, zakiyi kuka nan gaba idan ya auro undergrad, kina ji kina gani zai, mai dake gefe ya saka wancar a gabanshi idan bai yi haka ba toh yar aikin gidanki da kika bar mata gidan ita zai aura, idan mai tunani da tsoron Allah kenan idan kuma aka rasa haka, kina ji kina gani zai na bin yar aikinki suna masha'arsu, ko kuma yaje waje nima, wallahi muji tsoron Allah, wai tsabar rashin daraja a gurin mace mijinta zai raba gurin kwanciya da ita, sabida tana wari da hamami, wai nikam mi kuke shirin zamane matan arewa, tun a gida zaki koya mata gyaran jiki girki tareraya, iya magana, sabida sha'anin rayuwa baki san inda xata zauna ba, amna ina sai dai ki koya mata shan maganin mata, karki manta kishiyoyinki can yayi kyau amma rayuwarta ba kyau, wannan zuri'anmu guda biyu É—aya take cewa.
"Ana surutun Aanih ta lalace, abinda da wasu yaran suke a cikin Zuri'ar waye ya isa ya faÉ—a?

Ko su da suke auren wani kwanciyar hankali suke samu da ake mata gorin taki aure!.
Abin tausayi, sai nayi murmushi sannan nace musu suyi hakuri,

Fatimah karki manta wacece ke? Shin idan kika zauna lafiya a dakin ki, hankalin waye zai kwanta? Idan kika kaso auren ki suwaye zasu miki dariya
Da haka nake miki nasiha ki gyara rayuwar aurenki kija mijinki da danginshi a jiki wani sabon salo wai kuna kiran iyayen miji da ulcer ko hawan jini, a'a kuskure ne, ke zaki rushe dangantsrku ke zaki gini, ina da suruka, naki na saka ido akanta da mijinta, ina da yara mata baxan so nimaa cutar min dasu ba, akan Yan ukuna zan kwaɓe hijab da rigar malamta na gurzawa surukina rashin kirki, dan ni nasan abinda na bashi, idan yace min bata da kunya shi xan fara tuhumq kafin na tuhumeta, sabida karfe ɗaya baya amo sai da wani a kusa da shi, karki manta shi tashi Uwar bata raye sai mahaifin shi,.da matan Ubanshi.

Sannan zaki zauna da yara ƙanana masu karancin shekaru irin naki, shi zaki zauna ki biye musu ne kuyi ta abin kunya, kin san waye mijinki, dan akan laifin mari kawai ya iya wargaza miki lissafi toh idan kuwa haka ce Tabbas idan ya birkice miki zaki iya dakatar dashi.

Toh dole kiyi amfani da shekarunki, na farko kija girman ki, na biyu ki zauna lafiya a dakin mijinki koda kuwa matan shi suna tsaye akanki, zaman shi suke zaman shi kike, ke baki isa koran su ba, haka kema baki isa koran shi ba. Akan me zai saka ki d'aga hankalinki.

Fatimah Aryaan yana bukatar ki nutsu a dakinki, yana bukatar hakurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login