Showing 9001 words to 12000 words out of 119109 words

Chapter 4 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5444

daga wata nahiya tazo, baka ganin tab'a mata kimar karatunta zai shafi rayuwar ahalinta! Jay ka duba magabata, sannan kuma ba mamaki daga ma'aikata, aka turo ta kaga kenan yin haka zai iya tab'a aikinta, kunga ku share wannan batun kawai mu barwa Jay wuka da nama, shi zai iya kome amma kar mu tab'a kimar karatunta, dan dukkanmu nan Abu daya muka ke yi."

        Mik'ewa yayi sannan ya ajiye kudin coffen da suka sha, ya wuce gurin wata motar shi tare da d'aga musu, hannu.

   Ya shiga bai kuma magana ba, yaja motar yayi tafiyar shi.
"Hikmi! Baka da kirki idan kai ne akawa haka ya zaka ji?!"

    "Babu abinda zan ji! Sabida kayan makarantar bata muka zubda, kuma a shashin adalci abinda ya dace tayi kenan! Kuma shima ai Jay din ya sani, kunga mu daina aikata kuskure muna ganin dai-dai ne, dan muna da yakinin zai taya mu yaki! Shi din kamar shugaba ne kamata yayi muna bashi kwarin gwiwar...."
#MI
#HWA
#Mai_Dambu..
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

      Fatan Alkhairi Mommy Sayyid 😍🤣😂 Na gaida Uwar dakin Jay...

SHIDA
Kun gane mu zame mishi  abokan kwarai, domin kuwa wannan ba adalci bane sanya shi yana aikata kuskuren, idan kuna sashi yana aikata abinda bai dace ba. Ya kuke tunanin idan ya hadu da wanda ya fishi hatsabibanci, Jay Amininmu ne, kuma abokin arziki.

    Don Allah kar mu sanya shi yayi kuskuren da zamu yi dana sanin mara Amfani."

Daga haka ya mike ya bar gurin.

......
     Gudu yake sosai, har ya isa gidan su, tun kafin ya isa aka wangale mishi kofar shiga gidan, yana shiga ya tsaya a inda aka tanadar domin ajiyar motoci, kifa kanshi yayi saman motar, yana sauke ajiyar zuciya.

   Cizon bakin shi yayi cikin nutsuwa, yana kuma nazarin abinda zai aikata ga yarinyar nan da taci mutuncin abokin shi.

     A hankali ya kai hannu zai bude kofar ya fasa, tunawa da yayi yau ne, zagayowar shekarar Haihuwar Munubiya, tsaki yayi cikin miskilancin ya bude motar, ya fito bayan ya dauki wayar shi da, kuma yar computer shi ta karatu, ya shiga gidan.

              Yana tafiya, kamar wani hawainiya, tafiyar anayinta ne, Amma cikin wata irin izza da sadaukata, wanda zaka dauka yakai talatin da wani abu ne, a'a kawai kuruciya, ilimi, kyau da nutsuwa suka sanya shi jin wani irin yanayi na rayuwa, amma akan fusakr shi abu daya zaka shaida!

    Shine rashin walwala, wanda kamar dabi'ar shi ce, rashin magana fuskar shi kamar wanda aka zage shi, a hankali ya tura kofar tare da zubawa yan matan da suke falon kyawawan idanun shi, da sauri suka yo kanshi yuuuuu.

      Suna zuwa cikin zafin nama ya kauce musu, aikuwa suka zube a gurin har suna gware da juna.

    Aikuwa suka shiga fada da juna, akan shi. Shi kam har ya haura sama, a gajiye ya shige dakin shi, ya same ta tsaye hannunta hard'e a kirjinta.

         Takowa tayi idanunta jajjur, zata yi magana ya zubar da kayab a saman gado  hannun shi, ya wuce ban daki.

   Kuka ta sake mishi, me mugun cin rai. Bai fito ba sai da ya daina jin sautin kukan ta, sannan ya fito tare da fara kimtsa kanshi, yana gyaran jikin shi shigowa tayi tana kallon shi.

Bai ce mata kome ba, ya zauna ya saka kayan shi a nutse, tunda yasan ba fita zata yi ba, dan dai wandon shi ban daki ya shiga ya saka sannan ya fito.

   Kura mishi ido tayi, sannan ta taso tare da kallon.
"Ya Jay! Me yasa baka damu dani bane? Me yasa baka damu da nayi farin ciki ba, kafi kowa sanin kaine muradina. Ya Jay idan kace na baka kaina a shirye nake nayi hakan don Allah. Ko yanzun kace na amince zan baka rayuwata."

Riko hannunta yayi sannan ya kawo ta bakin kofar shi, yace.
"Ina zuwa!"
Ya rufe kofar da karfi, shi bai san me yasa Munah take mishi haka ba, amma sabida Allah me ke a cikin zina, shi da Allah ya daura mishi kyamar ta, shine mata suke mishi tsiya da ita.

  Sai da ya gama, shirin da sannan ya fito sanye da wata gajeren wando, iya gwiwar shi. Sai riga mai dogon hannu, da hular (facing cap) a hankali yake saukowa, ya hango mahaifiyar su, sam bai san inda Munah ta dauko wasu mugun hali ba.

   Dan yasan Ciki d'aya suka fito, kuma mahaifan su, suna matukar kaunar su, amma tun zuwan Munah biki Damagaran tazo da wata mugun hali, na kafewa sai ya sumbaceta ko ya rungume ta. Wannan kuma duk ba dabi'ar shi bace.

          Zuwa yayi ya kwanta a jikin Maman su, ya kafeta da ido.

    "Yarona! Ya karatun? Da fatan babu matsala."

    Daukar kafar shi yayi ya daura a saman d'an tabirin da aka ajiye dan Kawata falon, narkewa tayi a jikin Maman su, tana me b'are bakinta kamar zata yi kuka, tab'e bakin shi yayi, tare da lumshe idanun shi.

       Idan ka gan shi zata rantse barci yake, amma ina idanun shi biyu.
"Maam! Don Allah ki cewa, Jay ya kai mu inda za ayi party mana."

   "Shiiiiii! Tace mata tare da nuna mata shi alamar tayi shiru zai yi barci, tura baki tayi sannan ta mike tare da buga tabirin ta bar falon, yasan aikinta ne ko bude ido bayi ba, haka ya cigaba da kwanciyar shi.

               Sam ya manta da abinda ya faru, kawai barcin shi yake.

         ......
Washi gari, da wuri ya iso makarantar, yaje ya tsaya a bakin matakalar da zata kai ni tsagayar mu(wato department kenan kuyi hakuri har yanzun muna daular Hausa ce!😍😍😍 Kuma ina kishin yare na)

      Hankalina yayi gaba dan haka bazan iya bada labarin abinda ya faru ba, ko kuma abinda yake gaba na ba, kawai naji kamar ina yawo a tsakanin matakalar ne, kafin na fahimci abinda yake faruwa dani, na fado akan kafana, sai da kashin kafar yace.
"Kasssss!" Alamar ya b'alle kenan!  Rintsa idanuna nayi a hankali na bude su, lokacin hawaye sun fara sauka a idanuna.

           Dakyar wata yarinya ta taimaka min, na mike yana tsaye a kusada mu yana cin alawar chokulet. Dakyar na mike akan kafana na kuma komawa zan zube ta rike ni, wani irin kuka ne ya kwace min.

            Sosai kamar karamar yarinya, nake kukan.
"Idan kina da hankali" daga haka ya wuce abinshi asibitin makaranta aka kai ni suka duba kafar tare da min hoto.

.....
"Amma Jay baka tab'a b'ata min rai irin na yau ba, haba sai kace ba musulmi ba, ka karya musu yar mutane. Insha Allah sai Allah ya bi mata hakkinta." Inji Hikmi,
."toh munafuki dama kai ka fara yabawa da haduwata dan haka sai kaje can ku karata, Nagode Aminin kwarai.

     Kyale wannan banzan Ni dai tunda ka kakkaro min kimata, yanzun zata gane shayi ruwa. Muje yau dole mu sha ruwa."

           Kasa hakuri Hikmi yayi yace musu.
"Akan me zaku cutar da ita?"

       "Kanwar Babarka ce ita? Ko budurwan kace bamu sani?!" Jin Abeel, ran Hikmi ya b'aci ko gaban shi baya gani bai san lokacin da ya wankawa Abeel mari ba, dukkan su sai da suka sha mamaki.

   Kallon su yayi cikin zafin rai yace.
"Wallahi wani ya kuma zagar min iyayena, sai na dake shi na daki banza, kuma muna nan da ku."

Yana fadar haka ya tashi daga inda suke ya dauki jakar shi, cikin kurari, Abeel ya tashi Jay ya mai dashi. Yana murmushi. Amma ran shi a b'ace yake, kamar ana gaza mishi da wuta.

"Jay kyale ni!"
"Barshi mu gani!"
Kallon Jay sauran abokan su, suka yi.

      ----
Ni kuwa ina asibiti, ana daura kafar. Hawaye ke zuba daga idanuna,tsabar azaba da nake sha.

.ana gama daure min kafar muka fito tare da yarinyar da ta kawo ni, sintiri yake tayi muna fitowa ya karaso inda nake yana tambayana.
"Sannun kiyi hakuri!"

Ban kula shi, sai dai ya nace min da bi. Naki magana. Har inda aka ajiye motor da zata mai dani gida, tunda na shiga, shima ya shiga tashi har gida ya bini, ina fita ya tawo.
"Don Allah kiyi hakuri! Wallahi ba halayyar shi bane, kawai akasin kaddara ce da..."

Wani irin kallo ba mishi da jajjayen Idanuna, bai karasa maganar ba yayi wucewar shi.

         Komawa makarantar yayi, ran shi na kara b'aci,Koda ya nufi ajin su an fara karatu. Dakyar aka bude mishi ya shiga. D'aga nesa ya hango Jay tsakiyar yan mata kowacce so take ta tab'a mishi jiki amma yadda ya had'e fuska sai suka kasa yin komai,.

         Bayan an tashi a makarantar, kowa yayi wucewar shi, dan Hikmi mahaifin shi dan kasar Lebanon ne, kuma likita ne.
            Dan haka a guje ya bar makarantar, ya kuma dawowa unguwar mu, ya gama zaman shi, ya rasa yadda zai shigo gidan.

          Da dare, suna yawan zuwa gidan mashaya (wato club) wannan zuwan babu Hikmi, duk da basha kome suke ba, amma akwai bala'in son yan mata, dan haka tunda Jay ya zauna yake kallon kofin gaban shi, da Abeel da Asood suke shan barasa, kallon inda Hikmi yake zama yayi sannan ya tauna lebben shi ya kauda kanshi gefe.

   Yana jin d'aci a ran shi, tunda yake bai tab'a kawowa akwai ranar da mace zata iya shiga tsakanin  amintar su ba, sai yau.

          Kamar yayi ta faɗa yake ji, amma ba zai iya ba, a ran shi yana jin dole ya gyara musu zama, daga wancan me shegen tsayi kamar sallar dare nan.

             Haka yan mata suka yi ta rawa a gaban shi, bai saka ya d'ago kai ya kalle su ba, karshe mik'ewa yayi ya mika musu kudin abinda suka sha, sannan ya nufi hanyar fita, Abeel da Asood suka biyo shi suna maye, koda suka shiga motar shi dake bai sha ba, sai sune suke ta tanb'le, har suka isa gida.

            Ajiye kowanne su yayi sannan ya nufi gida, kamar yadda ya sab'a ya samu, Abbi a falo yana jiran shi, a hankali ya shiga falon, ba tare da yayi magana ba, yayi wucce sama.

"Mujaheed!  Meke damunka? Ba haka ka saba dawowa ba meke faruwa?"

     Cizon bakin yayi da karfi idan ya tuna ta sanadin wancan Yarinyar abokin su yayi fushi dasu, sai yaji ran shi ya kuma b'aci, dukar hannun matakalar yayi tare da cewa.
"Babu!" Ya haura da sauri ya wuce dakin shi. Ban daki ya shiga, yayi wanka sannan ya dawo ya saka kayan shi ya gabatar da sallar shafa'i da wutiri,

  Yana zaune ya haɗa kanshi da katakon gadon, yana nazarin abinda zai mata ya more.

   Mujaheed wanda suke kira Jay! Iyayen shi yan kasar Damagaran ne ta kasar Nijar, amma mahaifiyar shi, yar Sarkin Maraɗi ce, Jay suka fara haifa, sai Kanwar shi mai suna Munibah, sannan Babban malamin jami'ar,  Malam Harisoun Agla suna da sarautar a Damagaran suma.

      Jay matashi ne da yake masifar ji da kanshi, yana da tausayi da hakuri, amma a zahirance idan baya yinka,(🙄🤦🏽‍♀️🙆🏽‍♀️? ) ka shiga uku, domin mugune na bugawa a jarida, bai da mutunci ga girman kan Bala'i, sannan uwa uba miskili ne da bai cika dogon magana ba.

       Maganar shi bata huce kalmomi biyar zuwa shida, ya taso da mugun bakin hali, na rashin magana da daukar fansa, sannan idan zai yi abu baya sauraron kowa sai kanshi.

                Abinda ya tsana a rayuwar shi, kan abokan shi ya rabu, a take zaka  ga tashin hankalin shi. Dukda yasan  Hikmi yafi su gaskiya amma bazai tab'a bude baki ya bashi hakuri ba, ya gwammace, suyi ta wannan abin, kuma yasan abinda zai yi Hikmi ya dawo gare shi.
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

  Godiya nake Yan team din Jay🙄🤦🏽‍♀️🙆🏽‍♀️? toh bari mu gani yadda wasan zata kayya....

BAKWAI

Ya kuma san cewa, tunda Hikmi yayi fushi dasu, dakyar ya dawo gare su, dan haka ya fara tanadin yadda zai dawo gare shi, amma dole sai ya tsaya yaga yadda zasu kaya da yarinyar.

           ......
Tafiya yake a cikin duhu, yaji an rike mishi hannu, a hankali tace mishi.
"Muje na isar da sakon da na kasa, bana son yadda kake rayuwarka! Kaji."

    Bude wata kofa akayi yi haske ya cika mishi ido, firgi ya mike tare da ganin Na'am tana d'aga labulen d'akin shi.
"Bakwai saura kwata, shi yasa nace ka bar zuwa wayon dare amma dake kunnen kashi gare ka gashi ka rasa sallar asuba, tashi kayi sallah."

         Ban daki ya shiga yayi wanka da alola, sannan ya fito daga ban dakin jallabiyar ya saka ruwan madara da hularta, ya shimfid'a abin sallah ya fara gabatar da sallar.

     Yana idarwa ya mike, kamar ba zai shiga makarantar ba, ya kuma shirya cikin kananun kaya ya dauki jakar shi ya tsaya gaban madubi ya gyara gashin kan shi, sosai sannan ya sauko.

    Kallon Muniba yayi sannan ya kauda kanshi, ya ja kujera ya zauna.
"Amma ya dace zaman gida?"
" Ai gwara kayi mata magana na rasa gane kanta, tace ita bazata bai sai ka daina kula yan mata."

Kura mata ido yayi sannan ya sauke wata irin murmushi me tattare da miskilancin, sannan ya ɗan dibi abincin shi ya fara ci a hankali yana yi yana kallon agogon hannun shi.

   Yana gamawa ya mike, sannan yace.
"Indai akan yan mata ne!"

Fita yayi har ya kai bakin kofar fita ya saka madubin shi yace.
" Sai hakuri."
Daga haka ya gyara zaman jakar shi yayi ficcewar shi daga gidan.

       ---
Fadar da Abban Ablah da kuma Umma Fouzan suka min kamar nice na karya kaina da gangan, dan haka nayi kuka kamar idanuna zai fita, daukar takardun asibitin yayi yana dubawa yaga ashe tsagewan kashi ce, ba karaya ba.

   Ajiyar zuciya yayi sannan ya kuma ajiye ya fita, washi gari ina zaune Umma Fouzan ta kawo min wani kwando cike da fulawa tare da wasu takardun gaisuwa tare da ban hakuri akan abinda ya faru. Sai wasu kayan zaki.

   Yadda ta kafe ni da ido ya sani kauda kai nace mata.
"Ban san shi ba, ki ajiye a inda ya kawo!"
Na cigaba da abinda nake.

       ----
Hmm! Yaron ya takura min sosai, har takai ya shigo cikin gidan, sabida kawai ya bani Hakuri abinda abokin shi yayi min, sai da Umma Fouzan tayi min fada, sannan nake kula shi.

     Tun daga ranar, yana tasowa zai tafi makaranta zai biyo ya duba ni, idan kuma ya taso ma haka zai biyo duba ni.

   Har  na cika kwana sha biyar, da dauri, shi yazo ya kawo ni aka warware min suka duba ya had'e kashin.  Daga nan na tako har ajin mu, Barka yan ajin suka min, nayi godiya dake duk zaman da nayi, a gidan nan shi a banza ba.

Muna karatu musamman Ni da bana makarantar, ta online Class.

             ......  Hango d'an iskan yaron nan nayi, yana ajiye motar shi, addu'a nake Allah yasa nazo da wani abu me tsini, duba jakar nayi naga babu wani abu me tsine, har zan rufe sai naga ashe akwai yar roban kayan karafunan lissafi, budewa nayi na dauki Abinda zan dauka ina murna, ina maida jakar agogona yana faduwa kasa, dauka nayi dai-dai fitar malamin na fita da sauri ina gyara zaman agogona, ashe bai zauna ba, da sauri nake sauka, na shiga ts tsakanin motocin da suke gurin, ina zuwa gurin motar shi, na kace tayar gaba.

      Take yayi wani fitar da iska, na kuma komawa gefe na cake tayar gefen, ina gamawa na juya zan tafi, muka yi tawo mu gama dashi, karfen da agogona suka zube na juya da sauri na bar gurin, zuciyata na wata irin bugawa, na tsoro. Bai fahimci abinda nayi mishi ba, sai dai ya dauke karfen da agogona yana juyawa, cike da mamaki.

                       Ganin motar ya sauka kasa ce yasa shi fahimtar, abinda na aikata mishi daukar agogon yayi ya saka a cikin aljuhun shi, tare da dukar motar da hannun shi, ran shi na kara b'aci.

Idan dalibai suka san abinda ya faru da shi, tabbas zasu mishi dariya, dan haka. A fusace ya nufi ajin mu.

     Tunda ya shigo naga yadda idanun shi, suka kad'a jajjur har jini na kwantawa akai ya sani kauda kaina cikin tsoro. Ina shiga ajin naga babu agogona, kafin nayi wani yunkuri na hango shi yana tawowa.

  A hankali yake takowa har zuwa inda nake, ya dafa hannun shi akan tabirin da nake yace.
"Kin shirya?!"
Banza nayi da shi, kawai yasa kai zai fita, kawai yace.
"Toh bismillah!"
          Daga haka ya fita, ban damu ba, kawai dai naji a raina bai da mutunci kuma zai iya kuma min abinda yayi ranar, shi yasa da aka tashi nazo fita na kiyayye fita da sauri.

     Duk yadda nasaka rai zai min abu bayi ba, sai ma shirin da muke da Hikmi, take rashin ya kuma b'aci, dan haka ya shiga hada mana abinda zai rabamu.

      ..... Bayan sati biyu.
Na fito da sauri zan, isa inda muke haduwa da Hikmi domin yaron yana da ilimi sosai, sai naga baya gurin, dan haka na juya zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login