Showing 78001 words to 81000 words out of 119109 words
Chapter 27 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt
shi, murmushi yayi sannan ya d'aga min gira daya.
"Ni ban tura ta ba! Taji dai muna magana da Saif.."
Cizon bakina yayi, tare da b'ata fuska.
"Karki kuma kira min sunan wani kato a cikin gidan nan!"
"Toh Naji, amma."
"Baki tambayi taya aka yi na kasa wancan tuzurin saurayin baki ba?" Ya faɗa min.
"Toh ni nuna ruwa na"
"Zaki ga baki da ruwa."
Ƙoƙarin kwace kaina nake yi, yaki sake ni, "tun daga ranar da kika shiga rayuwata nake jin duk yadda aka yi, ina da nasaba dake.
Na rasa fahimtar haka, sai ma rigimar da kika ta takalowa, haka bai ishe ki ba, sai da kika kwafta min mari, sannan kika yi sanadin haɗuwa na da iyayena.
Ana saura sati daya bikinki, Baba Sarki yake gaya min shekaru Ashirin da daya, da suka wuce, sun daura mana aure. Bayan b'atar da nayi da shekara daya aka raba auren, iyayen mu basu sani ba, daga kakanin mu, babu wanda ya sani.
Sai gashi kin nimo mijinki, ko kunya baki ji, Baba Sarki da yake gaya min, nayi mamaki dan haka nazo har sokoto, na sami Dattijo, muka yi magana. Na kuma ce ko bana sonki a bani matana ko kuma a tashi Sokoto a tsaye da kafarta.
Ranar da na sauke ki, ai sabida kar wancan banzan ya kare miki kallo ne, dan haka ki ji a ranki ni har yau ina kan bakana, bazan tab'a sonki ba. Dan bana jin kome akan ki, sai yan uwanta ka."
Wani irin abu naji a raina, ban san lokacin da na ture shi ba, nayi juyawa na kwashi kayana, yana min magana tuni na isa d'akina na rufe kofar, na zauna a jikin kofar, tare da cusa kaina cikin cinyoyina. Wani irin abu nake ji a raina, me mugun ciwo, tare da jin tsanar Jay a zuciyata.
Bai bi takaina ba yayi ficcewar shi, kasa. Haka na kwana da b'acin rai da asuba nayi mafarkin wai an kawo min shi cikin jini baya numfashi. A firgice na farka na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallar nafilla, da sauri na shafa addu'o'in na fito kasa, na tsaya a bakin matakalar benen, ina jin ya fito daga dakin Munih na sauke ajiyar zuciya. Sannan na juya abuna, ya hango Ni, amma ya share ni kamar bai ganin ba.
Bai dawo gidan ba sai da gari yayi haske, ina kwance a saman...
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 9:59 AM - Ummi Tandama: *Zuma, ga zaƙi ga harbi*
Ina kwance ya shigo, dake Allah ya daura mishi niman rigima, idanuna na lumshe ya shiga ja min babban yatsar kafana, bude ido nayi tare da lumshe su, dan bana son damuwa. Da sauri na kuma buɗewa tare da b'ata fuska kamar zan yi kuka.
"Dan nace bana sonki shine kike fushi?" Ya faɗa min,
"Toh ina ruwana da kai, karka so ni mana, idan baka soni ba, dubunka sun so ni, dan haka ka kyale ni naji da abinda yake damuna." Fadar haka da nayi ya bashi haushi amma jin na fadi ya barni naji da damuwa ta, ya sashi zama kusada dani. Yana kallon fuskana.
"Batul!" Tsigar jikina ne suka mike sosai, a hankali na tashi zaune.
" Matso kusa dani naji meke damunki!" Ya fada min tare da mika min hannu, kamar zan yi kuka nace mishi.
"Babu kawai bana son magana ne!"
"Zo ki gaya min meke damunki!"
Ya mika min hannun, babu yadda zan yi haka na isa jikin shi. Kawai naji zuciya ta tayi mugun rauni, kuka ne ya kwace min.
"Ya ilahi! Dan nace bana sonki?"
"A'ah, ba haka bane kawai ina jin wani irin yanayi ne, da ban saba jin shi ba, sai da rasa wani abu daga jikina nake ji shi."
.zuba min ido yayi sannan yace min.
"Kamar Ya? Kawai naji kamar zan rasa wani na jikina ne"
Murmushi yayi sannan yace.
"Har yanzun akwai masu yarda da canfe kenan? Toh babu abin da zai faru sai Ikon Allah, dan haka karki kuma zubda wannan hawayen masu mugun tsada, kin san nawa darajar su take, da kike zubda min su?"
Girgiza mishi kai nayi, a hankali ya janyo hannuna yana fadin "yau ban yi sallama da."
Buge hannun shi nayi tare da dariya nace..
"Kai angon Munih ce, dan haka me zaka dauka a jikin yar tsohuwar da zata haife ka, kawai jeka gurin yan matanka."
"Lallai kin gaya min magana, Insha Allah zan nuna miki abin da zai baki mamaki."
Rufe idanuna nayi cikin jin kunya da dariya nace.
"Kai kan inda kunya tabi ina da yakinin baka bishi ba, kawai sai ka sake magana kamar yadda yake babu sakewa."
"Hmm! Da bance a bani wannan abin na tab'a ba." Ya faɗa yana nuna min kirjina, wani irin kunya ce ta kama ni, da gudu na bar mishi falon, Jay bai ga inda kunya ba, ina ga kunya na gabas shi yana yamma, biyo ni d'akina.
Haurowa gadon yayi, ya janye bargon, ya shiga min chakulkuli. Wayyo Allah na, kamar zan yi hauka, sabida tsabar dariya da wani irin farin ciki.
Tsabar ya addabi rayuwata da chakulkuli, karshe zuɓewa nayi a jikin shi, tare da k'amk'ame shi..ina sauke wata irin ajiyar zuciya.
Bakin shi a kunne na, ya sauke min wata irin numfashi, wanda ya saukar min da kasala, na kuma narkewa a jikin shi, d'ago kai na yayi tare da kallon fuskana, tare da zaro harshen shi yana lasar bakina, a hankali na bude idanuna akan shi. Ina jin hannun shi yana yawo a jikina,
Ji nake kamar a cikin Ƙwaƙwalwata yake min yawo dashi, kare narkewa nayi a jikin shi,.kirjina na wani irin bugawa, kallon fuskana yayi cikin nutsuwa yace min.
"Ina son kasancewa dake, amma ina ganin yin haka kamar cutar wa ce."
.... Kifa kaina nayi a kirjin shi, na rasa me zance mishi, duk yadda nake ji akan shi bazan iya sakewa na bashi kaina da jikina sabida yayi farin ciki ba, indai da gaske yana yina toh dole sai ya yarda da hakan tare da gayawa mutanen da yace musu shi yana yina. Hmmm lallai kuwa, ba dai wannan Jalal din ba domin baya jin zai iya ƙaryata kan shi....
D'ago kaina yayi tare da sumbatar goshina, yace min.
"Zanyi tafiya Katsina! Insha Allah yau zan dawo, d'azun na ganki ne shi yasa na zo duba lafiyar ki."
Mai da kaina kirjin shi nayi, wani irin tsoro na kuma kamani, mafarkin da nayi akan shi ya shiga dawo min, rintsa idanuna nayi cikin tashin hankali na bude baki zan yi mishi magana ya rufe min da nashi.
Tare da kashe min ido, dole nabi shi ba dan naso ba, ya gama cinye min bakina, kafin Allah ya kwace ni sakamakon bugun kofar da matar shi take kamar zata fasa mana dodon kunne.
----
Bayan ya janye daga jikina, ya fice da sauri, shi nan yana ƙoƙarin ƙaryata zuciyar shi, har ya isa bakin kofar ya same ta, da kayan barcin da ya barta, ko sallah bata yi ba, daure fuska yayi kamar bai tab'a dariya ba, sannan ya sauka kasa, taso shigowa ta zage ni, bai bata damar haka ba, dan haka ta sauko ta biyo bayan shi, lokacin ya wuce dakin Husnah, itama tana barci a cikin bargo yaga alamar tayi sallah.
Dan haka ya fita bai gaya mata zai yi tafiya ba, har ya nufi dakin Munih tana kallon shi ya shiga yayi wanka tare da gyara zaman tawol ya fita daga dakin ya nufi dakin shi.
Ya saka kayan shi tsaf ya shirya, sannan ya kuma dawowa d'akina, Tabbas da kayan na gan shi a tsorace nake kallon shi jikina kamar wacce aka tsoma cikin kankara, kayan cikina sun cure guri guda. Ga wani sanyin da yake damun jikina kamar ana kusanta ni da kankara.
Bakina yana rawa nace mishi.
"Karka je ka hakura da zuwa katsinar nan yau!"
Wata uwar harara ya watsa min tare da kauda kan shi yana min wani,. gargad'i sannan ya ficce daga d'akin, ko sallama bamu yi ba.
Yayi ficewar shi, ina kwance a gurin har wani barci ya rufe ni, kamar yadda nake cikin tashin hankali haka nake barcin cike da tashin hankali sabida miyagun mafarkin da nake wanda ya sani farkawa ina kwala mishi kira, zaune na tashi naga kamar giftawar mutum ta tsakanin baranda na, na sama mik'ewa nake son yi naji kamar ana wasa da ruwa a ban d'akina, wani tsoro ya kamani, dan dole na mike tare da lek'awa ban dakin babu kowa.
.ina juyowa naga wucewar mutum da sauri, a firgice na kuma juyawa. Kai karshe da tsoro ya gama kamani da gudu na dauki mayafina, na sauko daga sama, kasa ina sauke ajiyar zuciya.
Tsabar tsoron bala'i. Da sauri na yafa mayafin zan fita, naga Munih ta fito tana waya tare da yatsina fuska kamar yaga mugun abu, bata gabana dan haka na saka kai zan fita ta kalle ni.
"Gidan Uban wa zaki?" Murmushi nayi tare da saka kai zan fita ta riko min mayafina dina, da sauri na juya muka kalli juna, sake min da sauri.
Saka kai nayi zan fita, tare da fita filin gidan, tunda aka kawo ni gidan ban tab'a lekowa waje ba, kallon kaina nayi a madubin daya daga cikin motar shi, na kalli fuskana.
Murmushi nayi naga uban kumatan da na tara, a hankali na gyara zaman mayafina, sannan na nufi kofar da zata kai ni cikin gidan, tsabar na kwana biyu ban fita ba sai nake ganin gidan yayi min nisa, da sauri sauri na isa cikin gidan. Duk inda na gifta sai an zube an gaishe ni har na isa. Da sallama na shiga falon. Naga sun juya a firgice.
Tare da zuba min ido. Murmushi nayi na karasa a hankali na durkusa tare da gaishe su. Yadda suke amsa min gaisuwar yaci ace na fahimci rashin nutsuwa a muryan su, sai kawai na nime guri na zauna a kunyace.
Kowa sai kallona yake, karshe Mamah ta jani zuwa shashinta, na zauna sannan ta kuma fita ta barni can naga Raihanah karama, ta shigo fuskarta yayi jajjur, murmushi na mata tare da tambayar ta.
"Lafiyanki naga fuskarki tayi haka."
Cikin tausayi da damuwa ta kalle ni sannan tace min.
"Babu komai mura ke damuna."
"Allah ya sauwaka, kuma kisha magani zaki ji dad'in jikinki."
Daga nan tafita, sai bayin da suka shiga kawo min abin tab'awa har zuwa wani lokaci, naga babu wanda ya kuma shigowa, zuwa wani lokaci.
Na jima a dakin kafin Karama ta shigo, muka zauna muna yan hira dan itama bata jima da dawowa daga cikin gidan ba, muna zaune na duba yar qaramar jakar hannun da na fito da ita, na shiga duba wayata, kafin na turawa da Jay sakon.
*Da fatan ka isa lafiya?"
Babu amsa, ne kuma tura mishi bai dawo min da amsar ba, kawai sai na shiga kiran shi.
Bai dauka ba, har zuwa wani lokaci bai dauka ba, mik'ewa nayi na fito zuwa babban falon inda naji abin da ya kusan tarwatsa min kunne na.
"Eh toh! Har yanzun bamu ji labarin halin da yake ciki ba, amma munfi zargin cewa sun wuce dashi katsina tunda dama can zai je, yanzun na bar Fahad da Najim a gurin dayan su zai wuce Katsina daya kuma zai duba mana nan asibitin daura dan munje mun sami motar shi."
Zubawa Baba Aswad idanu nayi cikin tashin hankali na karaso tare da zuba gwiwata a kasa, na fashe da kuka. Na kasa cewa kome. Kuka nake har da shasheka, domin tabbas abin da na gani, ne yake faruwa.
Kiran layin Abban shi aka yi, ya saka a kunne, kawai ya furta.
"Alhamdulillahi! Toh gamu nan zuwa."
Kallon Mamah Sarah tayi sannan yace.
"Maryam, ko zaki zauna da Fatimah."
"Don Allah, Abba kuje dani.. Don Allah karku bar ni a gida zan je na gan shi."
Babu yadda suka iya dole suka tafi da ni, a wani asibitin kudi aka kai shi.
Koda muka isa zuciyata kamar zata fado kasa, har bakin dakin da aka shiga dashi.
Idanuna sai zubda kwalla yake tare da niman hanyar da zasu fito dashi, can bayan awa daya suka fito dashi kamar yadda na gani, hakan suka fito dashi rike bakina nayi wani irin kuka ya kwace min.
Mutumin da ya kawo shi yake bada labarin yadda akai hatsari, wai wata motar diban kasa ce, da wata motar itace, suka saka shi a tsakiyar su, suka yi ta make shi,karshe dai suka juye mishi kayan su akan shi, sannan wata mota yazo ya kuma buge shi ya faɗa a rami, Allah ya nufa zai yi nisan kwana. Kan shi kuwa yasha wata uban bandaje.
Abin tausayi, haka nake kuka duk yadda aka so na dawo gida naki, na kasa hakuri da halin da yake ciki, dan gani nake da zaran na dawo gida wani irin labari zan ji mara daɗi.
Ina zaune har aka kawo su Munih da Husnah, sun gama tsora ta, da halin da yake ciki. Muniba tace.
"Dama ai an gaya mana ke matar mutuwa ce, duk namijin da ya aure ki, sunan shi gawa, wallahi wani abu ya same shi kema mutuwa zaki yi."
Ban tab'a yarda da maganar ba sai yau, domin daga auren mu, har ya faɗa cikin wannan hatsarin.
Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, a gigice na zuba mata ido, na mik'e tare da fita daga dakin, na nufi Ofishin likitan da yake da ya duba shi. Ina shiga na fashe mishi da kuka tare da cewa.
"Don Allah a wani hali mara lafiyan nan yake ciki? Don Allah karku bar shi ya mutu, don Allah ka taimake ni kar ya mutu."
Zare madubin shi yayi cikin nutsuwa, sannan ya kura min ido. Duk yaga yadda na birkice da kuka yace min.
"Ranki shi dad'e, babu abin da ya dame shi, kawai dai muna zargin ya bugu ne a kan shi. Wanda bamu tabbata ba, sai zuwa nan da wani lokaci."
A rikice na zuba mishi ido, kamar yadda yake kallona, sanan na sake kukan da nake ta hadiyewa nace.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Na zama annoba. A cikin al'umma, idan Jay ya mutu me zancewa mutane, da wani ido zan kalli iyayen shi, wato nice dai damuwa." Mik'ewa nayi na fito daga ofishin sa, na tsaya daga jikin tagar dakin da yake ina kallon yadda yake cikin halin rai kwai-kwai mutu kwai-kwai.
"Kin shigo rayuwar shi, dan ki kashe shi, meye ribarki?....
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: _Kowa yaci ladan kuturu! Dole ya biya da yatsu_
Tafiya nake amma zuciyata cike da wani mugun tsoro, koda na shiga ji nake kamar zai fado kasa, haka na rike kirjina numfashina yana kaiwa da komowa, najima ina kiran sunan Allah kafin na samu sukuni, kasa kuka nayi, na zauna kwayam a dakin ina zare idanuna. Ina ji ina gani aka fara kome babu sanina.
... A hankali kome ya sauya, Jay bai damu dani ba, koda kuwa zamu hadu da juna kamar zamu buge juna matsawa yake ya bani hanya, wani lokaci haka zai ta kallona kamar yaga bakuwar fuska.
.... Can fada kuwa, abin da basu tsammani ba, shine ya fara faruwa. Domin cikin iya taku tare da Najim suka shiga gwara kan mutane, musamman ajiyar da Sa'i, yayinda suka hade kan su da Sa'i, haka ya bawa Ajiyar haushi, har ta kai sun fara rigima a tsakanin su, rigimar da ta kai har a cikin fadar suna iya yi a gaban kowa.
Idan suka yi fadawa ke musu magana tsawa su bari, sosai abin ya fara tab'a ahalin gidajen guda biyu. Yau ma Juma'a sun gama abin kunyar su a gabab Jay, yabi Sa'i har gida bayan sallar esha, bayan ya samu shiga Sa'i yace mishi.
"Jalal kai ne a gidana? ban kawo zaka zo ba, kai Nagode sosai." Cikin murmushi Jay yace.
"Haba Ranka shi dad'e gani nan, kawai nazo ne mu d'an zanta, na kuma baka hakuri da Abinda Ajiya yake maka ina ga zan dakatar da shi ma baki daya."
Nan Jay ya shiga tona mishi magana a bakin shi, tare da nuna mishi yadda yake jin haushin rigimar da suke da Ajiya, sannan dole ya dakatar da Ajiya, ai wannan bayi bane. Sosai ya zage yana fada. Fir Sa'i yaki magana, sai da Jay yace mishi.
"Karka gayawa Ajiya nazo gurinka, dan wallahi zai iya jin haushinka, domin shi yaso na zama yaron shi naki yarda dashi na sabida ina Son zama da manyan masu hikima da hangen nesa." Nan ya shiga yabon yadda Sa'i yake, take kan shi ya fara kato yana jin shi wani ne.
"Wato idan kana niman munafuki ka sami Ajiya ka samu." Mik'ewa Jay yayi sannan yace mishi.
"Kayi hakuri zan wuce gida! Idan na sami lokaci zan kuma kawo maka ziyara." Daga haka ya fice ko dogon sallama bayi ba.
Har ya fito daga cikin gidan, yazo gurin Najim ya ciro yar wayar shi, ya mikawa Najim sannan ya suka bar gidan. Shiru suka yi kafin Najim yace mishi.
"Kar muje gidan Ajiya! Ni na jima ina zargin su, amma dole sai ka shiga jikin su dukkan su biyun, dole ka hade kan ka dasu. Ana zaka kuma sanin abinda yake faruwa."
Sun jima suna tattaunawa, kafin suna iso gida, daga nan kowa ya kama gaban shi, dake dare yayi dan haka na yanke shawarar zama na jira shi ya gaya min meye nayi mishi ne?
Ina zaune har Allah ya kawo min shi, mik'ewa nayi tare da zuba mishi ido, murmushi nayi a raina nace.
"Abinda kake so yafi kome baka wahala." Da sauri yazo zai wuce