Showing 66001 words to 69000 words out of 119109 words

Chapter 23 - MAGAJIN IZZAH! COMPLETE Writing Mai Dambu.txt

07 Aug 2025

5467

ganin shin ya yarda da abin da suka ce, amma yaki kallona.

       Nan kowa ya shiga fadar albarkacin bakin shi. Daga nan suka min cin mutuncin akan Jay. Juyawa da suka yi zasu zagi Jay Ummi tace musu.
"Baku isa ba! Baku haifu ba, yar ku dai ku mata fada amma duk wanda ya Kuskura ya zaga min d'a ko ya sake kazamar bakin shi akan Jalaludeen. Toh na rantse da Allah sai masarautan nan ta tashi tsaye da kafaffunta.

     Sannan kai Annuwar da kake maganar cewa Jay da Aanih suna masha'ar su, kai meye ribar tozarta d'an uwanka a gaban jama'a?

  Meye amfanin cin fuska haka, sabida yana da hakuri ko? Sabida baya fada baya kome duk abinda zaku mishi akan ta bazai tab'a cewa kome ba.

       Toh wallahi ku kiyayye abinda zai sanya shi yayi magana, kai kuma Saifullah zaka aureta ko ba zaka aureta ba?"

    Bakin shi na rawa yace.
"Zan aureta!"

      "Tashi kar na kuma ganin me kama da kai sai ranar auren ku" da sauri ya mike, yana fita ta shiga gayawa yan uwan mu magana, tare da cin mutuncin su. Kamar yadda suka yiwa Baabi, cikin izza tace musu.

"Ban da nima a cikin nima, haramun ne da sai an nimawa Jalaludeen auren yarku muga ta karshen tsiyar ku, kuma a biya sadakin da ba'a tab'a biyan wata mace da shi ba a cikin masarautan nan ba."

Korata tayi sannan ta zauna tayi musu wankin babbar riga, sannan ta bar falon abin ta, tana zuwa ta amshi wayar hannu na, tare da kashewa.

   Bayan tafiyar ta, nan suka shiga fadan abin da yayi musu, har da cewa.
"Matukar  Aanih ta auri yaron nan babu mu babu ita. Taje can su kara ta, dan bazata  ja mana faduwar daraja ba, daga masarautan Zazzau ba."

                      "Hmm! Ban san me yasa Rahil take takama ba, ban san me yasa take jin ita wata ce ba, ko ce mata aka yi muma sakarkaru ne da zata zauna yana gaya mana magana, son ranta wato d'an Yar uwanta shine abin burgewa ta kare laifin shi.

        Toh Wallahi duk abinda take ji zata samu, dan.."

Shiru tayi sakamakon haÉ—a ido da suka yi da Ummi tazo gurin Baabi.
"Hajiya kenan! Da fatan na barki da ɓaɓatu! Duk ba laifi bane, amma kin san kome lalacewar gawar Giwa tafi kwando tara,"
Gaban Baabih taje suka yi magana sannan ta d'ago kanta. Mik'ewa yayi sannan ya basu hakuri da abinda ya faru.

......
.  Haka da yayi musu ya masifar d'aga musu hankali, nan suka fita daga gidan. Aka shiga yawo damu a cikin Zuri'ar mu.

   Su lallai Baabih ya min fada tare da Ummi, shi kuma bai ce komi ba, sai ma zuba ido da yayi.

    Abun ya zama rikici da ya janyo aka hanamu shiga cikin gidan kakanmu, hatta wasu abubuwan an hanamu shigar cikin shi, balle kuma irin su Suna da wasu abun.

..... Matar kanin Mamana ta haihu dan haka nayi ta rokon Baabih ya bar ni naje, ni da Hanisah. Muka tafi mun je an karb'e mu hannu bibbiyu. Muna zaune a dakin Ayyah kakanta ta gurin Mahaifiyata.

Sabirah da Hoor, suka shigo y'ay'an maza muke dasu, Baban su ke bin Mamana, suna gani na suka fara dariya tare da faÉ—in.
"Makara! Kece a gidan sunan bayan an hanaku fita sabida ana gaya muku gaskiyar da baku so?"

      "Shi yasa naga ganku cikin sanin ya kamata, zancen manyan na manyan ne, mu yara ina ruwan mu."inji Hanisah, wata irin B'oyayyen ajiyar zuciya na sauke tunawa da nayi ita din gwana ce a masifa, gyara zama nayi tare da zuba musu ido.

         "Ke karki min rashin mutunci!" Inji Sabirah.

Budar bakin Hoor tace mata.
"Ai gado ba karambani bane, abinda aka sha a non..."

   "Ni rawa gadon mai kyau ce? Wasu tasu gadon har abada ba zasu iya sakewa da mutane ba, Ni Yanzun idan Uwata ya zo nan an santa da zafi yanayinta kenan, uwar wata kuwa sai dai kaga ana tattara kome saboda dabi'ar bera gareta."

      "Kan uban can! Ni kika zaga?"  Inji Hoor!
                "Bafa zagi nayi ba, wai ina gaya miki gadon da muka yi ne, ke baki fahimtar Yaren ne."

    Ai kuwa suka fita, can sai gasu tare da dangin Mahaifiyata, suka shigo zasu dake ta, kallon su tayi sannan ta girgiza kanta, tace musu.
"Ko kunya baku ji ba, kun dibo jiki zaku wulakantata sabida an gaya muku karya da Karerayi akan yar yar uwan ku, ko tausayin rashin uwa da bata dashi baku yi. Kun zauna akan abinda aka gaya muku sabida ranku yana sosuwa da SOYAYYA da ta samu a gurin mahaifinta.

       Da yau dukiya tana dawo da mutum tabbas Hassanah Ummina zamu bada duk abinda muka mallaka daga masarautan daura har zuwa masarautan shehun Borno, tun duniya tana kwance ahalin mu suke taka rawan gani a kasar nan.

          Dukiya mun gan shi mun kuma san shi, soyayyar da Zuri'ar mu takewa Hammah Jay, ya wuce yadda kuke tsammani..akan shi kuke tsanar Mahaifiyata? Sabida son kai da son zuciya, toh ku dake ni, sabida nice nayi magana ba mareniya ba.

Ko kunya baku ji ba, ku iyaye kuna fadan abubuwan da basu dace ba akan yan uwanku, wallahi matukar Fatima ta shiga cikin Zuri'ar mahaifiyata sai kun gane cewa shi mulki da dukiya al'amarin Ubangiji ne, yau muna kallon Hammah Jay a matsayin Mahaifiyarshi ce, sabida shi daya ta bari.

   Bamu da madadinta sai shi, mahaifiyarta ta rasu ta bar muku  ita, domin idan kun tuna da ita ga madadinta sai ku mata addu'a, amma sai gashi babu wacce kuka tsana sama da ita, da yau ana mutuwa a dawo baku ji kunyar Mameeh ta dawo ta ga abinda kukewa Yar ta ba. Burin ku sunan ta ya b'aci ace sabida rashin amana mahaifinta ya gaza bata tarbiyyar da ya dace. Ku ji tsoron Allah akan zalunci da kuka mata. Allah sai yabi mata hakkin ta, karku manta akwai rayuwa akwai mutuwa.".
Daga haka ta riko hannuna zata fita ta kalli Hoor tace mata.

"Kuskuren ki tab'a min ji kimata! Shi yasa na tab'a naki, ba kare bin damu!" Daga haka muka bar gidan. Ina kuka Allah yasa ita ke jan motar dan dukkan mu Baabi ya saka an koya mana mota.

             "Nagode kanwata Kawata." Na faɗa mata cikin kuka, girgiza kai tayi sannan ta cigaba da tuka mota tana faɗin.
"Ban san me yasa baki iya karban kanki hannun mutane ba, nifa ba zanyiwa kowa kuka ba"

       "Sabida kuka da gadon taurin zuciya ba! Kuna iya boye kaunar abinda kuke so ba! Da zaki ji yadda nake son D'an uwanki da sai kin tausaya min."

  "Mun sani mana, toh ya zamu yi da dangin Baabi? Kin san Ummi ma ba sha tayi a hannun su ba, kawai tafi su baki ne. Wallahi kaf dangin Ummi babu wanda baya mutuntaki, ana ganin darajarki fiye da yadda baki zata ba, ko jiya sai Da Kaka Bana ya tambayi Hammah Jay, akan da gaske yana sonki? Yaki bashi amsa.
.da ya bashi amsa toh ina gaya miki sisin gwal ne sadakin ki.

     .ko Ni bana tsammanin zan sami sadaki sisin gwal, amma ke naji har kowa ya gama hada kome na sadakinki.. amma mara kirkin nan ya ce baya sonki."

     Lumshe idanuna nayi sabida kalmar baya sona ba sabon kalma bace da zan ji haushinta, kalmar ta jima da zame min Alakakai. Bude idanu nayi lokacin da naji ta ja burki.

          Ikrama ne ya sha gaban mu, da sauri nace.
"Ke tadda motar mu bar nan mahaukaci ne."

Sai da ta barshi ya kusan zuwa dab damu, kawai ta finciki motar da masifar gudu, ya kuma koma cikin nashi ya rufa mana.

  Da sauri na shiga lallubar Number Saif, ban san na fada kan Number Jay ba, kawai na shiga kiran shi.....

Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....
#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari.*

  "Saif! Ikrama ya biyo mu!" Na fada a rikice, muryana yana rawa,

       "Da alamu baki duba wanda kika kira ba ko?" Yana fadar haka ya kashe wayar.
Kafin nasan abin yi ya daki motar mu, wayar ta fadi nida Hanisah muka saka salati. Sai lallubar wayar nayi cikin tashin hankali, na kuma kiran Jay.  Naji yana waya.

        ---
Yana zaune a dakin shi, dan sunan yayi aure ne, amma babu abinda ya dame shi da matan shi,   suma tsoron shi suke dan Munih ta tab'a gaya mishi magana akan ya ajiye su babu abin da yake tsinana musu. Shi kuma da Iskanci yayi mata alluran fitina.

          Tayi ta hauka yana kallon ta, sai da ta gama fita hayacinta, sannan ya mata wani alluran da ya Sata barcin dole, shi yanzun burin shi a gini mishi asibitin shi ne baya son kome sama da haka.

   Ya zaune Aanih ta kira shi,  kamar ba zai dauka ba, dan yasan sarai yanzun zasu raba hali, da ita tunda daga shi har ita. Basu rena abun faɗa.

  Ganin kiran yaki karewa ne ya dauka tare da mannawa a kunnen shi, jin yadda take fada mishi halin da suke ciki sai da ya sanya shi tashi ya zaune. Sannan ya gaya mata ba Saif bane.

   Katse kiran yayi, sannan ya kira   Habib, sun jima suna magana. Kafin ya sashi ya had'a shi da mai girma Gwamnan Sokoton.

     "Barka dai yallabai!" Shiru yayi sannan yace.
"Ka kira yaron ka, kace mishi ya daina bin yarinyar nan ko kuma ni nasa a kwashe mishi kayan aikin shi baki daya, idan kuma kana ganin karya ne ka bani nan da awa daya zaka sami gawar d'anka!"

     Daga haka ya kashe wayar abin shi ko ta kan Aanih bai kuma bi ba.

          ***
Gudun da muke wanda ya kusan fitar damu garin sokoto, gashi yamma ta fara yi, ganin shi muka yi ya juya da gudu, muma kuma muka juya da gudun.  Gida muka nufa.

     Tunda muka shiga, a tare muka sauke ajiyer zuciya, nace mata.
"Na yafe fita ko ina, Insha Allah."

         Har zan fita Hanisah tace min.
"Addah! Ki kira Hammah Jay kiyi mishi godiya dan nasan wannan aikin shine da taimakon Allah, ya kub'utar da mu."

     Murmushi nayi sannan na fito daga motar. A raina ina kara jin son shi, Jay kenan, ga dad'i ga tsiya.

         Koda muka shiga cikin gidan, kowaccen mu daki ta wuce, muka yi alola da sallah magarib, sai bayan isha na kira shi, kamar yadda nai tsammanin zai dauka. Sai jin muryan Munih nayi Allah ya taimaka ban yi magana ba, kome ta ganin a jikin sunan wayar ta fara zagina. Kashe kiran nayi ban kuma gigin kiran shi ba.

    .......
    Lokacin da da yazo yaga wayar shi a hannun Munih, kallonta yayi sannan ya kura mata ido. Dake bata da kunya ce mishi tayi.
"Wata karuwa kasa batun?!"

     Kallonta yayi sannan yace.
"Ruhi ga ruhina! Haske ga Haskena? Ko zaki hanani kula mata ne?" Ya gaya mata,
"Toh kuwa naci Ubanta? Domin na zage ta!" Ta gaya mishi tare da wular da wayar a bisa gadon shi.

         Bai damu da ita ba, har zata fita ta juya tana faɗin.
"Wallahi tallahi billahil azim, idan ka kuma auro wata mace cikin masarautan nan, nice ajalinta. Domin zan kasheta har lahira."

   ... Sake baki murmushi yayi sannan yace.
"Insha Allah, saura kwanaki ƙalilan ki samu amarya domin zanyi kuwa."

    ..nan tafita tana banbami, kallon wayar yayi yaga batul! Tsaki yayi tare da kiran wayar aka ce ana amfani da wayar.

       ---
Bikina ya kankama, dan ana ta hididdinmu, kamar yadda ake ina can an sanya ni a daki, ana ta dirka min kayan gyara, tun ina jin haushin su, har na hakura da shan su, domin kuwa na gaji da kayan gyaran.

....ranar Laraba, aka yar ƙwarya ƙwaryan walima, ranar Alhamis. Kuwa aka mana lalle. Kin bakin nayi nace a min ja.

   Sabida lokacin da Jay ya tafi dani, abu ba abu ba, zai ce jan lalle nan tayi min kyau.

Kawai sai na tsinci kaina da sawa a dauke ni a hoto da jan lallen na tura mishi tare da mishi godiyar da banyi ba, sannan na mishi fatan zama lafiya da matan shi.

   ..... Can ya kuma turo min sakon da cewa.
_Allah ya bada sa'a! Ya kuma baki zaman lafiya! Ya kuma tabbatar miki da auren nan jibi._

     A rikice, na kira shi yaki dauka ya turo min.
_Karki dame Ni don Allah! Kiyi aurenki mana, ni dai Allah ya tabbatar miki da Alkhairi ayi shi ranar da Saif_

     *Don Allah karka lalata min rayuwar aurena! Fatan Alkhairi kawai na tura maka da godiyar abin da kayi min*

  _Ni nace miki zan lalata miki aurenki ne? Kar ki min sharri mana_

  _😭Don Allah kar ka min haka, wallahi zaka ja min magana a gurin dangin Mahaifina da Mahaifiyata_

    *Ai kuwa! Ni ban isa na lalata miki suna ba, kawai nayi abin da ya dace tunda gashi na miki fatan Alkhairi, amma kina zargina*

  _Nasan halinka! Na kuma san waye kai! A zamana da kai babu cutarwa! Amma kai_

    *Toh nagode daga abin arziki zaki bini da Sharri.*

Ya rufe wayar abin shi, shigowa Husnah tayi ta zauna a kusa da shi.
"Allah ya huci zuciyar Saraki!" Tace mishi,
"Don Allah jeki kaina yana ciwo! Bana son magana." Ya gaya mata.

         Bata damu ba, ta mike ta bar d'akin. Bin bayanta yayi da ido. Yarinyar tana da kawaici ba kamar Munih da take mishi kallon kamar zata cinye shi ba.

         ---
Yau Jumma'a, baƙin daga wasu sassa na jahar Najeriya suka fara zuwa, domin halartar daurin auren mu.

         Ina zaune Bayan sallar isha, ana min kwalliya, dan zamu tafi liyyafa, hankalina yana kan kwalliyar da ake min, tare da sauraron hirar da Hanisah suke da mai kwalliyar take cewa.
"Nifa turo min sako aka yi tare da kudi masu yawa, wai zanyiwa Yar Sarkin Musulmai kwalliyar bikinsu."

   "Ba kuma baki san shi ba? Zaki tawo?" Na tambayeta da sauri bayan na dakatar da.

"Gimbiya! Ni ai turo min sako aka yi ta email! Sannan aka ce na tura account dina, Ni kuma nayi kome, har da kuÉ—in jirgi aka biyan min. Kuma da na iso ya turo min da wancan kayan wai shi zaki saka. Ina ga angon ne!"

  Shiru nayi kafin na duba kayan, aikuwa munyi da Saif da na tura mishi kayan nake son sakawa yace ban fada Da wuri ba, ba zai samu saya min ba,  Ni kuma ina jin kunyar Baabi, domin yana ta tambayana me nake bukata nace babu, sai gashi Saif din ya kuma cika min alqawarina."

  Kamar zan yi kuka na dubi kayan, doguwar riga ce, ruwan kore mai duhun shi wanda ake kira(royal green) sai tare yake zuwa da wasu yan kunne da sarkan su na azurfa wanda aka samu su Duwatsu masu daraja.  Ji nayi kwalla ta cika min ido, lokacin da naga har da takalmin su dan iya rigar kawai na bukata, ina da wasu yan kunne da abin wuyan da zan saka.

            Dan nasan idan nace ya saya min gabaki daya zai ce a'a, kamar yadda nayi tunani haka ya faru, sai na share ban kuma cewa kome ba, ashe zai saya min.

   "Hanisah! Kin san lokacin da na gaya mishi cewa, ina son kayan ce min yayi bai da kuɗi amma kiga bazara da yayi min naji dad'i wallahi."

     "Ai kin gaya min. Ko kin manta ne. Kinga har da jakar kayan. Gaskiya Saif yayi Namijin ƙoƙari da ya saya miki kayan nan."

Haka na koma aka cigaba da min kwalliya na, sannan na tura mishi sakon.
_Nagode_

     Bayan an gama gyara min kwalliyar, aka shirya ni tsaf. Sannan muka fito, juyawa nayi naga Hanisah da Jannart karama na Katsina sun d'aga min rigar, ina saukowa daga shashin Ummi, wani irin kyau nake fitarwa, har falon kasa.

       Na samu yan uwan da kawayena na cikin masarautar suna jirana, kowa ya kalle ni sai yace masha Allah, sannan muka fita.

         A motar da Saif ya turo na shiga, ana gyara min zaman rigana.  Kafin Hanisah ta shiga ya ja motar da gudu muka bar gurin..kallon shi nayi tare da lek'awa.
"Jay!!" Na daka mishi tsawa.
"Kar ki kuma min tsawa."

    Gabaki daya ya dauke ni daga inda ya dace, can wani wani otel ya kai ni. Ya kama mana daki, sannan yazo ya ja ni ya kai ni da farko naso taurin kai, kallona yayi sannnan yace min.
"Wallahi zan dauke ki cak, na shiga dake."

      Ko tari banyi ba, na fito a hankali ya saka hannun shi ya tattara min jelar rigana, muka nufi cikin otel din, muna shiga dakin na zauna tare da fashewa da kuka.

.... Sosai har jikina yana rawa, bai damu ba kawai fita yayi a dakin na wani lokaci. Tun ina kallon agogon bangon dakin, har na daina, sabida tashin hankali. Jay bai dawo dakin ba, sai sha biyu da rabi ya zo ya dauke ni muka koma gidan. Bai damu ba,ya nuna min hanyar na fita.

"Allah sai ya saka min! Wallahi na yi dana sanin, sonka da nayi a rayuwata, Jalal kai mugu ne! Azzalumin wanda bai san kome ba sai son kan shi, me zancewa Mutane! Me zan gaya wa mahaifina da yan uwansa?"

    "Shi ya fiki sanin waye ni! Ya kuma san abinda ya dace? Fita ko na baki shaidar da zai tabbatar miki tsaf nake na kira kaina mijinki!" Da sauri na balle motar.

"Insha Allah ba zaka tab'a zama mijina  ba, kaje can gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login