Showing 27001 words to 30000 words out of 110313 words
Chapter 10 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
jiki, duk yau sau daya sukayi magana tace mishi tana makaranta, yanda yaita duba wayar shine yasa ya yanke hukunci fara yi mata magana. Dariya yayi yanzun kam mai sauti, bakomai yakan saka shi dariya haka ba
"Allah mai iko"
Fodio ya fadi yana kallon Hamza daya daga waya ya kara a kunne da alamun kira yakeyi, tashi wayar Fodio ya sauke daga kunnen shi yana sauraren hirar da Hamzan yakeyi da shigowar kiran Anna yasa shi yima Hindu sallama yana kashewa, ya kira Ann din yaji ko lafiya
"Mai gyara ya kawo mun mota ta yanzun"
Ta sanar dashi, ya jinjina kai, dan sunyi waya, ya rigada ya bashi kudin gyaran tun kafin ma ya gama
"Yawwa to, ki hau kiji, in batai miki yanda kike so ba saiki fadamun"
Hamza ya fadi kafin Anna ta kashe wayarta. Ya siyo motoci har biyu da kannen shi zasu dinga yawon su a ciki, amman baisan me yasa suke son daukar mata mota ba. Duk da bayason musu fada, amman wannan karin ya sauke musu sosai, idan suka gama aikin da sukeyi aka basu kudinsu, zai sai mata sabuwar mota, sai su karata da wannan din da suke naci.
"Zaka fara magana ko sai na nemo wanda zai mun hacking wayarka?"
Kallon 'Baka da hankali' Hamza yaima Fodio daya daga mishi girar shi duk biyun
"Kayi budurwa ban sani ba"
Kai Hamza yake girgizawa
"No... Nope.... Ba budurwata bace ba, kawai muna magana ne"
Dariya Fodio yayi mai sauti
"Kai? Hamza, kai? Kake magana da mace, kiranta kayi fa. Banda Mansura ka fadamun macen da kake magana da ita?"
Dan dakuna mishi fuska Hamza yayi
"Ina magana da wasu mata mana"
Ganin Fodio na mishi kallon 'Nine fa, karka raina mun hankali'. Shisa ya dora da
"Ok, naji, ina magana da ita saboda tamun kyau, ba budurwata bace, ina so in tasting ne kawai"
Sosai Fodio yake dariya irin ta gogaggun yan duniya
"Yanzun ka fito mun a mutum, me yasa ka tsaya kana wani boye-boye to, ka taya kawai"
Kai Hamza ya girgiza mishi
"Ina ganin ta ba kamar sauran ba, ina so mu hadu ma bansan ta inda zan fara ba, ni ban saba neman su ba kasani, su suke nemana"
Kai Fodio yake girgizawa yana mika ma Hamza hannu, da bai musa ba ya mika ma Fodio wayar yana furta
"Hindu"
Fodio ya jinjina mishi kai, ko mintina biyar baiyi ba ya mikama Hamza tare da fadin
"Ga address dinta nan, zaku fita cin abinci gobe"
Dan ware mishi idanuwa Hamza yayi yana amsar wayar ya duba hirar
"Woo Maza..."
Tashi wayar Fodio ya dauka yana dafa kujera ya mike, dan zaune yake kan kafet
"Kai ni yunwa nakeji, in zaka taso muje"
Kai Hamza ya girgiza mishi
"Kamun take away. Zan danyi abu"
Wucewa Fodio yayi batare daya amsa ba, Hamza kuwa murmushi yayi, da gaske yake da yace ma Fodio yana son dandano ne kawai a tare da Hindu, saboda yanda ta manne mishi a kai, yana son fitar da ita, bashida lokacin wannan a yanzun. Akwai matakin da yake son kaiwa tukunna, ginin da yakeyi ma bai karasa ba, saiya kammala tsaf, yaji wasu miliyoyi a account din shi, saiya nemo wata 'yar ustaziya ya kawo ya ajiye dan Anna ta kwantar da hankalinta da maganar aure da ta fara yi mishi.
*
Wasu kayoyi takeji sun mata tsaye a cikinta tun da ta tashi, gashi ko baccin kirki bata samu tayi ba, saboda tunanin yanda yau din zata kasance, dakyar ta samu bacci da safe, shima zuwa goma da rabi harta tashi, ta fita kitchen ta samu Asma har tayi wanke-wanke ta wuce Islamiyya abinta. Ko da suna gida, ko da Hindu bata da wani abin da zatayi, Asma bata jiranta, sam basa raba aiki, ita Asma bata da son jiki, ko Anty na fada. Hindu kam in zata iya gujema aiki tsaf zata guje mishi.
Shayi ta dan sha da biredi kadan, dan sam batajin yunwa, ta koma falo tana zama, daga Anty sai Khadee suna kallon Hanyar Kano da aka saka a tashar Arewa. Itama zama tayi suna yin kallon tare, lokaci-lokaci take kallon wayarta da tabar ma Hauwa sakon ta kirata tana zaune kusa da Anty. Zuwa can kuwa Hauwar ta kirata, daga wayar tayi tana sakawa a speaker
"Yan mata, ya ake ciki?"
Hindu ta fadi
"Lafiya kalau, ya su Anty da kowa?"
Hauwa ta amsa ta dayan bangaren
"Suna lafiya, tana ma jinki"
Ta karasa tana mikama Anty wayar suka gaisa da Hauwar, tukunna ta sake miko ma Hindu
"Ke kinji Aboje wai yau zaiyi lecture din shi ko? Karfe daya ne ko biyu, banma duba ba sosai"
Dakuna fuska Hindu tayi tana cire wayar daga speaker ta kara a kunne
"Kice mun wasa kike, dan ban niyyar zuwa makaranta ba yau, ni zan rage zane ne ma fa da in danyi karatun test"
Cewar Hindu tana jin yanda Anty take binta da idanuwa kamar ta gane shirine duk maganganun nasu, amman da gaske ne akan saka musu lecture ranaku irin haka. Ko idan suna presentation, yakan kai daga Alhamis har zuwa Asabar, ba bakon abu bane ba daman. Wata rana ma in sun kai Magriba wani a gidan kanzo ya dauketa su dawo. Bata taba karyar tana da aji ba sai yau, shisa ta tsargu, tana sauke wayar ta zabga uban tsakin da yasa Khadee yin dariya
"Yarinya sai a tashi a fara shiri"
Hararta Hindun tayi
"To Hajiya, ai sai da azahar akace ba wai yanzun bane, bari in tashi in rage wani abin kawai"
Hindu ta karasa tana mikewa kamar ranta ya baci da maganar fitar da zatayi
"Karatu sai da hakuri daman ai, wata rana sai kiga kamar ba'ayi ba"
Anty ta fadi, dan wani lokacin har tausayin Hindun takeji, duk idan taga alamar haske a dakin su idan ta fito, ko ta shiga dubasu taganta tsakiyar dare tanata faman zane da takardu a gabanta, karatunsu ba mai sauki bane ba.
"Allah dai ya nuna mana mu gama din mu huta"
Hindu tai maganar tanajin wani bargon rashin gaskiya daya lullubeta da karyar da tayiwa Antyn. Kafin Anty da Khadee su amsa da
"Amin..."
Hindu na wucewa daki tabarsu anan, tana shiga ta tura kofa ta tsugunna tana mayar da numfashi, zuciyarta na harbawa kamar zata fado daga kirjinta saboda tsoron da take ciki
"Wooo... Allah nagode maka"
Ta furta tana mikewa, sun gama magana da Hauwa, tace mata ta saka wandon pallazo, sai ta saka dogon hijab da takalma masu tsini, ta dauki jaka da zata tafi da shigar, ta dora tabaranta, karta cika wata kwalliya mai yawa, jambaki ma zaiyi, dan zai iya dauka cewa tayi kwalliyar ne kawai dan zasu hadu. Shisa take bala'in jin dadin kawancen su da Hauwa. Ba magana ta cika ba, asalima randa yan miskilancin nata suke kanta, tana iya wuni da fuskar nan tata a murtuke, kawai tasan kayane, ta kuma yarda da shigar alfarma, wanda basu santa ba zasuce ko tana karyane, kuma ba haka bane, da dukkan gaskiyarta take gayu, saboda bata son harkar zubar da girma.
Bata da hijabi, amma Asma nada su kala-kala, dan ita duk shigarta da Hijab takeyi, kuma doguwa ce sosai, tama danfi Hindun tsayi. Harma ta zabi hijabin da take so din ta dauko ta ajiye, sauran kayan ta fito dasu tana hadawa waje daya. Ganin lokaci yaki mata saurine yasa ta yanke hukuncin yin zane, dan yafi komai sa taga saurin lokaci. Aikam kafin kace wani abu har karfe daya ta saura kwata. Ta mike tana kara watsa ruwa ta dauro alwala, lokacin data dan murza mai da hoda a fuskarta har an kira sallah. Gabatar da azahar tayi tana yin azkar din bayan sallah tayi addu'a tana dorawa da
'Allah Ka san duk abinda yake a zuciyata, Ka san Hamza ne kalar mijin daya dace dani, Allah Ka tabbatar mun da mafarkina. Allah kasa wannan karin shine karshen wahalata, Allah Ka haskani a zuciyar shi, idan yana da wata ma ta fice fit daga ran shi, Allah kasa gabas, yamma, kudu da arewa idan Hamza ya juya kar yaga kowa, kar yaga komai saini'
Sabonta ne, shisa ta maimaita sau uku tana rufewa da Salati dan ya tunkuda mata addu'ar tayi saurin karasawa da sauri. Sannan ta mike tana sake kaya. Batasan ko ita kadai bace, ko dan ba zata ga muninta ba, amman tayi ma kanta kyau a mudubin data kalla, alamar shigowar text taji ta karasa ta dauki wayar
'Zan karaso nan da mintina sha biyar ko sama sa haka kadan'
Murmushi tayi tanajin wani abu ya kulle a cikinta duk da farin cikin da take ciki.
'Ok'
Ta amsa shi, dan batasan meya kamata tace ba, mintina goma ta bashi, tukunna ta saka hijab din da ruwan kasa ce mai haske, yadin mai yashi, sai roba da aka saka a jikin hannun, sosai taga tayi kyau, ba kadan ba Asma take mata kyau a cikin shigar hijabanta, kawai dai ita tafi jin dadin saka abaya ne. Tunda duka biyun sun rufe jiki yanda ya kamata. Tabaranta ta dauka na gayu ruwan kasa mai cizawa tana sakawa, sai taga ta fito a yar gayu sak yau, fiye da kullum, sannan ta saka takalminta baqi tana daukar bakar jaka ta sakala a jikin tsintsiyar hannunta, turare mai kamshin sauki ta fesa, ta cire tabaran tana rikewa a hannu, daman duk ta saka abinda take bukata a jakar harda wayarta, sannan ta fito.
Taji dadi sosai da taga Anty na sallah, dan haka ta furta
"Na wuce Anty, saina dawo"
Tana jan kofar ta fice daga gidan tana sauri, dan gani takeyi kamar Anty zata idar da sallah ta fito tace mata ta dawo tasan karya takeyi, sai da tabar gidan tana karya kwana sannan ta saka tabarau din a fuskarta tana takawa zuwa bakin hanya, sannan ta ciro wayarta daga jaka dan ta kira Hamza tace mishi ya tsaya a bakin hanya karya shigo kwanar gashash street din, ta fito.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 14
Daya koma gida kwanciya ya sakeyi, saboda yanda yakejin jikin shi, har wani zazzabin wahala ya rufe shi. Ya dauka inya sami wata zai rage abinda yakeji, amman fuskar Hindu ya dinga dorawa a ta yarinyar. In za'a yanka shi har ya baro hotel din ba zaice ga kalarta fuskarta ba, ballantana yanayinta, gangar jikin shi ce kawai ta kasance da ita, tunanin shi da ganin shi duk Hindu ce tayi kane-kane. Sosai abin yake tsorata shi, da ace baije gidansu ba, zai dauka ko aljana ce ya hadu da ita shisa ta dabai-baye rayuwar shi haka. Yanzun ma duk abinda ya durama cikin shi, bai daina ganinta tana gilmawa ta cikin idanuwan shi ba, bai kuma daina jin duminta a jikin shi ba.
Giyar yau taqi tasiri ballantana ta disar mishi hasaso lokacin daya rike Hindu a kirjin shi, daya rufe idanuwan shi sai yaji kamar har lokacin tana rike a kirjin shi. Ya rasa kalar jarabar data same shi haka. Dakyar ya iya zuwa sallar isha'i. Yaga text dinta ya share bau amsa ba, kamar yanda yaki daga kiran daya biyo bayan text din, muryarta wahala kawai zata kara mishi. Har tunanin yaje gidan su yaganta yayi, amman bayajin idan yaje zai iya controlling kan shi da abinda yakeji, kuma yana da yaqinin basuyi nisan da zai nuna Hindu asalin maitar shi ba. A hankali yake so ya jata, lokacin da zai ajiyeta ba zata san me ya faru ba, ko ya akayi ya faru.
Yanzun ma a kwancen yake a falo, kan doguwar kujera, dakin yana nan yanda su Fodio suka fita da safe suka barshi, sai robar coke da yasha rabi, yaje ya bude daya daga cikin giyar shi yana karasa cika robar da shi ya dawo falo ya ajiye. Arafat ke siyan abin zuqar lemo ya ajiye a gidan, ya dauka ya saka cikin robar coke din, bayajin dadin jikin shi, tun abincin rana rabon shi da wani abu, sai giyar da yaketa kwankwada. TV nata aiki, amman hankalin shi baya kai, tunanin shi na tare da Hindu, da abinda takeyi, sai robar coke din da yake dan dagowa yana zuqa daga kwancen a hankali, a hankali.
A haka su Fodio sukayi sallamar daya amsa can kasan makoshi, AbdulHafiz na dorawa da
"Ka gyara kwanciyar ka Malan"
Dan ya tsani yaga daya a cikinsu yayi ruf da ciki, sai yaita ganin kamar mutuwa zata iya dirar musu cikin wannan kwanciyar da batada kyau a addinance. Numfashi Hamza yaja yana saukewa da fadin
"Arafat baku gaji bane?"
Dakuna mishi fuska Arafat da yake cire jacket din jikin shi yayi, ya jefa kan kujera, yana kwance agogo kafin ya amsa Hamzan
"Asalin gajiya ma, kaji kasusuwan jikina kuwa"
Numfashi Hamza ya sake ja
"AbdulHafiz naga yana da sauran karfin takura mun"
Dariya Fodio yayi, AbdulHafiz ya dauki jacket din da Arafat ya cire yana jefa mishi a fuska
"Wai me yasa zaku dinga baza kaya ko ina?"
Cire rigar Arafat yayi daga fuskar shi yana rikewa a hannun shi
"Dan Allah karka fara dani, wai mu ba Maza bane ba? Me yasa ba zamu dinga baza kaya inda muke so ba. Fodio...."
Arafat ya karasa maganar yana mayar da hankalin shi kan Fodio daya sunkuya zai dauki robar lemon da Hamza ya janye
"Ba lemo bane kawai"
Ya fadi dai-dai kunnen Fodio din, daya jinjina mishi kai, sannan ya sakar mishi robar
"Fodio kana jina fa"
Zuqar lemon yayi sosai, ya mayar ma Hamza, tukunna ya kalli Fodio da yake harar shi
"Nan gidanka ne, kai ya kamata ka fadama AbdulHafiz ya dinga kyalemu muna barbaza kaya yanda muke so"
Dagowa AbdulHafiz yayi, dan kofuna yake tattarawa, a gajiye yake, koma bayajin gajiya ba zai bata bakin shi akan Hamza ba, yasan ko dan ya saka shi magana zai iya qin dauke kwanonin. Da sauri Fodio ya daga mishi hannuwa alamar bada kai, wato 'surrender'. Yanayin da ya saka Arafat zagin Fodio din yana dorawa da
"Matsoracin banza kawai"
Dariya Fodio yayi yana wucewa dakin shi dan ya watsa ruwa. Arafat dinma wucewa yayi, AbdulHafiz kuwa sai da ya tattara duka kwanonin da suke cikin dakin yakai kitchen, tukunna ya dawo yana wuce Hamza batare da yace komai ba, kara gyara kwanciya Hamza yayi yana zuqar lemon shi har lokacin. Wayar shi da yaji kararta alamar shigowar sako, yasa shi miqa hannu ya lalubota daga gefen shi, yana dubawa. Hindu ce
'Ina ka shiga haka? Kana lafiya dai ko?'
Birkitawa yayi, yana kwanciya kan bayan shi
"Bana lafiya wallahi, ke nake bukata a kusa dani"
Ya furta a fili, yana tura mata
'Inata hidima, kuma banama jin dadi dai'
Wayar ya saka a silent, yana sakata a key ya ajiye a gefen shi, text din da sukai musaya kawai na neman sake birkita shi. Sauran lemon ya karasa shanyewa, yanajin kan shi yayi nauyi sosai. Idan ya kara zai iya buguwa fiye da yanda yake so. Ba zai iya hada abu biyu a lokaci daya ba, tunanin Hindu kawai ya ishe shi, ba saiya hada da fadan AbdulHafiz da bazai kare ba, idan ya gan shi a buge. Da zai sha har sai ya daina gane abinda yakeyi. Ba zaice ga iya lokacin daya dauka ba, yanajin shige da ficen su Fodio duk da idanuwan shi a lumshe suke. Sai da yaji Fodio na kiran
"Kai ba zaka ci wani abu ba?"
Idanuwan shi ya bude da yakejin sunyi mishi nauyi sosai
"Banajin yunwa nikam"
Ya furta yana kara gyara kwanciya, Fodio nashi ya dauka yana fadin
"Sai da safen ku"
Arafat daman a fridge yaje ya saka, shi yaci samosa da lemo a hanya. Bacci kawai yake son yi, AbdulHafiz suka bari da yake zaune akan kafet yana cin abincin suna hira da Nabila da take mishi rikicin aiki yasa basuyi magana da yawa ba, ganin lallashi ba zai aiki ba, yasa shi nuna mata jan ido yasa ta sauka ta kwanta, tunda tace mishi tana da makaranta da sassafe.
"Kai me kaci?"
AbdulHafiz din ya bukata, dan ya san ba bacci Hamza yakeyi ba
"Ka kyaleni dan Allah"
Hamza ya fadi cikin bacin rai, bayason wata takura koya take a yanda yake jin shi, amman AbdulHafiz ne, in baiyi niyya ba, babu wanda ya isa ya saka shi barin abu, ko ranshi kake son ganin ya baci, sai yayi niyya ne zai nuna maka
"Me yake damun ka?"
Hamzan yasan inba maganar sukayi ba, AbdulHafiz zai share duk wani abu da zai fada yaci gaba da maimaita tambayar har saiya amsa
"Bana jin dadi"
Ya amsa a taqaice yana mikewa zaune, ya runtsa idanuwan shi saboda dakin dayaga ya wulwula mishi
"Ok"
AbdulHafiz ya furta yana dan ture robar take away din da take gaban shi, dan ya koshi. Yana karantar damuwa a fuskar Hamzan, ya kuma kula da yanda yake komai a hankali, kamar yanda yakanyi duk idan yasha wani abu, bayaso AbdulHafiz din ya gane. Yana kyale shine, saboda addu'a ce kawai zata fi saurin tasiri akan shi, tunda yana kokarin boyewa, hakan na nufin akwai sauran imani a tare da shi, akwai kuma yiwuwar shiriya zata same shi a kowanne lokaci.
Kai Hamzan ya girgiza
"Ka daina mun haka"
Fuska AbdulHafiz ya dakuna mishi cike da alamar tambaya, yana saka shi nuna shi da dan yatsa
"Gashi nan, abinda kakeyi ne bana so, ka daina yi kamar ni nake so in fada maka matsalata, bayan kaine ka tambayeni"
Mikewa AbdulHafiz yayi, ya dauki robar take away din
"Sai da safe, idan kana son shawarata, kasan zaka iya kwankwasa mun kofa"
Ya karasa maganar yana wucewa abin shi, numfashi Hamza yaja, yana komawa kan kujerar ya kwanta, bayajin karfin tashi ballantana ya wuce yaje ya kwanta, kuma shi bashi da matsala da kwana akan kujera, balle Fodio ya zuba kujeru masu fadi, yana jin dadin kwanciya a kai sosai. Ya lumshe idanuwan shi, yana addu'ar samun bacci, ko zai daina tunanin Hindu da son kasancewa tare da ita.
*
Kwata-kwata batajin dadin jikinta, duk motsin da zatayi sai taji kamar wani bangare na Hamza na liqe da ita. Sai take ganin kamar ta makara wajen tuban da tayi, kamar Allah ba zai amshi tuban nata ba, shisa takeji tamkar an tsaga fatar jikinta an tura mata zunuban da takejin nauyin su har lokacin
'Allah Kabani karfin gwiwar ko da ture shine idan ya sake kwanta irin hakan. Allah Kaa yafe mun Ka karemun imanina'
Shine abinda take maimaitawa duk juyin da zatayi, zanen ma ganin layukan na hade mata yasa ta hakura, ga rashin maganar da basuyi ba da Hamzan ya kara sakata shiga yanayi. Lokaci zuwa lokaci take