Showing 81001 words to 84000 words out of 110313 words

Chapter 28 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

shi, na fada maka aure bana kowa bane ba shisa ba'a tilasta shi bama"


Runtsa idanuwan shi Hamza yayi yana sake bude su


"Inda baka shirya haihuwa ba, kafi kowa sanin yanda zaka kauce ma samun cikinta, bakayi ba. Me yasa kake mun magana kamar baka taba hango cewar zata dauke shi ba? You step the fuck up kayi abinda ya kamata..."


Maganganun Fodio din yake ji har kasan zuciyarshi, yasan ya fahimci tsoron shi, amman ya manta asalin waye Fodio, ya manta in akazo maganar daukar nauyi ta fannin aure da kula da iyali, suna da ra'ayin da yasha banban da Fodio. Tsoron su ba kala daya bane ba


"Karka bani kunya Hamza"


Fodio ya karasa yana kashe wayar, numfashi Hamza yake fitarwa yanajin kamar iskar cikin motar bata kai mishi inda ya kamata. Hakan yasa shi fitowa babu shiri yana jingina a jikin motar


"Ko da wata rana zan taba aure bazan haihu ba, yara ne karshen abinda zan kawo a duniyar nan. Ba zan mutu in barsu su wahala kamar yanda aka mutu aka barni ba, kudin duk da zan tara musu in babu kulawa aikin banza ce..."


Maganganun Fodio suka dawo mishi


"Me yasa zaka auri yarinya kasan baka shirya kula da ita ba? Ina fada muku aure bana kowa bane kuna dariya kamar wasa ne magana ta"


Fodio din ya fada wata rana da Abdallah ke basu labarin wani mutum a unguwar su da yayi aure bashi da tsayayyar sana'a, karshe sai sakin matar yayi saboda ya kasa riketa. Sosai halayen su da yawa suka banbanta da na Fodio. Ko ranar farko daya fara ganin shi da kwalbar giya tsayawa yayi yana kallon shi


"Menene? Ka daina kallona kamar baka shan wani abu kaima"


Kai Fodio ya girgiza mishi


"Idan yau zan samu bacci batare da taimakon komai ba zan daina sha. Kai kasan me ya fara sakani shan wani abu tun daga farko, kana da zabi Hamza, kana zagaye da mutanen da zasuyi komai saboda kai, in ba zaka iya dainawa saboda kan ka ba, ka duba Anna, ka duba me zataji in ta sani ka daina"


Shiru yayi wa Fodio din a wancen lokacin


"Ni ba AbdulHafiz bane ba Hamza, ba zan iya jure tunasar da kai kullum ba, na fada maka abinda ban samu wanda ya fada mun ba lokacin da nake da damar bari. Zabin duk da kayi bayan wannan naka ne"


Kuma daga ranar bai sake mishi magana akan shan wani abu ba, ko kiran shi yayi ya biya ya sai mishi zaiyi. In kanata tare da Fodio, shawarar duk da zai baka ka bude kunnuwanka ka saurara, saboda ba zai sake maimaita maka ba, ko da kanka ka bukata ba zai maimaita ba. Kallon ka kawai zaiyi yaci gaba da abinda yake. Ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya sauke yana takawa ya shiga cikin asibitin, yana nufar dakin da Hindu take, a zaune ya sameta, ruwan da aka saka mata harya kare, tana murza hannunta. Yau kawai duk tayi wani irin zuru-zuru.


"Kanki babu dankwali"


Ya fadi wani irin kishi na tsirga mishi, wani katon banza ya shigo ya ganar mishi mata da kai a bude. Shisa bai bari ta cire hijabinta ba tunda ba dogo bane har kasa


"Yanzun na cire hijab din zanyi fitsari"


Ta amsa shi da dan murmushi a fuskarta, kai ya jinjina mata yana shiga dakin sosai, ya kama hannun da take murzawa ya dago shi, yana shafa inda yayi alamun fasawar allura, harya dan kumbura


"Sannu..."


Ya furta yana kamata ta mike, har kofar bandakin ta shiga, fitsari tayi ta kara wanko fuskarta tana fitowa.


"Wai zasu sallameni ne fa, ance kana ina"


Kai Hamza ya jinjina yana fadin


"Ina zuwa"


Tunda yasan yanda duk tsarin asibitin yake, yakai mintina sha biyar kafin ya dawo yana, da yar leda a dayan hannun shi, ya kama nata hannun yana fadin


"Muje..."


Kallon shi takeyi, ko takalma babu a kafafuwanta, saboda sungumarta yayi da zasu fito


"...You step the fuck up kayi abinda ya kamata"


Muryar Fodio ta dawo mishi, dan murza goshin shi yayi yana sauke numfashi a hankali, kafin ya zare takalman da suke kafafuwan shi yana tsugunnawa ya tura su saitin nata kafafuwan, kallon shi takeyi, zuciyarta na wata irin dokawa. Kafin ta daga kafafuwanta ta saka takalman, ya kama hannunta yana janta, bin shi take tana kallon yanda yake taka cikin asibitin suna nufar hanyar fita, babu takalma a kafafuwan shi. Kallon shi takeyi kamar har abada ba zai taba bata mata rai ba, kamar ko satin daya wuce basuyi tashin hankali da shi akan Mansy ba. Wani lokacin yana mata kamar yana da iska in ya juye haka.


*


Duk fadan da Hamza yayi da tace ya sai mata soyayyar doya ta bakin titi da taga wata mata nata soyawa, yayi parking din ya fita ya siya. Haka kawai taji doyar tayi mata, yawunta har tsinkewa yakeyi, tun a motar ta faraci, har suka karasa gida tana samu waje ta zauna. Kamar jira aman daya taso mata yakeyi ta karasa cinye doyar, gabaki daya saida ta dawo. Shi kan shi Hamzan hankalin shi yayi bala'in tashi, da kan shi ya taimaka mata ta watsa ruwa, ya dauko mata kayan da zata saka, sai rawar sanyi takeyi duk da ruwan mai zafine tayi wanka da shi, rigarta ya kama yana taimaka mata dan ta saka


"Me yake damuna haka? Naji sauqi fa kafin mu fito daga asibitin, me sukace ya sameni?"


Take tambayar shi


"Ba abinda ya sameki, ciki kike da Hindu"


Maganar shi ta sauke cikin kunnuwan shi da wani irin yanayi


"Ciki?"


Ta tambaya da murmushi a fuskarta, kai ya daga mata yana juyata, ya zage mata zif din rigar. Hannunta takai saman cikinta, tana lumshe idanuwanta, hadi da jero kalmomin godiya ga Allah da wannan kyautar da yayi mata, kyautar da tasan mata da yawa na raba dare suna addu'ar samu. Kwanciya tayi, ya ja bargo ya rufa mata, idanuwanta kawai ta lumshe. Bashi yake rashin lafiyar ba, amman a gajiye yake jin shi sosai, maganin da kala biyune kawai ya ajiye gefe yana fita. Robar ruwa ya dauko mata, yazo ya ballo magungunan yana tsugunnawa


"Ta shi ki sha"


Batayi musu ba ta mike, ta karbi maganin ta sha tukunna ta koma ta kwanta. Shi nan ya zauna kan kafet din yana jin wata irin gajiya na saukar mishi. Wayar shi ya dauko da yaga bacci ya dauketa yana kiran Auta, bugun farko ta daga


"Yayaa"


Ta fadi


"Auta kina ina?"


Ya tambaya


"Yanzun na fito daga makaranta, ina kan komawa gida. Ya naji muryarka can kasa?"


Numfashi Hamza ya sauke


"Hindu batajin dadi, ko zaki zo ki zauna da ita. I promise ba wani aiki zakiyi ba. Kawai kar a barta ita kadai, akwai abinda zanyi a wajen aiki"


Ya karasa, dan yaga Arafat nata kiran shi, tunda AbdulHafiz kadai yasan ya fito, shima bai fada mishi dalili ba, bai kuma tambaya ba


"Okay, bari in siya abu sai in taho"


Kai Hamza ya jinjina


"Nagode"


Ya fadi yana sauke wayar daga kunnen shi. Zama yayi har saida yaga Auta na kiran wayar shi, yasan ta karaso ne kuma, ba zata shigo ba. Ta tsaya a falo tana kiran shi, mikewa yayi ya leqa kai, yaganta a zaune kuwa tana warware mayafin da yake nade da kanta


"Nagaji wallahi"


Kai kawai Hamza ya girgiza, lalacinta bashi da na biyu, yana da tabbacin babu abinda tayi duk yau banda shiryawa ta fita makaranta


"Bacci takeyi, in ta tashi da wani abin ki kirani"


Kai ta jinjina mishi


"Ka fadama Anna ina nan, kaine kace in zo. Kaji"


Wannan karin shiya jinjina mata kai yana ficewa. Yasan tana so tazo gidan nashi, amman Anna tace me zata zo tayi, har karar Anna ta kawo mishi, ta hada su biyun ta zage. Da gasken babu abinda zatayi, kawai tana so tazo ne, itama tace taje gidan Yayanta, kamar yanda sauran kawayenta suke fadi. Anan falon tayi zamanta tana kunna tv, ta tsayar da channel din a MBC 2 da suka saka film din Step Sisters, ta kalla yafi a kirga, kawai bata gajiya da film dinne. Ice cream din data biya ta siya ta fara sha hankalinta a kwance tana kallon, dan sosai ta kwaso tarkacen ciye-ciyen da Anna kance suna tafiya a banza tunda ko yar kiba basa sakata.


*


*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*


Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank


Whatsapp Number
08074545149
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 24


Wani irin shiru take jin gidan tun fitar Hamza, bata gane akwai wutar lantarki ko babu, kasancewar solar da yake gidan, kullum a cikin wuta suke. Bata taba tunanin zata gaji da kallo ba sai yanzun da take da wadattacen lokacin yin shi. Tun karfe goma ta gama bacci, har sharar rashin dalili ta takalarwa kanta, duk da Hamza yayi maganar cewa za'a kawo mai aiki, a cewar shi Anna tayi mishi maganar, yace kuma ta samo musu. Riga da wando ne a jikinta, sai ta daura farin dankwali, zakayi tunanin fita zatayi saboda kwalliyar da take fuskarta. Tun satinta na farko wani ya kwankwasa kofa, ta saka hijab ta leqa, yace mata


"Oga yace kibani kayan wanki"


Matashine wanda da wahalar gaske ya girmeta, nata dakin ta shiga ta kwaso mishi kayan wankin da ta tara, ta shiga dakin Hamza ma, da kayan suke a cikin wani kwando duk ta hada, washegari suna tare dashi ma aka kawo kayan a wanke tsaf, sun sha guga, har cikin wasu ledoji aka saka su, ta jima tana mamaki, tunda an kawo mata injin wanki, da alama ba wani amfani zaiyi mata ba, haka ma ran asabar din shekaranjiya data cika sati biyu cif akazo aka amsa, sai ta saka a ranta cewa duk sati za'a dinga zuwa karbar wankin nasu kenan. Hamza ya tashi da azumi safiyar litinin din, ya fada mata shi baya suhoor, da yaci abinci da dare ya sha ruwa shikenan.


"Daman kana azumin litinin ne?"


Ta bukata daya fada mata zaiyi azumi, kafadu yadan daga mata, yana amsawa da


"Wasu lokuttan..."


Da gaske yakan yi azumi duk sanda Allah ya bashi ikon yin hakan, yanzun dai zaiyi azumin ne dan ya daga ma Hindu kafa ta dan huta, a idanuwanta yake ganin yanda ta gaji da shi, in ba hakan yayi ba gashi can tare da wata tun kafin suyi nisa. Tun daren auren shi rabon shi da wani kafar sada zumunta, ko yanar gizo zai hau da laptop din shi yake amfani, bayason cin karo da duk wani abu da zai tunzura zuciyar shi, yana son yin iya kokarin shi na danne abinda yakeji, Hindun ita kadai ta ishe shi rayuwa, shine abinda yake fadama kan shi, amman yanajin abu mai wahalar gaske ne, sosai zuciyar shi take karyata shi. Yayi ma jikin shi wani irin sabo da canjin yanayi.


Ko abinci kala daya bai cika gamsar dashi ba, ya fiso ko da guda biyu ne ya hada a lokaci daya, balle kuma mace da yake dauka yana ajiyewa a duk lokacin da yaso, rana daya ace hakan ya sauya, abune mai wahalar karbuwa a wajen shi, amman zaiyi dukkan kokarin shi, ko dan AbdulHafiz da harya daina bude sakonnin shi yanzun, tun bayan auren shi, kullum saiya turo mishi da tunasarwa kan illar shaye-shaye da neman mata, kamar bai sansu ba, kamar yace mishi ya manta da tarin laifin hakan. Yana saka shi jin dauda a jikin shi fiye da wacce yake ji batare da tunatarwar shi ba. Dan AbdulHafiz ne, shi kadai ne yake mishi wannan shiga hanci da qudundunen.


Zama tayi a falon sama, Hamza yace ta dawo nan taqi, tunda dai duka ko ina gidanta ne, kuma inda duk taso kwana zata kwana, da ace ma zai dinga daukarta yana sauko da itane, hakan zai mata dadi, amman taga Hamza bashi da wannan tunanin sam-sam, har Korean film tasa suka kalla da hakan ya faru ko zai sanar dashi wani abu, sai ma ca yayi


"Dan Allah jibi yanda suke daga matan su, da yake su ba wani kayan nauyi suke ci ba, amman a Najeriya ba yanda zaka juya matarka yanda kake so, nauyin tumbinta kawai yafi na irin yarinyar nan hudu"


Tashi tayi ma ta shiga bandaki, badan zatayi wani abu ba, sai dan takaicin daya rufeta, ita din ba siririya bace ba, amman kuma bata da wannan jikin da yake magana, tana kuma da tabbacin ba wani nauyi zatayi ba. Kuma Hamzan ai yana motsa jiki, duk girman shi yanzun take kula da mugun lalaci yayi mishi yawa, shisa har yake tunanin ba zai iya daukar kamarta ba. A yanda yake ganin shi, ta dauka ko yini yayi yana yawo da ita a cikin gidansun nan sam bazai nishi ba. Shisa ta lallaba zuciyarta, tunda Hamza sam ba zai gaji da basu kunya ba. Tun jiya tace mishi yayo musu cefane tayi girki, har da dankali ya siyo musu, shima ta soya tayi musu sauce da dare.


"Soya dankali da wahala haka daman? Kinga da kin bari mun siyo abinmu"


Hamza yace, da yake kitchen din ya sameta yayi tsaye, har saida ya gaji sannan ya koma falo ya zauna, ita kuma haka kawai taji tana so ta dafa wani abu taci, ta gaji da abincin waje. Kuma gara ma da tasa yayo cefanen, yanzun sai ta yi mishi kayan buda baki, tun da tazo ta zauna take tunanin abinda ya kamata tayi mishi, tunda ita da safen nan shayi ta hada tasha da cincin dinta na gara da sai yau dinma ta bude shi. Hamza ya kamata ace abokan shi sunzo, ta diddibar musu, amman zatayi mishi magana, su Dimples ma sunqi leqota har yanzun, a cewar su saita gama amarcinta.


'Yan gidansu kuwa batama saka ran ganin su yanzun ba, suna dai waya kusan kullum. Kuma sukan yi chatting, amman tasan ba barinsu zuwa za'ayi yanzun ba. Sai ta kara kwana biyu. Tasan yau aka koma makaranta, ko za'a fara wani abu sai wata litinin din, Hamza ya sani shisa batayi mishi maganar tana son zuwa ba, ca zaiyi zata wahalar da kanta. Kawai abu dayane yake mata dadi har ranta, da safe kafin ya fita yace zai nemo makarantar koyon tuqi, a koya mata. Yana so ta koma makaranta da motar ta, duk idan ta juya sai wani nishadi na daban ya lullubeta, ita din, Hindu Al'amin zatayi mota, sosai ya faranta mata rai, shisa itama zatayi kokarin ganin ta faranta mishi rai a yau din nan.


*


Wanka ta sakeyi tana dauro alwalar sallar Magriba, sunyi waya da Hamza sau daya, shima kawai yaji ya ta wuni ne, sai text da yayi mata bayan la'asar


"Nikam nagaji, yunwa nakeji"


Murmushi tayi kawai, dan lokacin harta gama farfesun kaji, tayi miya, ta fere dankali ta zuba mishi ruwa.


"Sannu da aiki, Allah ya dawomun da kai lafiya"


Bai bata amsa ba, kitchen ta wuce taci gaba da aiki abinta, bata kammala komai ba sai gab da magriba. Yanzun ma kwalliya tayi mai sauqi, ta saka riga da skirt na atamfa, ta zauna gefen gado tana jiran a kira sallah, tayi saita daura dankwalin ta, wayarta ta dauka, taga Hamza ya kira wajen biyar saura, tana kitchen, sai kuma text daya turo


"Karfa ki wahalar da kanki, ba sai kin dafa mun wani abu ba"


Murmushi tayi, tanajin dadi data ajiye qwiya a gefe ta shirya mishi kayan buda baki, tasan zaiji dadi. Ta kula in zasu fita kullum suci abinci a waje ba zai damu ba, idan ya bata kunya ta wani bangaren, sai yayi wani abu kuma da zai zo dai-dai da mafarkinta. Ana kiran sallah tana mikewa dan ta gabatar da sallar ta. Da Hamza manne a ranta lokacin da ta idar, sai takejin kamar motsi a falon kasa, yanke azkar dinta tayi tana mikewa ta daura dankwalinta ta fita, aikam Hamza ne zaune kan kujera, hannun shi ya mika mata, tasa nata a ciki, ya kama ya zagayo da ita tana zama gefen shi, sumbatar gefen fuskarta yayi


"Nayi kewar ki"


Ya furta da wani yanayi a muryar shi da yasa ta fadin


"Buda baki fa zakayi"


Murmushi yayi, sai lokacin ta kula da kwandon da yake ajiye a kan kafet. Da mamaki take kallon kwandon, kafin ta kalli Hamza


"Yunwa nake ji"


Ya furta, yana fita daga nan da safe gidan Fodio ya wuce, duk acan ya sami su AbdulHafiz. Arafat ne kawai yaje musu Abuja, Fodio nacin indomie, ko Hamza bai tambaya ba yasan AbdulHafiz ma yana azumi, tunda shi kusan duk litinin da alhamis din duniya yana azumi. Sai dai ko in rashin lafiya, kusan ranar duk aiki sukayi, har sai da suka dawo masallaci sallar azahar, yana shigowa Mansy na kiran shi, ya daga ya kara a kunne, maganar farko da ta fara yasa shi yatsina fuska


"Mansy azumi nakeyi ni, bana son iskancin banza"


Dariya tayi ta dayan bangaren


"Kai da kake da amaryar da ko sati uku batayi ba, me ya kaika yin azumi?"


Numfashi ya sauke


"Ya kike?"


Ya bukata cikin son canza maganar, yana da tabbacin in tayi tsayi, Mansy zata saka shi fadin abinda bai kamata ba yana azumi, amsa shi tayi suna dan yin hira


"Yau banajin zuwa aiki, ban fita ba, ko in maka kayan buda baki?"


Kai yake girgizawa tun kafin ta gama magana


"Ba zan stressing dinki ba, zamu fita da Madam"


Ko ma basu fita ba, inya kira Anna yasan za'a kawo musu abinci idan na gida yake jin ci, ko daga gidan AbdulHafiz duk yana da wannan alfarmar, Abdallah ma zai iya sakawa a dafa mishi. Duk da yau din ba shi bane ranar farko da Mansy take mishi girki, sosai yana son kalar abincinta, da yawan ranaku idan yayi azumi tana hada mishi kayan buda baki, ko tazo ta kawo mishi, ko yaje ya karba, duk da baya bari ta shigo har cikin gidan saboda AbdulHafiz, tunda akan abincin ma yana mishi fada


"Kai baka tsoron a zuba maka wani abu? Gara ka siyi abinci a hotel ko restaurant akan ka dinga karba daga wasu mutanen"


Murmushi kawai Hamzan yayi


"Mansy ce AbdulHafiz, ba zata zuba mun komai ba"


Ba tun yanzun yasanta ba, inda zata zuba mishi wani abu, tuntuni da tayi, duk iskancin ta bai kai nan bangaren ba, ita ce mace ta farko daya fara nema fiye da sau daya, kuma ta farko da zai kira da kawar shi bayan su Fodio, bafullatana ce, a yanda take fada mishi marainiya ce, ta taso hannun kawunta da tsantsar rayuwar boko ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login