Showing 66001 words to 69000 words out of 110313 words

Chapter 23 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

kana son ta, da gaske idan kana son ta, ba zaka tayata tara zunubi ba, ba zaka nemi wasa da kwanciyar kabarin ta ba"


Kuma tunda aurenta zaiyi, zai jira, yana azabtuwa da hakan ne fiye da yanda ita da AbdulHafiz zasu taba fahimta, ba wasa yake so yayi da kwanciyar kabarinta ba, dan shima nashi yana kan layi, ita dince take barazana da nutsuwar shi.


"Ya kike?"


Ya tambaya muryar shi a dishe


"Ni ina lafiya, kai zan tambaya ya kake... Ka karbo dinkin?"


Kai ya daga mata, yanda itama take zaune cikin kujerar ta kwantar da kanta na sakashi sauke numfashi


"Kinsan kina da kyau ko?"


Yar dariya tayi


"Kai baka ganin naka kyan? Dan wanda na samu shine baka gajiya da magana a kai"


Numfashi ya sauke, idan zai kwana yana mata bayani ba zata taba gane abinda yake nufi ba, ko magana takeyi sai yaji tsikar jikin shi na mikewa, wani irin kyau take mishi na ban mamaki, jin yayi shiru, ga wani irin kallo da yake mata yasa ta fadin


"Ya turo hulu nan?"


Wayar shi da take ajiye cikin gaban motar ya mika hannu ya dauko, cireta yayi daga mukulli yana shiga WhatsApp din shi, yakai kan inda yayi saving lambar mai hular, ya mika mata, shiga tayi tana dubawa, gabaki daya sunyi kyau, kuma zasu shiga da kayanshi


"Dubu arba'in da takwas?"


Ta fadi tana ware idanuwanta, ganin kudin daya daga cikin hulunan, amman dai daga zanen ma ta fita sosai, tana dai jinjina kudin, sai taga sauran ma suna da tsada sosai, guda dayace dubu sha biyar. Fita tayi daga kan lambar mai hulunan, tana ganin wadda take saman tashi da akayi saving da 1. Anyi sako, baima bude ba


"Naga alert din. Nagode"


Tagani, batasan me ya kaita ba, kawai ta tsinci kanta da bude sakon, haka kawai taji tana son sanin kudin menene ya tura, kuma waye ya tura ma, chat din ma baiyi tsayi ba, sama tayi tana fara ganin na farko daya tura


"Hi"


Kafin a amsa shi, zuciyarta tayi wata irin dokawa


"Sunan hotel da kuma kudin ki"


Ta karanta, tana ganin yarinyar ta turo kawunan mamaki da kuma alamar tambaya


"Karki bata mun lokaci. Ba zan maimaita tambayata ba"


Anfi awa biyu a tsakani kafin ta turo


"Assa pyramid hotel. 100k"


Wannan karin shiya tura mata kawunan mamaki


"100k? Sake turomun hoton ki ingani"


Tasan ya kamata ta daina karantawa, amman ta kasa dainawa, duk da zuciyarta na mata barazanar tarwatsewa a cikin kirjinta saboda zafin da takeyi, hotunan ta shiga, yarinyar da wahala idan musulma ce, dan kanta yasha kitson gashin doki, kuma riga da wandone a jikinta da suke bayyana duk wata halitta da take da ita


"Meye abin 100k anan? 15k idan zaki iya"


Sai da ta duba mintinan da suke tsakani kafin yarinyar ta amince, zuwa lokacin idanuwan Hindu cike suke taf da hawaye. Tana karasa karanta hirar da lokacin da suka saka zasu hadun, kuma jiyane, baizo yaganta ba. Ya samu lokacin da zai hadu da wata a hotel, har ranta ta dauka ya daina, saboda bata ganin maganar shi dasu a twitter, har Mansy tun bayan saka musu rana bata ganinta, ta dauka sun rabu itama, yanzun kuwa ya dawo mata da shakku da kokwanto, ga wani zafi da kirjinta yakeyi. Hamza na kallonta, yana kallon yanda hannuwanta suke rawa, yasan wani daga cikin chat din shi ta shiga.


Gudun ruwanta ya tsaya kallo, dagowa tayi tana kallon shi da hawayenta da sai lokacin ya samu damar zubowa, dagowa yayi daga jikin kujerar motar yana mika hannu ya fisge wayar shi, ya duba yaga abinda ta karanta, dan bata fita daga kai ba, fita yayi, ya saka wayar a key, ya mayar da ita inda ya dauko


"Hulunan sunyi kyau?"


Ya bukata, yana saka Hindu kai hannuwa ta goge fuskarta


"Huluna sunyi kyau? Shine abinda zaka ce mun? Hamza karka raina mun hankali, wallahi karka nuna mun kamar baka san abinda ya faru ba"


Hindu ta fadi a masife, kallonta yakeyi a kasalance


"Me kike so ince miki?"


Yanayin yanda yake very calm, yana kallonta kamar baiga wani abin tashin hankali cikin abinda tagani dinba na kara tunzurata


"Wow.... Da gaske? Da gaske baka san abinda zaka ce mun ba?"


Komawa yayi cikin kujerar ya kwanta, yana karkato jikinshi ya zuba mata idanuwa


"Hula na baki kigani, me yasa zaki bude mun wani abin daban? Na aike ki? Nace ki duba? Me kike so ince miki bayan ban saki duba mun waya ba?"


Hannu takai zata bude motar ta fita, yayi saurin rufe murafun motar gabaki daya


"Ke kin isa ki fita kibar mun mota Hindu?"


Cikin idanuwa take kallon shi, kirjinta kamar zai bude


"Ka bude mun mota in fita, bana son ganin ka"


Wani irin kallo yake mata, dan yaga alamar nata rikicin wasa ne, bai aiketa ba, baice ta duba mishi waya ba, yana mamakin mata, idan kinsan ba zaki iya jurewa ba me yasa zaki duba tun daga farko?


"Wallahi zan baka mamaki, ka bude mun mota"


Hindu ta fadi, dan yanda takeji komai zai iya faruwa, gara ya bude mata motar ta fita tayi kukanta ko zata samu saukin tuquqin bakin cikin da take ji


"Karki mun fada, karki fara cewa zaki mun fada. Ya kike so inyi? Hauka? Kince in daina tabaki, duk kokarin da nakeyi bakya gani?"


Sosai take kallon shi, mamaki da takaici duk sun hadar mata waje daya


"Dan nace ka daina tabani shisa kake bin wasu matan? Abinda ka fada ya maka kama da uzuri? Ya maka kama da dalilin da zai saka yin abinda kayi?"


Ta karasa maganar tana kokarin mayar da hawayen da suke cike taf da idanuwanta, cike da rikici shima yake kallonta yanzun


"Idan ban bisu ba zaki bani?"


Sake jinjina murfin motar tayi dan ta fita, bata son ganin shi, ko kadan batason ganin shi, amman a rufe yake, hannu ta mika da nufin ta dauki mukullin motar da yake jiki, ya damqe hannunta yana saka dayan nashi ya cire mukullin motar ya saka a aljihun jeans din da yake jikin shi, sannan ya saki hannunta yana tsare ta da idanuwa


"Karki gwada hakuri, kinga yanzun ke kika sa na tabaki, ki bari ki huce sai in bude miki ki fita. Ba zaki koma gidan mutane a haka ace na miki wani abu ba"


Fuskarta ta rufe da hannuwanta, wasu hawaye masu dumi na zubo mata


"Babe ki bari, ki daina kukan nan, kina sa inajin ina son in rikeki in lallasheki, kuma bakya so, ki daina kure hakurina, yanzun inbi wasu kice zakiji haushi"


Sosai yasan yana bin mata tun kafin su hadu, amman bashi da wannan jarabar haka sai bayan ya hadu da ita, rashin samunta yasa shi son kashe wutar da take kunna mishi da duk macen da ta tari gaban shi, amman a daddafe yake lallaba rayuwar shi, ita dince taki fahimtar shi, taki gane halin da yake ciki, gyara zaman shi yayi cikin motar, yana sauraren sautin kukanta, harta dago fuskarta, ruwan da yake cikin motar ya dauka ya bude yana mika mata, harar shi tayi da idanuwanta da sukayi ja


"Yi hakuri, ki sha ruwa to dan Allah"


Karba tayi tana shan ruwan, ya duba agogon shi, shidda harda arba'in


"Are you calm? Kice mun idan na tafi ba zaki sake yin kuka ba"


Shiru tayi ta kyaleshi tana kauda kanta gefe, har lokacin kirjinta kamar an zuba garwashin wuta takeji


"Babe... Kinsan a gajiye nake, kaina na ciwo wallahi, karki karamun, karki mun fushi. Ba laifina bane ba, bansan ya zanyi bane ba"


Ya fadi yana wani irin sauke murya da ya kashe mata jiki, kallon shi tayi


"Bana so, zuciyata na ciwo wallahi, dan Allah ka daina"


Ta karasa maganar muryarta na karyewa, kai ya jinjina mata yana hade hannuwanshi waje daya


"Karki mun fushi to, kinji"


Kai ta jinjina mishi, tasan idan har tanaso ta canza shi, dole sai tayi kokarin fahimtar shi


"Nagode... Kinsan ina sonki ko?"


Kai ta sake daga mishi, kuma soyayyar nan da yake mata ita zatayi amfani da ita wajen kokarin canza shi, mukullin ya dauko daga aljihun shi yana bude mata murfin motar


"Baki ce kina sona ba"


Ya fadi yana daga mata gira, murfin motar kawai ta bude tana ficewa, yau bazai sami wannan na tunda laifi yayi mata.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 19


"Hello"


Ta furta muryarta can kasan makoshi, kallo daya zakaiwa fuskarta ka fahimci yanda take cikin damuwar da tun jiya kowa yake dauka jimamin rabuwa da gidane


"An daura, Hindu an daura"


Hamza ya fadi daga dayan bangaren, runtsa idanuwanta tayi tana bude su, hadi da sauke wani irin numfashi, tun dazun take kallon agogo tana jiran karfe goma tayi, tana jiran taji canjin da marubuta kan fadi duk idan an daura auren ka, sai dai shiru, bataji komai ba, bataji a jikinta cewa an daura ba, da bai kirata ba sai dai idan taga dawowar wani daga cikin mazan gidan, yanzun ne dai muryar shi da tsantsar dokin da yake ciki yasa zuciyarta wani irin zirga-zirga a cikin kirjinta. Amman a kasan wannan akwai wani ciwo da yaki fitar mata tun jiya.


"Okay..."


Ta furta, tana jin hayaniya daga dayan bangaren kafin ta sauke wayar daga kunnenta tana katse kiran ta ajiyeta kan mudubi


"Ke anata neman ki, kin karya?"


Biebee data leqo dakin ta bukata, dan su sun tafi wata hidimar, kai Hindu ta girgiza mata


"Sugar bana jin yunwa wallahi"


Cewar Hindun kamar yanda takan kira Biebee wani lokaci, dan kallonta Biebee tayi


"Zaki zauna ulcer ta kamaki, aure fa akayi miki ba wani mugun abu ba, is not like ba zaki dinga zuwa gida ba"


Murmushin karfin hali kawai Hindu ta iya yiwa Biebee din, tana tsintar kanta da kasa furta komai


"Ni dai zan hado miki tea"


Ta karasa maganar tana juyawa, numfashi Hindu ta sauke, tana saka hannu ta gyara zaman dankwalin da yake nade a kanta, ba wata kwalliya bace mai nauyi a kan fuskarta, amman tayi kyau matuka, ba kunshin hannunta ba, yanayinta kawai idan ka kalla zaka gane itace amaryar, taji dadin kasancewar ita kadai a cikin dakin. Biebee batafi mintina biyar ba ta sake dawowa, wannan karin tana shigowa har cikin dakin, ta mika ma Hindu kofin shayin data hada shi da kauri sosai yanda zai rike mata ciki. Sannan ta fice daga dakin, kofin Hindu ta daga takai bakinta ta kurba a hankali, sai taji idanuwanta sun cika taf da hawaye


"Oh shit..."


Sune kalman farko da Hamza ya furta a daren jiya da misalin karfe tara da rabi na dare, bayan ya daga video call din da tayi mishi da alama babu shiri, bai kuma yi nufin ya daga ba, abin yazo mishi a shammace, yanda take ganin yanayin hoton na rawa, da alama so yakeyi ya kashe, amman a rikice yake


"Ka sallameni dare nayi"


Ta sake jin muryar yarinyar da ko idanuwanta ta rufe tun jiyan tana sake dawo mata, kafin Hamza ya kashe video call din yanata maimaita


"Oh shit"


Abinda ya taso yai tsaye bayan zuciyarta har yanzun tana jin shi, yaki fitowa, kuma yaki wucewa, hotunan kwalliyar da akayi matane da ta tura mishi taga baice komai ba, kuma tun da yamma basu kara magana ba, shisa ta kira shi video call din, dan tayi kewar shi a yinin ranar ba kadan ba, tana kuma da tabbacin ba bacci yakeyi ba, har yanzun tana dana sanin kiran shi da tayi. Yafi mintina talatin tsakani kafin ya kira wayarta, zuwa lokacin hawaye ma ta neme su ta rasa, harabar gidan ta fita dan ta samu sararin yin video call din dashi, jikinta babu inda baya rawa lokacin da ta kara wayar a kunnenta


"Bansan me zance miki ba"


Ya furta daga dayan bangaren yana ba hawayen da take ta nema damar zubowa


"Ran daren auren mu? Hamza ranar daren auren mu? Me kake nema? Me yake damunka da ba zaka iya jira ba? Awanni nawa suka rage mana? Me yasa zakai mun haka?"


Tana jin yanda yake sauke numfashi


"Bansan me zance ba"


Ya sake furtawa


"Karka kara cemun bakasan me zaka ce ba, wallahi karka kara"


Tayi maganar a masife


"Idan nace miki bazan iya jira bane zaki yarda?"


Numfashinta taji yana mata barazana, Hamza so yakeyi ya kasheta taga alama, inda wani yace mata wata rana kirjinta zaiyi kamar an dora dutse haka ba zata yarda ba, amman yau har wuta take ji kamar tana ci a cikin shi saboda zogin da yake mata


"Bazan iya jira ba Hindu, in ba mutuwa kike so inyi ba"


Bakinta ta bude tana neman iska ko zata samu tayi numfashi, kafin dakyar ta iya cewa


"Kai zaka kasheni Hamza, so kakeyi ka kasheni"


Tana jin numfashin daya sauke


"Karki karamun abinda nakeji, dan Allah yau kawai, yau kawai ki kyaleni. Awanni kadan ya rage mana kamar yanda kika ce, ki kyaleni inyi abinda zan samawa kaina sauki kafin su cika"


Ya karasa maganar yana kashe wayar, saukewa tayi daga kunnenta, wasu hawaye masu dumi na zubar mata lokacin da take danna wayar tana kiran shi, bata saka a kunne ba sai da taga ya daga


"Babe"


Ya kira da wani irin yanayi a muryar shi


"Wanne bangare na ki kyaleni ne baki gane ba?"


Hannu tasa ta goge fuskarta


"Baka isa ba, wallahi kayi kadan kaimun abinda kai mun sannan kace in kyaleka"


Ta karfi da yaji Hamza ya koya mata masifa, duk da bawai bata fada bane ba, na yanzun ne yafi na da, bala'in shi yasa bata shakkar gaya mishi magana lokutta irin haka


"Idan baki kyaleni ba ya zakiyi dani? Na zaba miki abinda yafi sauki ne amman kina so ki karama kanki ciwon kai"


Dariya tayi da bata da alaka da nishadi sam, zuwa yanzun batajin akwai wani abu, ko wata magana da zai fada ta bata mamaki sam


"Babu yanda zanyi da kai, amman batamun ran da kayi sai Allah ya saka mun"


Ta furta muryarta na rawa, bata jira mai zaice ba saboda kukan da takeji yana neman kwace mata, ta kashe wayar. Kan cinyarta ta dora tana hade kanta da gwiwa wani irin hawaye masu dumi na zubo mata, kamar yanda ta hada shi da Allah yanzun, haka zataci gaba da hada shi da Allah har saiya canza, tana da yakinin zai canza, ba zaizo mata da sauki ba, amman zata jure, zatayi wannan jahadin, zata canza shi. Idan tana gidan shi hakan zaifi saurin faruwa, zata tabbatar da ita kadai ta ishe shi, saboda zatayi mishi duk wani abu da yake so.


Kiran shi ne ya shigo, sai da taja hanci, tana sake goge fuskarta, tukunna ta dago kai, tana daukar wayar da ta yanke, ajiyar zuciya kawai take saukewa, sake kira yayi, ta daga ta kara a kunnenta


"Ni zaki hada da Allah? Hindu ni zaki hada da Allah? Tashin hankali kike nema dani ko?"


Dafe kanta tayi tana furta


"Kai! Kai jama'a, oh Allah na"


Saboda batasan me kuma yake so tayi ba, batasan ina yake so ta tsoma ranta ba, shi yayi mata laifi, amman yana neman yafita rigima akan abin, zuciyarta ciwo takeyi, baisan ya bata hakuri ko zataji sanyi ba, dan lallashi ma bata samu ba, amman shi yake so ya fita hayaniya


"Me kike nufi?"


Kai take girgizawa


"Babu komai, Hamza babu abinda nake nufi, sai da safe"


Har ranta wayar tayi niyyar kashewa, bata da karfin biye mishi, abinda takeji kawai ya isheta


"Babban kuskuren da zakiyi ki kashemun waya, wallahi karki kashe mun waya Hindu?"


Wasu hawayen taji sun sake zubo mata, kashedin shi na zauna mata


"Ya kake so inyi? Me kake nema dani? Baka tausayina ne? Baka san me nake ji ba ko?"


Tayi maganar muryarta na karyewa, tana jin yayi shiru, kafin cikin sanyin murya yace


"Kece bakya tausayina saboda bakisan halin da nake ciki ba, da kinsan me nakeji a daren yau da baki nemi hadani da Allah ba, kamar zunuban da nake dauka da kaina basu min yawa ba, shine kike son karamun wani"


Kara karya mata zuciya yake, balle cikin yanayin da yayi maganar kamar shima zaiyi mata kuka


"Ko dan kin fini saurin kuka? Shisa duk abinda zai faru nine mai laifi?"


Batasan me zatace ba


"Ki bani hakuri, kin batamun rai bayan banajin dadi, Babe ki bani hakuri"


Numfashi Hindu ta sauke


"Kayi hakuri"


Ta tsinci kanta da furtawa ko wayar zata zo karshe, numfashi mai nauyi ya sauke mata cikin kunne


"Ya wuce, ina son ki, kinsan haka ko?"


Kai kawai ta daga, kafin tace wani abu ya rigata


"Sai da safe, ki kulamun da kanki"


Yana kashe wayar kamar shikenan, kamar idan abinda yake ikirarin tayi mishi ya wuce a wajen shi itama abinda yayi mata ya wuce a wajen ta, kamar yarinyar da yabi yau laifinta ne shisa baiga dalilin da zai bata hakuri ba, takai awa daya a zaune a wajen, sai da taga bayan ciwon zuciya, zazzabin ciwon sauro na gab da kamata tukunna ta tashi ta shiga cikin gida, baccin kirki ma bata samu ba, dan duk yanda zata rufe idanuwanta sai taga Hamza da wasu matan. Haka ta tashi safiyar yau komai bayayi mata dadi, shisa bata ma neme shi ba, shima din daya kira tsintar kanta tayi da rashin son yin magana da shi.


Hawayen da takeji suna shirin zubo mata takai dan yatsa tana sharewa. Kukan zai jira, nan da yan wasu awanni zatayi mai dalili, dan da wuri za'a kaisu. Tea dinta ta kara kurba, tun da yan uwan Baba dana Anty, harda ma wasu cikin na Mama sukaje jere suka dawo suke maganar gidanta, kujeru saiti biyu Baba yai mata, Hamza ma yaso subar maganar kayan dakin, tadai fada mishi Baba bazai taba bari ba, amman taji suna cewa dakunan suna da yawa, ko falo guda hudu ne a cikin gidan, a biyu kawai sukayi jere, sauran ma duk an kawo kayan daki suna lullube a cikin ledoji ko bude su ba'ayi ba.


Kowa maganar gidan yakeyi, har ranta wannan yayi mata dadi, gidan da take mafarkine, ko a hoto Hamza bai taba nuna mata ba, basu ma tabayin maganar gida dashi ba har saida akazo maganar yin jere tukunna. Ance gidan Khadee ma babu laifi, duk da karamine, daki biyu, amman a iya karfin shi, yayi kokari matuka, ko ina yasha tayal. Khadee dinma da kanta sai da tazo cikin murna tana fadin


"Ke banza kinga yanda ake maganar gidan ki? Ance ya hadu wallahi, kina zuwa kiyumun video"


Murmushi kawai tayi, Hamza ya rage mata walwalar da ya kamata ace tanayi, ya kamata ace tana tunanin Dinner dinta da za'ayi karfe takwas na ranar. Amman zuciyarta ciwo takeyi mata, dakyar ta samu ta karasa shanye shayin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login