Showing 96001 words to 99000 words out of 110313 words
Chapter 33 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
ta mikama Allah lamurranta, hawaye ma a kwanakin nan sun kaurace mata. So take kawai ta juye abinda yake cikinta ko zata rage wani nauyin. Gashi yan gidan kowa yana kokarin ganin murmushi a fuskarta, musamman Asma da ko kwanciya ta juya sai taji ta tambayeta ko lafiyarta. Daren jiya ma sai da tace
"Asma lafiyata kalau fa, kiyi bacci kin ji ko?"
Anty kanta tana iya lekasu fiye da sau biyar kafin wayewar gari. Yau ma ganin yanda duk idan ta wuce suna binta da ido kamar mai shirin breaking a kowanne lokaci sai ta koma tana tausaya ma damuwar da suke ciki. Shisa tana idar da isha'i bata kwanta kamar yanda takanyi ba, ta fito falo ta zauna ayi hirar da ita, suna kallon shirin "Kwana casa'in" a tashar Arewa24.
"Ni fa Mal. Alin nan bala'in kunnani yakeyi"
Asma ta fadi, Jafar na jinjina kai
"Ai wawane, yanda yakeyi kamar yana da kyau shine abinda yafi batamun rai"
Dan murmushi Hindu tayi
"Kuji ikon Allah fa, celebrity ne fa"
Wani irin tsaki Jafar yaja
"Kuyita rage mishi dai kunji"
Cewar Anty da take zaune a gefe, da yake girkinta ne ranar. Mikewa ma take shirin yi ta shiga bangaren Baba, sai gashi ya shigo falon
"Me ake kallo haka?"
Hindu da murmushinta ya fito daga zuciyarta yanzun ta riga kowa amsa shi
"Baba..."
Ta furta cike da kaunar da takeyi mishi
"Hindu... Kinci abinci?"
Baba ya tambaya. Ta bude baki zata amsa shi, sallamar su Anna ta katse ta, sai da taji zuciyarta tayi wani irin dokawa kamar zata fito waje saboda wani irin firgici da ta tsinci kanta a ciki, har suka gaisa da Anty, aka basu wajen zama, sam bataji ba, hankalinta na kan Hamza da yake tsaye a gefe kamar magen da aka tsoma a ruwan sanyi. Kanshi sadde yake a kasa, lokacin da Anty tadan taba Hindu ne ta kula da har su Anna sun zauna, Asma da Jafar ma bata ga barin su falon ba
"Ina wunin ku"
Hindun ta iya furtawa muryarta na karyewa
"Lafiya kalau Hindatu, sannu kinji"
Appa yai maganar kamar yana neman wata Hausa da ta dace yayi amfani da ita, Anna kuwa duk kunya ta gama rufeta, tama kasa cewa komai, wani irin shiru na ziyartar falon, kafin Appa ya fara magana
"Wallahi Alhaji Aminu mu bamu san abinda yake faruwa ba sam sai yau din nan, yana zuwa ya same mu da maganar muna tahowa"
Kai Baba ya jinjina
"Haba bakomai, ai zance ya rigada ya kare ma. Har an kwaso kaya"
Kallon Hamza da ya kara sunkuyar da kan shi Appa yayi, kafin ya mayar da hankalin shi kan Baba
"Subhanallah..."
Sai dai bai samu damar furta wani abu ba, Baba ya riga shi
"Da ya fada muku ya saketa, ya gaya muku cikin dare ya korota waje? Ana tafka ruwan sama?"
Wannan karin Anna ce ta kalli Hamzan cike da bayanannen mamaki a fuskar ta, so take ya kalleta, so take ya karyata mata abinda Baba ya fada, dan tasan yaronta mai tausayi ne, Hamzan ta ko mace mai ciki yagani tsakiyar dare ana tafka ruwa zai tsaya ya taimaka mata, dan ta ba zai aikata wannan halin da zata alaqanta shi da na marassa tunani da tausayi ba, dan bata taba jin ko yan unguwa sun mishi shaidar zalunci ba
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Appa ya fadi yanajin lamarin yafi karfin shi, da Baba yace an kwaso kaya sai da ranshi ya sosu da rashin neman su da baiyi ba dan ai kokarin sulhunta lamarin. Yanzun kuma da yaji dalili, sai yaga sunyi mishi matuqar kokari da suka ma basu wajen zama.
"Bana so duk mu bata lokacin juna, aurene kaddara ta hada, yanzun kuma ta raba. Sai muyi musu addu'a Allah yasa hakan shine alkhairin su, ba zance zumunci zai kare ba saboda rabon da yake jikinta....aure kam in shaa Allah karshen shi kenan"
Baba ya karasa maganar da dukkan zuciyar shi, dan yaga takardar sakin, kuma a rubuce saki dayane Hamza yayi. Hindu tasan yagani, saboda Anty ta fada mata, su duka basu san saki biyu bane ba, har yanzun akwai kome a tsakanin su da Hamza, komen da ko a mugun mafarki bata fatan ya faru da ita balle kuma a gaske
"Baba dan Allah kayi hakuri, nayi kuskure nasani, amman kayi hakuri"
Hamza ya fadi zuciyar shi na wani irin radadi, ganin kallon da Baba yayi mishi yasa shi kallon Hindu
"Hindu ki bashi hakuri, kinsanni, ke kinsan abinda su basu sani ba a kaina. Ba zan sake ba, wallahi ba zan sake ba... Ki basu hakuri"
Ya karasa maganar yana takowa ya shigo tsakiyar falon ya tsugunna a gabanta batare daya damu da su Anna da suke zaune ba, ballantana kuma su Baba. Bayajin akwai macen da zata zauna da shi da halayyar shi kamar Hindu, baima san yanda yake son ta ba sai yanzun da yake ganin da gaske raba shi za'ayi da ita, da gaske sukeyi ba zasu hakura ba
"Ba zamu bar juna ba, duk abinda zai faru ba zamu bar juna ba, zaki zauna da ni har in canza, zakiyi hakuri dani har in canza..."
Hamza yake furtawa yana sauke idanuwan shi cikin na Hindu da suke cike taf da hawaye
"Kome zai faru ba zan barka ba, na yafe maka kuskuren ka na baya, zanyi kokari in yafe maka kuskuren ka na gaba"
Hindu ta karasa mishi hawaye na zubar mata, wannan shine alkawarin da sukai ma juna bayan ya sake ta, lokacin da yaga da gaske ta janyo akwati tana hada kayanta, hakurin daya bata a ranar tayi tunanin shikenan, ta dauka wani abu ba zai taba sake shiga tsakanin su daya danganci shan giyar shi ko Mansy ba. Shisa ta tayashi suka binne rigimar, babu wanda yaji ko yagani. Hannuwanta duka biyun ta saka tana goge fuskarta, wasu hawayen ne suke sake zubowa kamar an bude famfo
"Wannan alkawarina ne, nayi kokarin cikawa, ka manta naka?"
Wani abu da yaji ya tokare mishi makoshi yake kokarin hadiyewa
"Zaka canza, ba zaka sake dukana ba, ba zaka sake shan wani abu ba, matsalar mata ba zata sake zama dalilin rigima a tsakanin mu ba..."
A rayuwar shi ya lissafa abubuwa da dama da zasu saka shi kuka, amman bai hasaso mace bace ba, ko bayan da ya auri Hindu bai dauka rana irin ta yau da hawayen shi zasu zuba a kanta zaizo ba, sai yanzun da yaji idanuwan shi sun cika taf da hawaye
"Zan dora alhakin auren ka akan kaddara, amman yi maka uzuri a lokutta da dama kuskurena ne, ba zan sake maimaitawa ba, Hamza bazan sake maimaita wannan kuskuren ba"
Kai yake girgiza mata, idan yai magana gunjin kukan da ta karashe zancenta da shi zaiyi shima, fuskar shi ya dafe da hannuwa biyu. Daga Anty da take zaune, Baba, Anna har Appa jikin su ya gama yin sanyi. Kaddarar yaran nasu ce take taba su har kasan zukatansu, bude baki Hindu tayi zata roke shi daya tashi daga tsugunnan da yayi a gabanta, ya daina zubar mata da hawaye karya sa zuciyarta ta karaya, kar ya yaudareta kamar yanda ya saba, wani irin ciwo daya tsirga mata har ranta tayi zaton kashin bayanta ne ya karye
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un.... Baba bayana... Bayana ya karye Baba..."
Hindu ta furta cike da wani irin rauni da yasa Anna da tafi kusa da ita kamata, saboda ta kula da abinda yake bin kafafuwan Hindun, tasan naquda ce ta taho mata gabaki daya, ita da Anty suka kamata, banda salati babu abinda yake fita daga bakinta har suka samu suka karasa mota. Anna ce take tambayar Hamza asibitin da Hindu take zuwa, kafin su duka su dunguma zuwa asibitin.
9/19/20, 8:05 AM - mmn khalid: 30
BAYAN AWA GOMA
Ya sha kwana zaune, amman wannan ne awanni goma mafi tsayi a rayuwar shi, har Baba da yasan haushin shi yake ji sai da yai mishi magana ya zauna. Tunda duk a asibitin suka kwana, amman yaki, so yake kawai a fito musu da wani labari koya yane, shi baima san mata suna dadewa haka basu haihu ba. Da ba a jam'i yai sallar asuba ba, tabbas da ba zaisan abinda yake karantawa ba. Ruwa ma Anna ce ta bashi ya samu ya kurba yana jiqa makoshin shi.
Tunda daddaren Anna da kanta ta koma gida cikin kayan babies din da aka siya ta tattaro duk wani abu da take tunanin za'a bukata ta dawo. Amman ba'a sanar da su ta haihu ba sai karfe bakwai na safe, duk wasu maganganu da ake fadi Hamza bayajin su, kalaman farko kunnuwan shi suka tsinta suka koma suna rufewa ruf
"Ta samu 'yan biyu duk mata..."
Ba dan baisan yara biyu bane ba, baima san kafafuwan shi sun gaji da tsayuwa ba sai da yaji suna rawa, babu shiri yabi bango yana samun waje ya zauna, numfashi yake fitarwa kamar wanda yayi gudu, ranar da aka fada musu yara biyune ita kadai taje asibitin, tun a hanya take kiran shi in yana kusa su hadu a gida, ba zai manta yanda ta kama hannun shi ta dora cikinta ba
"Yara biyu, yara biyune a cikina"
Tun da ta samu cikin ranar ne karo na farko da yaji kaunar koma meye a ciki har bayan zuciyar shi, ranar ne yaji kamar yana bangare daya da wani abu mai matuqar muhimmanci
"Zamu basu mamaki..."
Ya furta da murmushi a fuskar shi
"Sai kowa yazo da tunanin yaro daya zasu ga biyu"
Kai take daga mishi, sai yanzun yake jin ashe ya adana sautin dariyarta a wani bangare na zuciyar shi. Ya adana abubuwa da yawa a tare da ita, abubuwan da yake kula da su yau da kullum, yanda take zagaya hannuwanta kan cikinshi ta dora fuskarta a bayan shi tana rungume shi duk idan tayi tunanin bai hakura da rigimar da sukayi ba, ko da shine da laifi
"Fushi kake har yanzun? Ni na hakura kaine za kai mun fushi"
Takan fadi, abubuwa da yawane suka dawo mishi, sosai yayi nisa cikin tunani, dan sai da yaji an taba mishi kafada tukunna ya daga kai yana kallon Anna
"Zaka iya zuwa kagan su"
Ta fadi farin ciki shimfide a fuskarta, ga yaran Ma shaa Allah, so take ta tafi gida yanzun, tunda hankalinta ya kwanta. Ta watsa ruwa, su sa suke tunanin yaro ko yarinya guda daya saiga biyu. Siyayyar kaya bata kare ba, harta gama tsara yanda jikokin nata zasu ga gatan da basu taba tunani ba. Kai ya daga ma Anna yana mikewa da kyar, dakin ne yake juya mishi, ji yake kamar yana yawo akan gajimare. Dakyar ya iya shiga dakin da Anna ta nuna mishi yanajin tana fadin
"Hindun tana hutawa saboda ta sha wahala sosai, amman zaka iya ganin yaran su..."
Ko kai bai iya daga mata ba, ya tura hannun shi yana shiga cikin dakin. Karo yaci da wata Nurse daya dan daga ma kai, muryar shi dauke da wani yanayi yace
"Ina yaran?"
Gaba tayi yana binta a baya, yanzun kam jin shi yake yana yawo akan gajimare, jin shi yake kamar a cikin mafarki. Bai sake jin yana wata duniya ta daban ba sai da Nurse din ta dauko yarinya daya tana sakawa a hannun shi, dokawa zuciyar shi takeyi kamar zata fito waje, ya kasa kallon fuskarta saboda yanda zuciyar shi take mishi rawa. Gyara yarinyar da yake ji tana hannun shi batare da yaji nauyinta ba yayi, yana dan gyara dayan hannun shi ana saka mishi dayar, bai iya kallon su ba sai da yaji fitar Nurse din daga dakin. Da wani irin bugun zuciya ya sauke idanuwan shi akan hannun shi na dama, bacci takeyi. Kiran sallah yayi mata cikin kunnanta, yana juyawa yayi ma dayar yarinyar ma. Kafin ya sake mayar da hankalin shi kan yarinyar da idanuwan ta suke a bude.
A duniyar shi kaf ya dauka bayan Anna ba zai sake dora idanuwan shi kan macen da zaiji kaunarta har cikin bargon shi ba, macen da zaiji yana so ya kare daga duk wani abu naqi da Allah ya saka a karkashin ikon shi. Sai ga mata biyu a hannun shi, mata biyu da in yana da iko ko sauro ba zai kusanto inda suke da sunan cutarwa ba. Mutane da yawa sun dauka hawaye shine karshen karayar zuciya, akan yaran da suke hannun shi idan idanuwan duka ake bukatar gani a kasa zai ciro su ya ajiye.
"Suhana..."
Ya furta daga wani lungu na zuciyar shi yana kallon yarinyar da idanuwanta suke a bude kamar tasan abinda yake faruwa. Fassarar sunan ta shine "Kyakkyawa". Shine kuma suna na farko da yazo cikin kanshi daya kalleta, watakila dan jinin shi ce, dan ta fito daga wani bangare na jikin shi, ko da bata da kyau zuciyar shi ba zata taba yardar mishi da hakan ba. Dakyar ya iya dauke idanuwan shi daga kan Suhana yana kallon dayar yarinyar da take bacci. Akan ce jarirai basu da kama, amman yan biyun da akafi sani da identical a turance tun suna jarirai kamannin su iri dayane. Nashi yaran basu zo a wannan jinsin yan biyun ba, kowacce kamanninta daban yake.
Kallon yarinyar da yakeyi ne yasan labarin nutsuwa yake ji, kwanciyar hankali na daya daga cikin abubuwan daya manta yanda ake jinsu, sai yanzun, bai taba cin karo da wata halitta mai nutsuwar yarinyar da tayi kwance luf a hannun shi tana bacci ba, a duniya yara sunfi kowacce halitta yarda, ko idanuwanta bata bude ba, ballantana tasan waya dauketa, ta bashi dukkan yardarta tun kafin tagan shi
"Amna..."
Sunan ya kubce daga labban shi, sau daya suka taba maganar sunayen yara da Hindu, tace mishi tunda sun zabi barin sanin jinsin yaran har sai sun haifesu, sunayen ma su bari a haihun, ba zai wahala ba. Yasan yayi sonkai daya zabar musu sunaye batare da yaji ko tana da wani zabi nata ba.
"Daga yau, zuwa ranar karshe da nake da aron ta, ba zan taba yin abinda zai baku kunya ba, ba zakuyi dana sanin fitowa daga jikina ba"
Ya furta a cikin zuciyar shi yana kallon yaran. Kafafuwan shi ciwo suke, amman bayaso ya zauna ya tashi Amna, bayaso ko motsi mai karfi yayi
"Ke me yasa ba zakiyi bacci ba? Ko yunwa kike ji?"
Yake maganar yana kallon Suhana da yasan karonta ne na farko da taji yaren fulatanci. Dariya yayi me sauti yana sake kallon su. Wani dan labule ne tsakanin inda yake tsaye da gadon da Hindu take a kwance, karasa takawa yayi yana shiga wajen, baisan ko idanuwanta biyu ba ko kuma takun tafiyar shine ya tashe ta, sai lokacin yayi dabara yana zama kan kujera
"Hey..."
Ya furta yana kallonta, amman idanuwanta ba a kanshi yake ba, yana kan yaran da yake hannun shi. Ta gansu, ta karbe su, dan an saka mata su a hannuwanta tun da sauran jini a jikin su, ta rike abubuwa da yawa masu daraja da hannuwan, amman sune na farko da taji har cikin tsokar jikinta. Bata kara fahimtar kaunar da take tsakaninta da Baba ba saida ta rungume su a kirjinta, sai take hasaso kalar kusancinta da Anty. Tana kara wata daraja ta daban a idanuwanta, tana da tabbacin wannan matakine da mata suke takawa a rayuwar su duk ranar da suka rike nasu yaran a hannuwan su.
Ranar zaka kara sanin darajata ta uwa, ranar da zaka fahimci dalilin da yasa take dora duk wani farin ciki naka a saman nata, yanda rayuwarta kacokan take tsayawa saboda taka ta cigaba. Kamar mahaifiya a duniya da zagayenta babu, duk yanda kake tunanin ka fahimci muhimmancinta ba zaka gane ba sai ranar da bayanka yai amsawar farko da ciwon naquda.
"Na kasa yarda suna hannuna, yaran mu Hindu, muna da yara"
Kai ta iya daga mishi saboda idanuwanta da taji sun cika taf da hawaye, dayan hannunta da babu karin ruwa, duk da akwai plaster a jiki ta dan mika mishi, tana saka shi yin danara ya mike ya taka har bakin gadon, sosai ya rankwafa yana mika mata yarinyar da take bacci har lokacin, tana nade tsaf cikin farin towel yanda ko kayan jikinta baka iya gani
"Amna"
Ya furta bayan ta karbi yarinyar, hakan yasa Honduras ware mishi idanuwa cike da son karin bayani
"Peace..."
Ya fadi ma'anar sunan da harshen turanci, dan ya tsaya a tsakanin nutsuwa da kwanciyar hankali, ya rasa asalin ma'anar da yaren Hausar da har yanzun mutane da yawa suke rainata a bakin shi. Har a ranshi ma baiyi niyyar musu magana da wannan yaren ba, Idan Anna taji zatayi kishin yanda ya yanke hukunci yi musu fulatanci. Idan suna da rabon jin nata yaren duk in suna tare da ita zasu tsinta. A bakin shi kuwa da yaren Appa zasu tashi, da jinin fulanin da yakeji har a kasan zuciyar shi
Rike yarinyar Hindu tayi tana lumshe idanuwanta, kaunarta na ratsa duk wani lungu da sako na ruhinta. Kujerar Hamza ya janyo sosai yana zama. Hannunta da yagani a kumbure ya mika nashi ya kama, tana janyewa da sauri kamar wanda yake shirin goga mata wani abin, a cikin idanuwanta yake fara ganin abinda yasa zuciyar shi mummunar bugawa, kafin kwakwalwar shi ta fara fahimtar da shi kuskure na biyu mafi girma da yayi bayan na korar ta, shine kin furta kalaman ya dawo da ita kafin ta haihu, ganin ya fahimci hannunta da ta janye yasa ta jinjina mishi kai tana tabbatar mishi da gaske ita ba halalin shi bace yanzun
"Zan ma Appa magana, sai a sake daura mana aure, muna da igiya daya a tsakanin mu..."
Yake fadi cikin tsantsar tashin hankali, musamman da tun da ya bude bakin shi take girgiza mishi kai, hawaye da yake cikin idanuwanta yana zubowa
"Auren mu ya rigada ya kare..."
Wannan karin shine yake girgiza mata kai, idan kukan take so yayi shima zaiyi, zaiyi komai dan karta rabashi da kanta
"Ya kare Hamza... Ya kare..."
Kan dai yake girgiza mata
"Ki kalle su, karki raba musu iyaye daga zuwan su"
Ko tana da hannun share hawayenta ma ba zatayi ba, tunda basu daina zubowa ba, naquda takeyi da tabbacin ba zata taba komawa auren Hamza ba, Allah ta roka ya bata shi, tana naquda take rokon ya musanya mata da mafi alkhairi idan har Ya kadarta mata sake wani zaman auren, zatayi, zata sake daga farko batare da maimaita kuskuren da tayi a baya ba. Yara da yawa sun tashi batare da iyaye ba, wasu ma