Showing 93001 words to 96000 words out of 110313 words

Chapter 32 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

da wata mace manne a jikin shi, ko dankwali babu a kanta, asalima rigar jikinta ko gwiwarta bata karasa ba, ita kanta Hindu daga inda take tana ganin duk wata halitta ta jikinta.


Harta karasa saukowa daga benen abin na mata kamar a mafarki, saboda tasan duk abin Hamza ko da wasa bai taba shigo mata da wata mace gida ba, yanzun ma yana kokarin boye mata abinda yake faruwa da wannan fannin na rayuwar shi. Ko giyar shi da tagane bai daina sha ba, ya sha yau bata tunanin zata gaya mishi ya shigo mata da wata mace cikin gida haka. Ta kasa yarda harta karasa gab dasu ta tsaya, tana karewa Mansy da ta boye bayan Hamza kallo.


Dariya Hindu tayi me sauti tasan mafarkine daman, saboda Mansy tafi tsana duk a cikin matan da yake bi, shisa ta kasance macen da mafarkinta ya hango mata a tare da Hamza


"I can explain, ba abinda kike tunani bane ba"


Hamza ya fadi yana kallon Hindun, har ranshi ba abinda yasan take tunani bane ba


"An shigar mata gidane, bata da inda zataje, kwana kawai zatayi da safe sai tasan ya zatayi. Nasan zaki fahimta"


Kallon shi Hindu tayi, tana saka hannu ta taba kirjin shi, taga yana nan dai, itama kanta ta mintsina taga da gaske na mafarki bane ba, wani irin ashar ne ya kubce mata, sam batasan duk zagin da takeji tana adana shi bane sai bayan ta auri Hamza, Mansy da ta kara shigewa bayan Hamza ta mika hannu ta fisgo


"Dan ubanki da nace ki kyalemun miji baki jini ba ko?"


Hindu ta karasa maganar wani irin kishi na lullube mata idanuwa, dan batasan lokacin da ta daga hannu tana shararawa Mansy mari ba, ko kadan bataji nauyin cikinta ba, niyyar fara jibgar Mansy din takeyi kamar ganga, dakyar Hamza ya banbare Mansyn da ta koma gefe tana rawar jiki, ita iya tashin hankalin da ta gani yau ya isheta, maruka tasha sunfi goma a hannun barayin nan, dan daya sai da yaso keta mata haddi, ogan nasu ya tsawatar mishi, tasan haushin hakan yasa shi shimfida mata wasu marukan.


"Hindu... Hindu..."


Hamza yake fadi, yasan ta iya rigima saboda ba karamar mace bace zata iya kallon idanuwan shi ta biyema tashin hankalin shi, amman ko dukanta yayi bakinta baya mutuwa, kuma saita fada mishi duk wani abu da tayi niyyar fada ko zai kasheta. A girman jiki Mansy ta fita, amman idan zai barsu, duk da cikin jikin Hindu dukan tsiya zatayiwa Mansy yasani


"Ta fitar mun daga gida...dan ubanki ki fitar mun daga gida kafin in karairayaki"


Kamata Hamza yakeyi tana zillewa, in bata jibgi Mansy ba sam ba zataji dadi ba, ko kuka ta kasa, haka Hamza yake janta harya samu ya shigar da ita daki


"Ina kike so taje? Bakiji nace miki barayi sun shigar mata gida ba?"


Kallon shi tayi


"Idan baka fitar mun da ita daga gida ba ku biyun zaku ga tashin hankalin da baku taba gani ba"


Idanuwan shi ya runtsa, kan shi yayi nauyi sosai, kuma ranshi ya fara baci


"Bafa gidanki bane ba, ina da damar da zan kawo wanda duk naga dama...bana son yin rigima dake. Zata kwana da safe zata tafi"


Dariya Hindu ta kwashe da ita da bata da alaqa da nishadi ko kadan


"Wallahi ba zata kwanar mun a gida ba, ka kawo kowa banda karuwar ka"


Kai yake girgiza mata


"Ki bari, karki sake..."


Ya karasa yana fita daga dakin, ta kuwa bi bayan shi, kitchen ta wuce bata sami wani abu a kusa ba, saboda ta manta ranar karshe da tayi girki, tukwane ne kawai a kusa, guda biyu ta dauko, tana fitowa daga inda take ta fara cillawa Mansy


"Dan ubanki ba zaki fitar mun daga gida ba ko?"


Dayar tukunyar ta sake dagawa tana nufar ta, da gudu kuwa ta fice daga gidan, Hamza ya tare Hindun yana kokarin karbar tukunyar da take hannunta, dakyar ya kwace, bata nutsu ba duk maganar da yake mata, haukan da takeyi mishi saika dauka tana da aljanu, sai da ya kwashe ta da mari tukunna ta fara dawowa hayyacinta


"Ki kiyayeni Hindu, wallahi ki kiyayeni"


Ya furta yana ficewa daga gidan, a harabar ya samu Mansy tana kuka kamar ranta zai fita.


"Kabani mota in samu ko hotel ne, matarka zata kasheni Hamza"


Dan dafe kai yayi, yana komawa cikin gidan ya haura sama, kudi ya dibo da baisan yawan su ba da mukullin dayar motar shi yana komawa ya bata sannan ya dawo cikin gidan


"Na fada maka ba zata kwanar mun gida ba"


Kallonta yake yana tunanin abinda yasa take kiran gidan shi da nata


"Wallahi idan nayi niyya ke baki isa ba Hindu, gidana ne idan ma karuwar zan kawo gidana ne"


Kallon shi takeyi tanajin yanda auren shi ya kawo mata iya wuya


"Sai dai ke kibar mata gidan idan ba zaki iya zama ba"


Kai take jinjinawa wasu hawaye na zubar mata


"Ka bani hujja kaga idan ban tafi gidan mu, ka sakeni kagani..."


Ran shi yayi matuqa wajen baci, yagaji da auren ta, ya gaji da yanda take nuna mishi saboda ya aureta bai isa yayi abinda yake so ba


"Kaddarar auren ki ce kaddara ta farko da nayi dana sanin ta Hindu a duk kaddarorin da suke cikin rayuwata"


Sai lokacin hawayenta suka zubo jin yanda kalaman suka fito daga zuciyar shi


"Baka ga kaddarar neman mata ba, baka ga kaddarar shan giya ba sai ta aurena? Na tsaneka Hamza, nayi dana sanin da ban saurari Yayana ba na aureka wallahi"


Kai ya jinjina mata


"Da kin fadamun tuntuni ai, dana saukaka mana duka damuwar mu kinyi gaba"


Hannu tasa tana share hawayen fuskarta


"Yanzun ma bai baci ba Hamza...ka bani takardata kaga idan ban bar maka gidan ka ba"


Yanda yakeji idan ya kara minti daya a wajen rufeta zaiyi da duka. Sama yahau ya samo takarda ya sakko, har lokacin tana nan tsaye tana zubar da hawaye, jinta take da gaske kamar a mafarki, tana kallon shin yana rubutu, harya gama ya ninke yana fadin


"Gashi nan, ki fita kibar mun gida"


Sosai take kallon Hamza saboda ta tabbatar ba kunnuwanta kadai suke jin alamar ruwan sama ba, hakan yasa ta dan kalli window din dakin


"oh karki damu..."


Ya furta yana wucewa kitchen din dakin, wata baqar leda ya samu ya kulle takardar a ciki yana janyo hannunta ya mika mata


"Sai ki fitar mun daga gida, ba zata jiqe ba, kina da abinda zaki nuna musu in kinje"


Kuka take zuwa yanzun, badan sakin yana mata ciwo ba, sai dan ganin da gaske Hamza janta yake zai fitar da ita daga cikin gidan ana ruwan sama, da tsakar daren nan


"Duka biyun ka karasa?"


Ta bukata tana kokarin kwace hannunta daya rike yana janta kamar zai karyata, tana son tuna mishi bata manta da sakin farko da su kadai suka san da shi ba


"Koma nawa nayi ba dawowa zakiyi ba..."


Ya karasa maganar yanajin iskar 'yan cin da yake shaka, kawai so yake ta fitar mishi daga gida, duk inda zataje taje. Da ta fara tirjewa sosai tana fadin


"Takalmina, ban dauki wayata ba Hamza... Ka bari in dauki takalmana..."


Wani irin mari ya kwasheta da shi sai da komai ya tsaya mata na wasu dakika, dan harya jata ya fita da ita, taja jin yanda yake ma maigadi kashedi amman wani irin sama-sama take jinta. Kamar yanda yake jin shi sama-sama, yanda yake jin shi kamar a mafarki yake, duk maganar da yake da yanda sabon tashin hankali yake ziyartar shi gani yake kamar zai koma gida ya gan Hindu.


Sai da yaga AbdulHafiz ya mike tukunna yace


"AbdulHafiz..."


Amman baiko nuna alamar yaji ba ballantana ya kalle shi, wayar shi da take gefe ya dauka ya saka a aljihu, yana daukar hular shi


"AbdulHafiz..."


Hamza ya sake kira cikin wani sabon tashin hankali, bai kamata yabarshi shi kadai ba. Ba zai yiwu ya gama bude mishi ciwukan shi yayi kamar hakan ba komai bane ba. Wucewa AbdulHafiz din yayi, yana cin karo da Arafat a bakin kofa


"Muje..."


AbdulHafiz din ya fadi yana sa Arafat kallon shi cike da rashin fahimta


"Ka wuce muje, kaima ba zaka so ka zauna da shi ba in kasan me yayi, ka wuce kawai Arafat"


Kai kawai Arafat ya jinjina yana wucewa suka fice daga gidan gabaki daya. Suna barin Hamza nan sake da baki, a karo na farko a rayuwar shi da yasan tabbas yayi babban kuskure, in har AbdulHafiz zaiqi sauraren shi haka, da gaske yayi kuskuren da baisan ta ina zai fara gyarawa ba.


*


*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*


Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank


Whatsapp Number
08074545149
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 29


Da wani ya tambaye shi me yayi a cikin kwana biyu ba zai iya fadi ba, ko da kudi za'a saka mishi kuwa. Ko masallaci baije ba a kwana biyun, tunda ya hau sama bai sakko ba, kwalaben giyar shi ma dibowa yayi ya ajiye gefen gado, daya mika hannu dauka zaiyi. Ranar farko yana dawowa gida ya sami su Muhsin a kofar gida, bai tsaya gardama da su ba yace su shigo su kwashe kayan, ya sanar musu kayan duk da suke a kasan na Hindu ne, sannan ya hau sama ya shige dakin shi, kwalaben giya ya dauka ya samu waje ya zauna, sai da ya daina gane abinda yake faruwa, bai sauran salloli ba sai cikin dare. Gabaki daya ya daina gane kan rayuwar. Jin shi yake kamar an kama kafafuwan shi an daga su sama an jirkice shi.


Dan snacks din da yake dashi a saman ne kawai abinda yake a cikin shi. Ko yau ma daya mike zaiyi alwalar Magriba saida ya koma ya zauna na wasu dakika saboda jirin da ya kwashe shi da bashida alaka da giya sam, tunda bai sha ba duk ranar. Badan sallah ba, motsi ma ba zaiyi ba. Wayar shi na falon kan kujera tun shekaranjiyar, idan an kirama bai sani ba, balle kuma ko da caji a jiki ko babu.


Yana samu yayi sallar ishai ya koma ya kwanta, ko kwan dakin da yake ji cikin idanuwan shi bai iya tashi ya kashe ba. Duk tsaftar Hamza a kwanaki biyun nan jikin shi banda ruwan alwala baiga wani ruwa ba, kayama amai da yayi ne ya jikasu garin wanke fuska shisa ya sake wasu. Kallo daya za kai mishi idan kagan shi kasan baya tare da natsuwa sam, dan rigar da wandon basu hadu ba, haka yasa kayan shi.


Kamar cikin kunnuwan shi yake jin ana sallama, sake runtsa idanuwan shi yayi yana shigar da kanshi cikin filo. Sosai yake jin sallamar na kara kusantowa kafin a fara kwankwasa kofar dakin da yake ciki


"Yayaa"


Yaji muryar Auta, kafin ta Abid da cikin yaren shuwa yake fadin


"Yayaa...ko dai basa nan?"


Da shakku a cikin muryar shi, suna zaune a gida kawai shi da Auta suka yanke hukuncin fita siyan shawarma, Anna ma sai da tace suyi order a kawo musu gida, sukaqi saboda yawon suke so. A hanyar su ta dawowa ne sukayi shawarar su biyo gidan Hamzan tunda kwana biyu basu gan shi ba. Suna da tabbacin aiki ne ya rike shi, idan bai kira su ba, yakan yi musu zuwan bazata makaranta ya duba su.


"Wanne irin basa nan, kana ganin wayar shi a kan kujera? Ni jikina na mun wani iri. Kuma falon kasa tas an kwashe kaya fa"


Auta ta fadi, kafin ta murza hannun kofar tana turawa


"Yayaa"


Abid ya kira cikin tashin hankali, su biyun suna turereniya wajen shiga cikin dakin, amman ko dagowa Hamza baiyi ba, basu tabbatar yana da rai ba saida suka hau kan gadon, Abid na kama shi ya juyo da shi


"Ka kyaleni Abid"


Ya furta yana kwace jikin shi, ko motsi bayason yi. Shiru yake bukata har sai ya samu dai-daito koya yake.


"Wanne irin in kyaleka? Me yake faruwa? Me ya sameka?"


Abid yake tambaya cikin tashin hankali, dan ba zai tuna ranar karshe da yaga Hamza kwance yana wani ciwo ba tun tasowar su. Baisan ko da yabar kasar ba. Auta ce da ta taba jikin Hamzan tana jin shi kamar wuta tace


"Zazzabi ne ma a jikin shi"


Kama Hamzan ya sake yi yana dago shi, yama ki bude idanuwan shi


"Yaya ka tashi mu kaika asibiti, baka da lafiya zaka zauna a gida. Ina Anty Hindun zata barka haka?"


Kai Hamza ya girgiza mishi yana bude idanuwan shi da yakeji sunyi nauyi, jin sunan Hindu na saka tsikar jikin shi tashi, hannun shi daya yasa yana ture na Abid


"Na ce ka kyaleni bakaji ba ko?"


Kallon juna Abid da Auta sukayi, cikin su babu wanda baisan kafiya irin ta Hamza ba, sauka daga gadon Abid yayi, mutane kance Hamza dogo ne, tsayayyen namiji, amman wanda duk zaiga Abid din saiya dauka shine Yayan Hamza, saboda a tsayi da girman jiki ya fishi. Akanyi mamaki ko da Hausa yayi akaji alamar fulatanci daya zauna a harshen shi, mutane na da yardar cewa fulani na da dan jiki, mafi yawancin su kuma basa girma.


Sai su dinga yi kamar Abid dinne bafullatani na farko daya karya al'adar su ta fitowa a siraran mutane


"Zaka iya tashi da kanka Yaya... Ko zan dauke ka. Wanda duk ka zaba shi zai faru"


Abid yai maganar yana kallon Auta


"Ki kira Ann"


Kai kawai ta daga mishi tana sauka daga kan gado itama, dan wayarta na cikin mota tabari, duk a zaton su 'yan mintina zasuyi su wuce gida.


"In dauke ka din kenan?"


Kallon shi Hamza yayi, baya cikin yanayin da zai iya yin wata gardama, dan haka ya mike, jirin da yake gani bai hanashi ture hannun Abid daya mika mishi cikin son ya taimaka mishi ba. A haka suka sauka kasa. Abid ne ya dauki wayar Hamzan yana sakawa a aljihu, a wajen suka hadu da Auta


"Babu asibitin da zanje, mu tafi gida kawai"


Ya furta yana bude bayan motar ya shiga. Cikin kasa da mintina da suka dauke shi ya fito daga cikin gidan ya shiga motar ya riga ya yanke hukunci daya, ya daina boyewa abinda yake faruwa, fadansu ya riga da ya kai gidan su Hindu, ko zata dawo mishi dole maganar ta kai nasu gidan. Da Anna taji me yake faruwa daga bakin wani cikin manyan Hindu, gara taji daga bakin shi. Ko ba komai ita ba zata bar shi kamar yanda AbdulHafiz yayi mishi ba.


Duk a cikin abinda ya faru daga kwana uku zuwa yau, babu abinda yake mishi ciwo har kasan zuciyar shi irin yanda AbdulHafiz ya tashi tsam bayan ya gama bude mishi ciwukan shi, yanda ya mike yana barin shi kamar yana tsoron idan jinin da ciwukan da ya bude mishi suka taba shi wata cuta zata kama shi. Sosai abin yayi mishi ciwo na gaske, sai da suka hada idanuwa da Arafat kafin shima ya zabi bin AbdulHafiz batare da yama san meya faru ba.


Har suka karasa gida wannan tunanin yakeyi a ran shi. Auta ce tayi sallama, dan a falo ta sami Anna a tsaye, tun bayan da ta kira ta fada mata Hamzan bashi da lafiya, gashi suna gidan shi ma, ta kasa samun natsuwa sam, itama ta sake kiran Autar, tace gasu nan ma zasuyo gidan. Hatta Appa ta fada mishi, shima yana falon a zaune, idan yace mata ta zauna ma ba zata zauna ba, shisa bai bata bakin shi ba.


Appa ya dauka ciwon ba zai wuce zazzabi ba sai da ya kalli yanayin Hamzan kamar wanda ya sami tabin hankali na wucin gadi, ga gashin da yake fuskar shi duk ya cukurkude saboda rashin gyara. Waje ya samu a daya daga cikin kujerun falon yana zama, ba sai wani ya fadama Abid da Auta abinda suke gani ba, sun san koma meye yake damun Hamzan ya girmi rashin lafiya. Dan haka kowa ya wuce dakin shi batare da sunce komai ba


"Hamza..."


Appa ya kira, dan Anna ma ta rasa abinda zata ce saboda tashin hankali, tunani takeyi barkatai a lokaci daya tana son hasaso abinda ya sami danta haka


"Appa ban kyauta muku ba"


Hamza ya fadi idanuwan shi kafe a jikin bango, yaki yarda ya kalli fuskokin su, jin yanda kafafuwan Anna suke rawa yasa ta samun waje gefen Appa ta zauna, numfashi Hamza ya sauke mai nauyin gaske, yana sauke idanuwan shi akan su Anna


"Na saki Hindu"


Ya furta yana jin wani irin shiru daya biyo bayan maganar da yayi


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."


Shine abinda Anna ta fadi, Appa na dorawa da


"Subhanallah, saki da tsohon ciki Hamza? Me ya faru haka?"


Dan daga kafadun shi Hamza yayi, baisan ta inda zai fara ba, baisan me zai ce musu batare da halayen shi daya dauki shekaru yana boye musu sun fito fili ba


"Bansan me zance ba Appa, kawai nasan ba laifinta bane ba...har sun kwashe kayan su"


Ya karasa maganar yana gyara zaman shi a cikin kujera. Yanayin shi yasa Appa fadin


"Yanzun aini gidan ya kamata inje..."


Saboda koma meya faru yanayin Hamzan ya nuna idan fada ya rufe shi da shi babu abinda zai fahimta. Tun ranar da abin ya faru ya kamata ace sun sani, baisan wanne kallo iyayen Hindu suke musu ba, ballantana ga tsohon ciki, haihuwa yau ko gobe, ace ya sakar musu yarinya


"Ai bakai kadai ba, harni ya kamata mu tafi"


Anna ta fadi tana daukar mayafinta da ta fito da shi da nufin ta bi bayan su asibiti. Ganin Hamza ya kara gyara zama yasa Appa fadin


"Kaima kasan ai ba zama zakayi ba ko?"


Numfashi yaja yana saukewa, bashi da wani zabi. Haka ya mike yana bin bayan Appa, sannan Anna ta furta


"Abid mun fita"


Cikin yaren shuwa, tana jin ya amsa mata tukunna itama tasa kai suna ficewa daga gida. Appa ne yaja motar suka nufi hanyar Barnawa da zata sada su da gidan su Hindu.


*


Wani irin bacci takeyi a kwana biyun nan kamar wadda ta tara gajiya mai yawan gaske. Tun da aka kwaso kayanta sai take jinta wani irin sama-sama, ga ciwon baya da take fama da shi da bata furtawa kowa komai a kai ba, asibiti ma da taje batayi musu magana akai ba. Tana jin yanda tai wata irin saduda da lamurran duniyar gabaki daya. Ko da wayarta da aka kawo mata, drawer ta ja ta jefata a ciki. Batasan karya ta fadama kanta na cewar Hamza da auren shi sun fita daga ranta ba sai da taji zuciyarta na mata wani irin ciwo bayan kwaso kayan.


Amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login