Showing 33001 words to 36000 words out of 110313 words
Chapter 12 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
akan fuskar shi, kafin ya sumbaci cikin tafin hannunta
"Bye..."
Ya iya furtawa yana sakar mata hannun da taji yayi wani irin nauyi. Harya shiga mota ta kasa cewa komai, tana kallo yayi baya da motar shi yana fita daga gidan, juyawa tayi, duk da bataji alamar akwai wani a bayanta ba. Sai take jin kamar anga abinda tayi, kamar wani yaga hannunta a fuskar Hamza, zuciyarta cike fal da tsoro ta samu ta dauki kujerun ta hade su waje daya. Anan tabar su ta dauki plate din da ruwan da bai shaba ta shige gida, zuwa kitchen din Mama tayi ta ajiye mata plate, ta mayar da ruwan mazaunin shi. Sannan ta wuce bangaren su tana sakun Khadee a zaune
"Shikuma menene laifin shi? Gajere ne? Ko katon hanci?"
Khadee ta tambaya cike da zolaya, zagayawa Hindu tayi ta zauna kan kujera, bata cikin yanayin da zata biyewa tsokanar Khadee din, yanayinta yasa Khadee fadin
"Lafiya? Me ya faru?"
Kallon Khadee tayi da wani irin yanayi a fuskarta tace
"Ina son shi Khadee..."
Ware idanuwa Khadee tayi, ita kanta Hindu mamakin kalaman takeyi, amman daga zuciyarta suka fito, mikewa tayi
"Ke dai ki mun addu'a. Allah ya tabbatar mun"
Khadee da kallon mamaki take bin Hindu harta shige daki tana barinta a wajen, da tunanin ko dai wani dan wasan fim dinne Allah ya jeho Najeriya suka hadu da Hindun.
*
A gidan su ya kwana, duk da bai shiga da wuri ba sai wajen sha daya na dare. Yanzun kuma karfe tara harya gama shirin shi, ya fito falo yana samun Anna da Auta a zaune
"Hamma na ganka rannan... Kai da wata ta wajen Byblos... Mantawa nayi in fada maka"
Wani kallo ya watsa mata
"Uban ki kike a wajen? Kuma baki iya gaisuwa ba?"
Yar dariya Auta tayi
"Ina kwana... Allah da gaske na ganka. Ni Anna ta aikeni ai ranar, kafin inje in maka magana harka shiga mota"
Numfashi Hamza ya sauke, yana jin idanuwan Anna a kan shi, amman yaki kallon ta, sai da tace
"Wacece ita?"
Dan kallon Anna yayi
"Ni banma tuna ranar bafa Ann, bazai wuce abokan aiki ba"
Ya fadi yana ganin yanda Anna bata yarda ba, amman ba zata fada mishi hakan bane kawai.
"Ko ita ce? Ban ga fuskarta ba sosai"
Auta tace tana saka Hamza watsa mata wani irin kallo da yasa ta fadin
"Allah ya baka hakuri. Ni shirin makaranta zanyi daman"
Ta karasa maganar tana tashi tabar dakin. Da idanuwa dai Anna take bin shi
"Ban san sau nawa zanyi maka magana kan nutsuwa waje daya ba, kana da aiki me kyau. Na rasa abinda kake jira"
Dakuna fuska Hamza yayi yana turo labban shi
"Ni zan fita wajen aiki"
Yai maganar yana nufar hanyar kofa, inda yaci karo da Appa dayai wa magana cikin harshen fulatanci, Appan na tambayar yanayin aikin Hamzan, shikuma yana amsa shi
"Maganar aure nayi mishi shine zai fita yabar mun gidan"
Dan juyawa Hamza yayi
"Anna mana"
Ya furta, yana wuce Appa ya fice daga gidan dan karma su hadu su biyun suna mishi maganar aure. Bai hango shi a wannan kejin ba dan nan kusa, babu wanda zai kulla mishi yarinyar mutane ya rasa yanda zaiyi da ita, haka kawai a takura shi a hana shi sakewa. Kullum dole ka koma waje daya ka dinga kwana, ba zai kwana a waje yanda yaga dama ba, saboda yayi aure. Bai shiryama wannan matsatsin rayuwar ba, kuma bai gama ginin shi ba, shine uzurin da yake amfani dashi wajen sakawa Anna tana saurara mishi da maganar auren.
Yana fita daga gidan ya tsinci kan shi da kiran wayar Hindu, ko muryarta yaji. Ga mamakin shi, kashewa yaji tayi, sai ga text tayi mishi
"Ina aji"
Tana sake turo wani
"Sha biyu da rabi zan fito, zan kiraja"
Titi ya kalla, kafin yadan kalli wayar shi yana fara rubutu
"Ok. Zan zo sai mu fita lokacin"
Ya tura mata, tukunna ya nufi hanyar da zata kaishi gidan Fodio. Yana karasawa ya samu suna karyawa, waje ya samu ya zauna shima yana cin dankalin da kwai, hannu yakai zai dauki kofin yoghurt da yake gaban AbdulHafiz ya doke mishi hannu
"Wallahi nayi brush"
Hamza ya fadi, yana saka Fodio da Arafat kwashewa da dariya
"Brush shine abinda zai tsarkake maka bakin ka?"
AbdulHafiz ya bukata yana daukar kofin shi ya rike a hannu, tuntuni ya gaya musu ya daina hada irin wannan abubuwan da su, ya siyo kofina daban yana kaiwa dakin shi
"To ni ina ma naje?"
Hamza ya tambaya yana dorawa da
"Dan Allah kabani in kurba"
Fodio ne ya sakeyin dariya, fadan AbdulHafiz din da Hamza baya gajiyawa wajen saka shi nishadi
"Karbi..."
Arafat ya fadi yana mika mishi kofin da yake hannun shi, lekawa Hamza yayi
"Kai ni bana shan tea dalla"
Bude baki Arafat yayi cike da mamaki, kafin ya jinjina kai yana furta
"Laifina ne da nayi maka tayi"
Banza Hamza yayi yana kyale shi, Yoghurt din ce ranshi ya biya
"Ido guba AbdulHafiz, ba kyau wallahi"
Ko inda yake AbdulHafiz bai kalla ba, yasan ba bashi zaiyi ba, saida yasha fiye da rabi tukunna ya tura ma Hamza kofin yana fadin
"Dan Allah Arafat ka tashi, yanzun yaushe zamu shiga Kano har mu gama mu sake kamo hanya? Bafa naso mu kwana"
Kofin shayin Arafat ya daga yana shanye na ciki, hadi da maida numfashi kafin ya mike
"Ba zaka bar mutum abinci ya narke mishi ba. Kaya fa kawai zan sake"
Harar shi AbdulHafiz yayi
"Daka wuce ai da yanzun ka sake kayan... Ka zauna mayar mun da magana"
Wucewar Arafat din yayi kuwa.
"Ko in shirya mu tafi tare?"
Fodio ya tambaya yana daga hannun shi ya kare fuskar shi
"Hararata yake ko?"
Ya tambayi Hamza daya daga mishi kai yana dariya
"Wanne wulakanci ne wannan? Sai ka tashi ai"
Da sauri Fodio ya mike yana wucewa daki dan ya watsa ruwa, idanuwan shi AbdulHafiz ya tsayar kan Hamza
"Kai ba zakaje ba?"
Kai Hamza ya girgiza mishi, ai yaji suna maganar zuwan tun jiya da rana, ya riga ya saka ma ran shi ganin Hindu yau. Ko ya bisu tunaninta damun shi zaiyi, gara dai yaganta din
"Kuje abinku"
Dan kallon shi AbdulHafiz yayi, yasan Hamza baya wuce tayin yawo, ko marar muhimmanci, balle kuma yanzun da aikine zai kaisu, kuma su dukan su, dan zasu biya su dauki Abdallah. Shi kadai zasu bari, yasan akwai dalilin da yasa ba zaije din ba
"Ka shiga uku AbdulHafiz, ka tambayeni dalili mana, nasan kana so ka tambaya, ina jin idanuwanka na mun rami a bayan kaina..."
Hamza yai maganar da wani yanayi tattare da muryar shi. Shiru AbdulHafiz din yayi, idan Hamzan na so yaji zai gaya mishi, ba zai fara saka hancin shi cikin abinda bai shafe shi ba
"Nabila na da aiki"
Hamza ya fadi yana saka AbdulHafiz fadin
"Jibi yanda kake kiran sunanta gatsau dan Allah"
Dariya Hamzan yayi
"Kana jina ashe, kayi banza ka kyaleni"
Shirun AbdulHafiz ya sakeyi mishi, har su Fodio suka fito suka wuce, Hamza yana karasa cinyewa nan ya tsallake yana barin kwanonin, zai tabbatar sanda zasu dawo baya gidan, ballanta AbdulHafiz ya sauke mishi fadan ba zai iya gyara waje ba. Kwalabe biyu ya dauka na vodka, duk da yasan yayi safiya ya bulbula ma cikin shi abu mai karfi haka, sai dai ita kadai ce zata taimaki yanayin da yake ciki, rabin kwalba yasha yana jin kan shi ya fara nauyi, hakura yayi ya kwanta, sai da ya saita alarm din wayar shi zuwa sha biyu da rabi, tukunna ya kwanta, yana lumshe idanuwan shi yabar baccin da yake son daukar shi yin aikin shi.
*
Karamin tsaki yake ja a mota, yana tuqi kamar zai tashi sama, kwata-kwata baiji karar alarm din wayar ba, sai bayan ya tashi wajen daya da kwata, sannan ya kula wayar a silent take gabaki daya. Yaga Hindu ta kira shi har sau biyu, ruwa ya watsa a gaggauce yana sake kaya ya fita. A hanya ya tsaya ya siya mata shawarma da kaji, sai lemuka, yasan ko yaushe in dai tana makaranta to zaiji tana tare da Hauwa, shisa yayi ledoji biyu. Yana shiga makarantar ya samu waje yayi parking, tukunna ya kira wayarta, bugun farko ta dauka
"Dan Allah karkice komai, kiyi hakuri, wallahi bacci nayi, wayar kuma tana silent, ki fito ina wajen parking din motoci..."
Hamza ya fadi muryar shi cike da ban hakuri, batace komai ba, shima wayar ya sauke yana jin babu dadi, saba alkawari ba sabon shi bane ba, balle shi yace ta jira shi zaizo. Ji yayi an kwankwasa motar, hakan yasa shi mika hannu ya bude mata, kai ta leqo tana mishi murmushin daya kasa mayar mata
"Kiyi hakuri..."
Ya furta kamar zai mata kuka, dariyar ta sakeyi tana shiga motar ta zauna.
"Ki rufo kofar akwai rana"
Hamza ya fadi, dan baima kashe motar ba, saboda AC din. Batayi musu ba ta rufo mishi murfin, sai take jinta wani iri saboda gilasan gabaki daya a rufe suke, kuma motocin duk da take ganin shi dasu tinted ne.
"Ya kike?"
Ya fadi yana yawata idanuwan shi akanta, yana ganin gajiyar da take fuskarta, yasan kuma karatune, ga ranar da ake kwallawa. Haka kawai yaji bayason ta koma cikin zafi
"Alhamdulillah.... Da baka zo bama"
Idanuwan shi ya kafe ta dasu
"Baki so ganina ba kenan?"
Da sauri ta girgiza mishi kai
"Aa wallahi, ba haka nake nufi ba, da kayi baccin ka dai"
Ledojin da suke ajiye a gefen shi ya dauko yana mika mata
"Bansan ko kunci wani abu ba, ke da Hauwa... Bari kar in rike miki sauran lokacin cin abincin"
Murmushi tayi, suna ma masallaci ita da Hauwa din, sanda ya kiratane suke tunanin zuwa suci abinci, dukkan su a gajiye suke. Hannu ta saka ta karbi ledojin tana fadin
"Mungode sosai"
Kai ya jinjina mata, yana kwance seatbelt din da yake daure a jikin shi, kafin tayi wani kwakkwaran motsi ya gyara zaman shi, bata san me ya faru ba, ba zatace ga yanda akayi ba, sai jinta tayi gabaki daya a jikin shi ya rungumeta hadi da fadin
"Yau nayi laifi, dan Allah kiyi hakuri"
Duka da rungumar da sakinta bai wuce minti daya ba, amman wani zazzabi taji ya saukar mata, da kan shi Hamza ya bude bangaren shi ya fita, ya zagaya yana bude mata nata bangaren, kafafuwanta ta janyo dakyar tana dire su a kasa tukunna ta fita daga motar.
"Ki kula da kanki dan Allah"
Ya furta, kai kawai ta iya daga mishi, tana jin kamshin turarukan shi da suka manne mata, dakyar take daga kafafunta tana takawa ta nufi hanyar da zata kaita masallacin da take tunanin shiga saboda zunubin da takeji a jikinta. Hamza kuwa daya koma motar yana rufe murfin, kan shi ya hada da abin tuqin yana maida numfashi, baisa ya akayi ba shima, kawai ji yayi idan bai riketa ba komai zai iya faruwa, yanajin bugun da zuciyar shi takeyi a cikin kirjin shi, numfashi kawai yake mayarwa kamar wanda yayi gudu.
Baisan abinda yake damun shi ba, yasan yanda yake akan mata, amman abinda yakeji akan Hindu yayi yawan da ya fara bashi tsoro, yakai mintina goma anan zaune cikin motar, kafin ya iya tashin motar, yana juyata ya fita, a bakin gate din ya tsaya yana ba masu gadin dan katin shigar da suka bashi, hadi da dubu biyu, yaja gilashin motar shi, bai damu da godiyar da suke ta faman yi mishi ba, da fatan sauka lafiya. Garama wannan, dan yana bukatar shi a halin da yake ciki.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 5
A karo na farko a rayuwarta da taji bata dokin hidimar biki, yan gidan kansu mamakin rashin kazarniyarta da rawar kan da ta saba duk idan taji maganar bikin yan uwa, balle kuma wannan da akeyi a cikin gidan su, abinda basu sani ba shine littafi hausa ta samu daya dauke mata hankali daga kan komai. Tun da ta kunna waya tayi mamaki sosai da bataga sakkonin Elias ba, da hannunta ta goge 2go din daya gama fita daga ranta. Banda kallo babu abinda tafi yi da wayar, tunda bata da wanda zatayi hira dashi sosai a whatsapp sai kawayenta da kusan kullum suna tare a makaranta, hirar da zasuyi a gida bata da wani yawa. Sai yanzun data samu littafin Hausar da Dimples ta tura mata.
'Tana Tare Da Ni' na Miemiebee. Gabaki daya littafin ya gama tafiya da ita, Anas yayi dai-dai da kalar mijin mafarkin ta, bata tsammani ko a cikin fina-finan da take kallo, daga na Indiya harna kasar Korea ta taba cin karo da jarumin da taga yayi dai-dai da tsarinta irin shi. Duk da ba ganin wannan tayi ba, amman an haska mata shi ta yanda zuciyarta ta zayyana mata mutum sak, fari, dogo, mai faffadan kirjin da ba zata taba gajiya da kwanciya luf a cikin shi ba, gashin kanshi bakine wuluk, a kwance luf-luf kamar na mutanen kasashen ketare, ga fatar shi nada wani irin haske kamar gilashi saboda rashin wani kurji ko tabo a jikin shi, labban Anas ruwan hodane da zaka iya rantsewa yana shafa musu janbaki.
Babu abinda yafi tafiya da imaninta a tare dashi irin idanuwan shi,blue ne masu hasken da zata iya misaltawa da sararin samaniya. Gashi miskili ajin gaske, magana ma sai kayi da gaske zakaji ya furtata, ajin shi wani irin ajine da yake wahalar samu, sai da Fannah ta shigo rayuwar shi. Ta hargitsa komai tana canza shi, kalar son da yake mata, yanda ta sake shi, kuma ita kadai take ganin canjin yayi dai-dai da ra'ayin Hindu. Anas ne duk ajin shi da jiji da kai yake kuka wiwi tamkar yaro dan wata biyu a gaban Fannah. Duk idan yace
'Flower'
Sunan da yake kiranta dashi sai Hindu taji wani abu ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta zuwa dan yatsar kafarta saboda shauqi. Da ace Anas zai fito daga littafin ya tsaya a gabanta ya furta mata kalmar so, zata amsa shi batare da wata gargada ba, ko baice yana sonta bama in dai zai aureta bata da wata matsala, dan in suka zauna zasuyi ta fada daga farko, amman tasan zasu shirya daga baya, zai fara son ta, wahalar abin ta fito daga wanka ayi dai-daito ya shigo dakin daga ita sai towel, ba zata jira tsautsayi ya kwance towel din ba, da kanta zata san yanda zatayi ya subuce. Sanda zai hargitse ta manne a zuciyar shi babu wanda zaiji labari.
Zuwa yanzun Hindu tayi wani irin zurfi cikin tunani, sam bataji maganar da Anty take tayi mata ba, sai da ta fisge wayar hannunta tana dorawa da
"Dan ubanki baki da wani aiki yanzun a rayuwar ki saina waya? Kinsan Allah na kusa haramta miki wannan shegiyar wayar tunda naga alama ke baki da hankali..."
Da hanzari cikin wata irin faduwar gaba Hindu take kallon Anty
"Dan Allah Anty kiyi hakuri, banji bane Wallahi"
Harara Anty ta watsa mata
"Daman ya za ayi kiji, kin saka kanwar uwarki a gaba... Mutane na can kinzo nan kin lafe kina danna waya sai tambayarki akeyi"
Anty ta karasa maganar tana dorawa da
"Ki tashi kibar mun daki ni..."
Mikewa Hindu tayi tana kokarin bata nuna bacin ran da take ciki a fuskarta ba, wayarta Anty ta miko mata
"Saura in shigo inga kina danna waya, idan na karba sai an gama hidimar bikin nan tas zan baki"
Karba Hindu tayi tana wucewa dakinsu ta saka wayar a caji dan tayi kasa sosai, mukulli ta dauka ta kulle dakin, shisa bata ganin laifin kawarta Aina'u da suke kira da Dimples da take cewa bata son mutane, saboda suna da bala'in sa ido da takurama yan uwan su mutane. In ba takura ba me zatayi musu, kamu ne an riga anyi, sunje sunyi kunshi da kitso, gobe Asabar daurin aure za'ayi tare da walima sai akai amarya tunda anan garin Kaduna zasu zauna. Bata ga me zataje tayi musu ba da suke faman tambayarta, inba salon son su shiga rayuwar ta ba.
Da sallama ta shiga bangaren Mama tana wucewa dakin su Halima da take jiyo hayaniyar hirar su, ta leka da sallama, Halima ce da kawayenta, sai wasu cikin yan uwansu da kusan sa'annin Halima din ne, wasu kuma duk da auren su ma harda yara daya zuwa biyu. Murmushi ta dora saman fuskarta tana gaishe dasu, kafin ta juya dan ba wajen zamanta bane, su Khadee ta nemo, suna zaune da yan uwan su, yaran kannen Baba da kuma na Mama da Yayyenta, sun kacame sunata hira.
"Ke banza ina kika shiga tun dazun anayi babu ke?"
Mimi ta fadi tana matsama Hindu ta zauna a kusa da ita, hadi da leqa wayarta tana ganin hoton Halima da Yaa Ahmadi, ya leko wajen kamun na yan mintoci akai musu hotuna
"Wallahi sunyi kyau ba kadan ba"
Mimi ta fadi tana mikawa Hindu wayar dan taga hoton sosai, zata iya rantsewa Halima har wani kyalli-kyalli takeyi da batasan ya akayi ba, wani irin kyau take mata tun satin bikin naban mamaki, ita batayi haske kamar su ba, ta biyo duhun Mama, amman tana jerin masu kyawun gidan
"Shisa auren namiji me kyau ma girma ne"
Hindun ta fadi batare da tasan maganar ta fito fili ba
"Kibari kawai yar uwa, namiji me kyau fa duniya ne, ba ka auri mummuna ya bata maka hotunan biki ba"
Saddika ta amshe zancen, dariya sukayi su dukansu, Khadee ta kalle da murmushi a fuskarta
"Allah ya shiryaku Wallahi"
Hannu Hamida ta daga mata
"Amin. Amman ki rantse har kasan ranki bakya son auren me kyau? Mijin da ba zaki boyema kawayenki ba"
Wannan karin Hindu ce take dariya sosai, dan an tabo mata inda take so, shisa wani lokacin tana son yan uwanta na bangaren Baba saboda wayewar su, ta dauka zasuce wani abu da tayi maganar Miji me kyau, ashe duk sun gane kan al'amarin. A wannan zamanin me akeyi da namiji mummuna. Khadee kai kawai ta girgiza musu, tana sa Hamida juya idanuwanta
"Kinji zancen ko? Hajiyata Allah ya bamu masu kyau"
Kai Mimi ta jinjina
"Masu kudi kuma"
Hindu na saurin amsawa da
"Amin thumma amin"
Fati da take gefe sai lokacin ta tsoma musu baki
"Banji kunce mafi alkhairi ba"
Tana sa Hindu amsa ta da
"Wannan ai itace karshe, in dai yana da kudi, yana da kyau... Ai da alkhairin shi yazo"
Sosai suka cigaba da hirarsu akan maza masu kyau da irin yanda zasu zaba su darje. Hindu ta jima tana mamakin dalilin da zaisa ka daga hannu wajen rokon Allah miji ka tsaya a iya 'mafi alkhairi'. A ganinta hakan babbar wauta ce, ka bude bakinka ka zayyana kalar shi tun daga sama