Showing 90001 words to 93000 words out of 110313 words
Chapter 31 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
yake ba mutuwa shima zata dirkar mishi kamar Ashir. Haka ya kwana anan wajen, bacci ko na dakika, asuba ma anan yayita, kan shi yake ji kamar zai bude.
Har zuwa yanzun da su AbdulHafiz suka shigo, kafin suzo din yanajin kiran da Arafat ya dinga mishi, amman bayason ko da motsawa ballantana yaje ya bude kofar. Yanzun ma kallon su yakeyi
"Inalillahi... Wai Fodio me yake faruwa ne?"
Arafat ya fadi, ganin hawayen da suka zubo mishi, yana saurin saka hannu ya goge su. Hamza ma dagowa yayi da sauri, kafin yaji cikin shi ya hargitsa da tashin hankali
"Fodio"
Ya fadi cike da mamakin ganin da gaske kuka yakeyi, nan wajen ya durkushe, baya kunyar kuka a gaban su, ba lallai su fahimci kalar tashin hankalin da yake ciki ba, Ashir bai mutu a gabansu ba, basu ga yanda ran shi yabar jikin shi cikin wasu yan dakika ba, su dukan su tasowa sukayi suna rasa abinda ya kamata suyi banda tsayuwa akan Fodio din.
"Ashir.... Ashir... Ya... Ya rasu"
Fodio ya kakalo maganar dakyar, su duka ukkun kowanne da kalar salatin daya fito daga bakin shi
"Fodio..."
Arafat ya fadi cike da tausayawa
"A hotel... Ya rasu a hotel"
Fodio ya karasa maganar yana tsayar da rinannun idanuwan shi akan Hamza
"Bamu da lokacin da muke tunani.. Hamza bamu da wannan lokacin"
Kan shi Hamza ya saddar kasa, tsoron dake cikin idanuwan Fodio na taba shi ta fannonin da bai taba tunani ba, fannoni daban da yanda suke taba Fodio, dan bacin ran da yake tare da shi ya nema ya rasa, hakan na bude mishi kofar da yayi amfani da bacin ran ya rufe, hakan na ba wasu abubuwa daban ziyartar shi, kamar wanda aka dokama guduma a kai ya kalli AbdulHafiz, kafin ya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Amman daga Fodio har Arafat sun dauka shima mutuwarce ta taba shi, AbdulHafiz ne kawai ya fahimci damuwar da take tattare da Hamzan bata da alaka da mutuwar Ashir. Kai Hamza ya dafe yana dan murza goshin shi, kafin ya sauke hannun hadi da furzar da iska ta bakin shi, yasan yanda yake idan ranshi ya baci, ya kuma san yanda yanke hukunci cikin fushi yake abokin tarayyar shi. Musamman idan yasha wani abu da ya kara taimakawa wajen tunzura shi.
"Hindu..."
Ya furta kasan numfashin shi, hanjin cikin shi na hautsinawa, hannun kofar da yake tsaye a kusa da ita ya kama, hakan nasa Fodio janye jikin shi ya matsa, Hamza ya bude kofar ya fice, su dukan su suna binshi da kallo kawai. Kafin Arafat ya zauna a gefen Fodio, AbdulHafiz ya zauna a dayan gefen, lallashin juna ba halayyar maza bace a yankin Najeriya, zasu zauna tare da shi har ya samu natsuwar da zai iya jinyar ciwukan shi da kan shi. Shine kawai abinda zasu iya yi mishi.
*
Yana zaune a mota yake gwada kiran lambar Hindu, tunda yayyenta suka zo gidan shi maganar kwasar kaya ya tabbata tana gida. Yasan yanda take a wajen Babanta, duk yanda zai dauki zafi, ita din zata iya lallaba shi, tunda tasan shi, tasan yanda yake idan ran shi ya baci, daya huce shikenan zasu shirya, yanzun ma da ta hakura har safe ta dawo gidan ya huce komai zai wuce musu kamar bai faru ba. Ba wannan bane gagarumin fadan da sukayi, kuma ko wancen dinma sun shirya, babu wanda yaji sunyi, sirrin su ya zauna a tsakanin su.
Sai dai har tayi ringing ta yanke ba'a daga ba, ya sake kira har sau hudu
"Bafa kabari ta dauki wayar ta ba"
Wata murya ta furta kasan zuciyar shi tana saka shi dukan abin tuqin da karfin gaske, kafin ya dora kan shi a jiki
"Bamu da lokacin da muke tunani..."
Maganar Fodio ta dawo mishi da yanayin da yake fuskar shi lokacin daya furta mishi wannan kalaman. Tunasarwar AbdulHafiz ta kullum ce, amman duk idan Fodio ya bude bakin shi, saiya fadi maganganun da Hamzan zaiji sun shiga cikin fatar jikin shi suna tsikarin shi a wajaje da dama hadi da barazana da zaman lafiyar shi. Lumshe idanuwan shi yayi, kafin wani abu ya tsirga mishi, Ashir ya rasu, fuskar Ashir din yake gani da ranar karshe da suka hadu, yanda yake maganganun shi cike da buruka masu tarin yawa
"Ba zaka gane rayuwar nan ba komai bace, sai kayi kokarin juya kwanciya bayan Allah ya mayar maka da ruhinka a gangar jikin ka, kaji kamshin kasa ya cika maka hanci, kana tunanin mafarkine, saika bude idanuwa kaga dundum, kafin mala'iku su dirar maka da tambayoyin da baka da yakinin zaka iya amsawa"
Dagowa Hamza yayi da sauri yana bude idanuwan shi, kan shi ya girgiza ko muryar AbdulHafiz da tsoron dake muryar zasu fice mishi daga cikin kai. Da ya sami Hindu ya lallabata zata dawo, tsautsayina yasa fadansu yakai kunnuwan yan gidansu. Ta dawo ya riketa a jikin shi ko zai batar da abinda yake faruwa da shi yau. Samu yayi ya murza mukullin motar shi, kan shi tsaye gidan su Hindu ya nufa, ya dade ko bayan an bude mishi kofar yayi parking a zaune cikin motar yana rasa ta inda zai fara. Bawai yana ta'ammali da kunya bane ba, kawai baisan ta inda zai fara ba.
Fitowa yayi daga motar
"Kuskure ne kayi Hamza, idan su basu fahimta ba ita zata fahimta. Tana son ka, zata yafe maka kamar kullum"
Ya furta ma kanshi a hankali yana kara samun kwarin gwiwa. Gidan nasu ba bakon shi bane, tunda bashi da wanda zai aika ya kira mishi ita, kan shi tsaye ya taka har ciki hadi da yin sallama yana shiga, da yake yasan gidan, baibi ta falon Mama ba, zagayawa yayi yana shiga falon Anty kai tsaye. Ita kuwa ta amsa mishi sallamar tana karasawa cike da bayanannen mamaki a fuskarta da ma muryarta ganin Hamza ne
"Anty ina wuni"
Ya furta yana sadda kan shi kasa, dan haka kawai yaji yau tayi mishi kwarjinin fiye da ko yaushe
"Lafiya kalau"
Ta amsa tana kallon shi cike da mamaki, dan bata tsammaci ganin shi yau ba, ko dame yazo kuwa. Zuwa tayi tana wuce shi, numfashi mai nauyi ya sauke ya sami waje ya zauna, da zaiga Hindu, da zata fito komai zaizo mishi da sauki, ko Asma ma, sai ta kira mishi ita. Yana wannan tunanin yaji muryar Baba kamar daga sama yana fadin
"Me yazo yi?"
Sai da zuciyar shi ta doka, baisan bashi da confidence ba sai ranar daya fara dora idanuwan shi akan Baba, muryar shi har rawa yaji tanayi, kuma gaishe shi kawai yaje yi wancen lokacin. Yanzun kam sai abinda Allah yayi, amman koma meye yayi laifi, wannan karin ya sani, laifin nashi ne daya bari rigimar su ta kawo gida
"Lafiya? Me ya faru?"
Baba ya furta yana zagayowa ya tsaya yana kallon Hamzan da har karfin halin zauna mishi cikin gida ya samuyi.
"Baba ina kwana"
Hamza ya furta yana wani irin sauke murya
"Me ya faru?"
Baba ya sake furtawa kamar baiji gaishe shin da Hamza yayi ba. Numfashi Hamzan yaja yana saukewa
"Ni mai laifine Baba, dan Allah kayi hakuri. Zuwa nayi in bada hakuri"
Wani irin kallo Baba yayi mishi
"To madallah....ka tashi ka koma, kar su Muhsin su karasa gidan kuma a kulle, bana son kayan nan su kara kwana"
Dagowa Hamza yayi yana kallon Baba cikin tashin hankalin jin maganar da yayi, abin babbane, yaga borin namiji ne
"Babaa...."
Ya fara, Baban na dakatar da shi
"Ka tashi ka ficemun daga gida...ba zan sake maimaitawa ba"
Yanayin muryar Baba ya saka shi mikewa, dai-dai lokacin da suka hada idanuwa da Hindu da ta fito daga dakin Asma da nufin ta dauki ruwa, ko muryoyinsu bataji ba saboda hankalinta na wani waje daban, aikam zuciyarta tayi wata irin mummunar faduwa, ji tayi kamar taga dodo, iskar da ta fara shaka ta daban na bace mata.
"Baba me yakeyi? Ni ba zan koma ba, dan Allah karku ce in koma"
Ta karasa muryarta na karyewa
"Hindu..."
Hamza ya fadi wani abu na matsewa a zuciyar shi ganin da gaske take furta maganganunta, har matsawa takeyi kamar zai karasa ya kamata su koma dole, kai take girgiza mishi
"Zaka fice mun daga gida ko saika kara firgitamun yarinya?"
Sosai ya kara kallon Hindu, kafin ya juya yana ficewa daga dakin, ita kam inda ta fito ta koma da saurin gaske, badan cikin jikinta da yayi mata nauyi kamar yana shirin fitowa kowanne lokaci ba, tsaf da gudu zata karasa cikin dakin. Anty ma nata dakin ta wuce, kome zata tsaya tacewa Baba bata bakinta zatayi, batace a saurari Hamza yanzun ba, koba komai dole su kwatarwa Hindu 'yancinta kafin su bari ta koma, amman yanda Baba ya dauki zafi idan tai mishi zancen komai ma zai iya faruwa, dan haka kai tsaye bandaki ta shiga tana daura alwala, abin yafi karfinta, ba zata wahalar da kanta ba, addu'a zatayi, tana da yakinin komai zaizo musu da sauqi.
*
*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*
Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number
08074545149
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 28
Jin shi yake kamar an watsa mishi ruwan kankara, sanda ya koma gidan Fodio a falo ya sami AbdulHafiz. Tun fitar Hamzan suna tare da Fodio, panadol yasa Arafat ya dauko ya bashi. Da kan shi ya shiga kitchen ya hada mishi ruwan shayi mai kauri ya bashi ya sha, suka fito suka bar mishi dakin. Sai bayan sun dawo sallar azahar ne ma ya leqa ya ga yana kwance, sake janyo mishi kofar yayi ya dawo falo ya zauna. Addu'ar neman Rahma yake ma Ashir da ko jana'izar shi ba zasu samu suje ba, zai so suje din, amman Fodio bashida wannan nutsuwar.
Arafat ya fita ya samo musu abinda zasu ci, hakan na nashi damar kiran Nabila, da maganar farko da yayi yasa ta fadin
"Me ya sameka? Me ya faru?"
Kai yadan girgiza
"Bani bane ba, Fodio ne...."
Duk da ajiyar zuciyar da tayi, bai hana wata damuwar bayyana a muryarta ba sai da ya ce mata rasuwa aka mishi, abokin shine ya rasu tukunna yaji ta nutsu
"Kaci wani abu?"
Kai ya girgiza kamar tana ganin shi
"Kaci wani abu dan Allah, karka zauna da yunwa"
Kan ya sake jinjina mata, yasan ta fishi rashin son magana, lokutta da dama yakanyi shiru ne dan yaji tata maganar
"Ke ma kici wani abu, na kira ne inji muryar ki"
Ko bai ganta ba yasan murmushi tayi
"Ka kular mun da kanka. Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya. Ina ma Fodio gaisuwa"
Sallama sukayi, ya sauke wayar daga kunnen shi kenan Hamza ya shigo. Kujerar da take kallon ta AbdulHafiz din ya zauna yana dafe kan shi
"Me kayi?"
AbdulHafiz ya tambaya, yana sa Hamza dagowa ya kalle shi, hadi da dan girgiza kai
"Ba zan sake tambayar ka ba, bana cikin yanayin Hamza, damuwar ku ba za taimun illa ba..."
AbdulHafiz ya karasa maganar yanajin shi a gajiye
"Bazan dinga neman damuwa a fuskar ku kamar kananun yara ba, kana jina, wallahi ba zan sake tambaya ba Hamza..."
Ran shi yake ji a bace, ba tun yanzun yake ganin damuwa a fuskar Hamzan ba, ya tambaye shi yafi a kirga yana ce mishi ba komai, nauyi ya mishi yawa. Lokutta da dama yanajin kamar ya girmi shekarun shi, ko a gidansu bashi bane babba, amman matsalar kowa da shi yake rabawa, ga kuma ta su Hamza. Sosai ya gaji har cikin kasusuwan jikij shi
"Duk wani kokari nayi, nayi Hamza..."
Dan babu yanda za'ayi ka taimaki mutumin da bayason taimakonka, ko ya kake son yin hakan kuwa. Ba wai magana bace Hamza bayason yi, ba kuma fada mishi bane ba zai iya ba, asali ya tara abubuwa da yawa da ya kamata ya fada mishi baiyi ba. Bai saba daukar laifukan shi ba, yanzun da hakan ya zame mishi dole, baisan ya zaiyi ba, ko ta ina zai fara
"Nayi kuskure..."
Ya furta da wani nisantaccen yanayi a muryar shi
"Ba jiya bane kawai"
Ya sake fadi, daga randa ya fara dagama Hindu hannu ne farkon kuskuren shi, a ranar kuma yaji a jikin shi yayi kuskure, dan ko idanuwa bayason hadawa da AbdulHafiz, satin da yaje gida sai yake ganin kamar Anna zata gane abinda yayi, musamman da yaga Appa, kamar zai gane ya samu rauni a matsayin shi na namiji tunda ya dagawa matar auren shi hannu. Sai dai me, tsintar kan shi yayi da kasa dainawa, ko cikin da yake jikinta baya dubawa, karamar gardama da wahalar gaske su karasa bai daga mata hannu ba
"Karka sake dukana, dan Allah karka sake dukana Hamza, idan zamuyi fadan mu muyi, amman ka daina dukana, zan tafi gidan mu"
Muryar Hindu ta dawo mishi wani lokaci bayan ya hankade ta tayi wata irin faduwa, har taso samun matsala saboda cikin jikinta, tsoron da yaji bayan sun dawo asibiti, ya dauka zaisa ya bari. Sai da ya sake, sosai wasu lokuttan yake binta da idanuwa yana neman dalilin da yasa take mishi uzuri, yana rokonta da ta taimaka mishi, ko barin shine tayi ko zai dawo hayyacin shi, ya rasa abinda yake damun shi haka. Sosai yake daga kwalba fiye da da, cikin son rage damuwar da ta zame mishi abokiya. Kwata-kwata bashi da farin ciki.
Inda wani yace mishi zai kai tsayin lokacin nan da mace daya zai karyata. Amman ko rage zafi ya fita yi da wata yarinya sai maganganun AbdulHafiz sun bishi inda duk ya shiga, wasu lokuttan kamar mai aiki da aljanu, yana dakin hotel din text din tunasarwar AbdulHafiz zai shigo mishi ya kashe duk wani abu daya shiga dakin da shi. Mansy ce kawai ta san yanda take tana samar mishi natsuwa ko da baya tare da ita.
Hakan yasa shi duk ya watsar da sauran matan, da ita kawai yakan yi chat yanzun, yana kuma kokarin ganin hirar tasu ta tsaya iya whatsapp din shi, yana gogewa duk idan sun gama, in ba tsautsayi da rabon suyi tashin hankali da Hindu ya gifta ba, ta dauki wayar tagani. Yau ma kamar kullum, uzurinta ta kawo mishi kamar yanda take yi duk satin nan, sai tace mishi bayanta kamar zai bude.
Hakuri take hada shi da shi, hakurin da baisan yanda zai fara yin shi ba, tunda bai saba ba, bar mata dakin yayi tunda ya riketa a jikin shima sai faman hakuri take bashi. Bayason suyi tashin hankali shisa ya hau sama yana wucewa ya dauko kwalbar giyar shi, ya bude ya ajiye, ya mike ya dauko kofin daya zuba kankaru a ciki ya dawo ya bulbula. Kirane ya shigo wayar shi, yana dubawa yaga Mansy ce ya daga
"Hamzy... An shigo gidana... An shigo gidana yanzun"
Ta karasa tana wani irin kuka kamar zata shide
"Hey...kina ina yanzun?"
Ya tambaya yana mikewa tsaye, amman kukan da takeyi ta kasa magana, hakan yasa shi yi mata magana cikin fulatanci
"Basu tabaki ba ko?"
Dakyar ta iya amsa shi da
"Eh...kudi kawai suka dauka da gold, sai su tv...bansan iya abinda suka dauka ba"
Kofin shi ya dauka yana karasa kwankwadewa
"Ki kulle dakin da kike ciki....bari in zo"
Yanajin kukan da takeyi har lokacin
"Dan Allah ka zo... Bansan wazan kira ba, kai kadai... Kai kadai ka..."
Kai yake jinjina wa
"Shhh.... Gani nan zuwa yanzun"
Ya karasa yana kashe wayar, ya duba agogo yaga karfe sha biyu saura. Mukullan mota ya dauka, kan shi ya danyi nauyi saboda vodka ya sha, tana da karfi, amman zai iya tuqi. Ficewa yayi daga gidan ya dauki mota, kan shi tsaye gidan Mansy ya karasa, ya sha mata magana kan ta sami ko maigadi ne, saboda yanayin shirun unguwar su, amman taqi ji. Aikam tana jin muryar shi ta bude kofar ta fada jikin shi. Riketa yayi sosai yana dan jijjigata a jikin shi
"Ba zan iya kwana a gidan nan ba, ka kaini wani waje... Dan Allah ka kaini wani waje"
Dan har ranta ta dauka mutuwarta ce tazo yau, yanayin su da makamai har su biyar ya firgitata, tazo rufe gida kenan suka afko mata. Kamata yayi suna fita daga gidan zuwa wajen motar shi, sai lokacin ya kula da tata motar ma bata gidan, kuma yasan su suka dauka. Inda zai nufa da ita yake tunani, yanda take a firgice ko hotel ya kaita yasan ba zata zauna ita kadai ba, shikuma ba zai iya kwana tare da ita ba saboda Hindu ita kadai ce a gida, ga tsohon ciki.
"Dan Allah karka barni ni kadai, yau kawai karka barni ni kadai, kana da mata nasani..."
Ta karasa cikin kuka. Kai ya jinjina mata yana nufar gidan shi kai tsaye, akwai dakuna da yawa inda zata kwana, yau kawai. Zuwa gobe sai acan yanda za'ayi. Ko ba komai kawar shi ce. Haka suka karasa gidan, yayi niyyar saiya fara kaita inda zata kwanta, sannan ya shiga wajen Hindu, in batayi bacci ba yasan yanda zaiyi ya fada mata Mansy zata kwana a gidan yanda ba zasuyi rikici ba. Amman sai hakan bai yiwu ba, saboda suna shiga tana saukowa daga sama.
Haka kawai bayan yabar dakinta take ganin kamar zai je yayi waya da Mansy, batasan ya haihuwa take ba tunda bata tabayi ba. Amman har a kasusuwan jikinta takejin tana gab da sauke abinda yake cikinta, duk da asibiti sunce mata tana da sauran satika uku, ko sama da haka, amman yanda bayanta yake amsawa kawai yana karyata likitocin. Amman Hamza yaki fahimta, kamar ranta zaibar jikinta haka takeji duk idan ya kasance tare da ita. Yanda ya fita a fusace har kwalla tayi, jarabar shi ta isheta, har auren ma ya fita a ranta, a hankali komai ma take tsintar kanta da jin baya ranta.
Musamman yanzun da take jin kafarta daya a duniya, daya a lahira, wasu kyale-kyale ne karshen abinda yake ranta, inda wani yace bata fara hauka akan siyayyar kayan baby ba zata karyata. Amman Hamza da yayi mata maganar ca tayi yaba Anna din da ta fara mishi zancen suyi duk abinda ya kamata, ita kam ba zata iya ba, so take kawai taga ta haihu lafiya. Duk da sun yanke hukunci basa son sanin meye zasu haifa din, gara yazo musu a ba zata.
Har bandaki ta duba shi bata gan shi ba, dakyar take saukowa daga benen, da hijab din da ta saka bayan ta daura alwala da nufin yin ko raka'a biyu ce ta nafila bayan fitar tashi, saita kasa samun nutsuwa shisa ta fito ta duba shi. Sai gashi ya shigo,