Showing 84001 words to 87000 words out of 110313 words
Chapter 29 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
gudanarwa, babu wanda ya damu da abinda duk takeyi, tana gama makaranta daga service, wajen da take aiki a Kaduna suka riketa, ta kuma kama haya take zaman kanta, yan wanda suka damu a dangi sun mata magana tayi biris dasu, saboda ita ba zata yanke yancin da ta samu saboda surutun mutanen da bayan rasuwar iyayenta babu wanda ya damu da ita ba, su biyu suka haifa daman, yayanta ya rasu tunda karancin shekaru.
"Babu wani stress, dan zan maka girkin shine zai zama wani abu, daman zan dafa nima. In zaka wuce gida saika biyo ka karba"
Kyaleta yayi tayi din, suka karasa magana kafin suyi sallama kan cewa zai biya ya karba din. Lokacin da taji labarin auren shi, ta daga hankalinta ba kadan ba, abinda ko a takalmin Hamza, ya jima da sanin Mansy na son shi, yana jinta har ranshi, amman ba irin wannan soyayyar ba, kuma tayi mishi tsufa, ko ba haka ba, bazai iya auren mace irin Mansy ba, kishin shi ba zai taba bari ba, ko zai bari Anna zata mutu kafin ta yarda da auren. Shisa kai tsaye yace
"Karki mun rigimar rashin dalili Mansy, ke kinsan ba zan taba auren ki ba, ba tun yanzun ba, kuma kinsan dole rana irin ta yau zata zo. Babu macen da zata daga mun hankali banda Anna a rayuwar nan, zabinki ne muci gaba da abokantaka ko kuma akasin haka"
Kwana biyu basa magana, kafin daga baya kuma ta dawo kamar da, dan shi tsaf zai yakice ta gefe. Kamar yanda ya fadane, har ranshi mace ba zata daga mishi hankali ba, Hindu ma da ta nemi barazana da zaman lafiyar shi, aurenta yayi, gashi nan yanzun komai ya lafa mishi. Shisa ya kira Hindu yace mata karta wahalar da kanta, tunda za'ayi musu abinci. Sai bata daga ba, amman yabar mata text, yasan kuma tagani. Suna gama aikin su da ya dauke su har yamma liqis gidan Mansy ya wuce, ko shigar da motar shi baiyi ba, anan kofar gida ya jirata ta miqo mishi ya wuce.
A hanya ya tsaya yai sallar magriba, kafin yanzun ya karaso gida
"Ka biya wajen Anna ne?"
Hindu ta bukata, tana kallon Hamza daya zame jikin shi ya sauko daga kan kujera, yana janyo kwandon, kafin ya girgiza mata kai
"Gidan AbdulHafiz?"
Ta sake tambaya, saboda tana son jin inda yaje ya shigo da kwando haka, a iya sanin ta dai restaurant ba zasu hado shi da kwando ba, kuma ta shirya mishi kayan buda baki, kulolin ya fara fito dasu, sai wasu robobi masu murfi, yana fara bubbudewa, pepper chicken ne, soyayyar doya da kwai, plantain, sai wata irin jalof din taliya da taketa baza kamshin daya cika wajen, ita kanta sai ta raina dan abinda take tunanin ta hada mishi.
"Nima fa na hada maka kayan buda baki"
Ta fadi da wani yanayi a muryarta da yasa shi kallon ta
"Na miki text fa, nace kar kiyi"
Dan rausayar da kai tayi gefe
"Ina ka samo duk wannan? Na tambaya ko gidan AbdulHafiz kayi mun shiru"
Cikin idanuwa Hamza ya kalleta yana sauke numfashi
"Ba daga can bane, kibarni ni kam, yunwa nakeji"
Tasan ya kamata tabarshi din, amman wani abu na azalzalar zuciyarta
"Ina ka samo abinci?"
Cokullan da suke nade ya warware yana daukar mai yatsu yasa a cikin taliyar yayi Bismillah yana fara ci, ba amsa bane bayason bata, ko ba zai iya bata ba, a gajiye yake jin shi, wani abu kuma na gaya mishi in ya fada mata daga inda abincin ya fito maganar ba zata kare dan yanzun ba. Kwalin Exotic ya dauko ya bude yana kurba, yanajin idanuwan Hindu a kan shi tana kallon shi
"Me kika dafa?"
Ya bukata, duk da bayason yin magana ko kadan idan yana cin abinci
"Koma me na dafa baka shigo da wani ba?"
Hindu ta amsa shi ranta a bace, ita bawai girki ya dameta bane tun farko, shisa abin yake kara bata mata rai
"Ina ka samo abinci? Siyowa kayi?"
Cokalin hannun shi ya ajiye cikin kular taliyar yana kallonta shima nashi ran ya soma baci
"Ban baki amsa bane saboda inajin ba lallai kiso amsar ba, ba siyowa nayi ba Hindu, Mansy ta dafamun, daga gidanta na samo abinci"
Ya karashe maganar yana daukar cokalin shi yaci gaba dacin taliyar a nutse, kallon shi takeyi wani irin abu na tasowa ya tattaru yayi mata tsaya a kirjinta. Mansy, abinci daga gidan Mansy, daga gidan wata tsohuwar banza shisa har yake mata text kar tayi abinci saboda Mansy zata dafa mishi
"Wow.... Like wow, saboda Mansy zata dafa maka shisa kace ni kar inyi kenan ko?"
Banza yayi ya kyaleta kamar ba dashi takeyi ba, yana cigaba da cin abincin shi, dan harya fara dibar plantain din yana hadawa da doyar
"Akan me zata dafa maka abinci? Saboda kana tunanin ni ba zan iya dafawa ba ko me?"
Hindu take fadi tanajin kamar ta rufe shi da duka, ga hawaye sun fara cika mata idanuwa
"Me yasa zaka dauko abincin wata banza ka shigomun da shi cikin gida?"
Abincin shi yake ci har lokacin ko dagowa baiyi ba, saboda ita bata isa ta hana shi cin abincin shi ba tunda yunwa yakeji, bata kuma yi shiru ba, surutai ta cigaba dayi, sai da yaji ya koshi, sannan ya rufe kulolin yana mayar dasu mazaunin su, ya mike ya dauki kwandon da nufin kaiwa Kitchen, itama Hindu ta mike
"Ba zaka mayar dani kamar bansan abinda nakeyi ba H..."
Yanda yai wata irin juyowa yana hade space din dake tsakanin su yasa maganar koma mata, cikin idanuwa yake kallonta
"Idan kina so mu zauna lafiya a cikin gidan nan zaki koyi yanda zaki dinga mun magana. Zakuma ki koyi girmama ra'ayoyina. Dan na miki shiru baya nufin ina gudun rigima dake ne ko wani abu Hindu..."
Numfashi yaja
"Zan shigo da duk abinda nayi niyya cikin gidan nan saboda gidana ne, zanci kuma abinda nayi niyyar ci, ke baki isa ki hanani ba wallahi, tun kafin in aureki nake cin abincin Mansy, dan na aureki me yasa hakan zai canza? Idan kinga zaki iya ci in nazo dashi kici, idan ba zaki iya ba ko ki fita ki siya, ko ki dafa bai dameni ba, amman ba zaki takurani ba, kina jina? Wallahi baki isa ki takurani ba"
Ya karasa maganar yana juyawa ya nufi kitchen din, hannu tasa tana share wasu hawaye masu zafi da suka zubo mata, yana fitowa daga kitchen din ta gefenta ya raba ya wuce, tana jinshi ya haura sama, ranta in yayi dubu a bace yake, ashar din da batasan ta iya ba, shi ta dibo tana aikawa Mansy data ja mata wannan bacin ran, kuma sai ta nemota ta zagi ubanta, in bata kyale mata miji ba, tabbas zasu kwashi 'yan kallo. Ta kai mintina biyar a wajen tana tsiyayar da hawayen bakin ciki, kafin ta shige daki, fuskarta ta wanke, tukunna ta fito tana nufar dining din data shiryama Hamza, yanda baiki cin abinci ba, itama ba zata fasa ba.
Tana cikin ci, ya fito ya sake kaya daga manya zuwa kanana, sai baza kamshi yakeyi, ko inda take bai kalla ba, hannu da taga ya kawo cikin plate din dankali da kwan ta, yasata janyewa
"Ba akwai ragowar na Mansy ba?"
Ta fadi tana watsa mishi harara, murmushi yayi, duk yanda take tunanin ta iya rigima bata kai shi ba, da wurin nan ya kamata tasan ita din bata isa tasa shi ko ta hana shi ba, ya tabbatar ma da kan shi auren nan ba zai takura shi ba, shisa ya daina jin kamar an daure shi da sarkoki, ba kuma zata dawo mishi da yanayin nan ba. Zagayawa yayi, ta sake janyewa, hannuwanta ya kama duka biyun ya rikesu da nashi guda daya, yasa karfi ya karbi plate din yana ajiye shi
"Wallahi ka kyalemun abincina, Hamza bana so, kaje kaci na Mansy, karka taba mun"
Sakinta yayi yana daukar cokali ya caki dankalin yasaka a bakin shi
"Ke kin isa ki hanani yin abinda nayi niyya?"
Ya furta yana wucewa yabarta a wajen, tunda ba yunwa yakeji ba, fita yayi ta kuma san masallaci zai tafi, hannu takai ta share hawayen da taji ya zubo mata, itama mikewar tayi, ta shiga daki tayi alwala, ta gabatar da sallar isha'i, karatun Qur'ani ta farayi, ta mike tayi nafila raka'a biyu, tana cikin yi taji Hamza ya shigo, ya zauna gefen gado, tana idarwa ta daga hannayenta biyu, kawai sai taji wasu sababbin hawayen sun sake zubo mata
"Tafdi jan..."
Hamza ya fadi yana karasa maganar cikin yaren da yasa bata fahimci me ya karasa fadi ba, kafin taji ya kama damtsen hannunta yana kokarin mikar da ita
"Tashi wallahi, kuka kike? Kin kalli gabas kin daga hannu kina sharara hawaye zaki hadani da Allah?"
Cike da mamaki take kallon Hamza da yasa karfi ya mikar da ita, kiciniyar cire mata hijabi ya fara ta kama hannuwanshi tana tutturewa amma a banza tunda ya fita karfi saida ya cire mata hijabi, kafin tayi wani motsi ya hade bakin su waje daya. Zuciyar shi sai bugawa takeyi, sosai hankalin shi ya tashi, inya barta tayi addu'ar nan da wuri Allah zai iya amsawa, duk da yanajin baiyi mata komai ba, amman dai bayason wani dan Adam daban ya nemi hada shi da Allah. Hindu ikon Allah take kallo kirikiri, mamaki ya hanata yin wani kwakkwaran motsi.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 26
Duniyar tayi mishi tsaye waje daya, kallo daya zakai mishi kasan baya cikin kwanciyar hankali, damuwar da take tare da zuciyar shi shimfide take kan fuskar shi
"Me yake damun ka?"
AbdulHafiz ya tambaye shi, kai kawai ya iya girgiza mishi yana fadin
"Babu komai"
Ya kuma ji dadin yanda bai matsa mishi da tambaya ba, saboda bashi da wata amsa tsayayya da zai iya baiwa AbdulHafiz din. A watanni biyun nan cikin Hindu ba karamin wahala yake bata ba, bata kwana biyu ba'a kara mata ruwa ba. Gara cikin satin nan yaga ta fara warware wa, watannin nan sune masu tsayi a rayuwar shi tunda ya mallaki hankalin shi da yayi su batare da mace ba. Shisa a satin nan har cikin idanuwan Hindu yake ganin yanda ko kusa da ita ya zauna a tsorace take da shi. Wuni yake bulbulawa cikin shi giyar da yakejin tana dakushe mishi abinda yake ji.
Abu daya Hindu ta kula da shi yanzun, in har yana gida, yana manne da wayar shi, ita kanta ba dadin take ji ba, sati daya kenan da take samu taci abinci ya zauna, duk tayi wata irin rama. Duk abin Anty sai da suka zo suka duba ta, Baba kuwa zuwan shi hudu, duk idan ya dawo aiki yakan biyo ya dubata, duk da sau daya ta samu ya shigo cikin gidan harya zauna ya sha ruwa. Sauran a tsaitsaye suke gaisawa, ya bata tarin siyayyar kayan ciye-ciyen da take lodawa a fridge, wanda zasu lalace ta baiwa mai aikinta, tunda ita ba iyaci takeyi ba.
Yau ta rasa abinda zatayi, da Dimples tace zata shigo ta saka mata films, saboda zataje gidan su Biebee da bikinta sauran satika uku, suna kan hidimar da ake ta faman yi babu Hindun saboda laulayin da take fama da shi, ta kuma kira cewar ba zata sami shigowa ba, dan wajen aiki basu barta tashi da wuri kamar yanda tayi tsammani ba. Tata wayar ta dauka, yanzun ta zama yar kallo a twitter saboda bakin kishi irin na Hamza, da tayi tweet ma idan yahau yaga maza sun yi magana baya ce mata komai, sai dai ta nemi tweet din ta rasa, ya goge.
Tasan duk inda yake yana gab da dawowa yanzun tunda har anyi sallar magriba. A nan inda ta idar da tata sallar take zaune tana danna wayar. Fita tayi daga nata account din tana shiga na Hamza da taga tarin Notification, ga kuma sakonni da yawa ta DM. Shiga tayi duk yanda zuciyarta take fada mata karta yi hakan, karta jama kanta abinda zai daga mata hankali, amman kuma wani bangare na zuciyar yana fada mata ta duba, tasan Mansy na nan tana bi mata miji, tana kuwa shiga, sakon farko nata ne
"Shegiya mai tallar taba"
Ta furta a fili, wani tuquqin bakin ciki na danne ta, shiga tayi tana ja ta koma daga farkon hirar da tayi mishi magana, tana duba lokaci, jiyane ma, karfe biyu na dare, saboda ita batasan darajar 'ya mace ba. Karfe biyu zata fara yi mata magana da miji, amsar Hamzan tagani, farko hira ce sukeyi mai tsafta, kafin Mansy din ta fara mishi wata magana da ta canza gabaki daya akalar hirar tasu, jikin Hindu babu inda baya bari saboda munin abinda ta kasa daina karantawa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ta furta ganin yanda Mansy take cewa Hamzan ya duba whatsapp din shi ta tura mishi hotunan da video din da ko ita da yake mijinta batajin zata taba iya tura mishi su, ko dan tsoron kar wayar tashi ta fadi, ko a sace da irin wannan abubuwan a ciki da ya kamata ace idanuwan shine kawai zasu gani. Kife wayar tayi, ko ina jikinta bari yake saboda tashin hankali. Ga hawayen da suke cike da idanuwanta sunma ki zubowa saboda zafin da zuciyarta takeyi, daukar wayar tayi tana fara rubutu
"Dan uban babanki duk hotunan da kika tura mishi suna wayata, da screenshot din wannan hirar gabaki daya. Idan bakiyi blocking din shi, kin daina mishi magana ba sainayi posting hirar nan da duka hotunan har da videos din a TL kowa yaga karuwancin da kike bin mazan mutane kina yi. Wawiya, jaka, ballagaza da batasan inda yake mata ciwo ba, tsohuwar banza kawai"
Sai taji zuciyarta tayi mata dan sanyi, da ace zata ga Mansy din ido da ido ta kamata ta jibga kamar ganga sai tafi hucewa, sau biyu tana sake sallar isha'i saboda ta farkon bata da tabbacin ga abinda ta karanta a ciki saboda tashin hankali, tana sallar tana kukan wannan jarabtar da take ciki, batasan ranar da Hamza zai bar zuciyarta ta samu hutun kirki ba. Ta dauka yanzun cikin jikinta yasa shi ya nutsu, duk tunanin da takeyi ya daina shan koma meye taga yasha a daren ta na farko a gidan, saboda bata kara ganin shi cikin maye irin wannan ba. Addu'ar da ta duqufa tana mishi ta karbu ta wannan fannin.
Duk da ta fara dora laifin wannan abin da taga sunyi da Mansy a kanta, watakila da ace bata nuna mishi gazawarta a satin nan bayan hakurin da yayi da ita na watanni biyu ba da bai komawa Mansy ba, da abinda ya faru bai faru ba. Tana sallame sallama sallah yana bankado dakin kamar zai karya kofar hadi da fadin
"Hindu!"
Yana hanyar dawowa, kan shi yayi bala'in nauyi saboda abinda yasha mai karfine, kuma babu wani abincin kirki a cikin shi, so yake yana shigowa gida ya watsa ruwa ya kwanta tunda yayi isha'i. Ya kusa gidan ma yaga kiran Mansy, harya yanke bai daga ba, sake kira tayi bai daga ba. Ganin tayi mishi kira na ukku yasa shi dagawa, dan ya tabbata akwai dalili me karfi da yasa take kiran shi, kukan da yaji tanayi ne yasa shi sauka daga titi yana yin parking gefe, yanda kan shi yayi nauyi ba zai samu nutsuwar yin tuqi da amsa wayar a lokaci daya ba
"Ki natsu kimun magana Mansy, bana gane me kike fadi, me ya faru? Me akai miki?"
Ya karasa tambayar da fulatanci, itama da shi take mishi magana
"Matar ka, matar ka taga hirar mu jiya, ka duba whatsapp kaga me tace mun. Hamzy ka rufamun asiri ka bata hakuri karta doramun hotuna a tl, in dai kaine na hakura wallahi..."
Cike da rashin fahimtar abinda take fadi yace
"Bangane ba..."
Amman kuka takeyi sosai, abinda bai taba gani ko jin tayi ba tunda yasan ta da shi
"Kai kasan a duniya kai kadai kake da wannan hotunan, ko na taba kasadar turawa duk iskancina saboda na yarda da kai. Wallahi ba zan yafe maka ba idan suka bazu, kayi mata magana"
Mansy ta karasa cike da kashedi tana kashe wayar, hakan yasa shi duba whatsapp din shi ko zai fahimci abinda take fadin, screenshot ne na sakon da Hindu ta tura mata
"What the fuck!"
Ya furta a harzuqe yana sauka daga whatsapp din ya kira lambar Mansy
"Bata da hotunanki ko daya, chats dinne kawai da ta gani. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru"
Yana jin ajiyar zuciyar da take saukewa
"Dan Allah Hamza..."
Kai yake girgizawa
"Na fada miki karki damu, babu abinda zai faru, akwai dalilin da yasa kika yarda dani tun daga farko, ki sake yarda da nace miki babu abinda zai faru"
Ya fadi, kafin tace wani abu ya kashe wayar, Allah ne kawai ya karasa kawo shi gidan lafiya saboda yanda yake fisgar motar. Bai aiki Hindu duba mishi chats ba, baiga dalilin da zaisa tayi abinda tayi ba, saboda bata da wata alaqa da Mansy, da shi take da, shikuma shine yake da alaqa da Mansy, shi ya kamata ta zaga ba ita ba. Idan mutuncin shi yake bukatar ya zube zaiyi da kan shi ba saita yi mishi ba
"Me kike tunanin kinyi?"
Ya tambaya yana kallonta, itama kallon nashi takeyi cike da tsantsar mamaki
"Me kake tunanin nayi?"
Ware idanuwan shi yayi yana wani murmushin takaici mai sauti
"Ki amsa mun tambayata, akan me zaki tura mata wannan sakon? Me tai miki da zaki zageta?"
Mikewa Hindu tayi tana son saka idanuwanta cikin na Hamza, tana son ganin da gaske ne maganganun da yake fada mata
"Idan da kunya a idanuwan ka zaka tsareni da wannan tambayar dan na zagi karuwar ka?"
Ta furta, kalmar karuwar shin na fitowa daga wani lungu na zuciyarta da yake mata ciwo na gaske
"Kin taba ganin alamar kunya a idanuwa na?"
Ya tambaya yana hade space din da ya rage a tsakanin su yana tsareta da idanuwan nashi
"Karuwa ta ce, shisa nake tambayar dalilin da zaisa ki zageta tunda baki da alaka da ita, ni ya kamata ki zaga ba ita ba inda kina da hankali"
Wata irin dariya taji ta kubce mata mai hade da wani sautin kuka, duk abinda yake faruwa, duk fadan da sukayi akan sauran yan matan shi, musamman Mansy da ta zame mishi wani bala'i da Hindu ta rasa ta inda zata fara tarbar