Showing 54001 words to 57000 words out of 110313 words

Chapter 19 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

ya zube zaiyi da kan shi ba saita yi mishi ba


"Me kike tunanin kinyi?"


Ya tambaya yana kallonta, itama kallon nashi takeyi cike da tsantsar mamaki


"Me kake tunanin nayi?"


Ware idanuwan shi yayi yana wani murmushin takaici mai sauti


"Ki amsa mun tambayata, akan me zaki tura mata wannan sakon? Me tai miki da zaki zageta?"


Mikewa Hindu tayi tana son saka idanuwanta cikin na Hamza, tana son ganin da gaske ne maganganun da yake fada mata


"Idan da kunya a idanuwan ka zaka tsareni da wannan tambayar dan na zagi karuwar ka?"


Ta furta, kalmar karuwar shin na fitowa daga wani lungu na zuciyarta da yake mata ciwo na gaske


"Kin taba ganin alamar kunya a idanuwa na?"


Ya tambaya yana hade space din da ya rage a tsakanin su yana tsareta da idanuwan nashi


"Karuwa ta ce, shisa nake tambayar dalilin da zaisa ki zageta tunda baki da alaka da ita, ni ya kamata ki zaga ba ita ba inda kina da hankali"


Wata irin dariya taji ta kubce mata mai hade da wani sautin kuka, duk abinda yake faruwa, duk fadan da sukayi akan sauran yan matan shi, musamman Mansy da ta zame mishi wani bala'i da Hindu ta rasa ta inda zata fara tarbar shi, yaune karo na farko da take jin dana sani na tasowa daga dan yatsar kafarta yana tattarowa daga dukkan gabbanta kafin ya samu wajen zama a kirjinta


"Kaine babban marar hankali wallahi, da kana da hankali ba zaka tsareni kana fadamun wannan maganganun akan wata ballagaza ba, kaine babban mahaukaci Hamza"


Da mamaki yake kallonta, a tsayin rayuwar shi banda AbdulHafiz babu wanda ya taba kallon shi ya kira shi da marar hankali cikin raini haka


"Ni kike kira mahaukaci?"


Ya tambaya, kai ta daga mishi tana saka hannuwa ta goge fuskarta da wasu hawayen bakin cikin suka sake zubowa


"Na kiraka mahaukaci, wallahi yaune na fara tir da mugun halin ka Hamza, na dauka zaka canza, na dauka zan iya canza ka, meye a jikin Mansy da ni bani da shi? Me take maka da ni ban iya ba?"


Tayi mishi tambayar da ta dade tana yiwa kanta, yau ta bari ta fito fili saboda da gaske a tsorace take, tsoro bana wasa ba da halin Hamzan, a karo na farko tanajin kamar bata isa ta canza shi ba, kamar shi din bayason canzawa, in kuma bayason canzawa ita bata isa ta canza shi ba


"Ka fadamun abinda take dashi da bani da shi, ka fadamun me kake nema a jikin ballagazar nan!"


Juyawa yayi da nufin fita yabar mata dakin, saboda sosai kalamanta suke kara harzuqa shi, musamman da yakejin tana gab da fada mishi tayi dana sanin auren shi, idan shi bai gaya mata yayi nata ba, ba zai jira ta fara fada mishi ba


"Ina zaka je? Ka amsa ni inji, ka fadamun abinda yake jikin karuwar taka da bani da shi"


Juyowa yayi, muryar shi can kasan makoshi yace


"Idan ba zaki iya karanta chats dina kiyi kukan ki ke kadai ba, karki sake shigar mun. Karki sake mun makamancin abinda kikai mun yau, wallahi zan baki mamaki, baki sanni ba har yanzun"


Sosai take kallon shi tana sake sa bayan hannunta ta goge fuskarta


"Wallahi idan yanzun na sake hawa saina zagi uban uwar Mansy, kana jina, saina zageta, akanta ne kake fadin zaka bani mamaki. Allah ya baka iko....na zageta, Hamza na zageta ka..."


Bata karasa ba saboda marin daya dauketa da shi, wata irin walkiya na giftawa ta cikin idanuwanta, da gaske ne, littafi bai mata karya wajen rubuta kalar marin nan ba, ta runtsa idanuwanta tana bude su yafi sau hudu dan ta tabbatar da kwayar idonta bata fado ba. Kafin ta dafe kuncin, ta nemi hawaye ma ta rasa dan azaba


"Na fada miki zan baki mamaki kinqi yarda ko?"


Ya furta da wata irin murya dashi kanshi ta sauka kunnuwan shi da wani yanayi, jikin shi har bari yake saboda bacin rai, ya dauka Auta ce mace daya a rayuwar shi da zai taba dagama hannu. Saboda bai hango Hindu zata tunzura shi haka ba, zata saka shi jin son ya jibgeta har saiya daina jin nauyin da kanshi yayi


"Mar... Mari, ni ka mara? Akan Mansy ka mareni?"


Tsaki yaja mai sauti, yana wucewa hadi da jan kofar da karfi, kafafuwanta da taji suna rawa suka sakata zama, amman jikinta bari yake, dole ta kwanta, tanajin hawayen da suke bin gefen fuskarta, ga kirjinta da yayi nauyi kamar zai bude, mutanen da suka taba marinta basu da yawa a rayuwarta, ta kuma manta ranar da hakan ta faru. Mijin da take karkashin inuwar aure da shi, ko a mugun mafarki bata taba hango zai daga mata hannu ba, ko da hakan ta faru ba'a kan karuwar shi ba. Ba akan ballagazar da ko kira ta 'ya mace ba zata nuna mata ba, ballantana kuma daraja.


Ta sha jin labarai na cin mutunci irin na da namiji, amman nata ne mafi muni da taci karo da shi a tsayin rayuwarta, yau ita Hindu, ita Hamza ya daga hannun shi ya dauke da mari saboda karuwa...!


***


"Ban gane yace zai saka ranar da za'a kwashi kaya ba, sai ku ka taho kukuma?"


Baba yake fadi ranshi a matukar bace yana kallon Muhsin da Huzaifa


"Baba bana so in biye mishine ni, saboda kar ayi abinda za'aji kunya ko da sauran zama"


Huzaifa ya fadi a tausashe


"Wanne sauran zama? Shi da wanene zasuyi sauran zaman?"


Shiru su Huzaifa sukayi, cikinsu babu wanda baisan halin Baba ba idan ranshi ya baci


"Ya kore muku 'yar uwa cikin dare da tsohon ciki har kuyi tunanin akwai sauran zama a tsakanin su. Halan bakwa kishin ta ne?"


Kai Huzaifa ya girgiza, yana shirin magana Muhsin yadan zungure shi alamar yayi shiru, tsaki Baba yaja


"Ku koma ku kwasomun kayan yarinya dan banason su kara kwana a gidan wannan marar mutuncin"


Muhsin ne ya fara mikewa yana ma Huzaifa ido, shima ya mike suka fice daga falon


"Kasan halin Baba babu abinda zai saurara yanda ran shi ya baci, kuma Hindu aka taba, ni wajen aiki zan wuce, zuwa anjima watakila ya huce yanda zai iya fahimtar mu"


Kai Huzaifa ya jinjina


"Allah dai ya rufa asiri. Ni naso inga Hindun ma wallahi"


Dan murmushi Muhsin yayi


"Ka rufawa kanka asiri ka wuce, anjima ka dawo kaganta. Yanzun wallahi Baba kaniyar mu zaici"


Shi Huzaifa ma sam ya kasa yin ko da murmushin ne saboda takaici. Shi kan shi idan za'abi shawarar shi za'a hakura da maganar Hindu ta koma gidan Hamzan nan. Tare da Muhsin din suka fice daga gidan, da shawarar duk idan kowa ya dawo daga neman halal dinshi zasu sake dawowa suyi ma Baba magana ko zai fahimci abinda suke son ya fahimta din.


Cikin gidan kuwa, Anty najin duk abinda yake faruwa, idan ta gwada yiwa Baba magana ita kanta ranta ne zai kara baci fiye da yanda ya baci yanzun. Shisa ta nufi dakin Asma tana samun Hindu a kwance ta zubawa bango idanuwa, sai taji tausayin ta ya cika zuciyarta


"Hindu..."


Ta kira da wani irin yanayi a muryarta, tana saka Hindun tashi dakyar ta jingina bayanta da gadon, karasawa Anty tayi tana shiga cikin dakin sosai. Ta zauna gefen gadon


"Hindu ke kadai kikasan meya hadaki da mijin ki, kamar yanda ke kadai zaki taushi zuciyar Babanku yayi hakuri abi komai a hankali..."


Tunda Anty ta fara magana taji idanuwanta sun ciko da hawaye


"Anty ki kyale shi kawai, ni ba zan taba komawa gidan shi ba, wallahi nagaji, tunda na fito na fito kenan da yardar Allah"


Ta karasa maganar tanajin wani zogi da ba sabo bane a zuciyarta. Karfin tahowa gidane bata da shi daman tun watanni biyun da suka wuce, da tuni ta kamo hanya ta gudo daga gidan auren daya zame mata qangin da bata tana hangowa ba, daga auren mijin da kowa zau kira da kyakkyawa amman a idanuwanta sai da ya juye ya koma kamar dodo. Ba auren Hamza kawai take son gujewa ba, gabaki daya kalmar aurene bata son ji


"Hindatu..."


Anty ta kira da wani irin yanayi a muryarta, kai Hindu take girgiza mata, tana wani irin gunjin kuka me sauti


"Anty karkice inyi hakuri, ya rigada ya sakeni, komawa ba zabi bane ko da ina so..."


Hindu ta karashe, ballantana tunda ta shigo gidan takejin tana shakar wata irin iska mai sanyi da ta kwana biyu bata shaqi irinta ba. Ya saukake musu auren daya zame musu karfen kafa. Da kan shi ya sauke aurenta daya kira da kaddara


"Kaddarar auren ki ce kaddara ta farko da nayi dana sanin ta Hindu a duk kaddarorin da suke cikin rayuwata"


Ko kadan baya dana sanin kaddarar bin mata, kaddarar shaye-shaye sai ita, sai aurenta. Hamza ya gama cire mata duk wani kyale-kyale na aure da take tunani, taso MIJIN NOVEL, a sujjadarta ta roki MIJIN NOVEL, sai dai bata roka da kalar halayyar shi ba, har a zuciyarta idan ta hasaso, kudin, kyawun da soyayyar kawai take gani. Ta dauka ita kadai ta isa ta rike auren su, bata dauka aure ya wuce duk wannan ba. Hamza ya bude idanuwan ta, ya wanke tunaninta tas, ya dasa mata neman asalin dalilin da yasa aka saka aure a cikin jerin ibadu


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"


Anty ta fadi, wani irin daci na zauna mata a zuciya, kalmar saki abuce mai muni a duniyar ma'aurata komin karfin dalilin yin hakan kuwa. Ko labarin saki taji sai zuciyarta ta tsinke, yanzun da labarin ya fito daga bangaren ta, daya faru akan 'yarta ji take zuciyarta ta matse a cikin kirjinta tana wani irin ciwo


"Allah Kai Kadai Kasan me Ka boye a cikin wannan lamarin. Allah Ka bamu juriyar cinye dukkan jarabtar da ka tsara mana"


Anty take fadi a cikin ranta, kafin ta dora da


"Alhamdulillah ala kulli halin"


Tana cigaba da maimatawa, hannu Hindu tasa tana share hawayenta


"Ya sakeni Anty..."


Ta sake fadi, kalaman na zauna mata, ba kukan rabuwa da Hamza takeyi ba, kukan tarin abubuwan da ta hadiya a karkashin auren shi da tunanin zata iya gujema kawowa inda take yanzun. Kamota Anty tayi, a karo na farko da hakan ya faru, gyara zamanta tayi tana kwanciya ta dora kanta a cinyar Antyn, kuka take kamar zuciyarta zata fito, kuka take yau da take samun lallashin da ta dade bata samu kalar shi ba, kuka tayi har baccin wahala yai gaba da ita...!


*


*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*


Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank


Whatsapp Number
08074545149
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 6


Zufa take da bata da alaka da zafin gari tana girgiza ma wayarta kai, dan bata ga dalilin da zatayi mata abinda tayi mata ba, ya kamata ta tabbatar da abinda take tunanin idanuwanta sun gani. Ga Asma bata da waya balle ta dauki tata, da dare baiyi ba tabbas bangaren Mama zataje ta karbo wayar Khadee


"Dan Allah.... Dan girman Allah ku kawo wuta. Ku taimaki rayuwata"


Take fadi kamar wadda ta sami tabin hankali, har a kasusuwan jikinta take son tabbatar da fuskar da tagani a jikin Hamza take, fuskar da ta sami waje tana zaunawa a zuciyarta. Lumshe idanuwanta tayi tana ganin nashi da ruwan kasane mai cizawa sosai, duk da kalace da ake samu a tattare da yan Nigeria, yankan idanuwan nashi abin daukar hankaline, shisa take so su taimaketa su kawo wuta, taga idanuwanta ne ko da gaske labban Hamza ne wani irin ruwan hoda da ba kasafai ake ganin su ba, ko a fina-finan kasashen ketare. Gashin kan shine bata kula ba, saboda askin shi buzz cut ne kamar, akwai hular rigar da take jikin shi.


Tsaki taja tana juya kwanciya, ba karamar cutarta yan Nepa sukai ba, duk kalar zagin da yazo ranta shi take auna musu, caji ta jona tana kunna socket din, da sun kawo ba saita tashi ba, ta lumshe idanuwanta, fuskar Hamza na dawo mata kamar yana tare da ita, kafin barawon bacci ya dauketa. Duk da haka a daren bata san adadin farkawar da tayi ba, tana ganin basu kawo wuta ba har lokacin, sai ta sake komawa bacci, a haka har aka kira sallar asuba, Asma ta tasheta, saboda ba wani wadataccen bacci ta samu ba, ta dai godewa Allah bata da lakca sai sha daya, dakyar ta idar da sallah, zata fara Azkar suka kawo wuta, dan casbin hannunta tayi cilli dashi gefe tana nufar wayarta kamar zata kifa


"Ikon Allah...."


Asma ta furta, ko inda take Hindu bata kalla ba, wayarta take kokarin kunnawa, amman taki kamawa, dan tsayawa tayi tana kallon wayar har tayi 1% tukunna ta kunna tana cire mukullin sirrin da yake rufe da wayar. Data dinta a kunne take amman wayar bata gama loading ba, ji take kamar tayi me dan zumudi. Tana samu wayar ta fara loading ta shiga Instagram tana komawa shafin Hamza, sai da ta fara danna 'Follow' tukunna ta bude profile din shi, yanda na Facebook yake haka wannan din yake shima. Hoton farko da taci karo dashi da dare ta fara budewa, tana jin bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta. Tafukan hannunta har wata zufa suke.


Duk da ma'abota lafazi kance zuciya ita take ganin kyawu ba idanuwa ba, zata rantse tunda take kalle-kallen fina-finai bata taba ganin wanda yai mata kyawun Hamza ba, kamar komai nashi shiya zaba, daga hancin shi, idanuwan shi, girar shi da take a cike, da kasumbar da take kwance a fuskar shi data kara mishi wani kyau naban mamaki.


"Oh Allah na"


Hindu ta fadi zuciyarta cike da shauki, dakyar ta iya danna Back tana fita daga cikin wannan hoton. Wani hoton takai tana ganin su shida abokan shi, rigar shi wannan karin babu hula, amman mai dogon hannu ce, gabaki daya abokan shi sun hadu iya haduwa, babu wanda ba zata iya aure ba indai suna da kudi, kyawun su yayi mata, amman a hoton zaka gane yanda kyawun Hamza ya bambanta dana sauran. Yayi tagging din abokan a kasan hoton, bubbude tags din tayi tana following su duka hudun. Fodio, Arafat, AbdulHafiz, sai kuma Abdallah.


Sannan ta dawo kan hotunan Hamza tana cigaba da dubawa, idanuwanta na tsayawa kan wani hoto shida wata mata mai matukar kyawu. Ya rubuta 'Ann❤'. Duk da sunyi kama dashi sai taga kamar tayi yarinta data haifi Hamzan, watakila babbar Yayar shi ce. Fita tayi tana shiga wani da ya saka 'Barka da Sallah' jikin shi sanye da farar shadda kal, har hular kanshi fara ce, kasa hakuri tayi ta zare wayar daga cajin tana share 'low battery' din data rubuta, da zumbuleliyar hijabin sallarta ta fice daga dakin zuwa bangaren Mama, tana shigewa dakin su Khadija ta sameta zaune da Qur'ani a hannunta


"Khadee kinga Hamza kuwa? Tafdin... Kinga Hamza"


Ta karashe maganar tana mikama Khadee wayar, data karba tana rikewa sai da takai karshen ayar da take karantawa, tukunna ta dago ido tana kallon Hindu da take numfarfashi kamar taga wani waliyyi, magana zatai ma Hindun ta dago wayar tana kallon hoton da yake kai


"Allahu Akbar....Allah mai halitta"


Ta fadi cike da jinjina Girma na Ubangiji da yake wanzar da halitta kala-kala a tsakanin yan adam, wasu kagansu munana, wasu tsaka-tsakiya, wasu masu kyau, wasu kuwa kyawunsu kamar ba mutane ba, kamar sun fito daga jinsin aljanu, Hamza na cikin kalar wannan mutanen


"Hmm... Kibari kawai, wallahi na kasa yarda cewar shi dinne"


Cewar Hindu, Khadee na dorawa da


"Sai kace aljani, Ikon Allah kenan...."


Wayar Hindu ta karba


"Bari kiga sauran abokan shi ma"


Tana komawa baya ta kai kan hoton Hamza da abokan nashi tana nunawa Khadee


"Jiba rashin adalci, shi yana da kyau duk saiya kwashe masu kyau yake abokai dasu, jiba wannan bakin... Inalillahi... Duk yafi su kyau harda Hamzan"


Leqa kai Hindu tayi


"AbdulHafiz ne"


Nata kan Khadee ta daga tana kallon Hindu cike da mamakin yanda akayi ta san shi


"Duk na duba sunayen sune, kuma wallahi baifi Hamza kyau ba, tafdin, dan dai yana da dogon hanci shima"


Sake dubawa Khadee tayi


"Kai mun handle din shi ingani, kin san Allah yafi Hamza kyau, hasken fata kawai zai nuna mishi"


Da sauri Hindu ta nemo sunan AbdulHafiz din suna shiga hotunan shi, na farkon da yayi murmushi har dimple din dake gefen fuskar shi ya loba ciki kamar ka saka dan yatsa


"Haba Hajiyata... Kiga gaye iya gaye... Haske fa Hamza zai nuna mishi"


Wayarta Hindu ta fisge


"Ban wayata ni, ke baki san kyau ba sam, ni karki batamun rai dan Allah"


Ta karasa maganar tana mikewa ta fice daga dakin, murmushi Khadee tayi kawai. Hindu taki yarda ne, amman AbdulHafiz duk yafi sauran kyau, amman dai-dai wani karkataccen wani, hankalinta ta mayar kan Qur'anin da take karantawa, dan shi yafiye mata alkhairi da maganar kyawun mutanen da basu san da zaman su ba, Khalifanta bashi da kyau kamarsu tasani, ba zatayi karya ba, amman shi dinne zabinta, kuma shidin take fatan ya zama alkhairinta.


Hindu kuwa daki ta koma ta mayar da cajinta dan wayar ta samu sosai. Tasan halin yan Nepa, sam basu da wata daraja. Zasu iya dauke wutar duk da basu kwana da ita ba. Bandaki ta shiga ta watsa ruwa dan karta fara bacci ta farka a makare. Tana shafa mai ta kwanta. Tun tanajin motsin Asma da ita karfe bakwai da wani abu na safe za'a kaisu makaranta harta daina ji, bacci ya saceta, wani irin bacci cike da hargitsatsen mafarkin Hamza, da bayan ta tashi duk yanda taso ta tuna me ya faru a mafarkin ta kasa.


Kiran Hauwa tagani har biyu, sai kuma text din data bude


'Ke kinji Arc Aboje ba zaizo ba, ya bada handout dai, ki karbar mun in kin shiga school dan Allah. Idan baki shiga ba kuma shikenan'


Numfashi ta sauke, taji dadin rashin zuwan da Malamin nasu ba zaiyi ba. Amman dai ko wajen sha biyu zata shiga ta karbar musu Handout din, gara ta kwana a hannunta sai tafi samin natsuwa. Ita bama sosai take printing ko photocopy ba, tunda Huzaifa na da shagon da akeyi irin abubuwan nan, sai dai ta aro na wani a aji, sai ta bashi yayo mata, yanzun ma duk da yana kwana gida ba sosai take ganin shi ba, tunda aka saka mishi ranar biki yake wahalar gani, dan lokacin da baya wajen aiki tasan yana can zance. Duk wasu sun kwace musu Yayye suna gani, haka Muhsin ma da haduwa da yarinyar da maganar auren duka kasa da wata hudu, abin ya jima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login