Showing 72001 words to 75000 words out of 110313 words
Chapter 25 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
mayafin ta dauka ta dora a saman kanta tana yafashi ta baya. Bata wani dauki takalmi mai tsini ba, flat ta saka sai jaka data dauka fara, kalar takalmin.
"Muje?"
Ta furta tana kallon Hamza da yakejin kamar su fata fita, dan dai ya fadama Anna zasu zo, amman Hindun tayi mishi kyau ba kadan ba
"Kinyi kyau"
Murmushi tayi
"Kaima haka..."
Ta furta, ya saka shadda, golden mai haske, sai daukar ido takeyi, ga kamshin shadda mai tsada daya hadu dana turarukan shi, mikewa yayi
"Ina wayar ka?"
Ta bukata, hannu yasa a aljihu, haka kawai yasan hoto zata dauke su, cire wayar yayi daga key yana matsawa kusa da ita ya daga camera din yana daukar su, sosai sukai hotuna wajen kala goma, dan wani ma saida ya sumbaci kuncinta tukunna suka dauka, dariya sukeyi idan sukayi wani style din, kafin bikin Hamza yayi kara
"Ke yunwa fa nakeji, ki wuce mu tafi wallahi"
Dariya tayi tana daukar ledar dayasa hannu ya karba suka fita tare, har mota shi ya bude mata, haka kawai sai take jinta da wani irin muhimmanci a wajen shi, bakomai dan har yanzun bai nadota a towel ba, tasan dabarar da zatayi hakan ya faru, bari dai ta samu ta kama zuciyar Anna. A nutse Hamza yake tuqin shi har suka isa gidan, yayi parking yana fitowa. Kallon gidan Hindu takeyi, yayi mata kyau matuqa duk da baikai na Hamzan ba. Shi ya fara yin gaba suna shiga cikin gidan da sallama, sosai gabanta yake faduwa, kafin matar da tasha ganinta a hotuna, kuma bata gajiya da mamakin cewa itace mahafiyar Hamza ta amsa musu sallamar
"Ann"
Hamza ya fadi yana karasawa da fara'a a muryar shi, dan rike mata kafadu yayi yana sumbatar kuncinta
"Ina kwana..."
Ya furta, Hindu na tsaye tana kallon su
"Kai ba zakace ta zauna ba"
Ann ta fadi cikin yaren shuwa, duk da Hausa Hamzan yayi mata, tana mayar da hankalinta kan Hindu hadi dayin murmushi
"Ina kwana"
Hindu ta fadi, da alama tanajin Hausa, kafin ta amsa Hamza ya karaso inda Hindu take yana fadin
"Ki zauna"
Batayi musu ba ta sami kujera ta zauna, dan kafafuwanta sun mata wani irin nauyi, kujerar da take fuskantar ta Hindu, Anna ta zauna
"Nifa yunwa nake ji"
Hamza yai maganar da harshen Anna din, duk suna saka Hindu jin wani iri
"Karki damu da shi kinji ko, kin tashi lafiya?"
Sai dai kafin Hindu ta amsa, wata siririyar yarinya da Hindu taga hartafi Hamza kyau ta fito, jikinta sanye da doguwar riga irin ta mutanen saudiyya, kanta daure da jan dankwali ta rigata da
"Inalillahi.....Ann tayi Hausa...."
Kusan a tare Hamza ma dayake tsaye baki a bude yace
"Ann!"
Ko kallon su Anna batayi ba, Hindu kuwa ta kasa daina murmushi, kafin yarinyar ta karaso ta zauna gefen Hindu
"Matar Yayan mu"
Kallonta Hindu tayi
"Yaaya kagama boye mana ita, yau gata har gida"
Dariya Hamza yayi
"Daman kune da gajen hakuri ai"
Gaisawa Hindu tayi da Auta, data mike daga inda take zaune tana fadin
"Nikam ban karya ba"
Hamza da sauri yace
"Wallahi nima"
Wannan karin Anna ce ta mike
"Ku gama karyawa, ina zuwa"
Dan taga Hindu a takure take, yarinyar tayi mata kyau, ta kuma burgeta matuqa, sam batayi mata kama da irin tsagerun yaran zamanin nan ba. Tana bar musu wajen, Auta na kama hannun Hindu ta mikar da ita
"Ki zo muje muci abinci"
Ba shiri Hindu ta ajiye jakarta tana binsu, har wajen cin abincin, suka zauna. Da kanta yarinyar ta zuba ma Hindu plantain da soyayyen dankali, ta kuma hada mata Tea
"Auta baki ganni bane halan"
Hamza da harya gaji da jira ya fadi yana mika hannu ya dauki kofin shayin Hindu, Auta ta kuwa rike mishi hannu
"Sake mun hannu"
Kallon shi tayi
"Kabar mata nata dan Allah, zan hada maka yanzun"
Da fulatanci tayi mishi maganar, saboda sam ba sabawa sukayi da yiwa juna Hausa ba. Ajiyewa yayi kuwa, ta hada mishi nata, ita Hindu duk da yunwar da takeji a kunyace take, sukam hira sukeyi kamar bata wajen, da alama itace ta takura kanta. Auta ma nan tabar su, sai lokacin Hamza yace
"Ke ba zakici abinci ba ko? Karki cemun kina jin yunwa Allah"
Murmushi tayi, da sauri-sauri take cin dankalin kafin su kara fitowa, sai dai harta gama babu wanda ya fito, falon suka koma suna zama ita da Hamza, da alama flashing yayiwa Anna, sai gata ta fito
"Tafiya fa zamuyi Anna"
Hamza ya fadi, kallon su tayi
"Ayita hakuri kunji, Allah ya baku zaman lafiya"
Hindu sunkuyar da kanta tayi, Hamza ne ya mike yana daukar ledar daya ajiye ya karasa ya mika ma Anna
"Wai a baki Anna"
Da murmushi tasa hannu ta dauki ledar
"Ma shaa Allah, nagode sosai. Allah yasa albarka"
Mikewa Hindu tayi
"Mungode Anna, Allah ya kara girma"
Sannan sukayiwa Anna sallama, tace musu Appa ya fita, dan haka suka wuce kawai. Suna fita daga gidan Hindu na sauke wani numfashi da batasan tana rike da shi ba.
"Matsoraciya"
Hamza ya fadi yana dariya
"Nace miki Anna bata da matsala baki yarda ba"
Murmushi tayi
"Nagani aikam, na dauka kana da kyau sai da naga Auta"
Dariya yayi sosai wannan karin
"Faruk yafi kowa kyau, duk zaki gansu a hankali, mu biya mu siyi abinda zamuci da rana?"
Kai ta daga mishi
"Har dare ma, mu saka a fridge..."
Kai kuwa ya jinjina mata, suka biya Chicken Republic, sannan suka wuce gida.
*
Sati biyun nan a jigace tayi su, ta dauka zaiyi mata kadan, yanda ta hasaso satika biyu babu inda zasu kaisu, amman yanzun da kanta take neman hanyar da Hamza zai fita daga gidan ko na yini dayane ko zata samu sauki
"Ba yau zaka koma aiki ba?"
Ta bukata, ganin ya bude system din shi, kallonta yayi ta kasan idanuwa
"Kingaji dani ne?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, amman yasan karya takeyi, a idanuwanta yake karantar hakan. Kuma dole ta koyi hakurin zama dashi tunda a yanzun ita kadai yake da ita, ganin yayi shiru ya bata karfin gwiwar yi mishi tambayar da take ta cinta a rai
"Ba zamuje honeymoon din mu ba?"
Saida yayi kamar baiji taba, tukunna ya dago idanuwa, kafin ya kwashe da wata irin dariya, ganin tana zaune dai tana kallon shi yasa shi fadin
"Wai da gaske kike?"
Kallon shi dai takeyi har lokacin, dan sam bataga abin dariya a maganar da tayi ba
"Da gaske kikeyi"
Ya furta yana tabbatar ma kanshi
"Hindu anan ma harkin gaji dani, idan muka tafi wani waje wallahi ba zaki iya ba, kuma kin kusan komawa makaranta ma..."
Dan turo mishi labba tayi, da gaskene ta kusan komawa makaranta, amman hakan baya nufin zai hana musu zuwa honeymoon dinsu in yayi niyya, kasar wajen a kwana nawa ma za'a iya zuwa a dawo
"Ni dai ba wani, a kwana nawa zamu bar kasar mu dawo"
System din shi Hamza ya ture gefe, saboda har ranshi ta fara saka shi nishadi
"In zamuje da wacce kasa zamu tafi to?"
Da sauri ta amsa da
"Paris"
Jinjina kai yayi, sosai kasar take burgeta, akwai wata Hawwaty a Instagram, can taga sunje da mijinta, kalar hotunan da suka kashe a wajaje daban-daban sun bala'in burgeta
"To yaushe ya kamata mu tafi, tunda kinga Monday zaku koma makaranta"
Dan shiru Hindu tayi, ranta yayi wani irin qal
"Ko gobe da safe haka"
Sosai Hamza yake kokarin danne dariyar shi, amman ganin da dukkan gaskiyarta yasa shi kwashewa da wata dariyar, system din ya dauka yana mikewa, Hindu ba zata kashe shi ba
"Ko Abuja zamuje ai sai haka Hindu, kinsan samun visa kuwa? Kina magana kamar zamuje Barnawa.... Kibar ni aiki zanyi"
Hamza ya karasa yana dariya, kafin ya fice daga dakin, sai dai a gabaki daya maganar da tayi bataga abin dariya ba. Yana magana kamar ba zai yiwu subar kasar a gobe ba, a littafi sau nawa ta karanta, rana daya za'a yanke tafiya kasar waje, sai dai a shirya a wuce airport, yanda wasu ma suka mayar da fita kasashen ketare kamar dakinsu, akwai littafin data karanta, gayen ciki duk juma'a a Madina yake sallar juma'a, duk da wannan suna da nasu private jet din, amman ai ba abin mamaki bane ba.
Kwanciya tayi tana daukar wayarta, gara ko hira su danyi da Dimples, Hamza ba zai gaji da disappointing dinta ba sam-sam.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 9
Dan baccin da ta samu bai shige awa biyu ba, sai taji kamar tana rufe idanuwanta ne aka kira asuba ta sake bude su, cikin yan dakika zuciyarta tai wani irin tsalle daya tuna mata akwai abinda ya faru da ita a daren jiya, kafin tai wata irin mikewa daga kan gado tana daukar wayarta, dan ko addu'ar tashi bacci ma batayi ba. Duk da daukar wayar da sassafe haka dabi'arta ce, Dimples kan ce
'Daga tashi da safe sai ka janyo waya, baka duba ko zaka iya magana ba, ka taka kafafuwan ka kaji ko suna nan lafiya ba, ka dauki waya. Baka ma godema Allah daya dawo maka da ranka ba, tsabagen rashin hankali. Sai ranka ka gama latsa wayar kayi ka mike ka kasa tukunna zaka dawo hayyacin ka'
Kuma maganar Dimples din tayi tasiri a ranta ba kadan ba, wasu lokuttan da tazo daukar wayar ta tuna sai ta ajiye ta fara yin addu'ar tashi, wata rana har alawala ma sai tayi indai da wuta, in babune zatai amfani da fitilar wayar. Amman yau baiyi amfani ba, dan so take ta tabbatar da cewa da gaske ne tayi magana da Hamzy. Tayi magana da Hamza Abu Abbas, Instagram din ta koma tana bin gabaki daya hirar hadi dayin wani murmushin nishadi, kafin ta tashi har Asma ta rigata mikewa ta shige bandaki, zaune itama Hindun ta tashi tana tunanin dalilin da zatayi amfani dashi wajen sake yiwa Hamza magana.
Mikewa tayi tanayi shiga bandaki, ganin lokaci ya kure yasa tai alwala ta fito tana gabatar da sallah, tadan yi karatun Qur'ani, ta gabatar da azkar din safe, tana kuma bin shi da addu'arta, ta yau da kullum. Wannan karin tana ji har a ranta tamkar addu'ar ta gama amsuwa. Sai da tayi wanka ta shafa mai, sannan ta sake kwanciya tana komawa wani baccin sanin cewa sai karfe goma da rabi take da lacka a safiyar. Sanda ta tashin ma goma tayi, fuskarta ta wanke, tana gyarawa ta sake kaya tayima Anty sallama ta fita, ko yunwa ma bataji, in sun fito sha biyu da rabi sunje restaurant ita da Hauwa.
Tana fita harabar gidan tana cin karo da Musa daya fito daga motar shi, yana sata jan karamin tsaki, duk da taji Mama na fadama Anty an saka bikin shi, bai hana mata haushin shi da take ji ba, manyan kayane a jikin shi ruwan omo, yana rike da hular kayan a hannun shi, ga kan yasha aski sal, sai taga yayi mata kama da dan ta'adda saboda kasumbar daya tara ya kuma salle kai tas, dan dai bata jin akwai gajeru kamar shi a cikin su, saura kiris taji ya cire mata son da takema kasumba a fuskar maza, tahowa yayi bigil-bigil, gajartar da askin na haduwa su saka shi yi mata tamkar kwalbar roll on.
"Hindu..."
Ya kira yana mata murmushin da yasa ta kara tamke fuskarta tana furta
"Sannun ka"
Ta rabashi ta wuce karma ya kara samun damar da zai mata wata magana da sanyin safiyar nan, ita bama kullum take son yawan haduwa da gajerun mutane tunda sassafe ba haka, Musa kuwa kai ya girgiza, ance zuciya bata da kashi, kuma masoyi baya laifi, shikam ya yarda da haka, dan har yanzun da sa ranar shi amman yana jinta har ran shi. Soyayyar da yake mata ba karama bace, haka dai Allah ya kadarta ba zai sameta ba, ya kuma rungumi kaddarar shi da hannuwa biyu. Tunda yanzun in ba wani dalili mai karfi bama, baya zuwa gidan sam-sam.
Da ta isa makaranta taji haushi sosai jin cewa Malamin ya fasa zuwa, ta kuma san ganin Musa da tayine ya shafa mata rashin sa'ar nan, Hauwa ta kira tana fada mata
"Taf... Kinga saurin da nake, kice inyi zamana"
Kai Hindu ta girgiza
"Banza kizo dan Allah... Ni banajin komawa gida ma sam"
Tana jin dariyar da Hauwa tayi
"Ashe in zo, bacci zan koma wallahi, kinji kaina yanda yayi nauyi"
Ita kanta Hindun da tasan ba zaizo ba kwanciyarta zatayi tai baccinta, ko ma ta kara rage assignment din da yake gabanta
"Ai shikenan, bari in koma kawai. Sai munyi magana, ki gaishe da Anty"
Tana sauke wayar daga kunnenta bayan Hauwa din ta amsa. Kamar yanda tace mata, gidan kuwa ta koma, sai dai batayi sauri ba, dan bata son komawa ta sake haduwa da Musa, kar ya kara shafa mata wata rashin sa'ar Hamza yaki kulata. Da ta shiga gidan ma a falo ta cire abayar dake jikinta tana ajiyewa da jakar, ta shiga kitchen. Dankali ta fere ta soya ta dauko ta fito, kayanta ta tattara tana shigewa daki dasu. Kan tabirin zanenta ta dora plate din dankalin ta linke abayar sosai ta mayar da ita inda ta fiddo da dan mayafin nata. Sannan ta dauki plate din da wayarta tana komawa kan gado.
Twitter ta leqa ta samu ana cece kuce kan maganar yawan sakin aure, mata na ba maza laifin, su kuma suna kin karba. Ta sauka ta koma Instagram tana shiga shafikan kwalliya, a nutse take duddubawa sosai, dan ita bakowacce mai kwalliya bace zata taba mata fuska idan bikinta ya tashi. Dinki kan shi tana da telolin da take hari, tasan duk yanda Baba yake sonta, bashi da kudin da zai mata kalar bikin da take mafarki, amman tare da hamshaqin mijin da zata samu, abin bazai wahala ba sam. Tunda tana da yakinin zai bata wadatattun kudi da zata gudanar da hidindimunta a cikin tsanaki.
Dabara ce ta fado mata a rai, tana sakata ajiye plate din dankalin a gefe tana mikewa, zanikan da tayi daren ta dauko, ta warware su tana dauka hoto daya bayan daya, guda shidda ne daman ta gama, sannan ta bude Instagram dinta. Sallama ta fara yima Hamza sannan ta tura mishi hadi da dorawa da
'Bansan ko nayi dai-dai ba'
Sannan ta ajiye wayar tana nannade zanen ta mayar inda ta fito dasu kafin ta koma kan gadon tana addu'ar Allah yasa kar Hamza yaki yi mata magana, ko da kalma dayace ya fada mata zataji dadi.
*
Da sallama ya shiga gida, Anna na zaune ta nade kafafuwanta akan kujera, ta amsa mishi, amman ko inda yake bata kalla ba, murmushi yayi, yasan bata kaunar yanda yake kwana a wani waje ba gida ba, duk da Appa ya goya mishi baya da fadin
'Namiji ne shi, kuma ya kai munzalin da zai fita ya nema har wata kasar ma'
Abin baima Anna dadi ba kwata-kwata. Tafi son yaje ya dawo gida ya kwana. Wani lokacin sai ta kira shi ta zage shi tukunna yake dawowa gida.
"Ann"
Hamza ya furta yana zagayawa ya zauna gefenta. Hararshi tayi, tana saka shi yin dariya
"Haba mana Ann... Aikine fa ya rikeni"
Ya fadi da harshen Hausa, duk da yasan Ann din ba zatayi mishi Hausa ba, kwata-kwata bata musu Hausa, asalin yaren kasarta take musu, larabci ne gurbatacce, duk da shi Hamza yanajin larabcin na kwarai, yana kuma yima kannen shi cikin kokarin ganin nasu ya gyaru kamar na shi. Kishin abinda Anna din takeyi yasa ta karfi da yaji Appa ma ya daina musu hausa yake yara musu fulatanci, sai suka taso suna jin yarikan duka biyu, ita kuma Anna a tsakaninta da Appa suna fahimtar kome zasu fadama juna da yarukan su, amman kowa bayayin na kowa.
"Hmm, ka kyauta dai, in kasa kafa ka fita daga gidan nan sai an ganka".
Dariyar ya sakeyi dan bayason maganar tayi nisa
"Ina Auta? Bakowa gidan? Appa fa?"
Kai ta jinjina mishi
"Auta na makaranta, su Abid sun dawo sun kara fita"
Sake gyara zaman shi Hamza yayi
"Me kika dafa? Yunwa nake ji Allah"
Mikewa Anna tayi batare da tace mishi komai ba, ta shiga kitchen din tana zubo mishi dambun shinkafa da yaji kayan hadi ta dawo ta kawo mishi
"Shisa nake son ki Anna"
Hamza ya fadi yana karbar plate din daga hannunta, hira suke kadan-kadan harya gama cin abincin. Da kanshi ya kai plate din kitchen ya fito yana wucewa dakin shi, samun shi yayi a gyare tsaf, ya kuma san aikin Auta ne, bayan ya sai musu gidan da suke ciki, yaso ya daukar musu mai aiki, saboda babu kalar wahalar da su Anna basu sha ba kafin rayuwa ta kawosu inda suke yanzun, idan dubu daya yake da ita, dari takwas daga cikinta a kansu take karewa, yana kokarin kyautata musu da dukkan wani abu daya mallaka. Ba wani dangi gare su ba, garama Appa akanta, sune komai nata, da wahala ta saka mishi doka ya tsallake.
Ita kanta tana alfahari da Hamza, tun yana karami kalar kwakwalwar da yake da ita yasa takeji a jikinta dan nata zai iya zama wani, yanzun kuma gashi zatonta ya tabbata. Shisa take da buri akan Hamza, bakowacce kalar mata bace zata bari ya aura, sai yar manyan mutane da suka san mutunci, wadda ba zata shiga tsakaninta da danta ba, dan yanzun rayuwa ta canza, mutane babu Allah a ransu. Sai ka samu iyaye da yaran su, kayi kokarin rabasu dashi, ta karfi da yaji ka fara adawa da kyautatawar da yake musu, saboda rashin tsoron Allah.
Shiga yayi yana karasawa kan gadon shi ya kwanta, tun jiya yake tunanin Hindu batare da wani dalili ba, kawai ta samu waje a cikin kanshi ta manne, kaf duk wani hoto da ta saka sai da ya duba, da yanayin yanda take magana da mutane daya bata mishi rai haka kawai. Dan har yau da safe sai da ya sake dubawa yaga tana hirar film da wani kato, shisa mata suke kamar hula a wajen shi, sai ya zaba ya darje, in ya dora na wani lokaci ya cire ya ajiye, yawancin duk matan daya taba mu'amala dasu, su suke kawo kan su wajen shi, da bakin shi bai taba neman mace ba, baima taba nuna ta mishi ba ko da ta mishi din.
Duka halin su daya, idan ba kyawun shi suka biyo ba, to kudin da sukaga yana da shi ne, garama Hindu yaga ita maganar Architecture tayi. Shisa shima baya kasa a gwiwa wajen amfani da wannan damar da suka bashi, in dai zasu mori juna to shikenan, daya gama yayi gaba abin shi, da wahalar gaske