Showing 87001 words to 90000 words out of 110313 words

Chapter 30 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

shi, yaune karo na farko da take jin dana sani na tasowa daga dan yatsar kafarta yana tattarowa daga dukkan gabbanta kafin ya samu wajen zama a kirjinta


"Kaine babban marar hankali wallahi, da kana da hankali ba zaka tsareni kana fadamun wannan maganganun akan wata ballagaza ba, kaine babban mahaukaci Hamza"


Da mamaki yake kallonta, a tsayin rayuwar shi banda AbdulHafiz babu wanda ya taba kallon shi ya kira shi da marar hankali cikin raini haka


"Ni kike kira mahaukaci?"


Ya tambaya, kai ta daga mishi tana saka hannuwa ta goge fuskarta da wasu hawayen bakin cikin suka sake zubowa


"Na kiraka mahaukaci, wallahi yaune na fara tir da mugun halin ka Hamza, na dauka zaka canza, na dauka zan iya canza ka, meye a jikin Mansy da ni bani da shi? Me take maka da ni ban iya ba?"


Tayi mishi tambayar da ta dade tana yiwa kanta, yau ta bari ta fito fili saboda da gaske a tsorace take, tsoro bana wasa ba da halin Hamzan, a karo na farko tanajin kamar bata isa ta canza shi ba, kamar shi din bayason canzawa, in kuma bayason canzawa ita bata isa ta canza shi ba


"Ka fadamun abinda take dashi da bani da shi, ka fadamun me kake nema a jikin ballagazar nan!"


Juyawa yayi da nufin fita yabar mata dakin, saboda sosai kalamanta suke kara harzuqa shi, musamman da yakejin tana gab da fada mishi tayi dana sanin auren shi, idan shi bai gaya mata yayi nata ba, ba zai jira ta fara fada mishi ba


"Ina zaka je? Ka amsa ni inji, ka fadamun abinda yake jikin karuwar taka da bani da shi"


Juyowa yayi, muryar shi can kasan makoshi yace


"Idan ba zaki iya karanta chats dina kiyi kukan ki ke kadai ba, karki sake shigar mun. Karki sake mun makamancin abinda kikai mun yau, wallahi zan baki mamaki, baki sanni ba har yanzun"


Sosai take kallon shi tana sake sa bayan hannunta ta goge fuskarta


"Wallahi idan yanzun na sake hawa saina zagi uban uwar Mansy, kana jina, saina zageta, akanta ne kake fadin zaka bani mamaki. Allah ya baka iko....na zageta, Hamza na zageta ka..."


Bata karasa ba saboda marin daya dauketa da shi, wata irin walkiya na giftawa ta cikin idanuwanta, da gaske ne, littafi bai mata karya wajen rubuta kalar marin nan ba, ta runtsa idanuwanta tana bude su yafi sau hudu dan ta tabbatar da kwayar idonta bata fado ba. Kafin ta dafe kuncin, ta nemi hawaye ma ta rasa dan azaba


"Na fada miki zan baki mamaki kinqi yarda ko?"


Ya furta da wata irin murya dashi kanshi ta sauka kunnuwan shi da wani yanayi, jikin shi har bari yake saboda bacin rai, ya dauka Auta ce mace daya a rayuwar shi da zai taba dagama hannu. Saboda bai hango Hindu zata tunzura shi haka ba, zata saka shi jin son ya jibgeta har saiya daina jin nauyin da kanshi yayi


"Mar... Mari, ni ka mara? Akan Mansy ka mareni?"


Tsaki yaja mai sauti, yana wucewa hadi da jan kofar da karfi, kafafuwanta da taji suna rawa suka sakata zama, amman jikinta bari yake, dole ta kwanta, tanajin hawayen da suke bin gefen fuskarta, ga kirjinta da yayi nauyi kamar zai bude, mutanen da suka taba marinta basu da yawa a rayuwarta, ta kuma manta ranar da hakan ta faru. Mijin da take karkashin inuwar aure da shi, ko a mugun mafarki bata taba hango zai daga mata hannu ba, ko da hakan ta faru ba'a kan karuwar shi ba. Ba akan ballagazar da ko kira ta 'ya mace ba zata nuna mata ba, ballantana kuma daraja.


Ta sha jin labarai na cin mutunci irin na da namiji, amman nata ne mafi muni da taci karo da shi a tsayin rayuwarta, yau ita Hindu, ita Hamza ya daga hannun shi ya dauke da mari saboda karuwa...!


***


"Ban gane yace zai saka ranar da za'a kwashi kaya ba, sai ku ka taho kukuma?"


Baba yake fadi ranshi a matukar bace yana kallon Muhsin da Huzaifa


"Baba bana so in biye mishine ni, saboda kar ayi abinda za'aji kunya ko da sauran zama"


Huzaifa ya fadi a tausashe


"Wanne sauran zama? Shi da wanene zasuyi sauran zaman?"


Shiru su Huzaifa sukayi, cikinsu babu wanda baisan halin Baba ba idan ranshi ya baci


"Ya kore muku 'yar uwa cikin dare da tsohon ciki har kuyi tunanin akwai sauran zama a tsakanin su. Halan bakwa kishin ta ne?"


Kai Huzaifa ya girgiza, yana shirin magana Muhsin yadan zungure shi alamar yayi shiru, tsaki Baba yaja


"Ku koma ku kwasomun kayan yarinya dan banason su kara kwana a gidan wannan marar mutuncin"


Muhsin ne ya fara mikewa yana ma Huzaifa ido, shima ya mike suka fice daga falon


"Kasan halin Baba babu abinda zai saurara yanda ran shi ya baci, kuma Hindu aka taba, ni wajen aiki zan wuce, zuwa anjima watakila ya huce yanda zai iya fahimtar mu"


Kai Huzaifa ya jinjina


"Allah dai ya rufa asiri. Ni naso inga Hindun ma wallahi"


Dan murmushi Muhsin yayi


"Ka rufawa kanka asiri ka wuce, anjima ka dawo kaganta. Yanzun wallahi Baba kaniyar mu zaici"


Shi Huzaifa ma sam ya kasa yin ko da murmushin ne saboda takaici. Shi kan shi idan za'abi shawarar shi za'a hakura da maganar Hindu ta koma gidan Hamzan nan. Tare da Muhsin din suka fice daga gidan, da shawarar duk idan kowa ya dawo daga neman halal dinshi zasu sake dawowa suyi ma Baba magana ko zai fahimci abinda suke son ya fahimta din.


Cikin gidan kuwa, Anty najin duk abinda yake faruwa, idan ta gwada yiwa Baba magana ita kanta ranta ne zai kara baci fiye da yanda ya baci yanzun. Shisa ta nufi dakin Asma tana samun Hindu a kwance ta zubawa bango idanuwa, sai taji tausayin ta ya cika zuciyarta


"Hindu..."


Ta kira da wani irin yanayi a muryarta, tana saka Hindun tashi dakyar ta jingina bayanta da gadon, karasawa Anty tayi tana shiga cikin dakin sosai. Ta zauna gefen gadon


"Hindu ke kadai kikasan meya hadaki da mijin ki, kamar yanda ke kadai zaki taushi zuciyar Babanku yayi hakuri abi komai a hankali..."


Tunda Anty ta fara magana taji idanuwanta sun ciko da hawaye


"Anty ki kyale shi kawai, ni ba zan taba komawa gidan shi ba, wallahi nagaji, tunda na fito na fito kenan da yardar Allah"


Ta karasa maganar tanajin wani zogi da ba sabo bane a zuciyarta. Karfin tahowa gidane bata da shi daman tun watanni biyun da suka wuce, da tuni ta kamo hanya ta gudo daga gidan auren daya zame mata qangin da bata tana hangowa ba, daga auren mijin da kowa zau kira da kyakkyawa amman a idanuwanta sai da ya juye ya koma kamar dodo. Ba auren Hamza kawai take son gujewa ba, gabaki daya kalmar aurene bata son ji


"Hindatu..."


Anty ta kira da wani irin yanayi a muryarta, kai Hindu take girgiza mata, tana wani irin gunjin kuka me sauti


"Anty karkice inyi hakuri, ya rigada ya sakeni, komawa ba zabi bane ko da ina so..."


Hindu ta karashe, ballantana tunda ta shigo gidan takejin tana shakar wata irin iska mai sanyi da ta kwana biyu bata shaqi irinta ba. Ya saukake musu auren daya zame musu karfen kafa. Da kan shi ya sauke aurenta daya kira da kaddara


"Kaddarar auren ki ce kaddara ta farko da nayi dana sanin ta Hindu a duk kaddarorin da suke cikin rayuwata"


Ko kadan baya dana sanin kaddarar bin mata, kaddarar shaye-shaye sai ita, sai aurenta. Hamza ya gama cire mata duk wani kyale-kyale na aure da take tunani, taso MIJIN NOVEL, a sujjadarta ta roki MIJIN NOVEL, sai dai bata roka da kalar halayyar shi ba, har a zuciyarta idan ta hasaso, kudin, kyawun da soyayyar kawai take gani. Ta dauka ita kadai ta isa ta rike auren su, bata dauka aure ya wuce duk wannan ba. Hamza ya bude idanuwan ta, ya wanke tunaninta tas, ya dasa mata neman asalin dalilin da yasa aka saka aure a cikin jerin ibadu


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"


Anty ta fadi, wani irin daci na zauna mata a zuciya, kalmar saki abuce mai muni a duniyar ma'aurata komin karfin dalilin yin hakan kuwa. Ko labarin saki taji sai zuciyarta ta tsinke, yanzun da labarin ya fito daga bangaren ta, daya faru akan 'yarta ji take zuciyarta ta matse a cikin kirjinta tana wani irin ciwo


"Allah Kai Kadai Kasan me Ka boye a cikin wannan lamarin. Allah Ka bamu juriyar cinye dukkan jarabtar da ka tsara mana"


Anty take fadi a cikin ranta, kafin ta dora da


"Alhamdulillah ala kulli halin"


Tana cigaba da maimatawa, hannu Hindu tasa tana share hawayenta


"Ya sakeni Anty..."


Ta sake fadi, kalaman na zauna mata, ba kukan rabuwa da Hamza takeyi ba, kukan tarin abubuwan da ta hadiya a karkashin auren shi da tunanin zata iya gujema kawowa inda take yanzun. Kamota Anty tayi, a karo na farko da hakan ya faru, gyara zamanta tayi tana kwanciya ta dora kanta a cinyar Antyn, kuka take kamar zuciyarta zata fito, kuka take yau da take samun lallashin da ta dade bata samu kalar shi ba, kuka tayi har baccin wahala yai gaba da ita...!


*


*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*


Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank


Whatsapp Number
08074545149
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 27


Ran shi in yayi dubu a bace yake, shisa ko sallama baiyi ba ya shiga gidan Fodio. Shi ya hadu da mutumin da zaiwa zane a Office yau, suna karasa magana kan shi tsaye nan yayo. Shi kan shi yaga kokarin da yayi har yai magana da mutumin batare da an samu wata matsala ba.


"Ina ta kiran ka baka daga ba"


Arafat da yake tsaye ya furta, kallon shi Hamza yayi yana daga girar shi batare da yace komai ba, tunda baisan neman me Arafat din yake mishi ba. In dan client din sune, ya rigada ya gama magana da shi


"Fodio ne daman..."


Arafat din ya fadi muryar shi na rawa, hakan yasa Hamza cewa


"Me ya faru? Me ya sami Fodio din?"


Kai Arafat ya girgiza


"Nima ban sani ba, tun jiya wajen karfe biyu na dare ya kirani naje na dauko shi, ko motar shi bansan ina ya kai ba, ya kulle kan shi a daki, duk yau fa bai fito ba"


Da mamaki a fuskar Hamza yake kallon Arafat din, baice komai ba ya nufi hanyar dakin Fodio din, Arafat na bin bayan shi. Kwankwasawa ya fara yi


"Fodio..."


Ya kira yana cigaba da dukan kofar, dai-dai lokacin da AbdulHafiz ya karaso hadi dayin sallama yana dorawa da


"Yanzun nake ganin text din ka Arafat, me yake faruwa ne? Me ya sami Fodio din?"


Kafin Arafat ya amsa, Hamza ya riga shi da fadin


"Da mun san me ya same shi ba zaka ganmu anan tsaye ba"


Sosai AbdulHafiz din yake kallon Hamza, yayi watanni yana ganin yanayin da yake shimfide a cikin idanuwan shi yanzun, abu kadan yaje bata mishi rai, duk da ba hakuri gare shi ba tun da can, amman na yanzun ya wuce misali, yasan Hamza, ya san shi kamar yunwar cikin shi, yau neman taimako yakeyi, yana kokarin boye damuwar shi a bayan bacin rai


"Ko me yake damun ka ya jira"


AbdulHafiz ya furta, yana karasawa ya kwankwasa dakin


"Fodio bamu da duk rana, ka bude kofar nan, nasan kana ciki, kana jinmu kuma, idan waje kake so duk mu baka, ka bude ka fada mana sai mu tafi..."


Shirun dai ne amsar da suka samu


"Idan na sake kwankwasawa zan dauka wani abu ya sameka, zan karya kofar in shigo Fodio..."


Wani shirun ya sake ziyartar wajen, kafin suji alamar motsi, ana murza mukulli, tukunna Fodio ya bude dakin, kallo daya zakayi mishi kasan baya tare da nutsuwa ko kadan, ga idanuwan shi sun canza launi, sun rine sunyi wani irin ja


"Me yasa ba zaku kyaleni ba?"


Arafat ne ya fara wucewa cikin dakin, kafin Hamza yabi bayan shi, runtsa idanuwan shi Fodio yayi yana wani irin sauke numfashi, takawa yayi da nufin fita daga dakin, AbdulHafiz da yake bakin kofar ya hankada shi yana mayar da shi ciki, shima ya shiga, sannan ya tura kofar yana jingina bayan shi a jiki


"What the fuck? Meye haka wai? Naji... Ku fita ina bukatar ku bani waje, kun ganni ai, babu abinda ya sameni, bana son magana ne da kowa"


Fodio ya fadi muryar shi a dakushe


"Baka san magana da kowa, tunda ka bude kofar kai kadai kake surutu Fodio"


Arafat daya sami waje gefen gadon dakin ya zauna ya fadi, AbdulHafiz na dan daga kafadun shi cikin yarda da maganar Atafat din yana kallon Fodio, kafin ya zame takalman kafar shi yana shiga cikin dakin sosai shima. Kallon su Fodio yakeyi, sosai yake kallon su, Hamza na zaune ya saka hannuwan shi ya dafe fuskar shi. Arafat ya hau saman gadon sosai yana jingina bayan shi da bango hadi da mike kafafuwannshi, sai AbdulHafiz da yake zaune shima, ya dora kafar shi daya akan dayar.


Ya san su, ba tun yanzun ba, kamar yanda yace bayason magana da su, ba zasu ce mishi komai ba, in zasu wuni zaune a dakin, ko a tsakanin su ba zasuyi hira ba, amman ba zasu taba barin shi ya zauna shi kadai ba a yanayin da suka gan shi. Tsikar jikin shi yaji ta tashi, kafin tsoron da ganin su yasa ya tafi ya dawo mishi yana cika mishi zuciya taf, idanuwan shi ya runtse yana jin shi a hotel din, yana jin kamar yana tsakiyar mata suna cashewa a hall din da aka kama dan gudanar da bikin cikar shekara na abokin shi da karatu ya hada su, shi kan shi kuma ya shigo Kaduna ne musamman saboda taron bikin.


Zai iya cewa, kafin su Hamza, Ashir ne abokin da yake da shi, kuma abokin shi tilo da suke waya, suka san gidajen juna a garin Kano. Kuma har su Hamza sun san Ashir din, dan in ya shigo Kaduna suna haduwa duk a gaggaisa, har fita sukanyi tare. Idan yana hasaso wani lokaci da zai tuba ya daina rayuwar da yakeyi, yakan yi zaton kowanne mutum na duniya mai irin halayen shi ma yana da wannan tunanin, amman banda Ashir. Ko maganar akayi mishi tunda lalacewar da gidansu sukaga yayi ne yasa su yi mishi aure ko zai kintsu, maganar shi daya ce


"Mai rabon shiryuwa fa zai shiryu, kana zaune in kana da rabo, ba sai ka wani wahalar da kanka ba, ku barni inyi shagalina"


Ashir na rayuwa kamar an mishi alkawarin shekaru masu tsayi, yana rayuwa kamar yana da tabbacin me goben shi zata haifar. Haka daren jiya ya kasance musu. Ko Fodio bai fita daga gida ba sai karfe sha daya da rabi na dare, tunda ance musu shagalin har asuba zai kai, kuma haka suka cigaba da rallewa bayan an yanka cake, misalin karfe daya da rabi na dare, da shi da Ashir sun saka wata yarinya a tsakiya suna tiqa rawa ta rashin mutunci, Ashir din na mishi alamu da ya ganar mishi yanayin fuskar budurwar shi ko tana kishi.


Dariya Fodio yayi yana girgiza kai, lokacin da yayi dai-dai da canjin daya bayyana a fuskar Ashir din yana dakatawa da rawar da yake hadi da dan dakuna fuska yana dafe kirjin shi


"Ashir?"


Fodio ya kira, amman sautin kidan da yake tashi bai bar muryar shi ta karasa fuskar Ashir din ba, kafin Fodio yai wani yunkuri har Ashir din ya yanke jiki ya fadi. Yanayin da yasa hankulan mutane da yawa komawa kan shi. Kafin wani lokaci gabaki daya hall din ya hargitse. Fodio ba zaice ga asalin abinda ya faru ba saboda tashin hankalin, abinda zai iya tunawa shine kalaman wani da baisan wanene ba yana fadin


"Wannan ai ya rasu fa"


Kalaman da suka gigita gabaki daya rayuwar shi, suka jefashi cikin wani irin firgici marar misaltuwa, wanda bashi kadai ba, dan da yawa mutane har an fara gudu ana fita daga hall din, cikin wannan tururuwar fitar ya tsinci kanshi da binsu, ya manta sam da mota yazo wajen, a haka ya samu ya fita daga hotel din zuwa titi ya fara tafiya, sai da ya karasa gidan man farko da yake hanyar tukunna ya iya tsayawa yana dan tsugunnawa cikin son neman numfashin shi da yake kokarin kwacewa.


Jikin shi babu inda baya rawa, ko da tunanin ya ciro wayar shi ya kira kowa ya fara samu yazo mishi, sau hudu tana subucewa ta fadi daga hannun na shi. Sai da ya tsugunna tukunna ya samu ya kira Arafat, muryar shi ma bata fita sosai, kalamai yake kokarin hadawa kamar mai koyon magana


"In zaka iya Fodio ka turomun location din da kake"


Arafat din ya fadi, hakan ya samu yayi, tukunna yazo ya dauke shi. Basuyi wata magana ba har suka karasa gida, kan shi tsaye daki ya shiga yana mayarwa ya rufe. Kayan jikin shi ya fara cirewa, yana wanka ya tsarkake jikin shi, ya fito ya nemi wasu kayan ya saka, zuwa lokacin har zazzabi ya rufe shi. Mutuwar bata kara gigita shi ba saida ya kwanta, tukunna wani irin tsoro ya shige shi


"Mutuwa na binku fiye da yanda tunanin ku yake baku wallahi, ba jiran ku zatayi ba, kuna tare da ita a duk takun da zakuyi, a duk inda zaku shiga tana jiran umarni, ku dinga shiga inda ba zakuyi dana sani idan mutuwa ta riske ku ba"


Kalaman AbdulHafiz da yake fada musu a duk rana suka dawo mishi


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"


Ya furta muryar shi na karyewa, da gaske AbdulHafiz yakeyi, mutuwa bata jiran kowa. Koya ya rufe idanuwan shi Ashir yake gani, yana kasa gasgata cewar a gaban idanuwan shi, a cikin hotel, da kida yana tashi mutuwa ta dirkar mishi. Ba abinda Ashir zai cewa Ubangiji Fodio yake tunani ba, shi abinda zai fada, baisan lokacin daya dirko daga kan gadon ba yana zama dirshen ya janyo kafafuwan shi, ba zai iya tuna ranar karshe da hawayen shi suka zuba ba.


Duk kuwa bakar wahalar da yasha a gidan su, tunda ya fara gane kwayoyi ma ko dukan shi sukayi da ya jefa hudu ko biyar komai yake bace mishi, amman yau kuka yake kamar karamin yaro, kuka yake yana rasa kalaman da zai amfani da su wajen neman yafiyar Ubangiji, balle kuma ta inda zai fara dan ganin ya kankare tarin zunuban da suke kan shi. Gani yake kamar ba zai tashi daga inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login